Free chapter · Read without an account

5

by Asmy b Aliyu · FADWAAH



washe garin dawowar sune Wacce tazamo bakar ranar ga Amina ,tana tsaye a kitchen tana hada masu break fast da misalin qarfe goma na safe ,Taji maganar yah Habee a tsakiyyar falon nasu tana kwala mata kira ,kiran da ya gigita Amina yasa ta fita a hayacinta ,doguwar riga ce ajikinta ruwan Zuma kanta da hular net fara ,Wanda kana hango tulin gashinta baki sidik.da hanzari Amina tafito daga kitchen tamkar zata fadi qasa ,

Baya baya tayi zata fadi Allah ya kado tariq yyi sauri tarota bi sannu Amina meye haka?

Cewar tariq Wanda ya zaunar daita daya daga cikin kujerun dake zagaye da falon nasu ,

Salati Habee tayi shikenan wlhi tariq ta Riga ta gama dakai hannu tasaka akai gamida sakin kukan munafurci ,

Saurin isa gabanta tariq yayi gamida riqo mata hannu yana fadin assha !Assha yah Habee mekuma yyi zafi hak?"

Buge masa hannu tayi gamida daka masa wata irin kafurar tsawa ,karka tabani tariq 

A yau ina maka umurni da babbar murya akan ka saki wannan matar ,kabata takardar sakinta bana son ganinta!duk tabi ta maidaka shanyayye mijinta ce sae abunda tace ."

Tashin hankali kwance a fusakarsa yake kallon Yayar tasa sae Yaji bazai iya yimata musu ba ,haka ta tsaresa da manyyan idanunta ,wani irin tsoro ya cikasa Jin yake idan baibi umurninta ba mutuwa zay yi ,da sassarfa ya wucesu ya nupi dakinsu na barci ,Cike da tashin hankali Amina tabi bayansa ,yayinda Habee ta qyalqyale da dariar mugunta gamida yin shewa ,samun kujera daya tayi ta qame tana Jiran Amina tafito.



Koda Amina ta samu tariq zaune yake agefen gado yana rubutu a takarda haka hawaye na zuba acikin takardar ,gabanta yyi wani irin bugawa badai tariq sakinta zai yiba da gaske?"shin idan tariq ya saketa ina zata?ina ta nufa !qarasawa tayi agabansa ,ta zube gwowinta a qasa lokaci daya ta fashe masa da kuka, tana roqonsa ya rufa mata asiri yyi mata rae kodan cikin dake jikinta ,

Cikin kuka yake faɗin kiyi hkuri Amina ,baxan iya ba jinake idan ban cika umurnin yah Habee ba mutuwa zanyi kiyi hkuri !kiyi hkuri Amina Dan allah kiyafemin bayin kaina bane ."!

Kibaiwa Dan da zan Haifa ko yar da zaki Haifa ,labarina kifada masa zan dawo garesa wata rana!idan namiji kika Haifa kisaka sunan Abbanki idan macce kika Haifa ,kisaka sunan umma na. *HAFSA* !kiyimin wannan alfarma zan turo maki kudi a account dinki Wanda zasu isheki ,zansa driver na ya maidaki Daya daga cikin gidajena da na mallaka acikin garin Gombe sae inda kikeso ki zaba ,amma Dan Allah Amina ki yafemin ,

Zan dawo gareki !wata rana."

Yana gama fadin haka ya dunkule takardar ya damka mata ,daganan ya fice daga dakin ,yana zubar hawaye itama hawayen takeyi wannan shine karshen Rabuwarsu da Abban hafsat wacce take kira babba fadwaah tun tana qarama ,

Wanda bata qara ganin wani nashi ba koshi kansa ,tasan dai saki daya yyi mata koda Kabeer yasamu lbr yyi bakin ciki sosae ,

Bayan wata Tara allah ya sauketa lfy ta samu kyakkyawar Jinjira mai kama da ubanta sak!da kalar fatar uban nata da fuskar nata komae nasa ne.

