Free chapter · Read without an account

Page 08

by Safiyya Haruna · Page 01

ZUCIYAR REEMA

© Mrsjmoon.


Page 08.


Tana nazarin abinda zatayi masa ta samu komawa mazauninta ta tsinkayi MC nabada umurnin su koma mazauninsu dan hutawa, ajiyar zuciya ta sauke tare da kai ƙafa ta take masa yatsu duk da tana da tabbacin ba zai ji ba sakamakon takalmin da ya saka cover shoe ne.


Siririn dariya ya saki tare da rungumota gefenta, ta sharesa dan batayi nufin janyewa ba, suka cigaba da takawa har zuwa mazauninsu, sai da ya zaunar da ita sannan ya zauna yana sauke mata wani kallo na sai kin raina kanki amma ga dubin mutane ba abinda suka hangowa sai kallan zallan ƙauna domin har da tafi suka sanya suna ambaton fatan khairan garesu.


A zahiri Sagir yafi Saifullah bawa matarsa kulawa Wanda jama'a suka soma tsegumi wai kamar Auren dole akayi musu amma abinda basu sani ba shi d'in mai kunya ne wanda taron jama'a na hanashi sakewa, ita kanta matarsa ta san da haka shi yasa sam yanayin bai dameta ba tunda bini-bini kan sunkuya ya ce mata "Affuwan, I love you." Shi yasa fuskanta yake cika da annuri.


A haka aka cigaba da gudanar da shagalin cike da natsuwa, Sagir ya takura Reema iya takura duk dan ta fitar da abinda ke zuciyarta kowa ya gano abin da take b'oyewa na k'in auren amma ta nuna masa bai isa ba.


A gefe ɗaya kuma Nawwara ta kasa ta tsare tana aikowa Sagir da kallon ƙauna wanda yana hankalce da ita sai ya riƙa jin nishad'in takura Reema da ababen da bata so cikin dibara batare da kowa ya sani ba sai kuwa Nawwara da duk motsinsu na kan idon ta, ta samu kanta cikin farin ciki hango fuskansa gami da hankalinsa na kanta har take jin mallakansa ita kaɗai ba zaiyi mata wuya ba tunda gashi tare da Amaryansa amma ya maido hankalinsa kanta.


Haske wayar Reema ta yi ta kai hannu zata ɗauka ya rigata sai ta take masa ƙafa da ƙarfi ya saki wayar ta cafe ta cilla cikin pose d'inta gami kallonsa ta kashe masa ido ɗaya ya kuma kaiwa waist d'inta cafka wanda tun d'azun hannunsa ke wurin na neman magana ta d'an zabura cikin sauke masa kallon kashiga hankalinka ya lumshe ido ya ware a kanta sai haske plash ya soma tashi ta kalli Jama'a fuska a sake suka haɗa idanu da Sanaaya tayi mata jinjina da babban yatsa sai ta murmusa gami da sauke kallonta kan 'yan matan da suka zo daga dangin Mahaifinsu suka riƙa d'ago mata hannu fuskokinsu cike da Annuri sai taji wani farin ciki na daban ya nashe ruhinta ta waiwaya gefen Nafee suka sakarwa juna murmushi sai dai kallon da Saif ya tsareta da shi ya sanyata jin fad'uwar gaba, ta kauda kai tare da kamo hannun Sagir ta matse suka tsirawa juna ido ta motsa lips a hankali ta ce "Mu tafi gida kaina ciwo."


Maimakon ya yi magana sai ya janyota jikinsa ta janye da sauri tana ware idanu, tafin da ya karad'e wurin ya ankarad da ita waftar da tayi na bawa kura ajiyar nama. Kunya ce gami da takaici ya mamayeta ta sunkuyar da kai ta d'auko wayarta ta duba sak'on da ya shigo.


'Kinyi kyau sama da kowa da ke wurin k'anwata.'


Lumshe idanu tayi tana jin rashin jin daɗin halartansa taron.


'Nagode kuma nayi kewar ganin fuskan shanun nan naka mai razana kowa amma banda Khareematun Ummie, na so ace kana wurin Babban Yaya.'


Ta tura masa tana sakin murmushi mai sauti, Sagir ya dubeta na son gano dalilin walwalanta. 


'Idan kinkoma gida zamuyi magana fuska da fuska domin nima nayi kewar fuskan tsiwa da idanun rashin tsoro haka ina da magana mai mahinmanci da ke.'


