Free chapter · Read without an account

46

by Azizat Hamza · Mutum Mugu Ne

*MUTUM.....Mugu ne*


                     46


Ana sallamar su a Asibiti direct gida Mommy ta wuce da ita duk da kuwa Zaytunah ta ce ita gidanta za ta je.

Duk faɗan da mommy ke mata ba wanda ya ke shiga kunnenta, abu biyu ta saka a ranta 'My One ya dake ta, Sady ta guje ta'

Tana zaune tana faman jiran Daddy saboda Mommy ta hanata tafiya sai Daddyn ta ya dawo tukunna kiran Sady ya shigo wayarta.

"Sady shine kika barni cikin tashin hankali, me ke faruwa ne wai?"

"Babe, dole na nemi wajen ɓuya aikin mu ya ɓaci, yanzu na kira ki ne domin duk abin da Sajid zai gaya mi ki akai na kar ki yarda da shi. Dole zai gaya miki ƙarya dan ya raba tsakaninmu amma kar ki yadda kin ji"

"Sady kin san mi Sajid ya min akan yarinyar nan kuwa?"

Sady ta ƙatse ta da cewa " we'll talk later Zaytunah ina hanya ne" ta kashe wayar

"Hello Sady....Sady...Babe" shiru ba ta amsa ba ta sa ke kiran numbar ta ji a kashe.

Bayan sallar Isha Daddy ya shigo gidan tare da Sajid. Mommy ta kira Zaytunah falon Daddy, tana zuwa da ta hango shi ta fashe da kuka ta faɗa jikinshi, abin ma dariya ya ba wa iyayenta. Daddy ne ya daka mata tsawa sannan ta koma gefe tana matse hawaye.

Tambayar da Daddy yai mata ya sa ta ɗago ido ta kalle shi "Zaytunah ke kika sa aka sace Naziha?"

Ta yi shiru

Ya sake wata tambayar "akan me kika yi haka?"

"Daddy na ɗauka meeting ɗin nan akan My Sajid ne, dukana fa ya yi, ya shi ya kamata a yiwa faɗa ba ni ba"

"Zaytunah!" Mommy ta daka mata tsawa

Shi dai Sajid kallon ta kawai ya ke bai ce komai ba.

"Mommy gaskiya ne ai, ni aka daka kuma ni za a ɗaurawa laifi, ni ina ga Naziha asirin Yarabawa ta yiwa my one, gara a nema masa magani"

"Subnallahi, Zaytunah a gaba na kike yiwa mijin ki magana irin haka" Daddy ya faɗa ransa a ɓace

" Daddy dan Allah kada ku ɗaga hankalinku, dama na zo tambayar Zaytunah abu ɗaya ne a gaban ku" Sajid ya faɗa yana kallon Zaytunah.

"Zaytunah ban hana ki mu'amala da Sadiya ba?"

Ta fara wiki-wiki da ido

"Answer me!" Ya daka mata tsawa

Maimaikon ta ba shi amsa sai ta fara kame-kame

"Daddy, Allah haka kawai ya tsani Sadiya ba abinda ta mishi, and Sady is a good person"

"Ya hana ki ko bai hana ki ba?" Daddy ya tambayeta

"Ehm...ya hana ni amma...."

"Abinda na ke son ji kenan Zaytunah, nothing more" ya miƙe tsaye ya ce " ka gafarce ni Daddy, amma bana buƙatan Zaytunah a gidana har sai ta fahimci banbancin da ke tsakanin miji da kuma ƙawa. Na barku lafiya"

"Wallahi ba ka isa ba, idan ma asiri na cinka ni garau na ke and I'm going back to my house" Zaytunah ta faɗa tana miƙewa itama.

"Zaytunah kin san da anyi nasaran raping Naziha kin bar gida na kenan, so I'm giving you a chance ki nitsu ki san muhimmancin aurenki. Ke wace irin wawuya ce da ba ki ganin Sadiya kashe miki aure ta ke so ta yi, for her own selfish interest. Da kin san manufar ta gare ki, da kin san abin da ta yi a bayan idonki I'm very sure idan ba ki kashe ta ba to kotu ce za ta rabaku"

"Ƙarya ne Sajid, sharri ka ke mata"

Daddy ya wanke ta da mari ya hau ta da faɗa. Shi kam ko ƙala bai sake cewa ba ya fice daga falon ransa a ɓace.

