Free chapter · Read without an account
13
"Allah ya muku albarka wallahi naji farin ciki a zuciyata naganin ku haka? kai Alhmdullah masha Allah" Ledar kazar da suka zo dashi Falmata ta ajiye a gefen Hajja "Ga wannan nace bari in sayo miki nasan zata burgeki Hajja ta" Jawo ledar Kazar tayi "Kai Falmata dawainiya haka? Allah ni zuwan da ku kayi ma naji dadin sa sosai, kuma sai ga dawainiya? To Allah yayi Albarka"
"Ameen ya rabbi"
"Yauwa nace ka fada mata zancen Yar Aiki kuwa? Ya kamata nanda kwana uku zuwa hudu a samu tunda Akwai halin daukowa, ta wajena nayi magana wa Larai ko ta wajen su za'a zamu Yarinya? Tace akwai wata Yar Yayanta A biuw zata kira taji ko zai bari, Amma ke ta wajenki akwai ne Falmata?" Murmushi Falmata tayi "Aa Hajja kina nan Ai bazanyi karanbani ba nasan zaki nema min"
"Allah ya miki Albarka".
"Ameen! wayar Falmata ce tayi Ringin, ganin number Gwaggo Hajara yasa tace ina zuwa Hajja Barin Amsa wayar Mama?"
"To Falmata dazu munyi waya da ita ki gaisheta"
"Za taji insha Allah" Ta Ambata ta fita "Ina su Sabriya? Ya labarin Maigida A makaranta?"
"Lafiyan sa kalau Hajja ya kusa dawowa huta insha Allah, naje na dubasa kwanaki ya danyi rashin Lafiya, Amma da sauki"
"Subnallah shine babu labari? Ai ko Halima da sunje sun duba shi?"
"Bakomai Hajja nima na wadatar Akwai nisa wajen"
"Hakane to Allah ya bashi Lafiya"
"Ameen ya warke Ai, Jidden ma na biya mata oumra nanda kwana shida zata tafi insha Allah" Kama baki Hajja tayi "Ban gane ka biya Mata Oumra ba? Ita Falmata ba Mutum bace kenan? Jidde sau nawa tana zuwa Aikin Hajji? Oumra kuwa tunda ka sami dama ko wata Azumi a can take rabi, Falmata ce ya kamata taje ba Jidde ba, wannan rashin Adalci har ina? Ka canza magana gaskiya, koka biya musu dukansu ko kuma Jidde ta fasa zuwa, akan me?" Ajiyar zuciya ya sauke "Hajja kiyi hakuri Maganar zuwan Jidde oumra tun kafin asa Aure na da Falmata mu kayi, nine nan nace ta bari ayi biki a gama kafin taje, Amma da A son ranta ne da yanzu tana can, ita Falmata tunda Allah ya hada dole za taje Saudi, kiyi hakuri Hajja banyi da nufi ba?"
"Dakata? bance kayi da wata nufi ba, Amma ya zama dole ka hada da Falmata tunda kana da halin haka, ita da take Amarya itace ya kamata taje Saudi wallahi" Ta karashe Maganar tana hura hanci "Kiyi hakuri Hajja zan biya wa Falmata idan har hakan zai faranta miki rai"
"Kwarai kuwa! Farantawa sosai ma"
"Allah ya huci zuciyarki"
"Ameen, Falmata ce ta shigo ta zauna gefen Hajja, Yauwa Falmata ki fara shiri zaku tafi Oumra ke da Jidde wata sati" Dafa kirji Falmata tayi "Hajja Oumra?"
"Eh dama Matarsa za taje nan da kwanaki shida, shine nace kawai ya hadaku duka ku tafi tare"
"Kai Alhmdullah wayyo Allah, Amma nagode Hajja, Yaya Allah ya kara arziki?"
"Bakomai ya amsa, ya kamata mu tafi ko?"
"Gaskiya kuje dare ta fara, gobe duk yanda Larai su kayi da Yayan ta a waya zan kirasa kona kiraki in fada miki, Allah yayi Albarka nagode sosai?"
"Ameen Hajja, Allah ya tashemu Lafiya". Haka suka fito Kubra ta rakosu har Jikin Motor, tunda suka dauki hanya Alhaji Goni baice wa Falmata uffan ba, tunaninsa idan yaje yace wa Jidde Falmata za taje Oumra nan ma wata masifar ce zata kunno, tunda ga irin kalaman da take fada " Yaya Meyasa kake saka damuwa haka a zuciyarka?"
