Free chapter · Read without an account
5
Hausawa sunce ranar wanka ba'a boyan cibi, kuma duk Abinda aka saka mishi lokaci to sai yazo da yardan Allah. Yau take Asabat! shi yayi dai-dai da ranar da Alhaji Goni zai zamo angon Falmata. Tun karfe takwas na safe daya farka yake kirayen waya ta yanda za'a hada liyafar cin Abinci da Manyan bakin sa idan Andaura Aure lafiya.
Sassanyar kamshi mai kwantar da zuciya ce ta bugi hancinsa, A hankali ya daga ido izuwa jikin kofa. Jidde ya gani tsaye ta rike kugu tasha Ado cikin wata danyar leshi da tasha dinki doguwar Riga na gani na fada, hannayen ta da kunnen ta sai walwali suke na adon zinare. Masha Allah Alhaji Goni ya Ambata tare da sauke Ajiyar zuciya. cikin taku irin ta yaudarar Miji ta karasa cikin dakin ta zauna A gefen sa gami da sauke Murmushi "Abban Abie ka tashi lafiya?"
"Lafiya kalau Uwargida sarautar Mata, kuma ruhin zuciyar Goni, irin wannan gaye haka Jidde? Sai kace budurwa? Kin fito ras da ke kamar baki haifi su Abbie ba? Ai sai ki hanani zuwa daurin Auren?" Dariya tayi Wanda ya baiyana kyawawan hakoranta waje "Kana da Abin Dariya Abban Abie! Yau idan ba kaje Auren ba Ai Falmata tayi garin kuli da kai" Dariya yayi ya kama hanunta ya dunkule cikin nasa "Kin manta Ina da wakili ko? Ina daga waya nace masa ba zan samu zuwa ba magana ta kare Jidde, idan kin Amince in kirasa yanzu musha soyayyar mu?"
"Uhum kai dai zancen kake so karka isheni da dadin baki, ya kamata Ace ka shirya harka fita, kasan lokaci bayi jira?"
"Kwarai yanzu nake so nayi wanka, saiki jirani muyi photo ko? Amma ki sani babu wani dadin baki A magana ta, Jidde ina miki so ne irinta dabi'a, So wacce bata karewa, kuma ina da yakini kema irin So da kike min kenan, nasan duk rinsti duk wuya Jidde kina tare dani Jidde, ko Akwai Arziki ko babu Arziki, bani da kamarki Jidde ta".
"Uhumm Abban Abie kenan, barin hada maka breakfast kafin ka fito ko ?"
"Aa kinsa Akwai lunch da zamuyi idan An daura Aure! so A can zanci Abinci kawai ki kawo min Lipton"
"Ba matsala Ango" Ta fada gamida mikewa tayi waje, murmushi yayi ya bita da kallon So da kauna harta fita A dakin, Ajiyar zuciya ya sauke ya fada toilet ya watsa Ruwa, yana fitowa ya samu ta Aje mishi Lipton akan table ta fita. A gaggauce ya samu yasa kaya yasha Lipton din ya fito, lokacin karfe Tara ta gota, Kai tsaye dakin Jidde ya nufa, Saddiqa ya samu tana kara gyara dakin sabida bakin daza suzo, har kasa ta durkasa tace "Barka da fitowa Alhaji?"
"Yauwa barka Ina Matar gidan?"
"Suna harabar gida". Ok yace ya fice A dakin ya nufi waje, A jikin flowar ya hango Jidde da Hafsa sai photo suke da Yara, tun daga nesa Sabriya ta hango Daddyn nata, hakan yasa tasa gudu ta nufo garesa. shafa fuskarta Yayi "Sabriya ya Akayi dai?"
"Daddy wai yau za'a kawo mana Aunty inji Mummy?" Dan murmushi yayi yace "Aunty Falmata ce zata dawo mucigaba da zama"
"Laa Daddy Aunty Falmatan gidan Hajja? Wacce take mana tsiwa?" Dariya yayi "To Ai Baku jin Magana shiyasa take muku fada".
" Daddy? "
"Barin karasa wajen Mummy ko?" Kama hanunta yayi suka karasa jikin Flower, Hafsa tana ganinsa ta gaishesa cike da ladabi ta koma gefe ta zauna. Haka Alhaji Goni ya fito da wayar sa ya dau lokaci yana daukarsu selfie kafin ya shiga Motor ya nufa wajen dauren Aure. Jidde tana ganin ya kule wa ganinta taja Hafsa suka nufi cikin gida, kai tsaye dakinta suka nufa, suna zama Hafsa ta dubeta "Aunty Jidde nifa ban fahimci inda kika dosa ba! wai ke baki gayyoto kowa bane? Anjima da la'asar fa kika ce Amarya zata iso? Ai ya kamata Ace iwar haka Jama'ar ki sun cika gida?"
