Free chapter · Read without an account

01

by Fareeda Aliyu · Taƙaitaccen Tunani

Assalam Alaikum mutane na


Kamar yanda na yi alƙawarin kawo maku littafi na na farko da na rubuta kafin KOWA DA ƘADDARARSA, yau zan fara sauke nauyin alƙawarin. Idan akwai shawara ko gyara a game da labarin sai a taimaka a ja hankali na zuwa wurin, zai iya yiyuwa ajizanci na ɗan adam ya sa ban ankara ba. 


Dole kuma na fara da 'yan group ɗin Fadda_banan, thank you for being there upon all this silence, i appreciate you hanging in there. Ina yin ku overrrrrrrrrrrrrr! Kuma zaman na ku ne ya sa na kawo maku littafin nan kafin BA NI DA MASANIYYA da ya kamata ya zama littafi na na gaba.

*********************


Garam! Na ban ka ƙofar banɗaki, a lokacin ne kuma na samu kukan da nake nema ya zo mani, yanda ka san na kashe kaina haka nake ji. Sai yanzu na tuna ashe ana cewa INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN idan musiba ta same ka.


Da ƙyar na maimaita sau biyar sai kawai na daina karantawa saboda tuƙuƙin da ziciyata take yi mun, lallai ashe abun ba daɗi dama? Ina da yaƙini a raina abin da nayi ne ya dawo kaina.


Amma ai wanda nayi ƙwayar zarra ne akan abin da aka yi mani yanzu. "Na bani na lalace" na faɗa cikin ɗagawar murya, har a lokacin kuma ina jiyo hayaniyar mutane a cikin gidan mu da yayi kamar ya fashe saboda cinkoson jama'a.


Na ɗaga fuska ta na kalli madubin banɗakin, idanuwa na har sun kumbura suntum kuma sun kaɗa sun yi jawur, kai fuska ta kan ta a kumbure take. A take naji wani jiri na ɗauka ta, kai anya ba ciwon zuciya ne ya kama ni yanzun nan ba? Don ban san wurin da nake ba, sanadin duhun da rufe ilahirin gani na.

*****************


Dishi-dishi na fara gani lokacin da na buɗe ido na sai na mayar da su na rufe, a hankali na sake buɗewa na kalli sama. Fanka na juyawa a hankali, yanda take juyawa haka tunanin abin da ya faru ya fara dawo mun a hankali, hakan ya sa na fashe da kuka.


Kukan nawa ne ya jawo hankalin ƙanwar innar mu ta taso tazo kusa da ni tana ta faman hamdala ga Allah kafin daga bisani tace "Halima don Allah ki yi shiru ki bar kukan nan, kar fa ki manta komai kika ga ya faru to kuwa mukaddari ne daga Allah, don dama can haka ya ƙadddara. Kuma komai za'a yi don a hana faruwar al'amarin abu ne da ba'a isa ba a wurin Allah. Ai kin ga zahiri, domin ko don shawarwarin da aka dinga ba ki ai ya ci a ce kin ɗauka....." Ƙara fashewa da kukan da nayi ne ya katse maganar da take yi, ta ja bakin ta tayi shiru tana kallo na.


A kuma lokacin ne innarmu ta shigo ɗakin, ganin ina kuka sai hakan ya tunzura ta, ta hau faɗa tana cewa da kukan banza za ta ji ko kuma da tsegumin jama'a, ta ci gaba da faɗin "Tunda aka kawo ki asibiti mutane ke mana zarya, yau kwana uku kenan muna ta addu'ar Allah ya farfaɗo da ke, wai maimakon da ki tashi mu ji salama sai kuma wani sabon tashin hankali kenan?" Sai ta juya wurin ƙanwar ta tana tambaya ko ta je ta faɗa ma'aikatan asibitin na farko ko zama tayi ta yarda na sa ta a gaba ina kuka?


Ni kuma a gefe mamaki fal zuciyata, yau kwana na uku ban san a wurin da nake ba? Kai, ikon Allah da yawa yake, ashe da gaske ne da ake cewa 'Ramuwar gayya tafi ta gayya zafi?', lallai Allah ba azzalumin kowa ba ne! Sai kawai na tsinci kaina ina maimaita faɗin "Alhamdulillah" saboda tunda Allah ya ramawa wanda na cuta makamancin abin da nayi masa alaa ce ta Allah ya so ni da rahamarsa.


Da likita ya gama duba ni ya tabbatar da samun lafiya ta, don haka Inna ta roƙe shi ya ba mu sallama, idan ya so a ƙarasa mun ragowar alluran a gida idan mun koma.