Wanan karan siririyar dariya ta sanya tare da matse wayar a tafin hannunta tana jin wani abu na sukar tsokar naman zuciyarta.


"I really miss you."


Ta ambata tana tsotsan gefen lip d'inta, kallonta Sagir yakeyi cike da jin kishin fitar kalman ga waninsa duk da baijin damuwa da ita wanda zai kai matakin kishinta amma da ya ji kalamin a kan waninsa ya sauka ya k'ona masa Rai. 


"Best friend dinmu ce ko?"


Ya sami kansa da jefo mata tambayar duk da ya san ba hakan ba ne.


Banza tayi da shi tana ci gaba da doka murmushi sai ya ji gabansa ya fad'i ya juya kai gefe idanunsa ya sauka kan Nawwarah ta sakar masa murmushi tare da yi masu signer cike da barikanci ta hanyar nuna masa k'irjinta da harshenta, kauda kai ya yi najin buk'atuwar son kasancewa da ko wacce irin mace ce na bijiro masa amma da ya tuna ya kusa mallakan Amaryansa sai ya sami kansa da ambaton kalaman tuba. Ya juyo ya manne da jikin Reema na sake wadata fuskansa da walwala. Ta so janyewa amma ya hana mata damar hakan lamarin da ya fusata Nawwarah ta fice daga wurin cike da alwashin jik'awa Sagir aiki ta inda baiyi zato ba.


"A shawo ta wuce bazaka biya ba?"


Ta ambata ba tare da ta kalle shi ba."


"Kishin ganinta kikeyi kenan?"


"Dana gama asaran rayuwa na yi kishin wanda bai san ciwon kansa ba."


"Wallahi duk ranar da kika shigo hannuna sai na lahira ya fiki jin dad'i dan haka ki saita kalamanki kada su janyo miki ganin masifun da basu da iya ka."


"Har a kwai sauran masifa da ya ragemin na gani daga gareka bayan wanda ka ganamin kashi da kashi? To ka sake shiri domin Nima na tanadi kalan nawa jafa'in da zan janyo maka ciki har da bawa a shawo d'akin kwana a gida daga nan kowa ya gano fuska biyunka, azzalimin banza, mugu kawai, wallahi na tsaneka har cikin ruhina."


Tsuke fuska yayi cikin cije lips amma tunowa a taron jama'a suke sai ya saki fuska na doka murmushi tare da kallon fuskanta ya furta "Ina sonki da gaskiya my love."


"Iskana na wahalar da mai kayan kasa."


Ta furta cikin murmushi tana kallo cikin danunsa.


***

Lamura ya cigaba da gudana cikin tsari mai burgewa zuwa can aka sake bawa Amare da Angwaye damar da su ciyar da junarsu, Saif ya d'ebo cake da yafi k'arfin bakin Nafee ya tura mata ta rungumeshi tana goge masa a jiki, aka saka ihu gami da tafi, ya sanya hannu na taping bayana tare da rada mata "Zan kula dake fiye da haka iyalina domin kafin ki nemi abu zan ranadar miki."


Jinjina kai tayi tare da d'agowa ta d'ebo itama da yawa ya wage baki ya amshe duka aka sanya tafi. MC ya bud'e murya na cewa "To masha Allah, alamu ya nuna dai ma'airatan zasu bawa juna kula yarda d'an uwansa zai rasa gane waye gwani a fannin, Alhamdulillah haka muke fata, aure ya yi dad'in da baki zai kasa kwatanwa."


Bayan anyi shewa da nishad'i ta hanyar sakin sauti sai aka dawo kan su Reema inda Sagir ya d'ibo daidai misali ya bata ta gutsiri kad'an cikin kallo idanunsa, akayi tafa, sai itama ta d'ibo mai yawa, sai da ya bud'e baki zai amshe sai kawai ta tura abakinta tare da yayyafa masa b'urb'ushin na ganinta a bakinsa. Tafi da ihun da aka saka ya zarce tunani sai ambatan kalman "Weldon " Ke fita daga bakunan mafi yawan 'yan mata da tsirararun Samari yayin da MC ya kasa cewa komi sai baki da ya saki na tattaro sharhin da zaiyi. Bai samo abin cewa ba ya hango Reema ta rungume Sagir tana goga fuskanta a k'irjinsa aikam a hanzarce ya soma magana cike da samo abin ambata "Oh ya Allah, wannan k'auna abar koyi ce wato Amarya Reema dai ta b'oye kalan kulawan da zata bawa Ango Sagir, hak'ik'a ita d'in matar sirri ce, kai tubarkallah masha Allah, abu ya yi armashi , ya rabbi ya bar k'auna mara algus, Angwaye da Amare."


