Free chapter · Read without an account

04

by Fareeda Aliyu · Taƙaitaccen Tunani

A na gobe graduation party ɗin mu muna zazzaune a harabar makaranta muna ƙarasa tsara abubuwan da ba mu gama ba, don so muke mu bar magana wa students bayan mu, kuma so muke a ce ba wanda party ɗin su ya kai namu.


Gaskiya zan iya cewa na daɗe ban ji ni cikin nishaɗin da nake ji a tare da ni ba a wannan lokacin. DJ sai baje mana waƙoƙi yake yi, ni ma kuma rawa ta nake babu abinda ya dame ni. Hotuna kam an yi su babu daɗi, don fiye da rabin mu sun zo da camera ɗin su me film irin wadda ake yayi a lokacin. Takaici ɗaya naji shi ma saboda na hango Abba tare da Habibah suna wani rawa har ana shiga jikin juna, na ja tsaki na juya ɗayan ɓangaren ta yanda ba zan ma sake hango su ba.


Sai kuma ga Fahd bayan na baro filin rawan, yana murmushi ya ce "Anty Halima...." Na katse shi cikin zaro ido na ce "Kai Fahd ka fita ido na, ni ce antyn ta ka?"


Sai ya kama dariya ya ce "To ya zan yi tunda Ya Faruƙ ya ga wurin zama? Yanzun ma aiko ni yayi na nemo masa ke yana bakin hall a waje. Na ce masa ya shigo ma amma ya ƙi." Hararar sa nayi kawai ban amsa ba na doshi wajen.


Faruƙ ɗin na zaune a saman bonnet ɗin motar shi yana wasa da makulli lokacin da na ƙaraso tare da yin sallama. Yana amsa sallamar yana ƙare kallo, kafin daga bisani ya sauka ya tsaya yana cewa "Kai Halima! Irin wannan kyau haka? You look so take away my dear."


Na motsa bakina amma na kasa cewa komai, sai ya sake koma saman bonnet ɗin ya zauna tare da matsa yana ɗan dukan gefen shi ya ce "zo ki zauna"


Na kalle shi na kalli tsawon wurin nace lallai ma, a tunanin sa zama zan iya yi anan? Don haka sai na girgiza kai na ce "A'a, ba komai don ban gaji da tsayuwar ba. Dama ka zo mun koma ciki, ai baƙon mu ne kai."


Ya kalle ni ya ɗan girgiza kai kaɗan ya ce "No. Ki yi haƙuri idan ke ma na hana ki zaman ciki. Tun da safe nake garin nan amma Fahd yace mun kina cikin organizers ɗin party ɗin naku, yanzu ka sa daurewa na yi don satin mu uku kenan yanzu ba mu haɗu ba. Ki yi haƙuri na takura maki." Ya zan yi? A wani sigar rarrashi yayi maganar dole na share na zauna wurin shi.


Tun daga nesa nake ji ana ƙwala mun kira,na waiga, Abba ne. "Wai ina kika ajiye key ɗin? Habiba ce ke tambaya za'a fara rabo, i can see you don't have time." Ko kallon wurin da Faruƙ yake bai yi ba balle na sa rai zai gaishe shi.


Dama haushin sa nake ji, kuma ya zo bai gaishe da Faruƙ ba, don haka makullin na jefa masa an ci sa'a ya cafe amma ko ƙala ban ce masa ba balle ya samu kallon arziki.


Kusan minti biyu dukkanin mu mun yi shiru, can Faruƙ ya nisa tare da kallons ya ce "Halimatu ya ya ne?" Murmushi nayi kawai. Ya sake cewa "Wannan firend ɗin naki ya sanni kuwa?" Da sauri na amsa da sosai ma kuwa.


"Me yasa ya ke wani irin abu? Kuma ba wai na damu sai mun yi mu'amala da shi ba ne, ina yin hakan ne saboda ke, tunda babban abokin ki ne." Kai kawai na ɗaga masa, Abba bai kyauta mun ba, ya bani kunya, yanzu da nice nayi masa haka da ya sa ni a gaba da faɗin abinda nake yi bana kyautawa blah blah blah....


Daga nan bai ƙara minti ashirin ba yace zai tafi, kar na ƙarar da lokacin a wurin shi, idan yayi haka bai mun adalci ba kuma. Muka yi sallama ya wuce. Ai kuwa har aka tashi daga partyn namu avoiding Abba nake, kuma hakan yayi mun sauƙi saboda it's obvious he is trying to avoid me too. Kowa fushi yake da ɗan uwansa. Perfect!