"Bakomai Falmata" murmushi tayi "Haba Yaya ko cewa da Hajja tayi muje Oumra tare da Jidde ce yasa kake damuwa?"
"Sam ba haka bane kawai damuwa ce banso"
"Hakane ko ni akayi wa haka zanji zafi, Amma da zan baka shawara da nace ka biya full family tunda kana da halin haka, hakan zai hana fitinar da kake tunani afkuwa"
"Ban fahimci Hausar kiba?"
"Yauwa! Yanzu idan kaje kace mata ka biya min Oumra Abin zai mata zafi, tace daga zuwata gida na fara hada kaina da ita, Amma idan kace mata zamu tafi gaba daya harda Yara inaga hakan ba zai jawo matsala ba tunda harda Kai, ko meye ka gani?"
"Kuma fa kin kawo shawara, wannan ma dabarace, hakan kuwa za'ayi" Sai wajen karfe 11 kafin suka isa gida, Kai tsaye daki Falmata ta nufa domin barci ne a idanunta sosai, Alhaji Goni kuwa yana hawa sama dakin Jidde ya nufa, Key yasa Amma da mamaki yaki budewa, Ajiyar zuciya ya sauke 'Kenan daga ciki tasa key karma na bude mata daki?' Murmushi kawai yayi yasa Kai yayi dakin Falmata. Dake shima barci ne A idon nasa Sallar Isha'i kawai yayi da bai samu dama yayi A masallaci ba ya haye gado ya kwanta.
Jidde kuwa Idonta biyu, tana jin taba kofar da yayi ta duba Agogo, ganin karfe 11 yasa ta sake gaskata maganar Falmata cewar hotel zasu wuce, shiyasa tana jin knocking dinsa tayi banza dashi ta juya ta kwanta.
Washe gari da Assalatu bayan ya dawo daga Sallah dakin Jidden ya sake shiga, wannan karo ta cire key din, zaune A sallaya ya sameta tana lazimi, kallo daya ta mishi ta kauda kai gefe "Antashi lfy Maman Abie?"
"Lafiya da godiya" Ta amsa ta nade Abin Sallah ta shiga toilet, haka ya zauna kusan 30minute yana jiranta kafin ta fito, ko kallon sa ba tayi ba hanyar kofa ta nufa "Jidde?" Ya Ambata da sassanayar murya "Na'am?" Ta amsa ta tsaya cak "Ina so zanyi Magana dake? Kamar ba zata dawo ciki ba! ko tunanin meye tayi sai kuma ta dawo ta zauna nesa dashi, kallonta yayi sosai, Haba Jidde Meyasa kike so ki koyi Abinda ba halinki ba? Kiji tsoron Allah, kar kishi yasa kiba shaidan dama ya lalata miki ladar da kika jima kina tarawa"
"Meye nayi wanda ya kauce da za'ace inji tsoron Allah? Kaine ya kamata kaji tsoron Allah sabida hanyar daka dauka ba mai bullewa bace, kai kanka kasan inda Kishi nake da Matarka daba haka ba wallahi, kawai dabi'un da kake so ka tsiro dashi don kayi Amarya shine zai haddasa maka fitina A gidan ka, Amma ina ruwana da Auren ka?"
"Jidde ki duba irin kalaman da kike fada min? Na yau tafi na jiya ma? Daga kawai na kara Aure? Idan kince ba kishi bane Ai da baki fada min magana babu respect haka? Shikenan ku Mata daga An karo muku Abokiyar zama sai ku sauya daga yanda Aka sanku?" Wani kallon raini tayi mishi "Idan Abinda kazo fada min kenan ka sake tarwatsa min zuciya ka fita min a daki don Allah? Babu wani dadin baki daza kayi min yanzu tayi tasiri A zuciya ta, sabida Maza munafukai ne, sai kuce baku san Abu Alhali karya ne, ni wallahi Sai yan zuma nake jin haushin kaina, Dana Amince da cewar baka son Falmata aka aura maka ita, ka fada ne kawai don ka kwantar min da hankali Amma dama can kana son Auren"
"Haba Jidde wai meye Hakane?"