"Amin!!!."


Wurin ya d'auka.


"Wallahi ko ruwa bazan tab'a baka ba dan haka ka shirya yiwa kanka komi kafin burina ya cika a cikin satin da aka kaini akulkinka domin bazan kisa da sunar gida ba."


Abinda Reema ta ce da shi kenn sadda ta rungumeshi.


"Kasheni zakiyi kenan?"


Ya cillo mata tambayar cike da tsoro.


"Relax mr. man, ni ba 'yar ta'adda ba ce amma dai tabbas burina zai cika a satin dana tare a gidanka in ko kaga bai cika ba to ban wuce kwanakin wata ban sami cikar burina ba, wannan a rubuce ya ke, ka ajiye a brain d'in ka."


Daga haka ta sake shi suka zauna cikin walwala tamkar wanda sukayi musayar kalaman k'auna. Tsoro ya bayyana a fuskan Sagir wanda ke kokarin b'oyewa amma tsaf Reema ta harbo jirginsa.  


"Uhm malam Sagir wuyar aiki ba a soma ba."


Ta ambata a hankali, banza ya yi da ita tamkar bai ji ba sai dai ya shiga nazarin matakin da zai d'auka kafin ta rigashi nasara.


***

Sai da aka soma kiran sallah magriba sannan a tashi cike da farin ciki. Tamkar wal'kiya haka Reema ta bacewa ganin Sagir ya ciji yatsa cike da takaici domin ya k'udurce yaga mata mutunci ko ta halin tsiya a wannan daren dan har ya sanar da abokinsa ya bashi key da ga shi sai amaryansa zasu koma. Haka yayi ta raba idanu ko zai ganta Amma har motocin gidansu suka gama wucewa bai ganta ba komawa ciki ya yi na sake dubata amma still babu alamarta wanda ita kam a lokacin ta kusa isa gida tare da Sanaaya dan tana zillewa wurin Sanaaya ta isa jikinta na rawar sanyi wanda ta k'irk'iro aikam kafin tayi magana ta ja hannunta suka fice zuwa motarta sai da suka hau kan titi sannan ta sanya dariya tana cewa "Lafiyata lau Aunty kawai na gaji da rashin kunyar k'aninki ne nayi miki haka wanda in da na fad'a miki gaskiya wallahi bazaki amince ki kawoni ba dan cewa zakiyi mukarata ta rashin kunyarmu."


"Allah zan kawoki k'anwata saboda nafahimci k'enen nawa basa da ta ido wai har da barrister ya iya rungume matarsa a gaban jama'a kai yau nagama gamin abinda ya isheni, dama ke da Sagir wannan banyi mamaki ba tunda ko gaban waye kiran juna kukeyi da kalman k'auna."


'Uhm 'yar uwata kenan, ina da buri babba da ace zaki maramin baya da ke ce ta farko da zan sanarmawa sai dai kash bazaki tab'a fahimtata ba dan haka sai na aiwatar zaki ji, wata k'ila ki dukeni ko fushi da ni.'


Jin shirunta yayi yawa yasa Sanaaya ta b'ata ta sauke ajiyar zuciya tare da kafeta da ido.


"Meke damunki?"


"Tunanin rabuwa da Ummiena."


"Inaga zan cewa Abba a sakaki a plat d'in da ke kusa da part din brother AB kinga kullum kina tare da Ummie, tunani ya k'are."


"Ka da ki soma aikata hakan saboda k'aninki zai ta kura."


"Ja'ira kidai ce zaku takura."


Wuya kai gefe tayi tana murmushi wanda ke k'ara mata kunci a ruhi. Suna isa gida ta fice da sauri tana cewa "In tserewa hukuncin k'aninki amma dan Allah kice kece kika janyoni da k'arfi ba tare da raina ya so ba."


Dariya Sanaaya ta raka bayanta da shi tana motsa kai.


A d'akinta ta yi masauki gami da kulle k'ofa ta fad'a saman gado gami da fashewa da kuka mai d'auke da tarin damuwa. Sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta cire kayan jikinta ta koma da ga ita sai bra da legis, kirane ne ya shigo wayarta ta kalla sai ta sauke ajiyar zuciya ta janyo madai-daicin hijab ta saka sannan ta d'auki wayar.


