Free chapter · Read without an account

MAR'ATUSSALIHA BOOK 1

by Hafsat umar dangoro(safhat) · MAR'ATUSSALIHA BOOK 1

2


______________Tun da ya shiga cikin mota'' yafara tuki'' gudu yake shararawa'' a titi'' ko kallon gabansa bayayi'' idonsa ya riga da yarufe'' ransa inyayi dubu ya bacii'' zuciyarsa ko kamar garwashin wuta haka take tafasa'' a haka dai yasamu ya isa gida'' ammafa ba dan Allah ya tsareba''da bansan iya kacin abin da zai faruba...


Yana zuwa bakin get din gidan su'' yashiga danna hown amma shiru megadi bezo ya bude ba''Afusace'' ya daki sitiyarin motar ya daka tsaki,ya bude motar ya fito'' yana fita ya bude karamar kofar gidan ya shiga'' yana shiga sukayi karo da megadin yana kokarin bude kofar'' mukullin kawai ya hurgamasa yayi cikin gida da sauri'' fuskar nan kamar daran Bala'i sabi da tsananin bacin rai''...


Me gadi ko'' baki ya saka yana bin bayansa da kallo'' daga bi sani kuma ya jijjiga kai domin ya fahimci yau ba lafiya ba''akwai wani da ya tabo shi''.. Acikin zuciyar sa kuma yace Allah ya sassauta abin'' daga nan kuma ya mike yanufi motar ya shigo da ita gida'' yayi parking dinta a parking space....



Ton da yashiga falon'' ko sallama beyi ba, ya haye sama'' dakin sa ya bude ya shiga'' kai tsaye bathroom ya nufa'' ya fadakan bed dinsa '' ko takalmin 茩afarsa be cireba'' runtse ido yayi a hankula Abubuwan da suka faru,suka shiga dawo masa'' wai Ni zata kalla tacewa''kashin kare yafini'' daraja'' why'' ita ''yar uban wane a garinnan'' wallahi sai na nemota'' muddum ban koyawa yarinyar nan hankali ba''hankalina bazai taba kwanciya ba''shiru yayi yana tunanin abin da zai aykata'' mata wan da zai sa ya samu sassauta acikin zuciyarsa....'' kofar dakinsa yaji anturo an shigo'' Ana nufo inda yake'' ko bude idonsa beyi ba sabi da ya gane wace ke tafiya'' don yasan in banda ita din babu meshigo masa daki ko sallama babu''


Kara sowa tayi'' dai dai bakin bed din'' ta tsaya ta zubamasa ido tana kallon sa'' har ga Allah azuciyar ta tayi tunanin bacci yake'' hakan yasa tayi yunkurin'' cire masa takalmin da yake kafar sa'' ay tana fara warware igiyar takalmin'' taji wani saukar maruka ''zafafa har guda biyu a kuncinta'' wasu taurari tagani sun gifta''tsabar zafin marin tafiya tai zata fadi'' da 茩er ta samu ta sa hannunta a jikin ban gon ta tokare'' sabi da kada ta fadi'' murya na rawa ta dago ta kallesa'' tace ya 饾棝饾棓饾棔饾棞饾棔 me nayi maka?" Daga gwaninta sai ka mareni'' hannu ya daga mata cikin masifa'' yace'' fitar min daga daki'' Anisa'' nace kifita'' i se get out Anisa'' a guje ta fice daga dakin''ta na kuka ta sauka kasa'' sai ga sallamar Hajiya adama'' ay da gudu taje ta fada jikinta'' ta rungumeta'' tasaki kuka'' har da majina'' ...


Ay Hajiya adama'' na ganin ''yarta tilo na kuka'' ta zab ga wata uwar ashariya'' sannan tace'' kan ubanca'' Amma fa yau za a yi tashin hankali a gidannan'' me akayi miki fadamin"?" Anisa kam dago wa tayi'' ta kalleta fuska duk a kunbure gashatun hannun Habib'' a nanne a kuncinta'' Ay Hajiya adama'' tana ganin haka ta ce'' uban wane mareki?" Nasan bazai huce'' dan isakan yaron ce ba ko'' to wallahi da Hajiya adama'' yake zancen''an fada musu baiwa na kawo masa'' ke kuma so haukane'' nace miki kirabu da'' wannan azababban yaron wan da ko murmushi ba yayi kinki''narasa ma uban me yayi har ya burgeki haka'' ay ga irinta nan zai je ya hallaka ki a banza'' ya cuceki''ya cuceni'' kefa nace miki ki hakura'' duk mazan duniyar nan wadan da suka fi habib ko mai''amma ke kin makale sai shi ''to gaki ga Habib nan'' wallahi idan ke kin jure wannan cin mutuncin Ni bazan jureba'' ina ita fateeman take'' tun da ay ita ta daurewa dannata gindi''


Momy ce ta shigo falon ''dauke da murmushi a fuskarta'' irin nasu na manyan mata'' tace'' a,a to Hajiya adama'' kece a gidan namu'' ?"sannu da zuwa''


Bansa Ni ba'' da banzo ba kenan da kun kashemin ''yar kun barni da wayyo Allah' ko sabo da baki da asara ....


To adama'' nikike fadawa haka ?" Tukunnama me yafaru'' ne har kike tada hankalinki haka?" Au bamakisan me yafaruba''kinacan danki zai hallaka min tawa''yar uban me tai masa ''kodan tanuna tana sonshine'' to wallahi daga ke har dan naki'' hawai niyar ku takiyayi ramata'' idan ba haka ba wallahi za ay tashin hankali a gidannan'' dan kinsan halina'' idan na fara bala''i'' gwara gobara akan Ni adama'' . Dan nafi zawo rashin hakuri...


Momy ce ta ce'' haba adama'' kiyi hakuri mana abi abun a sannu'' anki abari abi abin a sannu'' wato nufinki na ja baki nayi shiru acutar min da ''ya ko?"




Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.