*******************


         Bayan Sati Biyu

Dukkanin sati biyun nan nayi shi ne a ɗakina a gidanmu, idan ka gan ni a tsakar gida to kuwa alwala ko wanka ne ya fiddo ni, don ko yunwa ba ta fito da ni daga ɗakin balle wani abu daban. Ramar da nayi kuwa kai ka ɗauka idan wata guguwa ta taso tsaf za ta ɗaga ni sama ta jefar, nayi haske na rame na ƙara tsayi, ni abun ma har mamaki yake ba ni.


Kuma kafatanin sati biyun nan na yi shi ne cikin ƙunci, domin duk iya bakin ƙoƙari na na kawar da abin da ya faru daga raina na kasa samun nasara ko na sakan ɗaya.


Washegari kam ina tashi daga bacci, shi ma sai ƙarfe ukun dare na samu ya ɗauke ni shi yasa ma baccin nawa yayi tsayi, na yanke shawarar zuwa gidan aminiya ta Ruƙayya ko na rage zafin wannan ɓoyon da nake yi wa kaina a ɗaki saboda masu zuwa gulma a matsayin dubiya,"munafukai!" Na faɗa da ƙarfi tare da yin ƙwafa.


Wurin ƙarfe uku da rabi na fara shirin fita don har ma na tambayi Innarmu kasancewar Baba ba ya nan ya fita, a raina nake jimamin yanda Baba yake ji idan ya fita, ko don saboda shaguɓen mutane. Duk da dai maza ba ruwan su, amma daga ni har Inna mun daina fita ko ƙofar gida saboda kunyar idon mutane.


Tunda na fito daga gida dauriya kawai nake, a mugun tsarge nake, ban san ko ido na ba ne amma kamar ni kowa yake kallo. Ga shi ramar da nayi ta sa rigar jiki na har faɗowa take yi ta kafaɗa ta, da ba don zani na ɗaura ba nasan da ban isa ya zauna a ƙugu na ba. Kai ni fa har da masu nuna ni da yatsa na gani ban da masu ƙus-ƙus, ko kuma ido na ne yake mun ƙarya.


Da ƙyar na kai kan layin gidan su Rukky, a daidai majalisar wasu samari naji wani yana cewa "Yauwa Sabo ga Halimar da nake ta kwatanta maka, dama nace maka tana yawan zuwa unguwar nan....." Ban bar kaina na ji abinda yake ƙoƙarin faɗa ba na ƙara sauri na shige layin ganin gabaɗayansu sun juya suna kallo. Ni na manta nan ne wurin zaman su idan yamma tayi. Ina jiyo dariyar su ta rufo mun baya.


Duk saurin nan nawa bai hana ni jiyo abin da wasu suka faɗa cikin ɗagawar murya ba "Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani." "Dama an karɓe mu da hannu biyu ai da haka ba ta faru ba", "Inaaaaaaa! A kai kasuwa mun yafe." Kaɗan daga abinda kunne suka ɗauko mun kafin na faɗa gidan su Rukky kenan.


Na yi sallama, maman su na zaune daga gefen rijiya tana yankan alayyahu da ya kuwa, da alama shirin abincin dare take yi tun yanzu. Ta amsa sannan ta ƙara "A'a, Halima ya jikin naki? Ɗazu nake taɗi a zuciyata nake cewa in shaa Allah yau ko bayan magriba ne zan je na sake dubo ki in ga yadda jikin ki ya samu ci gaba."


Na ce "Mama na warke sosai ai." Ta amsa "za dai ki warke, kin ga ramar da kika yi kuwa a satittikan nan? Yanzu haka ai Ruƙayya lukuta ce a kan ki."

Nayi murmushi na ce "To Mama ya za'a yi? Ai haka Allah ya nufa." Ta ce "To Allah ya taƙaita." "Ameen." Na amsa da sauri. Sannan ta sanar da ni "Ki shiga ciki, yanzu Ruƙayyan za ta dawo, ta tafi sayo kayan miya wurin Bala."


Na shiga ɗaki na zauna, can na jiyo muryar Maman na faɗin "Halima idan za ki ci abinci ga shi nan a kula saman firij, alala ne don nasan kina son shi."


Da sauri na miƙe tsaye tare da ɗauko kula ɗin, na ajiye mayafi na sannan na fito na doshi kicin domin ɗauko kwanon da zan zuba abincin a ciki. Daga kicin ɗin nace "Mama ina yajin yake? Ban gan shi a wurin ba." Ta ce "Duba cikin durowar sama, akwai na tafarnuwa wanda kika fi so."


