Free chapter · Read without an account

1- It's 2018

by Azizat Hamza · TSOHUWAR SOYAYYA


1

️

It's 2018

Wajen liyafar ya cika da mutane musamman ma'aikatan BBC Hausa har da ma na sashen BBC English. Familyn Bulama suna nan a wajen 'ya'ya da jikoki. Musamman wanda dama su ke London a wannan lokaci ko kusa da London ɗin. Wanda su ke nesa ma sun zo, saboda Mom Aaliyah ta kowa ce.

Tana zaune aka kira sunanta *Aaliyah Badamasi Bulama* ta taso tana murmushi wanda ya ke ƙara sanyawa fiskarta alhini. Ta je wajen podium ta ƙarɓi award da aka bata sannan ta amshi mic ta yi jawabin godiya da Hausa sannan cikin turancinta na ƙwarewa ta ɗaga award ɗin ta ce "This is for my late husband Ahmad Wamako, may his soul rest in Jannah, Amin"

Hawaye ne suka ciko a idanunta ta yi saurin sa hannu ta goge tareda barin wajen, tana saukowa aka sa tafi.

Da sauri Zaid ya nufo ta ya rungumeta yayinda sauran 'yanuwa suka fara zuwa ɗaya bayan ɗaya suna ma ta congratulations...

Wata budurwace da ba za ta fi shekara ashirin ba ta ƙaraso wajen da Aaliyah ke magana da wasu turawa.

"Excuse me, can I take a picture with you ma'am?"

Aaliyah ta yi murmushi ta ce "sure" selfie ta mu su kusan guda uku sannan ta ce "thank you"

Kai tsaye wajen da Zaid ke zaune yana magana da wasu 'yanuwansa ta je. Neman izinin magana ta yi da Zaid wanda ko kallo ba ta ishe shi ba.

A hankali ta ce "please Zaid ka taimaka ka bani minti ɗaya naka, abinda zan gaya ma ka is very important"

"Zaid ka saurareta ma na" in ji Hafiz wanda yarinyar ta gama burge shi.

Ko ɗagowa bai yi ba balle ya amsa ya cigaba da danna waya.

Ta fito da wayarta daga cikin purse ta danna kira. Sai ga wayar Zaid ta na ringing, ganin baƙuwar number ya sa shi yin tsaƙi sannan ya ɗauka

" Hello"

"Hello, Aaliyah ce"

Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta. Kallon a ina ki ka samu special number na ya mata.

Murmushi ta ma sa sannan ta ce " na san za ku je Nigeria cikin satin nan so I will be waiting for you there" ta wuce ta barshi da mamaki.

"And who the hell is she?" ya faɗa da ƙarfi

Hafiz ya ce "kai zamu tambaya ai"

Tsaki ya yi dan ya san irin matan nan ne ma su bibiyarsa.

"Kai amma fa tana da kyau" in ji Rabi'u da ke gefen su.

Yarinyar na fitowa daga ɗakin taron kai tsaye taxi ta shiga sai airport. Tun a cikin taxi ɗin ta kira Abbanta ta sanar masa jirgin su ƙarfe goma shabiyu na dare zai tashi, ya ma ta addu'an Allah ya kawosu lafiya.

Tana cikin jirgin ma selfie da su ka ɗauka da Aaliyah Badamasi ta ke kallo. A hankali ta furta ' it's now or never' ....

***

Wanka ta yi sannan ta gabatar da shafa'i da wutri, da ta idar tana jan carbi aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.

"Come in" ta bashi umurni. Sanye ya ke da silk pyjamas baƙi. Murmushi ta yi ganin ƙwan na ta ɗaya a duniya.

"Ba ka yi bacci ba?"

Zama yai gefenta ya riƙo ɗaya hannunta da babu carbi ya ce "Mom are you Ok?"

Ta ajiye carbin ta sa hannu ta na shafa gashin kan sa mai tsantsi da yalwa ta ce

"I'm Ok son, thank you"

"Kin missing Daddy ko?"

Ta ɗaga kai alamar eh.

"I miss him too"

ya jima a ɗakin kafin daga baya ya mata sai da safe ya fita.

Ta jima tana addu'o'i kafin daga bisani ta je ta kwanta.

