Free chapter 路 Read without an account
Fifteen
馃實DUNIYA MAKARANTA!!馃
Arewabook
https://arewabooks.com/u/nanabmb
My novels
RABON KWADO...!!
JARABTAR MU!!
RABO!!
AND NOW
DUNIYA MAKARANTA!!
Page fifteen
Koda Ridwan ya fita kai tsaye gurin da Rafeeq yay parking yanufah shima yanata sintiri tunda yaga shigan Papa ya tabbatar akwai damuwa za a iyayin batatta, ilai kuwa yadda ya hanga Ridwan yasan babu nasara betanka masaba seda suka fara tafiya sannan Ridwan din ya soma masa magana cikin french!"
" Manma ba jinina bace niba dansu bane! Rafeeq wlh ban taba shiga tashin hankali irin wan nan bah! Meyasa rayuwa ta juya min baya? Ko a mafarke ban taba ganin kaddara irin tawaba, shin ina zan dosane yanzu? ina nawa ahalin yake? Meyasa zasu rabani da nawa iyayen gaba daya ma ji nake kamar bani bane Ridwan!!" Ya karashe maganar muryan sa na rawa kamar zeyi kuka, rafeeq sauke ajiyan zcy yay cikin muryan tausayi yace.
"gaskiya ban taba tsammanin hakaba! taya hakan zata kasance suwaye iyayen ka? wannan wani irin tashin hankali ne! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!! Ridwan meyake shirin faruwane a yanzu haka anata bincike akan kisan Jawaheer gari ya dauka kowa yana cewa kaine ka kasheta inda najee dadima babu wanda yake goyon bayan mahaifin ta saboda abinda suka aikata kisanne hukuncin ta dama, badon hakaba da tuni an kamaka!!" cikin wani irin yanayi Ridwan ya kalleshi yace. " kaima kana tunanin zan iya kashe Jawaheer da hannunah?" Rafeeq ya girgiza kansa gami da cewa. " ko kadan bana wannan tunanin kuma ban taba rayawa zcyt zaka aikata hakan ba kawai dai nasan da biyu akayi maka hakan!" cije bakinsa Ridwan yayi sannan yace Alhaji Hamraz ne ya shirya duk wannan abun shida mahaifin ta wlh Rafeeq ban taba tunanin ina rayuwa da marasa imani bah se yanzu sam basuda tausayi ina matukar tausaya wa Manma dani kaina! wan nan waca irin kaddara ce? sedai koba komai naji dadi Alhaji Hamraz dabe kasance mahaifina ba gaba daya rayuwa nakeyi a baibai Rafeeq sam bansan waye nibah! ta ina zanfara neman iyayenah? jin wannan kalmar bakuwa nakeyi agareni!"
Dafashi Rafeeq yayi yace." please calm down Ridwan wannan abun daya faru shine mafi alkhairi a garekah insha Allah tunda Alhaji Hamraz ya bayyana wa duniya kaiba dansa bane to haka ze shiyda mata suwaye iyayen ka dolen sane kuwa munsan tahanyar dazamu bullo masa!" murmushin dayafi kuka ciwo Ridwan yayi yace. "Yasoma tunanin barin kasan nan Rafeeq dole bazan taba barin hakan ta kasance ba,bazan iya rayuwa batare danasan kowaye nibah ina jin zafi a zuciya ta tun farko danake rayuwa a duhu" Dafe kansa yayi cikin matsanan cin yanayi yace." wayyo ina zan tsoma rayuwata meyasa zasuyimin haka why why!!"