Da sauri na ɗauko, ina fitowa sai ga Ruƙayya ta shigo, tana gani na ta taho da gudu ni kuwa na zame ina cewa "Ba ruwa na da ke, ƙyale ni kawai malama." Na kumbura fuska kamar gaske.


Na wuce ɗakin ina jin tana cewa "Mama ba za ki ba ta haƙuri ba?" Ta ce "Wace ni? Ai tsakanin ku ne." Ta ajiye ledar kayan miyan ta nufo ɗakinda nake zaune, lokacin har na fara cin alalen da yake ta gwangwani ce ba ta leda ba. 


Tana shigowa ta ce "Ga mai a ƙaramin kwano a can." Ta nuna wurin, na ce "A'a ke ma kin san yajin ne kaɗai nake so."


Muna hira sama-sama har na kammala cin abincin da rabon da na ci mai yawan shi haka na kai wata guda. Sannan na fara ba ta labarin yanda yau da ƙyar na iya ƙarasowa gidan su, na ce "Wai kana gefe kna sabgar ka, ashe kowa idon sa na kan ka. Yau da baki zai cinye ni da yanzu na daɗe da tafiya. Kin ga yanda ake tanka ni kamar kowa ba shi da ta shi irin ƙadaddarar. Addu'a nake yi Allah yasa na cinye jarabawar nan." Na ƙarasa ina kuka mai soya zuciya. Da ƙyar na iya cewa "Ba ni ruwan sanyi" hannuna tallafe da ƙirji na.


Tunda na kafa kai a gorar ruwan sai da na sha fiye da rabin robar, nan take kuwa amai ya taso mun, tuni nayi waje da gudu na amayar da abin da naci ga yajin ya gigita mun kai da hancina. Mama sai sannu take yi mun, suka ja ni zuwa gado na kwanta ina ta maimaita innalillahi a zuciya, har zafin ya fara rage mun.


Farkawa nayi daga bacci ido na ya sauka kan agogo da ya nuna ƙarfe goma, na juya na kalli wurin da nake na ga duhu, kenan goman dare ce. Da sauri na miƙe zaune, mikewar Ruƙayya ce ta sa na lura da ita a wurin. Sannu ta fara yi mun, da taga na miƙe tsayw kuma zan fita sai tace "Ina za ki kuma?" "Alwala mana."


Lokacin d na idar da sallah nayi ta faman roƙon Allah ya yaye mun abinda ke faruwa tattare da ni, ni nasan ƙaddarar Allah ce, kuma yanda ya so haka ya faru.

Nasan ba ni da wayo ko ƙarfi balle dabara da zan kauce mashi, na maimaita addu'ar da nake yawan yi tun lokacin da abun ya faru, addu'a ce da ake yin ta yayin da abinda ba ka so ya faru da kai watau 'Ƙaddarallahu wa ma sha'a fa'al' sannan na karanta wadda ake yi idan al'amari ya tsananta a wurin mutum watau 'Allahumma la sahla illah ma ja'altahu sahla, wa'anta taj'alul hazna iza shi'ita sahla.'


Ƙarfe sha ɗaya da minti takwas idona ya gani lokacin da na miƙe daga kan abin sallar, a raina na ce, watau wani imanin na mutun ba ya taɓa zuwar masa sai abu ya same shi.


Lokacin da nake jin duniyar wata aba ce, addu'o'in nan ban damu da yin su ba, kuma fiye da rabin su ma ban san su ba kwata-kwata, wahala ce ta sa na koya yanzu.


Har na dawo kan gado na kwanta da kayan jiki na amma Rukky ta ki bari na, sai da na canza da rigar bacci sannan. A kuma lokacin take sanar da Inna ta aiko bayan isha da ta ji ni shiru wai anya kuwa na zo? Shine Mama ta bi ɗan aiken da kan ta taje can gidan bayan Alhaji (babansu Rukky) ya dawo. "Kin san meye tsoron Inna?" Cewar Rukky, na girgiza mata kai, ta ci gaba "Tana tsoron kar surutun jama'a ya sa ki yi ƙoƙarin guduwa, tace hankali bai game mana jiki ba tunda har yanzu mu yara ne...."