"Huhmm Hafsa kenan, kina dai ganin Abinda su Halima sukamin Agaban idonki, yau idan na gayyoto jama'a akazo aka wulakantani in kallesu da wacce ido? Saratu ce kawai na fada mata, domin Akwai Fahimta tsakanina da ita"
"Huhmm Lallai Sannu Aunty Jidde? Amma wallahi....
"Bakomai Hafsa zai wuce kiyi shuru kawai" Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke zuciyarta nayi mata zafi, ta kuma dauki Alwashin sai dai komai ya faru, Amma duk wacce tazo gidan ta fada musu bakar magana sai ta mayar mata. basu wani dauki lokacin suna zaune a daki ba Saratu ta samu isowa. Tun shigowarta Palon gidan take mamakin ganin gidan babu kowa, tana shiga dakin Jidde da tambaya ta soma "Maman Abie wai ya gidan haka shuru? Ko sai gobe Falmata zata iso dakin Mijin nata?" Murmushi tayi ta dubi Saratu "Kiyi hakuri ki zauna dai sai muyi magana?" Zama tayi a gefen Hafsa "Ina jinki?"
"Saratu tsoron Abinda zai biyo baya nake, kar su Halima suzo su kunyatani A gaban Jama'a ta, wallahi shine dalilin da yasa nayi fada ma kowa"
"Huhmm tadjima wato duk Maganar da mu kayi dake ranar baki jiba? Na fada miki Uwar Miji ce kawai za kiyi hakuri da duk Abinda zata miki, Amma wallahi banda kannensa, akan miye? Ko wata shegiya tana dakin mijinta tana jin dadin zamanta saita tazo tace zata daga miki hankali? To wallahi gwara ki cire wannan Akidar a zuciyar ki, idan ba haka ba Falmata sai taci tuwo A saman kanki kinji na fada miki, Haba Jidde?". Fuska dauke da damuwa Jidde tace "Ba zaki gane ba Saratu, duk Abinda zai bata ran Alhaji ina kiyayewa, bani son Abinda zai hadasa da Hajja".
"Dakata Uwar bayani?Kannen suzo har Inda kike su nemi ci miki kashi Akai sai ki barsu sabida Abban abie? To bari kiji? Mahaifiyarsa ce kawai zaki amsa mata Ran Abban Abie ya baci, Amma banda wasu taron Yan iska, ni dai yau ina gidan nan wallahi duk wacce tace miki kule zance mata Cass"
"Kwarai kuwa Aunty! Cewar Hafsa, nima Abinda na gama fadi A zuciyata kenan, wannan irin Ruwan ciki har ina? Wallahi ranar ba kiga abinda su kayi mata ba, Amma sabida na Amsa harda marina, kuma hakan bashi zai saka tayi farin jini A wajen su ba".
"Gaskiya Jidde Akwai gyara, Allah ya kyauta kawai" Kalmar Hakuri da baza ku fahimceni ba shi ka dai take fada musu.
Bangaren Amarya Falmata kuwa Ansha gaye fuskar nan ta koma kamar balarabiya, gaba daya ta kasa zama waje guda, kunnen ta makale da waya suna magana da Babangida yana sanar da ita abinda yake wakana A wajen daurin Aure. Ana daurawa kuwa Babangida ya sanar da ita an daura tasa ihu ta nufi dakinta inda taron Kawayenta suke, cike da murna tace "Andaura wallahi"
"Kai masha Allah Amarya A gidan Alhaji Goni, to Allah ya bada zaman lafiya, shikenan Falmata kin zama hamshakiya, Saudi duk shekara?" Cike da jin dadi tace "Kwarai Kuwa ku fada ku sake fada" Haka dai ta zauna suka cigaba da raha har akayi kiran Azahar. Falmata tana fitowa da niyyar zuwa harabar gida suka hadu da Gwaggo A Palo "Yauwa wajenki zanje, kizo gasu Hajja Naja sunzo suna son ganinki! Maza hanzarta" To Mama ta ambata tayi dakin Mahaifiyarta bakinta dauke da sallama, waje ta nema ta zauna ta dubesu "Anyini lafiya?"