Yana komawa gida 'yanbiyu da Nurain ya samu a falo suna kallo sai Aamir da tuni ya yi bacci akan kujera, ya ɗau Aamir ya haura da shi ɗaki ya sa masa kayan bacci ya gyara masa kwanciyarsa. Ya duba ɗakin Azra ba ta nan ya ɗau waya ya kira Yassar ya tambaye shi ina Azra, ya ce mishi tana ɗakin Naziha ya kashe waya ya shige na shi ɗakin. Kai tsaye kan gado ya hau ya kwanta yana tunanin abubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau, abu biyu sun bayyana masa, na farko soyayyar Ziha da ya ke ɓoyewa tuntuni, na biyu kuma zaman haƙuri da ya ke da Zaytunah ya kai maƙura, dole ya ɗau tsatsasauran mataki akanta. Sai yanzu ya gane zamansa da Zaytunah ita kaɗai matsala ce gareshi, he needs another woman da zata bashi kwanciyar hankali. Ya jawo wayarsa ya kira Nadia, a taƙaice ya mata bayanin abinda ya faru yau bayan wayarsu na farko. Of course ya ɓoye batun kissing Ziha da ya yi.

Nadia ihu ta dinga yi a waya tana dariya " finally, finally za a yiwa Almighty Zaytunah kishiya, kai Alhamdulillahi Allah. Ya Saj ba ka da matsalan kayan aure daga yanzu zan fara haɗa maka komai"

Dariya ya yi sannan ya ce " haɗa kayan auren yarinyar da ba ta amince da soyayyata ba, sannan iyayenta ba su ba ni ita ba, that's a bit fast Auta"

" Ya Saj ƙarya ne ta ce bata son ka cause na gani a idanunta. Iyayenta kuma in dai mutane na gari ne sun baka ita an gama"

"Nadia the seer. Stop fooling me, kin san dai Yoruba ba su bawa Hausa Fulani 'ya'yansu"

"Kai Bafulatanin usul ne, ga jinin mutanen Ethiopia da ke yawo a jikinka. They have no choice Ya Saj. Handsome, Educated, Rich, Smart, kai Ya Saj Masha Allahu ka haɗu ta ko ina"

"Let's just keep it a secret for now, har sai Iyayenta sun amince"

" kar ka damu Yayana, amma 100% sun amince ma har an gama. Kuma dan Allah ko Alhaji ya kira ka maganan Zaytunah kar ka yadda ka amince ta dawo maka gida da gigin hauka, ka bari har sai maganan ku da Naziha ya tabbata sai muga ko mutuwa za ta yi idan ka auri Ziha"

Shi dai murmushi kawai ya mata.

Washegari tun da suka bar gidan ko gaisuwa bai haɗa su ba hasalima ya lura kunyar haɗa ido ta ke da shi. A cikin jirgi ma duk da sun zauna kusa amma babu mai magana cikinsu, ita kam ma Ziha littafi ta fidda tana karantawa. A zahiri karatu ta ke yi amma kuma cikin zuciyarta cike ya ke da damuwa.

***

.....KADUNA....

Yau kwana biyu kenan da Layla ke fama da naƙuda amma haihuwa shiru.

"Alhaji mu kai Layla Asibiti, ba za ta iya haihuwa da kanta ba ga shi tana jin jiki"

" wai bance ba na son maganar Asibiti ba, ke ma macece, ki taimaka mata har ta haihu lafiya, amma ba za a kaita asibiti ba"

"Dan Allah ka kira Likita, Alhaji kar mu rasa Layla"

"Mom...Mom mara ta" Layla ta faɗa tana nishi. Mom ta juya bakin ƙofa ta hangi Layla tsaye tana dafe da tuƙeƙen cikin ta. Da sauri ta ƙarasa wajen tana faɗin "Alhaji ina jin fa haihuwa ne, dan Allah mu kai ta asibiti"

"Ki yi ƙoƙarin taimaka mata kawai Fatima, amma a gida za ta haihu"

Bai kai minti shabiyu ba Layla ta haifo jaririn ta yana ta tsala kuka.

" kawo shi" Alhaji Kadi ya faɗa lokacin da Mommy ke ƙoƙarin yanke cibiyar yaron.

Murmushi ɗauke fiskar shi ya ƙarɓi jaririn da ke ta tsala kuka ya fita da shi. Kai tsaye ɗakin tsafinsa ya wuce da shi ya shiga da baya-baya. Dama musabbabin ajiye Layla a gida kenan domin ya shayar da dodo jinin jariri ko jaririyar da ta haifa.