A tare muka yi murmushi ni da Rukky, kafin na ce "Abin mamaki ko da wasa wannan bai taɓa faɗo mun a rai ba sam-sam. Ni kawai dai nasan ina tunanin da ma zasu yarda ita da Baba da sai na koma wurin Anty Hafsatu (ƙanwar Inna) Zaria, idan ya so ko karatu sai na cigaba, tunda an ce "Idan wuri yayi maka zafi, an yar je ka yi hijira ko za ka samu sanyi." Na ƙarasa maganar ina jan bargo domin yin bacci. Duk muka yi shiru kowa da saƙe-saƙen sa a zuciya har bacci yayi awon gaba da mu.


Washegari sai ƙarfe biyar da rabi muka baro gidan su Rukky, kayan Ruƙayyar na sa amma duk da haka sun yi mun yawa. Haka muka sake gota majalisar jiya, amma yau kam ko don ba ni kaɗai na ce? Sai na ji ban wani damu irin na jiya ba.


Mun gota su kaɗan, Murtala (wani abokin mu ne) ya hango mu, yana ƙarasowa ɓangaren Ruƙayya ya nufa, abun ya ba ni mamaki, domin idan za mu haɗu sau dubu ni zai fara yi wa magana kafin ita, da yake ya fiya tsokana sai ba su cika shiri da ita ba.


Kafin na gama mamaki naji yana cewa "Rukky sai ina? Gidan su mutuniyar za ki je? Don Allah ki ce ina yi mata jaje ina kuma yi mata addu'ar zaɓi mafi alkhairi."


Ta amsa "Da yake kai makaho ne shi yasa ba ka gan ta kusa da ni ba ko?" Ya waigo da sauri muka haɗa ido, a take ya fara ba ni haƙuri akan cewar wallahi bai gane ni ba, ya ɗauka wata ƙawar Ruƙayya ce shi yasa ma ko kallo na bai yi ba. Ya ƙara da faɗin na koma 'yar ƙarama. A haka ya raka mu da ɗan nisa kafin ya koma, kuma ina ga hakan na daga cikin abinda ya hana masu tsokana ta jiya su cigaba, domin sun san halin sa baya ɗaukar raini.

**************


A ƙalla yanzu an samu wata biyar da ƙadaddarar da ta same ni, an ɗanrage yawan gulmar kam yanzu ba laifi, har ma zunɗena idan na fita, ni ce kawai bana son fita, wai ma idan na fita ina zan je to?


Kuma lokacin yayi daidai da fara rigistar yin jarabawar private WAEC da NECO, na yanke shawarar siyan duka don takardu na da nayi ba wadda ta yi kyau.


A tsakar gida na samu Inna tana harhaɗa robobi, na ce "Inna ni so nake ki faɗawa Baba a siya mun form ɗin jarabawar WAEC ta private na sake zanawa, sai na samu na shiga makaranta, don ban ga amfanin zama na haka ba."


Ba ta kalle ni ba kuma ba ta daina abinda na iske tana yi ba tace "Ai sai ki faɗa masa da kan ki..." Da sauri na tare ta "Don Allah Inna ba don ni ba, ki faɗa masa. Ni ban san ta yaya zan faɗa ba, ki yi haƙuri kin ji Innata." Na ƙarasa cikin alamar marairaicewa, har sai da ta yarda na tashi ina murna.


Sai kuma na sake dawowa na tsuguna na ƙara saukar da murya ta nace "Inna da so samu ne kuma, ku taimaka ku bar ni na tafi wurin Anty Hafsatu, sai nayi jarabawar a can kawai. Ni da sai na fi jin daɗi ma, kin ji Inna?"


Tayi ɗan jum! Sai naji gaba na na faɗuwa, ina ta addu'ar Allah ya sa ta amince, domin idan ta yarda da wuya Baba ya ƙi yarda, can ta ce "To shi ma sai ki jira mu ji me zai ce?"


Sai bayan kusan sati ɗaya maganar mu, Inna ta tabbatar mun da cewa ya yarda amma da sharaɗin ina gama jarabawar zan dawo gida. A take naji kaman an sauke mun wani kaya mai nauyi da ya daɗe a kaina.


Ranar Laraba da safe har na gama haɗe kayan tafiya ta, don har mun yi sallama da Baba kafin ya fita da safiyar ranar, ya kuma ƙara jaddada mani da na tabbatar na dawo da zarar na gama zana jarabawar.


Yanzu ma zaune nake tare da Inna ina jiran Ruƙayya ta zo, mun yi za ta zo ta raka ni tasha. Ni don ɗoki ma ko karin kumallo na kasa yi, Inna dai ta kawo ido ta zuba mani. Rukky kam ba ta ƙaraso gidan mu sai da ƙarfe goma tayi, ina ganin ta na fara faɗa, ita ma ja ta ƙyale ni ba har tana ce mun Ganɗoki kawai.