Da muka fito don tafiya ma su Abubukar na bi suka sauke ni, unguwar mu ɗaya da su. Kuma duk abinda ake yi Abban na zaune a motar gidan su yana kallona bai ce kanzil ba.

******************


Kwanan mu biyar da gama makaranta, ina ta son tahowa Kano kamar yanda muka yi da Baba tun farko kafin ya bar ni na taho Zaria, amma ina ta jiran Abba ya zo mu yi sallama don ta iya yiyuwa ba zan ƙara zaman Zaria ba sai dai hutun da ba zai wuce sati biyu ba.


Ƙarfe huɗu na yammacin wannan ranar har lokacin ba Abba ba kalarsa, sai kawai na tashi nayi wanka na shirya na cewa Gwaggo zan je wajen su Auntie nayi masu sallama don nasan nan da Laraba zan koma Kano. Tunda nake ban taɓa zuwa gidansu ba, amma nasan unguwar gidan ne kaɗai ban je ba, ban kuma san a ina ba ne, kawai nasan ba zan ɓata ba in dai nayi tambaya tunda ai nasan layin.


Ina shiga layinsu na hango shi tare da wani suna ta dariya kuma dariyar ba 'yar kaɗan ba. Yana sanye da wando iya ƙwauri da singlet, hakan ya sa na fi tsammanin a kofar gidansu yake don haka gidan na nufa kai tsaye.


Sallama kawai nayi masu da na ƙaraso kusa da su kamar baƙi na wuce na shiga gidan ta gate ɗin da ke buɗe, tun kafin na yi nisa naji shi biye da ni yana kiran sunana, ban kalle shi ba na ce "Ka daina bi na, ba wurin ka na zo ba, gara ma ka koma wurin abokin ka da ka baro."


Da Fatima na fara cin karo ta fito daga kitchen riƙe da doya da wuƙa, a wurin ta yar da shi tana ihu ta yo kaina ta rungume ni. Ihun ta ne ya fito da Auntie sai ihun ya zama biyu hakan kuma ya sa Hajiya ta leƙo da kan ta, don murnar ta yi yawa.


Tana gani na ita ma ta fara dariya, don haka wurin ta na dosa na tsugunna ina gaishe ta. Ta amsa tare da ɗago ni tsaye tana cewa "Gaskiya muna da babbar baƙuwa a gidan nan, ni aka zo gaisawar wa ko wurin su Auntie kika zo to?"


Ina dariya na ce "Hajiya wannan ai zuwan ki ne, su zan yi masu nawa daban."


"To shi kenan ai, ƙaraso daga ciki. Ina Abba yake ne? Ya zo ga Halimatu."


Daga bakin ƙofa yake amsawa "Ni na fara ganin ta ai Hajiya, amma tace kar na kula ta ba waje na ta zo ba."


Hajiya ta ce "Lallai na yarda da gaske baƙuwa ta ce, bari na karɓi aba ta da kyau." Da kanta ta ɗauko lemo ta ajiye mun, su Fatima sun zagaye ni sai zungura ta suke wai na tashi mu tafi ɗakinsu. Mun daɗe a falon Hajiya har ma na shaida mata na zo yi masu sallama ne zan koma gida. Sai da ta ce da Fatima "Wai ina girkin ne? Kin ga Halimatu kin shiririce ko?"


Tare muka koma kicin ɗin, ni dai ina zaune ni da Auntie Fatima na shirin girkin ta muna ta surutu, ita kaɗai take aikin ta. Ban ma san ina Abba yayi ba. Sai bayan da muka yi Isha sannan Hajiya ta sa direba ya maido ni gida bayan an cika mun leda fal da abun arziki, kuma ta sa Fatima, Auntie da Abba su rako ni gida. A kan hanyar mu sai da muka biya gidan Ya Khadija, finally Allah yayi dai. Kyautar atampha tayi mun tana ta mun ɗan biki wai na ƙi zuwa wajen ta sai da na gama makaranta.

******************


Ranar talata ana saura kwana ɗaya na koma Kano, Abba ya kawo mun hotunan da aka yi a graduation party ɗin mu. Wannan zuwan da yayi ne muka shirya. A ciki na ga wani hoto an yi mun ina waje tare da Faruƙ, na daga hoton ina nazarin sa na ce "Wa ya ɗauka wannan? Fahd ne ko?"

"A'a, ni ne, gani nayi kin yi kyau da yawa sai na ɗauke ki ina tsaye bakin ƙofan hall ɗin."