Kwantawanta ke da wuya maganganun Ahmad ya fara dawo ma ta, daren rasuwar shi.

*"Na zalinceki Aaliyah, na hukunta ki da horo mafi tsanani ta hanyar rabaki da ɗanki na tsawon lokaci, ki yafemin. Don't be lonely after my death, ki..."*

Ta yi saurin toshe kunnuwanta saboda yadda maganar ke tuno ma ta da abin da ta daɗe da binnewa a zuciyarta.

"Na yafe ma ka Ahmad, haka ƙaddarata ta zo" ta faɗa a hankali...

....................................

Bayan ya yi waya da Aaliyah sai ya ci gaba da kallon program ɗin har sai da aka gama. Ta rame ma sa, haka nan kaman ba ta da lafiya ya ke gani. Zulumin rashinta da zai yi ya ke. Shekara ashirin da biyar bai taɓa fashin jin shirye-shiryen ta ba tun ta na yi a BBC english har ta koma na Hausa haka nan kuwa a duk lokacin da kewarta ya addabeshi toh programs ɗinta ne suke ɗebe masa kewa. Yana da record na programs ɗinta tun daga 1993 zuwa last program da ta yi a farkon shekaran 2018.

"I pray you have peace idan kika dawo Nigeria, Aaliyah"

........................................

"Abba, Abba...."

Muryar 'yar ta sa ya doki kunnensa. Yanzu ya ke shirin fita ya je ya ɗauko ta. Ya fito daga ɗaki da sauri, a stairs su ka haɗu saboda yadda ta shigo gidan da gudu. Ta rungumeshi ta na faɗin "I miss you Abba nah"

"Yanzu ke da na ke shirin zuwa na ɗauko ki, sai ga ki"

Ta kissing goshinsa ta ce

"what's important is that i'm home"

Ya ɗan ja kunnenta ya ce "na hanaki gudun nan ba kya ji ko"

"Sorry Abba" ta faɗa tana murmushi.

Kai tsaye ɗaki ta shiga ta yi wanka sannan ta fito, a dining ta ga ƙannenta na breakfast sai a lokacin su ka ganta saboda lokacin da ta shigo gidan ba su tashi a barci ba. Ta joining ɗinsu su ka karya tare, suna ci tana basu labarin bikin da ta je a London...

***

Gaba ɗaya ta gama haɗa kayanta tun jiya, ita da London yanzu kam sai dai ziyara wanda ba ta tunanin za ta yi shi nan kusa, amma ba dai zama ba. Ta yi murmushi lokacin da ta tuna farkon zuwanta gidan nan. Rayuwa kenan komai yai farko zai yi ƙarshe. Gashi yanzu ƙarshen zamanta a London ya zo, ƙarshen kasancewarta matar Ahmad ya zo.

"Mom an gama fitar da kayan?" Zaid da ya leƙo ɗakin ya ke tambaya.

"Yes son nima ina saukowa yanzu"

Ok ya faɗa sannan ya tafi.

A hankali ta ƙarisa wajen dressing mirror ɗinta, ta ɗan tura shi ƙasa sai ga wani safe a jikin bango. Ta danna number kamar haka 0108 sai gashi safe ɗin ya buɗe. Wata ƙaramar jaka ce a cikin safe ɗin. Ta fito da jakar tareda rungumewa tana hawaye. Muryan Zaid da ta jiyo yana bawa ma su aikin gidan umarni ya sa ta yi saurin ɗaukan jakar ta sa acikin handbag ɗin ta, da shi ke handbag ɗin babba ne sannan ba komai a ciki, ta cusa ciki ya zauna daɓas. Ta yi saurin goge hawayenta sannan ta ɗau jakar ta fito.

Har su ka isa airport zuciyarta bai bar bugawa da ƙarfi ba. Haka kawai gabanta ke faɗuwa. Tun rasuwan Ahmad rabonta da Nigeria wannan kaɗai ya isa ya sa ma ta fargaba musamman idan ta tuno rabuwar ta da Hajiya Inna.

Hannunta saƙale da na ɗanta Lokacin da su ke fitowa daga jirgin. Da mamakin su har lokacin ba su ga wani ya zo ɗaukan su ba. Cikin ɓacin rai Zaid ya fara kiran 'yan gidansu saboda rashin mutunci bayan ya riga ya shaida mu su yau za su taho amma ba wanda ya zo ɗaukan su, kuma har lokacin da za su sauka ya faɗa.

