Free chapter · Read without an account

3- Aaliyah and Saeed's diary

by Azizat Hamza · TSOHUWAR SOYAYYA

️Aaliyah and Saeed's diary

Tun tafiyar Aaliyah ya ke kallon hotunan, yana yi yana zuƙar tabarsa. Tabbas ya san Mom da Dad arrange marriage a ka musu. To dama haka ake yi ai, rich girl for a rich boy. But for thirty years Mom would've fall in love with Dad ai. Zuciyarsa ta raya ma sa. Amma kuma idan ya tuna maganganun Dad sai ya ga kamar har ya rasu babu soyayya tsakaninsu. Anya kuwa? Good 30yrs fah.

Ya maida hotunan tareda cigaba da tuno rayuwarsu kafin Dad ya ɗauke shi a London. Duk da yana da ƙarancin shekaru amma yana iya tuno wasu events da su ka faru. Ƙarar wayarsa ne ya fargar da shi. Ya amsa kiran ganin wanda ya bugo.

"Zaid mi ya faru ne, Fatima ta kira ni tana kuka wai dole a raba gado. What is happening?"

Sai da ya zuƙi taba wanda itace ta uku da ya ke sha ya ce " Uncle, abinda ta ga ya fi ma ta kenan. And i'm Ok with it"

"A'a Zaid, Ahmad ba zai so haka ba, ka san yaran Fatima mata ne kai ne ubansu yanzu. Responsibilities na su na hannunka har su yi aure. Zan zo ranan Friday sai mu zauna a tattauna matsalar"

"Ok Uncle"

Sai daya ajiye wayar sannan ya tuna ko breakfast bai yi ba. Dama breakfast ɗin zai je yi a wajen Mom ya tarar da badaƙalar da su Inna su ka shiryawa Mom...

..................................

Kwana biyu da tafiyan Aaliyah amma kuma ya kasa cire maganganunta a ran shi, musamman idan ya kalli Mom sai ya ga kamar tana cikin damuwa. Idan ya tambayeta kuma sai ta ce ma sa ba matsala.

Yau ma suna cin abincin dare tare amma ya lura a takure ta ke kamar ba ta jin daɗin abincin duk da kuwa ita da kanta ta bada order abinda su Eliza za su girka.

"Mom is there something you are hiding from me?"

"Ofcourse not son, mi ka gani?"

"Mom kamar akwai abinda ke damunki, you always look disturbed..."

"Zaid" ta katse shi

"I'm fine son, yes I look worried saboda yanzu ba da bane, but nothing else"

"Mom that night, twenty years ago...."

"Zaid!" Ta faɗa da ƙarfi.

"Shikenan tunda ba kya son maganan"

Ajiye cokali ta yi ta ce " I've lost my appetite"

Sai da ta shige ɗaki ya sauke ajiyar zuciya. Ba zai manta abinda ya faru shekara ashirin da suka wuce ba. He was only eight amma yana iya tuno komai. Lokacin da Dad ya ɗauke shi daga London kullum sai ya tuna kukan Mom a daren ranar. The screaming, the cries, everything.

Maganan Aaliyah ya tuno da ta ce akwai babban al'amari a rayuwar Mom that he needs to know about. "Could it be related to what happened 20yrs ago?" Ya tambayi kansa.

He was only eight years lokacin da ya rabu da Mom and ba ta taɓa nemansa ba. She stays in London all the while. Ya tuna lokacin da ta zo Nigeria ya ƙi ya je wajenta. How she knelt and cried. Hawaye suka gangaro ma sa. Lallai ne dole ya nemo diary ɗin Mom atleast he will find some answers a ciki...

Ta ya Zaid zai tuno ma ta da abinda ta ke ƙoƙarin ɓoyewa iya tsawon rayuwarta. This is too much for her.

Ta sa key ta buɗe drawer, ta fidda jakar da ta jima tana adanawa.

"If only you came Saeed, if only you came that day" ta faɗa hawaye na zirya a idanunta.

*"Ke ce zuciya ta Aaliyah, idan na rasa ki, na rasa zuciya ta gaba ɗaya" * ta tuna maganganunsa lokacin da ya sanya ma ta zobe a hannunta. Ta kalli yatsarta da ke ɗauke da tabon ƙuna. Ko ba zoben a wajen akwai shaidar zaman zoben a yatsar.

Gani ta ke kamar yau ne komai ya faru. Da saka zoben da kuma cire shi.

"Makhtub" abinda mai duban ya faɗa kenan lokacin da ta tambayeshi.

"Zan auri Saeed?" Tambayar da ba za ta taɓa mantawa ba kenan.

"Makhtub yarinya, rubutacce ne, ko sama da ƙasa za su haɗu sai kunyi aure. Sai dai....."

Ƙaran wayarta ya fargar da ita ta yi murmushi lokacin da ta ga Aaliyah ce.

Ta ɗauka wayar tana murmushi, lokaci guda Allah ya haɗata da yarinyar nan amma ba ƙaramin shiga ranta ta yi ba.

...........................

Mom ba ta wajen aka yi zaman saboda Zaid bai ma sanar da ita ba. Idon Hajiya Fatima yai zuru-zuru lokacin da lawyer ya gama bayanin sa. "Wannan gidan da kuke ciki na Aaliyah ce. Aaliyah, Ahmad ya bawa gidan nan"

Gidan da Aaliyah ba ta zauna a ciki na cikakken shekara ba. Ta ya Ahmad zai mata haka? Fatima ta tambayi kanta

"Hajiya Fatima, ina so ku daure ku yi zaman lafiya tsakanin ku. Idan kika cire wannan gida da Ahmad yai wa Aaliyah kyautarsa Aaliyah ta yafe gadon Ahmad. Daga ke, 'ya'yan ki sai Zaid ku kuke da wannan dukiya, kuma idan aka ce a raba kowa yai na sa waje ba za ku ji daɗi ba. Zaid shi kaɗai ne ɗa namiji dan haka ki bashi haɗin kai ya kula da ƙannensa" lawyer ya faɗa yana harhaɗa takardun da ya nunawa su Hajiyar.