Na juyo na kalle shi sannan na ce "Ka tuna mun ma, shi ne don wulaƙanci kana ganinsa ka kasa gaishe shi ko? Ko da bai yi maka ba tunda ni yayi mun ba sai ya ci daraja ta ba?"


"Au dama saboda shi ki ke ta wulaƙanta ni kina basar da ni?" Sai musu ya kaure tsakanin mu kafin daga bisani aka samu matsaya.


Abba ya ce "Yanzu idan kin tafi gobe sai yaushe kenan?"


"Gaskiya babu rana, ƙila na tafi kenan sai dai ko ɗan zuwa hutu." Ya tsare ni da ido yana kallona bai ce komai ba, ni kuma sai na ji kaman hawaye zai kawo ido na sai na sauke kallo na ƙasa kawai duk muka yi shiru.

*****************


Kashegari ma shi da su Auntie suka zo suka kai ni tasha kuma suka biya mun kuɗin motar, muna tare har da motar mu ta tashi sannan.


Ni dai tunda na dawo Kano sai na rasa farin ciki sosai, kewar mutanen Zaria ta cika ni, ji nake kaman na koma can gaba ɗaya. A ɓangare guda kuma aminci na da Rukky ƙara ƙarfi yake yi sosai, don ma yanzu tana zuwa school of management studies wurin da take diploma ɗin ta, can titin Yahaya Gusau. To ita ma yanzu babu lokacin haɗuwa irin na baya saboda makaranta ta cika lokacin na ta.


Sai a wannan lokacin nake nadamar ƙin yin jamb da ban yi ba, ina kallo su Abba suka yi da wasu 'yan ajin mu, amma ni na dage sai na ga result ɗina tukunna.


Watanni kaɗan da gama makarantarmu labari ya zo mun jarabawar ta fito. Rukky na jin zan tafi Zaria tace na ɗan jira ta gama jarabawar ta tunda a cikin yi suke, sai ta raka ni Zaria. Na san gulma take son zuwa yi.


A ranar Alhamis da muka isa Zaria, a yammacin ranar gab da magrib ta dame ni akan mu je gidan su Abba. Bai san na zo ba. Tunda mu gidan mu ba mu da yawa, unit nake siya a telephone booth na kira su Auntie mu gaisa lokaci zuwa lokaci.


Muna isa gidan, duk sallamar da muka dinga yi ba wanda ya jiyo mu sakamakon hayaniyar dake fitowa daga ɓangaren Hajiya, saboda haka can muka wuce. Ina ɗaga labulen na ga mutane fal ɗakin, ji nayi kamar na juya na koma.


Auntie ce ta fara ganin mu don haka ita ce ta fara murnar gani na. Hajiya kuma sai faɗin cewa "Kabo kabo! Lallai gidan nan yayi albarka yau. Ku shigo."


Falon kam a cike yake, Ya Khadijah da yaran ta su duka ukun suna nan, sai wasu samari da suke zaune tare da Abba da ban san ko su waye ba. Na fara gaishe da Hajiya kafin ragowan baƙin fuskokin, Abba ne kawai ban ce wa ƙala ba, sai ɗan murmushi da nayi masa.


Hajiya ta ce "Halimatu ba ki gane yayan naku ba?"


Ina murmushi nace "Au! Yaya Abdallah ne?"


Ta ce "A'a, shi sai wani satin. Saifullahi ne wannan."


Da yake nasan sunayen, fuskokinsu ne ban sani ba yet. Sai na juyo na kalle shi tare da cewa "Ya Saif barka da sauka."


Ya amsa "Yauwa Halimatu, mun same ku lafiya?" (Kamar ya sanni, don ya ji Hajiya ta kira sunana ne ya riƙe).


A ka ɗan yi jum, Abba ne ya katse abun ya ce "Ke 'yar ƙauye, kin kawo baƙuwa ba ki yi introduction ba." 


Kumbura kumatu nayi ina hararar shi na ce "Ina ruwan ka ma? Ko wurin ka muka zo?" Su Fatima suka fara dariya suna cewa yau dai mun gan ku a rana.


Yayi saurin ce wa"Ba wani nan, rabu da su ta wajena, ai ba wanda ya isa ya gan mu a rana."


Rukky ta amsa "Ba wani nan, ko ni da nake baƙuwa na gani. Ruƙayyan Kano ce."


"Rukky?" Cewar Abba. "Sannu da zuwa Rukky, i heard so much about you! Ke Fati ba za'a ba ta ruwa ba ne."


"Laaaaah! Ya Abba jira muke ku gama gaisawa mu tafi ