Free chapter · Read without an account

Chapter 17

by Khadeeja Candy · TA ƘI ZAMAN AURE

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: ***


*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*



✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧



𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆



*Book 2 - Chapter 2*


Kusan zan iya cewa na saba da kuka a duk lokacin da rai ya bace, balle kuma yanzu da kaddara ta sauya min mu'amala da dabi'u. Kuma ta rufe ni a cikin wani dakin da ban isa na fitar da kaina ba. Idanuwa na saka ina ta kallon yadda ake ta kai da kawo na sha'anin bikin aureni a yayinda bani da wani kuzari na magana ma balle na motsa, kamu, walima da wani event da ake yi na aure ban shirya ko daya ba, Hana ce mai kokarin ganin na yi wasu abubuwa amman ban saurareta ba domin ni kadai ya san yadda nake ji a rayuwata na auren mutumen da ba shi a lissafina. 


Ana sauran kwana biyar adaura auren Hafiz ya saka a sallamomi, a lokacin na ci kuka har na sauya kalar idanuwana, sai na fito ina tafiya kamar bana son isa inda yake tsaye. Daga jikin kofar gidanmu na tsaya na rumgume hannyena kaina na kasa domin bana son kallon fuskarsa ma. Daga inda yake jingine jikin mota sanye da kananan kaya ya dago ya karaso kusa da ni kamshin turarensa na kara kusantar hancina. Wayarsa ya ciro daga aljihu ya kunna haske fitilar ya haska fuskata. 


“Noor Lafiya kike kuwa?”


“Ni ban taba lafiya ba tun da kuka shigo rayuwata”


Na amsa masa ba tare da na kalleshi ba. Wayar na ga ya kashe ya saka aljihunsa. 


“Daman na zo ne na tambaya me zaki yi a cikin shirye shiryen da yan mata suke yi?”


“Ba zan yi komai ba”


Na amsa a takaice. 


“Okay, daman dai na zo na ji saboda na bada kudin shirye shirye idan har zaki yi, kuma Balkisu wato uwargidana kenan ta shirya Walima da Kamu, saboda na fada mata daman abu ne mai wahala ki iya shirya wani event, wannan ina fatan zaki je?”


“Ba zan je ba”


Ya tsaya kallona kamin na ji saukar ajiyar zuciyarsa. Ya gyara tsayuwarsa ya fuskance ni da kyau sannan ya kira sunana kai tsaye da siffar da be taba yi ba. 


“Khadija...”


Na daga kai na kalleshi duk da kasancewar bana ganin fuskarsa da kyau saboda duhun dare. 


“Ina son na yi wata magana dake, na san kina da kiriniya kina da kurciya amman duk da haka kina da hankali kuma kina da tunani irin na mutane domin ke mutum ce. Kin ga tun farko ni da ke ba mu san juna ba, ban san ki ba baki san ni ba, amman da Allah yayi nufin hada wani abu a tsakaninmu sai ya kawo dan'uwanki a gurin kasuwancin abokina, duk da haka kuma be hada ni da ke kai tsaye ba sai ya hada ki da abokina wanda shi ne silar faruwar komai a yanzu”


Yayi shiru na wasu dakiku sannan ya shiga. 


“Wallahi Noor ban saka ran aure nan kusa ba, kuma ban yi tsammanin zan aureki ba, ina wani tunani da tsari ne na dabam a rayuwata game da ke ashe abun da Allah yake tsara mana dabam, kuma dai kamar wasa na amsa abun nan gashi ya zame min gaske, ban san zafin rabuwa da masoyi ba, amman na san dadin auren wanda kake so domin matata ta farko auren soyayya muka yi, sai dai ke ina hango miki wani abu a yanzu wadda na kasa gani a baya, kuma ina hangen wani rame da yake shirin fadawa da ni” 


Ya gyara tsayuwarsa. 


“Shiyasa yau nake son mu kai karshe da ke, Noor ko dai mu karbi kaddarar nan ko kuma mu hakura da juna, saboda ina jin tsoron abun da zai je ya dawo, ance idan gemun dan'uwanka ya kama da wuta to ka shafawa naka ruwa, Zan iya samun Mahaifinki na fada masa cewar na sanyi zancen auren nan, domin na lura san baki ra'ayi na, yadda nake tunanin zan iya juya ki kamar hakan sai gagara a gareni” 


Na kalleshi da sauri ina girgiza kai hawaye na sauko min. 


“Fasa aurena ba zai saka Baba ya amince na auri Zafeer ba a yanzu, kawai zai janyo min matsala ne tsakanina da shi, zai tsine zai yi fushi da ni, Kareem ya riga ya kawo ka a rayuwata kun ruguza min komai”


“Babu ruwan Kareem a cikin matsalar nan, da kin san yadda yake son farincikinki da baki furta haka ba, abu ne da aka riga da aka tsara tun farko, shiyasa nake son ni da ke mu karbi wannan kaddarar...”


Ya jinjina kai alamar gamsuwa ina share hawayen da suke sauka a lebena. 


“Na karba Hafiz, na karba...”


Na amsa masa sannan na juya ina kuka na shige cikin gidan. Rasa na yi gurin da zan raba na yi kuka dan haka na dauki buta na shige bandaki na rufe baki na dinga kuka kamar raina zai fita. Daga ranar sai kukan ya rubbanya, domin ina jin a zuciyata na rabu da mutumen da shi ne farincikina. Hankali be kara tashi ba har sai da yan'uwan Baba suka fara sauka gidan wasu daga dangin mahaifiyata dake zuwa kullum suna kawo min maganin mata da ya zame min cilas Ina sha ba dan zuciya na so ba. 

 Ranar Alhamis aka yi kamu a gurin da uwargidan Hafiz din ta kama, sai dai ban samu zuwa ba saboda zazzabin da ya rufe ni ya hana ni ko da bude ido. Mafi akasarin dangin mahaifina suna dorawa Mama laifin damuwa na ne, sai na kasa sakewa ne saboda bata kusa da ni, ta ki ta leko bikin aure, wata kanwar Baba ma cewa take Baba ya fada mata ita ta hure min kunne nake son bijire masa a auren mutumen da ya saya masa gida kuma ya dauke masa komai na aure. 


“Ke ni fa ba dan Hajara ita ta haifi yarinyar nan ba, Wallahi sai na ce bakinciki, domin yau mijin da Noor zata aura Miji ne da ko wace uwa take son a aurawa yarta, mutum mai alheri mai son yarka”


Cewar Gwaggo Saude, Gwaggo Hasana ta amsa mata da cewar. 


“Tohm ke ma dai kya fada, tun ba yau ba fa Yaya yana kuka da Hajara, wasu abubuwan da Noor take ma ni sai nake ganin kamar har da goyon bayanta, domin dai Yaya yana tsaye akan yaransa suna tsoronsa amman ita kam aa sam so take ma su raina shi, yanzu ba gashi ta yi ma kanta ba ina dadi ayi auren yarka kai kuma naka auren ya mutu? Ka koma gida da tsufanka da komai kana zawarci, yaran matasa ma yanzu ya suka kare balle kai da ke da manyan yaya”


Gwaggo Saude ta yi kwafa. 


“Ai muje dai zuwa nan gaba kadan sai ta yi nadama, gashi babu gyara balle ace za a gyara, kuma Yaya dai aurensa zai yi domin yace ana yin auren Noor shi ma zai yi nasa”


“Ai ni Wallahi ban dauka zai kai yanzu ma be yi auren ba”


Anty Larai ce ta katse hirarsu tana kanrar da su abun da suka manta. 


“Yaran nan fa suna jinku kuna zagin uwarsu babu dadi”


“Gaskiya muke fada Anty Larai, da a fada bayan idonsu ai kara a fada gaban idonsu, su ji komai saboda tuwon gobe ake wanke tukunya, ai da gulmarta zamu yi ba zamu yi a inda zasu ji ba”


“Toh ban da abinki Saude su kansu yaran ai ba tsoronsu muke ba balle mu kasa fadar abun da yake ranmu, ita gaskiya ai dole a fade ta”


Anty Larai ta ce 


“Hassana dan Allah a bar zancen nan ai ana barin halak dan kunya, kuma babu kyau cin gira kusa da ido, yara kuma duk da wayonsu kawai suna son dasa ma kanku kiyayyar ku a zuciyar yaran ne idan kuna cin fuskar uwarsu suna saurare, dan Allah kar wanda ya sake tada zancen nan”


Daga haka ban sake jin wata maganar nan. Daga ni har kanwata Hana ba mu motsa ba, ba wannan ne karon farko da suke yawan bawa Mama laifi idan wani abun ya faru ba, domin Baba yana zaunawa da yan'uwansa ya zageta ya nuna bata da gaskiya ko da kuwa ita ce mai gaskiya.  

 A duk lokacin da suka zo ko ta hadu da su suna yawan fada mata maganar da duk ta so bakinsu marar dadi kamar da gatse, ma'ana dai Mama da yan'uwan Baba suna irin zaman nan ne na doya da manya, sai dai ba duka ba.

 A yanzu na kara tabbatar da hakan domin daga Baban da ya kasance Miji a gareta da yan'uwansa babu wanda yayi marmarin dawowa ta a gidan ko da a munafurce ne. 


Ina cikin dakin kwance Baba ya shigo gidan da dan saurinsa. Yan'uwansa suka amsa sallamar sai ya tambaya ina nake, tun kamin na ji dalilin neman gabana ya fadi. 


“Ina tunanin tana daki kasan ba fitowa take son yi ba kamar mai tsoron mutane”


Gwaggo Saude ta fada. 


“Wai yaron nan ne ya matsa yana son magana da ita, yaje ya same ni cikin mutane sai rokona yake jama'a duk sun saka baki mi Wallahi har kunyata ni yayi a cikin mutane”


“Wane yaro kuma Yaya?”


“Zafeer mana”


Na tashi zaune da sauri kirjina na bugawa da karfi jin Baba ya amsawa Gwaggo Hassana da sunan masoyina. 


“Toh Lafiya? Me yake nema”


Natsuwa na yi sosai ina saurarem irin amsar da zata fito daga bakin Baba tare da fatan zai amsa mata da cewar ya fasa aurar da ni g Hafix zai aura min Zafeer din da nake so. 


“Wallahi gaba ya saka ni da roko da komai yana son zai yi bankwana da Noor”


Na tashi da sauri na isa bakin kofar dakin na tsaya ina kallon Anty Larai dake fadin. 


“Bankwana kuma? Ikon Allah ban taba ji haka ba...”


Gwaggo Saude ta tabe baki. 


“Waya sani ko wani sherin ya dauko yake son ya shafa mata? Albashi idan taje ta kasa zaman aure ko kuma ta miJin ya juya mata baya, kai wannan yaro da naci yake”


“Gaskiya Yaya karka barshi, tana ina zaka yarda taje su yi bankwana waya sani ma ko sace ta zai yi su gudu”


Na kalli Gwaggo Hassana kamar na yi magana amman na kasa domin ban isa ba na yi wata maganar ace wani abun muke shiryawa. 


Anty Larai ta juyo ta kalleni sannan ta juya ta kalli Baba. 


“Me yasa yake son magana da ita?”


“Wai bankwana zai mata”


“Bankwana ma auren da zata yi ko kuma na me? Bankwana kamar ya?”


Gwaggo Hassana tace. 


“Waya sani Anty Larai ko wani abun ya dauko ace da sun hada ido zata ce bata son wacan shi take so, kuma yarinyar da ya rage kwana biyu a daura mata aure ai matar wani ce ta ina za a bar wani da ba mijinta ba ba muharraminta ba ya ganta... Ni dai zuciyata ba ta natsu da wannan ba” 


Ajiyar zuciya Anty Larai ta sauke sannan ta ce. 


“In har ya zama dole to ya shigo nan a gabanmu idan wata maganar ce ya fada mata, amman ba za a fitar da ita waje ba, kuma ba zai kebe da ita ba”


“Ni dai kam da za a dauki shawarata ba zai ga ganta ba, ba mu san sherin da ya dauko ba, duk abun da yake son fada mata ya rubuto mata a takardar a kawo mata”


“Eh to kuma kin kawo shawara Saude bari ayi haka din a huta kawai zai fi”


Baba ya amsa sannan ya juya ya fita, kusan ni da hoto banbancinmu kadan ne a lokacin domin bana iya motsi kuma na kasa cewa komai hawaye ne kawai abun da ke fitowa a idanuwana. Anty Larai ta taso ta dafata ta shigar da ni daki sannan ta fito tana fadin. 


“Ni dai kam da dai Yaya be yi wannan abu ba, ina ganin kamar Hajara ta fishi gaskiya a nan domin yaran nan suna son junansu”


“Haba Yaya Larai yaron nan fa be tashi aure ba irin masu batawa yan mata lokaci ne kawai ga wanda ya shirya sai kuma ace ba za'ayi da shi ba, kuma kowa yana son ya kai yarsa inda zata huta Yaya yana da gaskiya Wallahi”


Haka suka yi ta juya maganar tsakaninsu, ni kuwa na kashe kunne ina ta sauraren dawowar Baba, amman be dawo ba har dare ya fara yi sosai, wasu ma tuni sun fara bachi. 


“Yaya sannu da zuwa”


“Yauwa Larai baki kwanta ba”


Na ji Baba ya amsa yana sauke gajiya. 


“Shiru kuma dazun baka dawo ba ka bar mu da tsammani da jira”


“Ai ina fada masa cewar ya hakura ba zai samu ganinta ba Gwaggwaninta sun hana sai ya fara gajiya, ni kuma bukaci ya rubuto ko ma minene, da na fada mata sai na wuce tare da Malam Usman daman tare muke, to bayan na koma can majalisa bayan sallah Isha'i ya same ni ya ba ni takardar”


A zatona Gwaggo Saude ta yi bacci domin ban ji motsinta ba tun bayan da suka gama tsinewa Zafeer a dazun, ashe ban canka daidai ba sai jin muryarta na yi tana fadin. 


“A bude A duba idan ba wani maganin ya saka a ciki ba”


“Ni zan karbe ta ma sai da na yi addu'a na yi bismillah sannan na karba kuma na bude tun a can na duba ban ga komai ba, ban san dai abin da ya rubuta ba saboda ba gane karatun zamani nake ba da ma ace ajami ne zan gane”


“To a karanta gaban kowa kowa kuma ya ji”


Gwaggo Saude ta fada sai Anty Larai ta tari numfashinta. 


“Aa wannan kuma be dace ba, sirrinsu ne a bata ita ta duba abunta.. Noor”


Ta karasa da kiran sunana sai na tashi jiki na rawa na fita daga dakin na isa inda take na duka, sai ta karbi takardar daga hannun Baba ta mika min. 


“Ga sako inji Zafeer yace a baki”


Hannu biyu na saka na karba sannan na mike tsaye na koma cikin dakinmu, babu wutar nepa da hasken fitilar da aka kunna mana na yi amfani na bude takardar ina hade yawu zuciya cike da fargaba. 


“Wannan kam ta karshe ce, bankwana ne da ban yi tsammanin zuwansa ba, ban taba mafarkin ko tunanin zan rayuwa da wata macen da ba ke ba Noor i love and i will love you unconditionally, wannan wani abu ne da yake tabbatacce a rayuwata. Sai dai kuma ba zai hana na manta da wannan cin amanar ba, ba kuma zai saka na fasa fada miki hakkina zai bibiye ki ba. Noor ana halittar ko wace mace da rib din mijinta ne, kuma ke ce rib dina and I'm yours, zaki gane hakan nan gaba, zaki neme ni a lokacin da nema ba shi da amfani a gareki, zaki yi nadama bayan kurewar lokaci, Noor ba zaki sake ji daga gareni ba, It time to say good bye Ba zan iya zama na ji ko na ga daurin aurenki da wani da ba ni ba, Noor idan kika ce na fasa tafiya zan tsaya, idan kika amsa cewar zaki aureni kin wanke ni daga damuwa, ina kaunarki Noor ba zan daina kaunarki ba har abada... Tafiya ce da ba ta waiwaye ba... but this is not the end...! Wannan be kare ba, Zan jiraki Noor zan jira...”


Na karanta na sake karantawa hawaye na sauko. Na rumgume takardar a kirjina ina kuka marar sauti. 

Da wane zan ji? Bakincikin auren wanda bana so ko kuma na rabuwa da wanda shi ne sadaukin rayuwata? Ko kuma na dora min laifi da Zafeer yake? Me yasa ya kasa bude ido ya kalli irin kunnar da nake ciki? Shin labari be je masa cewar dole aka min ba? Ko kuma zuciyarsa tana da nauyin karbar gaskiya ne? Yadda na ga rana haka na ga daren babu wani banbanci, saboda kuka da bakinciki mai hana bachi kusantar idanuwa. 

 Washe garin ranar, rana ce mai tsananin daraja da martaba ga duk musulmi, sai dai ni na ji ta a dabam, saboda kusancewar abun da nake aunawa da mutuwa. Bana iya komai sai ance tashi ki yi duk wadda ya kalleni ya san bana farincikin da auren da zan iya cewa Baba siyar da ni yayi aka ba shi kudi. Ko kuma na ce rawar kai ya janyo min na dauko ajalina har gida na kawo. Misalin karfe uku aka zo da motA daga gidan ango aka dauke ni tare da kawata Zainab, zuwa wani shagon kwalliya, ana fente fuskar ina hawaye hakan ya hana kwalliyar. Daya daga cikin matan da aka je dauko ni tare da ita ce ta kama hannuna ta jani zuwa wani guri na dabam da muka kebe daga ni sai ita. 

Ta zauna kusa da ni sosai ta kai hannunta ta dago kaina muka fuskanci juna. 


“yarinya aure sirri ne, kukan ba shi da amfani a gareki mijina mutum ne mai tsananin tsoron Allah mai kawaici mai adalci, miji ne da ko wace mace mai hankali zata so kasancewa d shi, da ace kin san halinsa na gari da kuma yadda yake taka tsantsan da duniya da baki zubar da wannan hawayen ba, tun da muka yi aure da miji be taba wulakanta ni ba, haihuwata uku da shi ga ciki na hudu, ba zan miki karya ba mu kan samu tsabanin amman babu wanda yake sani, saboda baya bari a san sirrin gidansa”


Kallonta nake irin kallon da na gagara yarda da gaske Matarsa ce. 


“Wacece ke?”


Ta lumshe ido ta bude 


“Abokiyar Zamaninki yar'uwarki kuma yayarki...matar mijinki”


Na hade yawu mamaki ya saka hawaye yanke min a take, a wacan karon da ya fada min ta shirya Kamu da Walima ban dauka da gaske ba, domin ban yi tunanin akwai wata mace da zata yarda ta shirya wannan wa kishiyarta ba, a yanzu kuma taje ta mota suka dauko ni zuwa gurin kwalliya, hakan duk be wadatar ba har sai ta fada min kyawawan halayyar mijinta anya Hafix mutumen kwarai ne kuwa. Ta dafa hannuna tana murmushi. 


“Na san zaki yi mamaki jin furucina, zuciyarki zata raya miki cewar ko dai mutumen da za a daura min aure da shi ba mutumin kirki ba ne? Ko?”


Na daga mata kai domin abun da yake shimfide a zuciyata kenan. 


“Ko kadan, Wallahi Barrister mutumen kirki ne, kawai ina fada miki gaskiya ne saboda hankalinki ya kwanta, karki ce bana kishi ina yi, amman na yi Kokarin fin karfin zuciyata ne, saboda ina son farinciki Mijina, kuma idan har yana neman goyon baya akan wani abu ina tunanin ni ce ta farko da zan fara bashi wannan goyon bayan, Barrister ya so ni, ya kaunace ni ya nuna min gata, ya sauya lissafina ya banbanta ni a cikin dangina, kuma ya tsaya tsayin daka ganin yan'uwansa sun nuna min girmamawa da kauna, ni kuma ba zan yarda na bata wannan alakar ba, ba zan saka masa da mummunan sakamako ba”


Na sake dubanta irin duba na kokarin tantance gaskiyar mutum da akasinta. 


“Baki kishi ne?”


Kamar jira take na yi mata tambayar sai hawayen da ke makalle a idonta suka zubo mata. 