Washe Gari
Tunda su Bilal suka koma gida ya rasa abinda yake masa dadi yakasa dena tunanin Jawaheer har zuwa dare,gashi nan nedai, shida Daddy suna kan hanyar komawa gida daga masalla ci Daddy yake cewa." Bilal meke damun kane tunda muka dawo bakada walwala?" shikuwa Bilal sauri yakeyi sakama kon wayar Jawaheer daya tuna tana gunsa ya dauke a cikin handbag din mummy, to gudun karyay tunanin wani abun ne se ya danyi masa yake yace. " Banajin dadin jiki nane Daddy shiyasa!" Daddyn yace." Ashsha bazaka sami zuwa ganin kayan furnitures dinda aka kawo mana na Italy ba kenan?" kara marai rai ce fuska Bilal yayi yace." meze hana mubari zuwa gobe Daddy?" " is ok Bilal kabari kaji sauki sosai se muje in ba dama se munje hospital ayi maka medical checkup har yanzu baka gama dawowa dai dai bah!" saurin girgiza kansa yayi yace." No Daddy base munje hospital bama am I just need sleep!" "Dukda haka mu karasa gida nakira Dr yazo da kansa tunda bakasan zuwa kai!" shiru Bilal ya masa don baya son yin musu da mahaifin nashi suna shiga gida be tsaya gurin kowaba yay upstairs,koda yashiga dakinshi jakanshi yazuge yasoma fito da kayan ciki dasauri haryazo na karshe ya dauke su ya dauko wayar ya duba yaga babu charge ma wayan ya kusa daukewa shiyasa ya zauna gefen bed ya tsirata a charge har yana me sauke ajiyan zcy wayan yafara dubawa ga mamakin sa se yaga gaba daya mummy ta share duka kiraye kiraye da akayi a waya wanda se a time din ya kula da babu sim ma a ciki ta cire shi shima, ay kuwa wani bakin ciki daya lullube shi cije lips dinsa yayi yana sauke ajiyan zuciya yana tunanin meyasa ne mummy tayi hakan? Meyasa bazata barshi yaje Nijer dinba, gashi komai ta goge shi a yanayi mara dadi yace." I want to know your origin, I want to know who you are but how? how? mummy kin hanani zuwa garinsu" yana daga zaune yasoma duba abubuwan cikin wayan pictures dinta na wayan ya kallah duka kuma babu wanda take da kayan azziki a hoton koda ya shiga vidios zuciyar shice tai wani irin har bawa sakamakon vidios dinta da yagani irin shaye shayen da take irin kwayoyin da takesha tanata vidio dakan ta kuma, gasunan vidion dayawa harya rasa wanda zekalla mah idon shine ya sauka kan wani vidio dayaga tayi rolling shikadai ne vidio datasa kayan mutunci koda yayi playing tana zaune idanunta suna zubar hawaye tana bayani da frence,
" Ya kai masoyi na Ridwan? kasani zan mutu da kaunar ka a zuciya ta bantaba kaunar wani namiji sama dakai ba naci burika kala kala akan ka na rayuwar dana keso muyi a matsayin ma aurata se gashi karshe ga yadda rayuwa ta ta kasance bantaba tunanin irin wannan mummunan kaddarar zata fadomin ba, ko a mafarki ban taba tsammanin zan iya kisan kaiba...... sam Bilal besan sanda wayan ta subuce daga hannun shiba sakama kon kalmar kisan da tadaki kunnen shi tsayawa makawai yayi yanabin wayan dakallo yana tunanin anya kuwa dai dai yaji duk da baya fahimtar french sosai yana tsin tsinta ba laifi, kuma tana yin mix da English da dakyar yayi karfin halin dur kusawa ya dauki wayan yakuma dawowa baya domin tabbatar da abinda yaji tafada lalai kam kisan kai ta ambata baki bude kuwa ya cigaba da kallo, "Sonka ne yarufe min ido banada tunani akanka Ridwan inada matukar kishi abinda Jamila tamaka, zuciya ta kwasheni na biyewa kawaye nah har mukai sanadiyyar ajalin ta gashi yanzu munata nadama! a tunani nah kudin mahaifinah bazasu bari doka tayi aiki akaina ba sam yanzu natsani rayuwa ta Ridwan tunda aka rabani dakai banason zama a kurkuku mutuwa nakeso,abinda yasa nayi wannan donna wanke laifin ka a gurinsu Abbah na tabbatar na mutu a yanzu mahaifi na ze dora maka laifi, nasan bazan iya rayuwa me tsayi ba duba da irin abinda nake aikata wa lafiya ta yanzu, koda Allah ze kawo min kai zan danka maka wayata a hannun ka ina Addu'ah Allah yasa a hannun ka zan mutu saboda nayi maka kallon karshe, wan nan ne burina ina fata kuma ze cika saboda nasan zaka biyoni duk inda nake, saboda haka inaso ka gwada ma mahaifi na vidio dinnan danayi ni Jawaheer iname neman gafarar ku Abbah na da umma ta, ban kasance mace ta gari bah shiyasa rayuwa ta koyar dani darasin daze bini har mutuwa, ina fata zaki sake haifa wa Abbah wata diya wacca zata debe muku kewa! Ina kuma rokon alfarma karku tsangwami Ridwan saboda yana goyon bayan gaskiya ne, nice na aikata kisan kan nina kashe Jamila kuma ba akan komai ba akan Ridwan ne masoyi nah bazan iya lamin ta wata na gaya masa kalmar so na jure bah, ina neman alfarmar kada ku tsangwame shi a rayuwa bashida laifi,abinda yadace kawai yakeyi, koda nazo nan rayuwar babu dadi kuma koyau she asirin mu ze iya tonuwa shiyasa nayanke hukunci kara na mutu kafin ciwon zuciya ya kashe ka Abbah na!!" wannan kalamin shine na karshe a vidion sam Bilal besan Sara ta shigo dakin ba yanzu koda ta kalleshi tayi mamaki yadda taga yabawa wayan hannun shi full attention bemasan tayi sallama ba tasan baya haka shiyasa tayi mamaki aikuwa tasoma sanda domin taga shin meyake gani haka ahankali take takawa izuwa gurinsa se akayi rashin sa ah wani vidio na Jawaheer ya shiga wanda take sanye da bra da pant kadai tana zaune tagama buguwa tanata zuba hauka,shikuwa Bilal hankalin shi yadauke daga kan wayar yatafi dogon tunani idanun shine kawai kan screen din wayar besan abin dake faruwa bah kawai se jiyayi anwa wayar wata irin muguwar warta a hannunshi har soyay ya tsorata ma kawai yaga Sara atsaye a kanshi tanata huci tana kallan vidion dafe kansa yayi yana sauke a jiyan zuciya ita kuwa Sara wasu zafafan hawaye ne suka soma sakkowa daga idanunta tana salati tafara cewa.