Haka Hajia Amina ta riqa rainon hafsatul Fadwaah Wacce ta taso cikin gata.da kulawar mom dinta da kuma uncle Kabeer Wanda shima bayan wasu shekaru yagama karatunsa cikin nasara ,haka yasamu aeki mai tsoka Wanda nan take yazama billionaire ,aure ne dai biye ba,

Sosae yake nuna ma Fadwaah gata shiyasata nursery skull ,lokacin tana ya'r Shekara hudu bata mancewa ,nan ne parkon haduwarta da Sahlaah ,

Har zuwa primary skull ,inda suka zama friend's nan ne Asalin dangantakar Abotar mom da mamin su Abhi.

Yayinda Mami na matuqar son Fadwaah ko dinki sallah akayiwa sahlaah agidan su sae anyiwa fadwaah dan kowa yasan da zamanta.

Ya'yan Mami ukku ne a dunia ya'rta ta farko ,Raheema wadda ke auren Dan governor Gombe ,maici a yanzu amma Gaba daya suna Rayuwarsu a garin Abuja .yayan su biyu a dunia macce da namiji maccen ce ta farko mai sunan Mami ,suna kiranta baby ,sae maisunan uban Mijin Raheema ,Muhammad suna kiransa Mooha.

Sae mai bita Omar Wanda yaci sunan mahaifin Mami tun yana qarami suke kiransa Abhi ,tun yana qarami yake son police idan yaga police acikin T.v.haka zay fasa Rigima sae daddy ya siyamasa kayan police ,

Haka yataso da tsananin son police ,idan kuna son kuga fara'ar Abhi kuyimasa zancen police ko Ku kunna masa American movie na police ,

Bayan gama secondary dinsa ne Daddynsa wato Alh.salman kurfi ,ya kaisa makarantar *Police academic*"dake Jihar kano zo kuga murna wurin Abhi ,cikin nasara ya fara karatunsa ,shekara hudu cikin na biyar ya fito da first class Dan umar kurfi mutum ne mai hazakar gaske ,mutum ne mai hakurin gaske da wuya ka bata masa rae shiru shiru yake baya magana idan kaga maganar sa,yana cikin ya'n uwansa ne da haka ta gefen uwar da uban suka dauki son dunia,

Suka Daura masa ,tareda taimakon wani abokin Alh.salman kurfi Abhi ya samu aeki ..a *Headquarter*dake garin Abuja ,

Cikin nasarori masu yawan gaske ,ya karbi aekin sa hannu bibbiyu ya riqa mukamai da dama ,a hankali aka riqa qaramasa girma ganin yadda yake qoqari da maida himma a aekinsa.atakaice Omar kurfi ,yanzu haka yana matsayin mataimakin commissioner. Na ya'n sanda ,

Asalin mahaifinsa ya'n katsina ne acikin wata karamar hukuma mai suna (KURFI)amma Alh.salman bai girma acan ba ,agarin Gombe ya girma anan kuma ya taso yaga iyayensa ,Alh.salman mutunen mai tausayin gaske ,haka mutun ne Mae Arziki Wanda abun dunia bai rufe masa ido ba har ya wulakanta talakkawa ,idan kaganshi cikin tallakawan garin sae ka Rantse da allah shima irinsu ne ,ya riqa manyyan mukamai da dama ,kamar su p.d.p.chairman Senate da sauransu haka mutune na mutane ,Wanda manyyan ya'n siyasa ke hurda dashi.


Azeezah Akilu Dala.

Asalin cikakken sunanta kenan ,Alh.Akilu dala ,sunan shi yayi fice acikin Nigeria da wajenta ,business man ne Wanda yake da manyya manyan company's acikin Nigeria ,da yammacin kudu ,

Bbu inda sunan sa bai zagayaba acikin Nigeria da wajenta ,agurguje Azeezah takasance ya'mmace kwara dal agun mahaifanta ,gaba day'a yayunta ukku maza ne ,kuma itace auta ,Dan haka mahaifanta suka dauki son dunia suka Dora mata,musamman Hajia Ruma wadda itace mahaifiyarta ,Azeezah tataso cikin gata haka sangartatta ,Dan tun daga kan secondary skull har zuwa Jami'a Awaje tayi karatun ta ,Tarbiyar gidansu tana tangarda Dan sae Abunda ya'yan keso shi iyayen keso .farkon dawowarta gida ne ,tafita yawon shakatawa cikin garin Abuja yayinda driven ta ke janta ,

Tana chatting da wayarta ,sae kawae taji motar ta tsaya.da balai ta dago kanta Dan yiwa driver masifa ,

Taji yana salati motarsu ce ta bugi wata farar Benz, Aza hannu akae tayi ta saki ihu gaba daya ta gigice cikin ikon allah motar ta tsaya ,cak!

Haushi ya kamata ta fito daga motar haka mutane sun taru wurin mafi yawa suna gurin 

Daga ido tayi zatayiwa mai Benz din masifa ,idonta suka fada cikin na Omar kurfi abun mamaki duk Jin kan Azeezah duk rigimarta haka ,duk girman kanta .

Sae gata ta raina kanta ,gaba daya ta rude da kyawonsa idonsa cikin nata yyi murmushi ,mai kyau cikin sanyi murya yake fadin am sorry madam.!''

Sumane kawae zeezah batayi ba ,

Itama murmushi tayi ,gamida fadin am sorry plss murmushi yamata gamida komawa mota yadan leko ,

Gamida fadin bbu komae madam."anan ya wuce yabarta ,tabi motar tasa da qallo.

Sannu a hnkali soyayyar Azeezah da Abhi ta fara nisa son Junan su suke tamkar su hade Juna ,

Tashin farko Hajia Ruma batason Abhi acewarta me ya'rta zatayi da Dan sanda ita da take da buri masu yawa akanta ,sae da azeexah ta kwanta gadon Asibiti sa'annan Hajia Ruma ta saduda ,

Azeezah batajin kunyar ko agaban wanene ta nuna ma Abhi soyayya son nata har yafi nasa,

Lokacin da Azeezah ta gabatar da Abhi agaban Alh.Akilu dala ,yyi na'am da halayen Abhi ,inda yace ya turo magabatan sa.

GOMBE... Lokacin da yasamu Mami da zancen sae da tasha Jinin jikinta ,hnkalin Abhi ba qaramin tashi yayi ba,cikin sanyi murya yake fadin Mami bakyason zeezah ne?"wlhi idan bakyasonta na hakura ,na hakura Mami .

Murmushin qarfin hali Mami tayi gamida shafa kan Abhi ,cikin sanyin murya take fadin waye ya fada ma bana son Azeezah? "Duk abunda babana keso shinakeso ,Rungume Mami yyi yanajin farin ciki na ratsa sa,

da gaske Mami kinaso Azeexahna ?"

Gyada masa kai tayi ,murna ya hauyi tamkar zai Goya mamin dan ddi."daddy na dawowa ,Mami tasanar masa dama kuma sunyi zancen da Abhi ,

Da kwana biyu daddy ya tura kaninsa da wani abokinsa nemarwa Abhi auren azeezah ,

Bbu laipi an karrama su dan Alh.Akilu dala ba qaramin mutun bane,

Komae da komae aka yanke nan da wata day'a zaayi bki ,harda dan qaramin party azeezah ta hada itada friend's nata ,

Haka ta cika trolley 5 da kaya zataje ta gaisheda mamin Abhi ,

Yadda Mami taga azeezah nayi yasa tasha Jinin jikinta ko kadan Azeezah batada tarbiya,

Saukarsu GOMBE keda wuya ko ruwa bata shaba,take tambayar Mami ina ne part din Abhi?"

Sahlaah da shegen iyayi da kicififi taja hannun azeezah zuwa part ,din Abhi Wanda gaba day'a bedroom nasa pics dinsa ne Dana azeezah ddi kasheta ,

Haka ta fada kan bed nasa tana shakar kamshin sa..





#ASMY B ALIYU

#Abhi Kurfi

#Azeezarh kurfi




Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.