Da Hajiya Fatima da Inna duk ba wanda ya ce wani abu har Zaid da lawyer suka fita a falon.

...........................

Sai da aka yi sati biyu da dawowar su sannan Mom ta shirya ta tafi Maiduguri. A wannan lokacin Zaid ya samu damar bincika ɗakin Mom. Ya jima yana dube-dube a ɗakin amma shiru bai ga diary ba.

Ya zauna akan gadonta yana haki.

"Kodai Mom ta tafi da shi Maiduguri ne ko kuma Mom ba ta da diary?"

Zuciyarsa ne ya tuno ma sa ɗaya daga cikin drawers ɗin a kulle ya ke da key. Ya tashi da sauri. Ya nemi key ɗin wajen bai gani ba. It's obvious duk sauran wajen ba a sa key ba sai last drawer ɗin definitely akwai abu mai muhimmanci a ciki.

Ganin neman key ɗin zai ɓata ma sa lokaci ya sa ya fita dan ya nemo guduma ya kwaɗe, ya san duk rintsi kafin Mom ta dawo zai sa a gyara ba za ta ma ganeba...

To his surprise wata jaka ya gani a cikin drawer ɗin. Tsohuwar jaka ce wanda aka yi yayinsu a irin 80's ɗin nan. Ya sa hannu ya ɗauko jakar tsaftsaf ta ke ba ƙura ko dauɗa a jiki. Sai da ya zauna da kyau a tsakiyar ɗakin sannan ya buɗe jakar. Diary guda biyu ne a ciki sai album. Album ɗin ya fara buɗewa yana ganin hotunan da ke ciki. Hoton farko na Mom ne lokacin tana jaririya sai da ya jima yana kallon hoton kafin ya cigaba da kallon sauran, cikin hotunan da ya ke dubawa ya ga harda wanda Aaliyah ta bashi. Sai daya gama kallon hotunan sannan ya jawo ɗaya daga cikin diary ɗin ya buɗe date ya gani a sama sannan aka rubuta *The beginning*

Rufe diary ɗin yai ya kwashe komai ya maida cikin jakan sannan ya ɗau jakar ya fita daga ɗakin...

***

Tana kitchen tareda Abba su na girki ƙaninta Abdul ya shigo ɗauke da wayarta da ke ringing.

"Z Wamako na kiran ki Anty"

"Abdul ka maida wayar ka ga aiki mu ke zan kira daga baya" ta faɗa tana ƙoƙarin saita nitsuwarta.

"Tun ɗazu fa ake kira" Abdul ya faɗa yana miƙa mata wayar. Tana amsar wayar kiran ya sake shigowa. Abba ya ce " ki je ki amsa wayar ki"

Haɗiye miyau ta yi ta amsa wayar tareda ficewa daga kitchen ɗin da sauri.

Minti biyar sai ga ta ta dawo fiskarta ɗauke da farin ciki. Abba ya kalleta ya ce " waye *Z Wamako*?"

"Ehm. Abba ƙawata ce da mukayi makaranta ɗaya. Zainab....Zainab Wamako sunanta"

Kamar faɗin Wamako ya tsikareshi lokaci guda ya furta *Wamako*

"Abba ka san wani mai irin sunan ne?"

Ya jima bai ce komai ba, hankalinsa ma ba ya wajenta. Sunan Wamako ya taɓo ma sa wani tabo da ke zuciyansa tsawon shekaru.

"Abba are you Ok?"'

Yai firgigit ya ce " yes, yes princess"...

..............................

Ba ta sha mamaki ba da Abba ya amince da tafiyarta amma da sharaɗin za ta dawo kafin ƙarfe shida na yamma. Ko ba komai za ta samu ta yi abinda za ta yi kafin nan.

Driver ne ya kaita har gidan su Nawal. Kamar yadda ta tsara. Da dreban su ya tafi sai ta kira Nawal ta fito da motarta suka fita. Har cikin compound ɗin gidan su Zaid Wamako ta shiga da ita, su ka rabu akan za ta kirata.

Kiran Zaid ta yi akan ta iso ya ce ta shigo ɓangaren Mom.

A zaune ta sameshi yana karanta jarida.

"Wamako da gaske ka samu diary ɗin?"

Hararanta yai ya ce "idan ban samu ba zan kira ki ne"

"Oh. Ina diary ɗin? Ka karanta?"

"Aaliyah kike ko wace, I don't trust you. Ki faɗamin mi yasa kike bibiyar Mom ɗina?"

Ba ta bashi amsa ba sai ta buɗe jakarta ta fitar da wani diary daga ciki ta ce "wannan diary ɗin shi yasa na san wacece Mom kuma shine dalilin da ya sa na ke bibiyarta"

Kallonta yai na wasu daƙiƙai sannan ya ce biyoni.

Ɗakin Mom su ka shiga inda ya fito da jakar da ya gani a drawer.

Lokacin da ya fitar da abinda ke ciki Aaliyah harda ɗan ihunta.

Zaid ya ce "lafiyar ki kuwa"

Aaliyah ta ɗan yi gyaran murya ta ce "duk farin ciki ne ya jawo haka"...

A ƙasa suka zauna bayansu na jingine da gado. A haka suka fara karanta diary ɗin Mom...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.