Free chapter · Read without an account
Chpl
by Maryamahmad · DUHUN DAJI
***
Masu tambayar duhun daji daga farko ku following channel ɗin zaku same shi tun daga farko har ma da wasu book din nawa Nagode sosai
DUHUN DAJI
Story and writing by
Matar dear
*GENTLE WRITERS ASSO.....*
*Alhamdulilah nagode sosai da kulawar ku masoyana ina mai farin cikin haɗuwa da ku da na yi mutanen kirki.*
Phone number ***
Bismillahir rahamanir rahim
11&13
Yau kwanan Hajiya shidda a dubai yau tunda wuri "baba ta tashi tafara gyara gida saboda gobe uwar gidan nata zata dawo gida komi zai koma nit ne, tana cikin gyaran dakunan ƙasa riya ta ce ki nunamin inda zan tayaki nima mu sauri mu gama"
A'a "riya ki bari duk yanzu zanga ma in sha Allah, sai da riya ta shawo kan baba da ƙyar ta amince ta kaita ɗakin sama ta nuna mata ɗakin shakatawa idan zata huta ta ce to ki gyara iya nan ma kawai Nagode kinji riya ta' ta aje mata mofa da tsinstiya duk abinda ya kamata ta aje mata shi kuma kafin ka ce mai tana daga zaune sai ga daki ya dawo fessss dashi ta tashi duk wani daki da ke sama sai da ta gyara shi ya dawo da hasken shi, sai ga ta a ƙasa inda baba take duka ɗaki biyu ta gyara kuma Kusan dakuna biyar ne ai ko tai maza ta gyara baba tana shiga tai ta mamaki da yaushe ta gyara wannan ɗin bacin bata zo ba haka dai ta bar zancen da ita ta gyara sai ga riya tana kwala kiran baba nagama"..
______________________________
Tunda ga ranar"Alhaji yake Amfani da ƙare kuɗi ko sai hauwa hawa suke ga mulki da yake kai wanda yanzu haka ana neman ƙara mai girma, shidai tunda ga time ɗin Muhammad ya daina Amfani da kuɗin dady ɗin sai na shi da yake business kuma Allah ya daukaka mashi shi don har gidan marayu yana dashi da almajirai da yake taimakamawa matsalar shi ɗaya club ɗin da yake zuwa sai dai baya neman mata illa kawai shafe_shafe da suke aikatawa baya shigar macce"
Kamar kullum yau ma " dady ne ya fito yana ma momy sallama domin zai tafi Ingila wani aiki ya taso mai zapi, sai ga md ya fito ya mashi Allah ya tsare tare da fita domin zai tafi office ne nan ya barshi shi da momy ya tafi"
Kwana biyu da tafiyar alhaji cikin dare ƙarfe 2 dai-dai "Muhammad ya fito sanye da jallabiya ya dan rike kasan saboda sauri ya nufi ɗakin dady abuɗe yake dakin yana ta binciken dakin amma bai ga komi ba wannan ɗakin da yake kusa da bayi ne kulle babu mukullin shi ya duba sama ko ƙasa babu shi can ya duka karkashin gadon alhaji sai ga wata tunkunyar ƙasa babba amma ba ta ita yake ba shi dai mukullin nan kawai yake san gani can ko ya hango shi kusa da tukunyar an lullubeshi da takarda ya dauko shi ya nufi ɗakin yana buɗewa gaban shi sai faduwa yake kamar me sai addu'a yake ko wacce kala tazo mai yin ta yake"
**********************
Ko da baba suka gama gyaran gidan suka shiga kinchin don daura abincin rana" riya ta ce kije ki kwanta nima zanyi girkin Yau don Allah ki barni baba"
Murmushi "baba tai ta ce riya keda baki iya ba ki bari na yi kinga kada su ameer ɗin su kicin abincin ma fa."
Allah baba na iya kawai dai ki kawo ki huta nasan nai girki yau sai kowa na gidan ya dunga lashe hannu saboda daɗin shi.......
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai md ke maimaitawa saboda abubuwan da yagani cikin ɗakin masu uban tsoro, wata akuya a kulle gabanta duk ya buɗe sosai saboda amfanin da ake da ita ga wani mutum da yake fitar da kuɗi ta bakin shi kamar an kunna famfo, wata akuya kuma fitar da jini take ta tubu rar ta yana zuba a cikin wata roba wanda ba asan ranar cikarta abubuwa dai kala_kala ne cikin ɗakin nan ya kulle ɗakin kamar bai buɗe shi ba ya maida mai mukullin shi inda yagani duk abinda ya taɓa ya maida shi inda yagani kamar bai gani ba, ya fito yana ta barza kuka Kamar ƙaramin yaro ya tafi daki yana mai nema ma Alhaji yafiya wajen Allah, Allah sarki md ya fada koda da safe da ya tashi "momy ya tambaya wai yaushe dady zai dawo ne?"
Tambayar shi tai "Muhammad Lafiya ko wani abu ya faru da shi ne ban sani ba?"
A zuciyar shi kuwa ya ce komi ya faru momy na Allah ya sa dai bai sa maki cuta ba a fili kuma ya ce" nooo momy kawai dai ina so na bashi mamaki ne ta hanyar canza mana fentin gidan da kujerun gidan da albashin da na samu!"
Murmushin jin daɗin tai tare da faɗin ina tunanin zai kai 1month a can......yau to gobe zaki tashi daga gidan nan suma yau ma aikatan duk na sallame su Yau, haka akai duk wata hanya da Alhaji zai same su ya bi ya daƙile ta karshe ma can j.r.a. ya sai gida mai bala'in ƙyau ya buɗe wani bank ya kwashe kuɗin duk ya maida asabo ya number alhaji yasa ta Black list duk dai wata hanya ya rufe ta da zata sada su su haɗu dashi..
...................washe gari ma suka ƙara gidan ƙarfe 12am jirgin su "hajiya ya sauka su Ameer ne suka ɗauko ta koda aka zo za ai mata sannu da zuwa har ameer ya kalli riya zai faɗi wacece ita ta mantar da shi komi kuwa aka shashantar da zancen shi kenan"
Da daddare ne "baba taje tai ma Hajiya bayanin wacece riya da Farko da ta ce ina ba dai gidan taba sai kuma ta sakko ta hakura"
Abangaren kuwa "maman Zarah duk ta fice daga haiyacin ta miji ba kula shine ta ce ita dai zata fara aikatau don ta riƙa cin abinci, Allah sarki abun tausai haka tafara karshe biba taje ta zuga bata da hali shi ne suka sallame ta gidan aikin yanzu ba inda take zuwa aiki illa abinda aka sanmata ta ci, yanzu dai tana neman malam ya barta ne ta tafi birni aiki"
Please continue