Ta ajiye littattafan hannun ta tana cewa "Ga su nan, economics ne ban gani ba." Na ce "Ni kuma kin ga ina da shi." Ta ce "Allah yasa dai note ɗin cikakke ne, bani na gani don nasan ba ki da cikakken note, ai ba ki ma taɓa ba."


Tana buɗewa ta ce "Ɓarauniya! A ina kika ga littafi na har kika sace?" Ni dai dariya na dinga yi mata ina sanya littattafan a cikin Ghana-must-go ɗin da zan yi tafiya da ita.


Muna yin sallama da Inna muka fito tare da taryar 'yan mashin sai tasha. Wurin wani ɗan unguwar mu muka bada ajiyar kayan mu, saboda ina son na siya irin hair relaxer ɗin da nake amfani da shi a wani shago ɗan nesa kaɗan da tashar.


Muna doso ƙofar fita daga tashar na hango Ya Buhari, nai saurin jawo Ruƙayya ina cewa "Zo mu koma." Ta tsaya tana kallo na "Menene kika gigice?"


Na ce "Ya Buhari na gani." 

"Yana ina?"

Na juyo domin nuna mata wurin, amma abun mamaki ko kalar sa ban gani ba. Rukky kam ko magana ba ta ƙara ba ta ja hannu na muka siyan abin da za mu je siyan.


Ba ta ƙara maganar shi ba, har sai da muka dawo, kuma ɗan unguwar mu ya taya mu kai kayan zuwa motar da ke lodin Zaria. Kafin motar ta cika muna gefe a tsaye muna ɗan hira bayan na ajiye robar ruwa a wurin da na kama da zan zauna ne, ta ce "Wai yaushe rabon da naji kin ce Ya Buhari? Zancen wasa a gefe, don Allah shi kika gani ɗazun?"

Da sauri na ce "Wallahi shi...." Numfashi na kusan ɗaukewa yayi, a lokacin da na lura da shi yana tahowa ta ɓangaren da muke, don mun daf da daf,da bala'in wuya bai ji maganar da muke yi ba.


Jin na yi shiru ya sa Ruƙayya ta kalle ni alamun na cigaba, da ta ga ban yi magana ba, ta buɗe baki za tayi magana kenan ta ji an ce "Malama Ruƙayya barka da safiya."


Ta juya ta wurin da ta ji maganar, ta ce "Lah, Ya Buhari ina kwana? Kwana da yawa da yawa. Ina zuwa haka?"

Murmushi yayi ya ce "Abuja na nufa yanzu, daga can kuma zan wuce Jos wurin aiki na."

Ta ce "Allah ya ba da sa'a."

"Amin."


Sai a lokacin ya waigo sashen da nake tare da rage walwar fuskar sa sosai kamar ana yi masa dole ya ce "Sadiya ya gida? Ya su Inna?" Bai kuma jira amsa ta ba, ya wuce wurin da ake lodin motar Abuja, bai ƙarasa ba ya waigo wurin mu da duk mun zuba masa idanuwa ya ce "Af! Yi haƙuri Rukky, hankali na ne yayi gaba. Allah ba mu alheri, sai watarana."

Da sauri tace "Ayya, babu damuwa wallahi. Allah ya sada mu da alheri."

Ya juya yana faɗin"Amin", ban da motsin da bakin sa yayi da ba ta yanda za'a yi mu ji amsawar ma.


Wata ajiyar zuciya na saki, na dafa Rukky na ce "Wai! Na daɗe ban ji kunya irin ta yau ba, da na san zan gamu da Buhari a tashar nan ban ga abinda zai kawo ni ba, almost 5 years kenan ban sa shi a ido na ba. Allah ma ya sani ina ta so na haɗu da shi na roƙi gafarar sa, amma kalli na haɗu da shi kuma kaina da baki na duka sun kulle. Kuma ciwon abun na nan har yanzu a zuciyar shi, sai idan ba ki kalli idanun sa ba.

Daure hawayen idona kawai nake har motar mu ta tashi, har muka isa ko kalma ɗaya ba ta ƙara fita daga baki na ba.

***************

To ga labari nan mun fara ba, kar dai a manta shi ne na farko kafin Kowa da Ƙaddararsa...lol. Kar a ce Mr. Coke sun fi zama 'yan zamani akan waɗannan. A ba mu chance tukunna dai. How far? Ina jiran ra'ayoyin ku my people.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.