"Kaga Malam fita min a daki, koka manta ranar girkin Falmata ce? Koso kake wata matsalar ta kunno maka?" Ganin da gaske take yasa yace "Allah ya kyauta, Amma kisani idan irin wannan halin shi zaki cigaba dayi min to tabbas Falmata zata kwace miki ni Akwana a tashi, ita da nake tunanin zata bani matsala sai take bani farin ciki" Yana gama fadan haka ya fice Rai a tsananin bace "Aikin banza dama can kana sonta munafurci ne kawai, ta baka farin ciki sai me?" Kwafa tayi ta koma bakin gado ta zauna, 'Ashe haka Saratu ta dan-dana? Tabdijam. Ganin tunani zai tarwatsa mata zuciya yasa ta fito tayi dakin Saddiqa, dake Yau Monday ta samu ta hada wa Yara breakfast su tafi, A kwance ta sami Saddiqa da Alamar barci ta koma, hanu tasa ta taba jikinta "Ke Saddiqa? Tashi tayi tana murtsuke idanu, kin manta Yau Monday ko? Yara za suje makatanta?"
"Wallahi naman ta Aunty meye za'a dafa?"
"Kiyi musu Abu mai sauki kawai kin san makarantarsu suna da tsanani kar suyi latti"
"Shikenan Aunty angama" Tare suka fito Jidde tayi dakin Yaran ta tashesu Abarci, zama tayi sukayi Alola sukayi Sallah, kafin tayi wa Amaan wanka, suna fitowa Sabriya ta shiga tayi, da kanta ta shiryasu sabida kar Abin tayi wa Saddiqa yawa, tare suka fito gaba daya zuwa dining, da ikon Allah kuwa Saddiqa ta kammala komai, shiyasa babu bata lokaci Yaran suka gama breakfast Driver ya daukesu zuwa Makaranta, bayan ta rakosu kitchen ta shiga ta samu Saddiqa tana wanke kwanuka "Yauwa Aunty meye za'a dafa wa Alhaji?
"Kin manta Falmata ce da girki? Ai tace bata bukatar taimakonki? idan yana bukatar wani Abu za kiga ta fito, kawai ki karasa Ayyukan da kikeyi ni zan shiga in dan kwanta"
"Shikenan Afito Lafiya Aunty"
"Alright" Tana shiga daki ta haye gado tuni barci ya dauketa.
Alhaji Goni kuwa yana shiga dakin Falmata ya samu tana waya da Gwaggo tana mata albishir da zuwanta Oumra, yana zama ta mika masa wayar, haka Gwaggo tayi mishi godiya tare da Addu'an Allah ya kara arziki. Bakomai yace da ita ya mika wa Falmata Wayar ta, kwanciya yayi domin gaba daya Jidde ta bakanta mishi Rai da kalamanta marasa fasali. Falmata tana gama waya ita ma ta haye ta kwanta A gefensa, A hankali barci ya sake daukarsu.
Jidde kuwa barcin hour biyu tayi ta farka, lokacin karfe goma saura, toilet ta shiga ta tsala wanka ta fito, Kananan kaya ta fito dasu riga da skatt wanda idan tasa zasu kama jikinta, jikin mirror ta nufa ta tsala kwalliyar data jima ba tayi ba, tana kallamawa ta dauki wayarta ta sauko kasa. Wajen shuru sai kamshin turare dake tashi, da Alama Saddiqa ta kammala Abinda za tayi ta kwanta ne, zama tayi ta cigaba da charting dinta hankali kwance.
Alhaji Goni kuwa sai wajen karfe 11 kafin ringin din wayarsa ta farkar dashi, ya jima yana Amsa wayar kafin ya katse ya tashi Falmata, Hamma tayi ta dubesa "Yaya?"
"Ina so zanyi tafiya zuwa Azahar, ki tashi ki hadamin Breakfast kafin na fito A wanka".
"Angama ranka shidade ina za kuje?"
"Wani kauye za muje Akwai shanu da aka min tallah guda 50, to fulanin da farko sunki Amincewa muyi ciniki, to yanzu shine suka kira P.A akan naje mu tsayar da Magana please hanzarta bani so na dauki lokaci a irin wannan wajen?"
"Shikenan Allah yasa mu dace ya kawo Alkairi" Mikewa tayi ta fice shi kuma ya fada toilet, tun kafin ta karaso ta hango Jidde A zaune A palo cikin kananan kaya masu jan hankali, murmushi tayi "Su gaye manya? Wato har anfara kyar-kyaran Miji? Za kici Ubanki! Ta karasa cikin palon sai kada jiki take! Antashi Lafiya Jidde?" Kanta yana jikin waya tace "Da godiya"
"Ya jiki? Yaya yace min jiya jikinki tayi nauyi zazzabi yana damunki ba zaki iya zuwa gidan Hajja ba? Allah ya sawaka".
"Lafiya ta kalau kawai ba zanje bane, ba gashi kunje kun huta ba? Ai godiya ya kamata kimin".
"Huhmm gashi fitan da nayi Ashe Alkairi ke kirata, munje gidan Hajja Yaya yake ce mata za kije Oumra, shine in fada miki tace zata biyamin muje tare da ke, to yanzu kuma da gari ya waye Mutumin ki wai idan har zan tafi Oumra sai dai mu tafi tare mu 3, ba zai iya barina har tsawon sati biyu ba, shine nace idan har Hakane to a hada harda Yaran mu A tafi, sai a tayani godiya wajen Hajja ni barin hada mishi breakfast" Ta Ambata tasa kai zuwa Kitchen. Tunda Falmata ta soma magana harta gama bakin Jidde A wangale sabida mamaki, da kyar ta iya Aro Jarumta tace "Wai lafiya? Meye yake faruwa dani haka?" Da sauri ta kira number Saratu idanunta har basu ganin screen, tana dauka tayi sauri ta haura sama ta shiga daki ta fashe da kuka "Subhanallah Jidde lafiya? Na shiga uku?"
"Saratu ina cikin tashin hankali, gidan Miji na yana neman ya zamomin tamkar gidan yari, wallahi a yanzu ji nake kamar nace wa Alhaji ya sauwake min, Allah idan haka za'a cigaba dayi A gidan nan bazan iya ba Saratu"
"Innalillhai wainna ilaihi rajuum wai meye aka miki Jidde kike magana haka kamar kin zauce?"
"Saratu bazan iya miki bayani A waya ba, don Allah kizo, ni munyi fada dashi bazan iya tambayar sa, Amma tabbas ina bukatar taimakonki?"
"Shikenan insha Allah zan shigo bayan la'asar"
"Yauwa nagode sai kinzo" Tana gama wayar ta kwanta tana sauke numfashi sama-sama, idan haka karin Aure yake da zafi tabbas Wanda Aka musu kishiya sun d'an-dana, haka ta rinka sauke Ajiyar zuciya kukan ma ta kasa yi.
Falmata kuwa tana shiga kitchen ta fere dankali da sauri ta soya mishi da kwai guda biyu, A tire ta jera ta hada da kayan tea ta fito, tana ganin babu Jidde A Palo tace "Ahayye sai ni Fatima Batula naci dubu sai ceto" Tasa kai tayi gaba sai wani jin kanta take. A zaune tasamesa ya gama shiri ita kawai yake jira, murmushi tayi ta zauna ta dauki plate din A cinyarta tace "Yaya ka tsaya ni zan baka?"
"Ayi haka kuwa Falmata?" Kada kai tayi "Kwarai kuwa Ai Aikin lada ne" Bude bakin yayi yace "Allah ya miki Albarka" Haka ta bashi chips din yaci ya koshi kafin ta Ajiye plate din ta hada masa lipton. Yana gamawa ta kama hanunsa suka fito "Ki sauka barin yi sallama da Jidde?"
"Okay ta ambata tasa kai tayi gaba. Shikuwa dakin ya nufa yasa key ya bude, tana jin shigowar sa tayi sauri ta rufe ido, jikin gadon ya karaso tare da Kare mata kallo, kayan dake jikinta sunyi matukar birgesa "Nasan idonki biyu ganina ne kawai baki son yi, Allah kuma yasa ki gane ni mai kaunarki ne, zanyi tafiya zanje kauyen da nayi miki hiran Maganar shanu, kimin Addu'a saina dawo?" Ganin ba zata amsa ba yasa ya kada kai kawai ya fita. Har jikin Motor Falmata ta rakosa, tana ganin fitarsa ta koma, dakinta ta nufa ta bude drawer din da kayan Mata yake ciki ta dibi wanda zata diba ta hada ta shanye, tana gamawa tayi Sallah tabi lafiyan gado......