"Lafiya kalau Falmata suka Amsa a tare, ya gida ya hidima? To Allah ya baku zaman lafiya" Murmushi tayi ba tace komaiba. Hajja Barira ce ta dubi Falmata "Kin san dai ke ba yarinya bace da za'a zauna Ana fada miki miye za kiyi a gidan Aure? Kinyi Aure shekara kusan takwas kike nema A dakin Miji, kinsan miye Ake nufi da Aure. To Falmata ya zama dole mu fada miki gaskiya sabida Mahaifiyarki duk duniya bata da aminai sai mu, ke tamu ce ya zama dole mu dauraki A hanya ta gaskiya, sanin kanki dai Surajo yayi hakuri da wau ban zan halayya taki da kika tsiro dashi shekara daya zuwa biyu, wallahi Falmata idan wancan Rayuwa da kikayi a gidan Surajo shi za kije kiyi a gidan Alhaji Goni to muna tabbatar miki za kiyi nadama. Kin san dai auren hadi Akayi muku, ba wai ya ganki bane yace yana so, to yana da kyau kiyi karatun ta nutsu wa kanki, ki zama ta gari ki jawo hankalinsa gareki, kin samu Miji wuce sa'a Falmata. Magana ta gaba tsakaninki da Matarsa ganin girma da Arzki, Ku hada kanku ku zauna lafiya kuba Mijin ku farin ciki, kinga gidan su Surajo? Hajja Luba ta Ambata, har gida aka kawo min gulmar Ashe wai sabida mugun nufi yasa kika dage sai kin kashe Auren, sun sami labarin Ai Alhaji Goni tun kina budurwa aka so kuyi Aure Amma ki kace sam, sai yanzu da kika Gansa ya zama daya daga cikin masu kudin garin nan shine kika San hanyar da ki kayi kika kashe auren ki, to wallahi Falmata ki nutsu ki Ajiye duk wasu munanan hayalla don kiba marada kunya. Kwarai kuwa". Suka Anbata gaba daya "Insha Allah nayi muku Alkawari za kuga canji"
"Yauwa Falmata Allah ya miki albarka" Ameen ta Amsa. Hka dai suka cigaba dayi mata nasiha har Gwago Hajara ta shigo, nan itama ta tofa albarkacin bakinta Akai.
Alhaji Goni kuwa bayan sun gama lunch da Abokan Arziki nan ya lissafa Aminansa kamar guda goma suka nufi gidan Gwaggo Hajara gaisuwa. Falmata da Kawayen ta suna daki su kaji Mai gadi yana shelan Hajiya ga baki sun iso ? Da sauri Falmata ta bude labulen window tana duba suwaye, tana hango Alhaji Goni cikin farar shadda yasha kyau tamkar bakin balarabe ta dafa kirji gamida runste ido. Masha Allah ta ambata ta dawo ta zauna "Ango ne suka iso da tawagarsa"
"To alhmdullah bari mu fita mugaisa mu karbi rabon mu" Murmushi kawai Falmata tayi.
A babban Palo suka yada zango, Gwaggo da Aminanta guda uku suka fito fuska A washe suka nemi waje suka zauna. cike da ladabi suka gaishesu, godiya Aminan Gwaggo Hajara su kayi, nan dai suka danyi mishi Nasiha akan zaman takewa A matsayin su na Mannya, nan kwawayen Falmata suka fito suma akayi gaisuwa dasu, sai wani washe baki suke ko za'a basu kudi. tsawon Mintuna Ashirin suka dauka kafin su kayi sallama suka fito.
Gidan Hajja suka nufa! nan suka samu Anyi decoration idan an dauko Falmata a tsaya A danyi liyafa, daga nan sai A wuce da ita gidan ta. gaba dayan su dakin Hajja suka nufa, tana hakimce A kujera su kubra da Kawayenta suna gefe suna kwalliya, suna ganinsu suka mike suka bar dakin, gaba daya A kasa suka zube suka mika gaisuwa, fuska dauke da Annuri Hajja ta Amsa "Yanzu Gwaggon naka take sanar dani kunje Ai, Allah yabar zumunci ya muku Albarka"
"Ameen ya rabbi Hajja"
"Karfe uku na keso aje a dauko min Falmata, sannan su Halima za suje suga dakin nata ko Akwai abinda za'a kara a ciki"
"To Hajja bakomai duk yanda ki kace haka za'ayi"
"Yauwa Allah yayi albarka"
"Ameen". Suka Amsa basu jima A dakin ba suka yi mata sallama suka koma masauki.
Bayan fitar su Hajja ta kira Halima akan su tafi gidan Alhaji Goni su gano mata dakin Falmata. To Halima tace ta fita ta hada kan sauran kannenta suka dauki moto suka fita.
Jidde da Saratu da Hafsa suna kallo A palo su kaji an hankado kofa, kallon Raini su Halima suka bisu dashi, daga karshe su kayi musu tsaki suka haura sama "Iyeeee? Tabdijam wa'innan fa?" Cewar Saratu "Kannen Mijinta Wanda su kazo suka zageta tsaf na Amsa ta mareni akan su".
"Ikon Allah Lallai Jidde, to wallahi Yarinya ta fito ta sake min tsaki sai dai duk Abinda zai faru ya faru, wannan Ai wulakanci da rashin tarbiya ce.....