"Har kinyi sallah?"


Ya ambata mata murya can k'asa."


"No."


"Why?"


Shiru bata amsa ba.


"Kin riga kowa dawowa gida Amma har zuwa wannan lokacin baki gaisar da mahaliccinki ba? Anya Reema Auren nan naki da Khairan kuwa? Kece fa mai tunashe da kowa lokacin sallah ya yi idan aka shagala da hira amma ace yau kina halin lafiya ba laluranku na mata kike ciki ba, kin kasa yin ibada balle ki roki mai amsa buk'atun bayi nasara a duk kan lamuranki gami da samuwar kwanciyar hankali a gidan aurenki?"


"Affuwan Yaya yanzu zanyi wani lamari ne ya sha kaina."


"Mene ya sakaki kuka?"


"Ni banyi kuka ba."


Murmushi ya Mai sauti yayi tare da cewa "To da kin idar ki kirani vedio call muyi hirar mai ban al'ajabi."


Bai jira amsawarta ba ya datse kiran, tayi tsam tana kallon wayar zuwa can ta mik'e ta fad'a toilet cike da kasala. Ko da ta idar da sallah sujjada ta koma tayi ta jero addu'a wanda bai wuce samun nasara a cikar burinta ba. Sadda ta d'ago hawaye da majina sun bata mata fuska, tissue ta d'iba ta goge fuskan sannan ta gyara zama a gefen gado talatsa number Abdul basit cikin jin bugawar zuciya. Yana zaune shima gefen gado na latsa system kiran ya shigo ya daga gami da sauke dubansa a kan fuskanta da a bayyane ya nuna kuka tayi bada jimawa ba.


"Amarya haka zamuyi da ke?"


Ya ambata a hankali na sake k'ureta da kallo. Kauda kanta tayi gefe cikin murmushi ta ce "Barka da wannan lokacin, ya Madeena?"


"Alhamdulillah amma ba lau ba."


A razane ta kalle shi ya lumshe idanu na motsa mata kai gami da cewa "Bakiga na rameba? Nayi kashin wuya kuma nayi duhu, to bana samun barci ne, k'anwata ina jin dama ban zo ba, dama nayi zamana a gaban su Abbie ko halin da nake ciki ya ragu."


"Ya salam meke damunka Yaya?"


"Abinda ke damunki."


"Tsam tayi tana kallonsa a d'an tsorace.


"Yes cutar da ke damunki shi ke damuna domin baya da magani sai Allah."


"Nikam lafiyata lau yaya."


Ta ambata cikin rawar murya."


"Karya kikeyi khareematu, na san karatun ruhinki tun kina k'arama haka har yanzu bai sanja ba kamar yarda nawa ya gaza sanjawa duk da na san bakin alk'alami ya bushe."


Shiru ya ratsa sai ajiyar zuciya Abdul basit ke saukewa da k'arfi ya yin da Reema ta soma kuka mara sauti.


"Kidaina d'igamin dalma a zuciyata Reema domin zan iya komawa gadon Asibiti idan har kika cigaba da yimin wannan kukan."


Cak da d'auke kuka tare da kafeshi da idanu bakinta na rawa ta ce "Ciwon mene kakeyi Yaya?


"Wanda ki keyi shi ne kika sanmin."


Kauda kai tayi gefe tare da cewa "You mean ciwon so?"


"Yes but nawa ya zarce so sai dai a kirasa ciwon K'auna tunda na son rab'amin lafiyar zuciya."


Kallonsa takeyi bako kiftawa shima haka. Kowa da karatun da zuciyarsa ke tisa mashi.


"Ciwona ya zamo sirri kinji k'anwata?"


Kai ta motsa tana share hawayen da zuba zubo mata.


"Ban sanar da ke ba dan ki saka damuwa a ranki sai dan ki zamo jaruma akan abinda ba kyaso amma zama da shi farillah ne idan har kina son gamawa da mahaifiyarki lafiya. Reema ki zauna lafiya da Sagir duk abinda kike kitsawa ki yi watsi da shi saboda shi din kaddararmu ne."


Tsit yayi na jan numfashi yayi da kanta ke sunkuye tana jin shigar kalamansa cikin ko wacce tsokar fatar jikinta.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.