" Bilal? mezan gani haka? me kake aikata wa haka?"
Juya bayan wayan tayi taga batashi bace bama,sam Bilal be ankara ba yaga tanufi kofan fita da gudu tana kuka dayake yafita zafin nama taku uku yayi ya damkota tsam yariketa ajikin shi yace calm down honey! ba abunda kike tunani bane zomuje inyi miki bayani!"
Cikin matsanancin bacin rai ta fisge jikinta daga nashi gami da cewa." Allah ya isa Bilal ka yaudare ni nizaka mayar mara tunani mezaka gayamin bayan yau na kamaka a sirinka ya tonu yau! saboda mugun hali harwata boyayyan waya ne dakai wacca kake iskancin ka aciki! wlh Allah ya isa Bilal tsakani na dakai!" saboda zafin da kalaminta suka masa besan sanda yakai hannu ya dauketa da maribah wanda yasa ta kusa faduwa kuka tasaki sosai ya sake matso ta yace. " Ni kike jifa da irin wannan mugayen kalaman? kamar bakisan wanene niba! but fyn and good bani wayata kifitar min adaki tunkan zuciya ta debeni nakara bata miki rai!!" cikin zafin rai itama tace. " Bazan bayar ba din bakaso asirin ka yatonu koh! senakai wa su Daddy sunga abinda kake aikatawa!"
Da mamaki Bilal yake kallon ta yace." Sara dama bakida hankali!" cikin fusata tace " Barima kaga karshen haukan nawa juyawa tayi da zummar fita taji yayi wa hannun ta wata irin cafka har seda tasaki kara ata dole tasakar masa wayan, Daddy da mummy da Dr suna parlour a zaune Daddy yace " kinji yaran nan shiru Sara daga turu ta ta kirashi kuma sesu zauna ga Dr na jiranshi maryam hau kigano min su!" rufe bakinsa kenan suka jiyo kukan Sara tana sakkowa da stairs da gudu tazo tawucesu Ta nufi dakinta suduka suke hada baki gurin tambayar lpy ina sam bata saurare suba mummy kuwa tabita da sauri shikuwa Daddy kallon Dr yayi yace "ina zuwa Dr kajee" saman Bilal din yahau ya shiga bedroom din nashi yasa meshi yana zaune fuskar sa babu annuri yama rasa wani kalar tunani zeyi cikin damuwa Daddy yace " Bilal meya hadaka da Sara? kuma shin mekayi mata ta sauka tana kuka dakyar bilal ya iya cewa "Daddy ita taso ai ban taba sanin Sara batada tunani bah seyau! harni zata kallah tazaga! matar da nake shirin aure itace zata rainani haka gaskiya da sake Daddy ai bansan batada da kunyaba seyau!" " Ah uzubillahi minash shedanin rajim!! Hasbinanlah wa ni imal wakil! sharrin shedan ne ya akayi kabari yaci galaba akan ka yau? haba Bilal da hankalin ka zaka biyewa mace! hankalin ta danaka fah badaya bah meyasa zaka yarda har kusami sabani bayan kuna rayuwar ku cikin kwanciyar hankali! matafa dole se ana hakuri dasu kuma nasan hakkan nan Sara bazata yi maka rashin kunya batare da dalili bah lapiya kalau naturo ta ta kiramin kai saboda na kiraka baka dagaba a waya saboda haka mekayi mata?" "Daddy kawai shigowa tayi ina duba abu awaya kawai saboda taga mace ne zata rufe idonta kamar batasan wanene nibah! c'mon saboda taga mace zata fara zagina sabida rashin tunani! ta tambaye nima taji dalili baza taiba zata fara zagina a tunaninah tafi kowa sanin halina baruwa na da mata ammah 1 time zata yimin haka! ta matukar bata min rai Daddy kammani zata kalla takira dan iska mijin da zata aura!!" dafashi Daddy yayi yace " tsaya Bilal! kasan halin kishin mata dai yadda suke seka ce bakasan yadda mummy kah take minba dole hakuri zakayi ka danne kishi yarufe mata ido yanzu komai zata iya gaya maka" cikin fushi Bilal yace "Ai kuwa wlh dasena tattaka yarinya" a yadda yayi maganar yaso bawa Daddy dariya kada kansa yayi yace lallai har yanzu da sauranka Bilal wai me tagani awayan daya haddasa wannan bala in....鉁嶏笍