"Zaid Ahmad Wamako" ya ji wata siririyar murya ta kirashi

Murmushi ta ke mu su har ta iso. Kamar dai ya taɓa ganinta amma ba zai iya tunawa ba dan 'yanmatan da ya gani cikin satin nan kaɗai sun fi ashirin.

Ta ƙaraso ta rungume Mom, "i'm so happy na same ku da ban san ya zan yi ba."

"And who are you?" Zaid ya tambaya da ƙarfi. Ta maida kallonta ga Mom ta ce " Mom ni die hard fan ɗin ki ce, saboda ke na je bikin retirement ɗinki a london" ta fito da wayarta ta na nuna ma ta selfie da su ka yi ranan.

"Ayya, 'yata ya sunan ki?" Mom ta tambaya.

"Aaliyah"

"Ashe ke takwarata ce, na gode"

" Mom da alama ma su zuwa ɗaukan ku ba su ƙaraso ba, ki min alfarma na kaiku gida"

"Kar ki damu 'yata za su ƙaraso nan ba da jimawa ba"

"Please Mom do this for me, ko dan son da na ke mi ki"

Mom ta ce " Ok dear" ta kalli Zaid ta ce "mu tafi"

"But Mom you don't even know h..........." ya katse maganar lokacin da ya ga Mom ta fara tafiya da Aaliyah, Aaliyar ce ma ke jan akwatin ta. Ba yadda ya iya dole dai bin bayansu ya yi.

Wata haɗaɗɗiyar mota su ka nufa wanda driver ke tsaye a wajen yana jiran su. Sai da ya ƙaraso wajen ya hango motar gidan su na shirin tsayawa ya cewa Mom da ke shirin shiga motar Aaliyah "Mom ga driver ya zo, barin bi shi"

Ta ɗaga masa kai.

Har su Aaliyah suka bar airport ɗin bai shiga motan ba yana tsaye yana zubawa driver masifa.

Sun yi nisa da tafiya Aaliyah ta ce "Mom bari ki ji wani surprise" ta bawa driver wayarta ya haɗa da radio ta fara playing wasu recordings.

Muryanta ta ji a cikin recording ɗin, ba za ta iya tuna shekarar da ta yi wannan program ɗin ba amma ta san ya jima, ƙila tun farkon shekaran da ta fara aiki a sashen BBC Hausa ne. Ta sake tabbatar da hasashen ta lokacin da ta ji muryarta na faɗin *"shiri ne wanda ni Aaliyah Badamasi Bulama zan gabatar"*

Aaliyah ta katse record ɗin ta kalli Mom da idonta ya cicciko da hawaye ta ce "you are surprised ko?"

"A ina kika sami wannan?, ina da tabbacin sanda na ke gabatar da shirin nan ba a haifeki ba"

Aaliyah ta yi dariya. "Gaskiya ne Mom, sai dai kamar yadda na faɗa mi ki ni Fan ɗin ki ce tun ina ƙarama. Na taso da soyayyar ki da son sanin ke ɗin wace ce"

Mom ta zaro ido

"Don't be surprise idan na ce mi ki ina da records na duka shirye-shiryen ki, tun lokacin da kika fara aiki har zuwa ƙarshen program ɗinki a gidan radio"

ta yi wani ƙayataccen murmushi ta ci gaba "ku masu aikin gidan radio ai farin jini gareku. Zazzaƙar muryarki mai sanyaya zuciya. Kar ki sha mamaki idan na ce mi ki takanas saboda ke aka sa min suna Aaliyah"

"Wow! I'm speechless dear"

Aaliyah ta cigaba da kunna ma ta records ɗin wanda Mom ce ta buƙaci hakan. Tana ji tana tuna lokacin ƙuruciyarta a wajen aiki da kuma girmanta. Muryar dai idan ba ka lura ba ka iya cewa bai chanja ba iya waɗannan shekaru sai dai fa ita ma'abociyar muryar ta chanja sosai girma ya kamata, shekaru ashirin da biyar ba wasa ba ne, shekaru biyar a sashen Turanci sai shekaru ishirin a sashen Hausa. 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.