“Ina yi mana, musamman da na san ke din budurwa ce yanzu ne MiJina zai yi auren budurwar da saurayi, domin ni a bazawara ya aureni, Wallahi Noor Barrister mutumen kirki ne idan kika yi rasa shi kin yi babbar hasara...”


Ta share hawayenta, ta dafa kafaduna duka biyu. 


“Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa, damuwarki tana saka shi a cikin damuwa shiyasa ana dag da auren nan yake ta nanata min yana son ya janye, babu amfani kuka a public place kamar wannan, idan ma zaki yi ki bari sai kin kebanta kinji”


Na daga mata kai daman tuni hawayen suka tsaya min saboda mamakinta. Kalamanta kuma sun karfafa min guiwa duk kuwa da kasancewar zuciyata bata yarda 100% mijinta mutumen kirki ba ne. Wata kila dai zagon kasa take min. Anyi kwalliya cikin nasara saboda na bada hadin kai, bayan an gama ta dauko min wani farin lace na saka rigar ta yi min yawa sosai saboda jikin nawa ba na irin sauran yan mata bana daman ni duk abun da na saka sai ya min yawa, ta saka na cire tufafin aka fita da su aka rage sannan aka dawo min da su na saka suka min cif. Kowa yabon kyau na yake a falon na kwalliya saboda yadda na yi kyau daurin dankwalin ma kansa abun kallo ne saboda yadda ya tsaru akaina. Gurin da muka boya dazun ta sake boya da ni ta kira mijinta facetime.


“Madam...”


“Barrister ka iya zabi”


“Da na zabo ki ko?”


Ta kauce fuskarta ta kara masa tawa fuskarka. Natsuwa yayi na wasu dakiku ya dauke wuta yana kallon fuskata kamin yayi murmushi. 


“Noor...”


Na kalleta sai ta yi min alama da na amsa. Sai dai ban amsa din ba kuma ban mayar masa da murmushin ba. 


“Please Smile”


Ya fada yana cigaba da kallona, sai na lake masa kafada alamar ba zan yi ba. Sai na ga murmushin dake fuskarsa ya kara fadada. 


“Noor kin yi kyau Maa Shaa Allah, Allah ya muku albarka ke da ita”


Ban ce masa komai ba, amman a raina na amsa da ba Ameen ba domin bana bukatar addu'arsa. 


“Madam...”


Ya kira sunanta sai ta amsa ta yi facing dinsa. 


“Ke ba a miki kwalliyar ba?”


“Yanzu za a min an fara kwalliya wa a amaryar ka ne, na ce bari na nuna maka kamin masu hoto su daukar maka”


“Kin kyauta Allah ya miki albarka”


“Ameen sai ka dawo”


Ta kashe wayar sannan ta kama hannuna muka fito. Sai da aka mata kwalliyar sannan muka wuce a tare zuwa gurin walimar da sun riga da sun shirya komai. Na yi mamakin da na samu dangin mahaifina da wasu daga dangin mahaifiyata har an dauko su an kawo su gurin. A guri na musamman aka zaunar da ni masu manyan wayoyi suka fara wani flash na wayarsu musamman dangin da nake kyautata zaton na Hafis ne ba kuma dan na san su ba sai dan ankon da na ga sun yi kala daya wasu kuma suna kama da shi sosai. Na ga kauna na ga soyayya na ga haba haba na ga marhabun daga dangin Hafix da kuma matarsa na yi mamakin yadda suke ririta ni kamar nice matarsa ta farko, kuma na yi mamakin yadda matarsa ta aje kishi a gefe ta mu'amalanceni kamar kanwarta ba kishiyarta ba. 


Jikina yayi sanyi sosai na tsorota da yadda na same su. Sai bayan sallah Isha'i suka dawo da ni gida domin daga gurin Walimar gidan wata kanwarsa aka wuce da ni na huta na yi wanka aka min gyaran kai sannan suka dawo da ni gida. A gidan na tarar kowa sai yabon halin matar yake da yan'uwan Hafiz har wasu na cewa na dace, indai abun ya bi haka. 














I have few pages for book 2 ragowar Pages din na wadanda suka biya ne.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.