Alhaji Kadi ya ɗau wuƙa ya yanka Jaririn sai ya ɗaga jaririn sama, jinin jaririn na tsiyaya zuwa cikin harshen gunkinsa. Take ya ji wani razanannen ƙara da yai kama da tsawa " ta ya za ka shayar da ni jinin ɗan halal?" Aljanin da ke jikin gunkin ya faɗa cikin wani sauti mai amo, nan ta ke gunkin ya ɓace ɓat. Alhaji Kadi ya diririce yana "faɗin wannan jinin shege ne ya Zunubu, ka taimaka ka dawo, wannan jinin shege ne..."

......

Fitan Alhaji Kadi da minti uku Layla ta yi wani nishi Mommy ba ta ankara ba sai ga kan wani jinjirin na shirin fitowa. Ta tallafa mata har ya fito, wannan bai bata wahala kaman na farkon ba.

"Alhamdulillah! 'yanbiyu ne, Alhaji, Alhaji....." muryanta ya sarƙe lokacin da ta ji wani razanannen ƙara, jaririn ya tsandare da kuka lokaci guda. Ganin ƙaran ya lafa sai Mom ta kimtsa jaririn ta ba miƙa wa Layla dan ta bashi nono ya sha. Allah Sarki na farkon ko ɗimin uwarsa bai ji ba balle ya sha nononta.

"Mom ina mijina?" Tambayar da ya sa mom sandarewa kenan daga inda ta ke tattara kayan jini

"Layla...miji ... miji a ina?"

"Mom ba dai har yanzu bai dawo ba tun tafiyarsa....wash Allah na" ta sa hannu ɗaya ta dafa goshinta yayin da abubuwan da suka faru suka fara dawo mata. Mom ta katseta da cewa " Layla ki min bayani, me ke faruwa? Ki fitar da ni a duhu"

" Mom ku yi haƙuri na ɓoye muku aurenmu, na yi hakan ne saboda son da na ke mi shi. Mom mun yi auren sirri da AY a Kano. Baba Malam Musa ne ya ɗaura mana aure"

"Innalilahi wa Inna Ilaihi Raji'oun....Kai Alhamdulillah" Mom ta rasa mi ma za ta ce, ta zo ta rungume Layla da ke riƙe da jariri tana faɗin "na fi kowa farin ciki yau, ga kyautar jikoki 'yanbiyu ga shi da aure aka haife su"

" Ina ɗaya jaririn?" Layla ta tambaya dan haka kawai ta ji ƙirjin ta na bugawa da ƙarfi

"Yana wajen Daddyn ki barin ma kira shi ya zo ya ji labari mai daɗi"

Mom na shiga ɗakin Alhaji Kadi ta jiyo muryansa yana faɗin " Ya zunubu jaririn shege ne, ka dawo ka ƙarɓi jininsa" Take jikin Mom ya fara rawa,

duk da yanayin da ta tsinci kanta sai da ta ƙarasa inda ta ke jin maganar, tana saka hannu jikin bango wajen ya buɗe ta shiga.

Alhaji Kadi ta gani riƙe da jaririn Layla, idonta ya kai ga wuyan yaron da ke ɓulɓular da jini. Alhaji yana tsaye gaban wata kujera sai sunbatu ya ke.

"Al.....haji.." Mom ta faɗi a ɗakin tsafin a sume...

***

.......Mangu, JOS....

Inda ya ke zaune tare da Malam Buba Jo'o a bakin shagonsa na saida hatsi da dawa ya tashi a firgice yana kallon gefe da gefensa. Ganin yanayin inda ya ke, da kuma kayan da ke jikinsa sai ya fahimci akwai matsala.

Malam Buba Jo'o ya ce " ya dai Muhammadu, mi ya faru?"

Da mamaki ya kalli mutumin da ya kira shi da Muhammad ya ce " Baba ban gane ba, sunana Alyasa'a ba Muhammadu ba"

Malam Buba ya tashi tsaye yana faɗin "Alhamdulillahi, ka tuno sunan ka? Alhamdulillah, ai ka jima damu anan ko sunanka ba ka sani ba. Kai mutumin ina ne?" Ya tambaye shi yana son tabbatar da lallai Alyas'a ya dawo hayyacinsa

"ni mutumin Zaria ne, amma ina zaune a Kaduna, Ina da 'ya Aaliyah da kuma matata Layla"

"Alhadulillah, asiri ya karye a jikinka"

" Baba ya aka yi na zo nan?"

"Ba ri mu koma gida Alyasa'a, zan ba ka labarin komai"


*yeh! AY is alive*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.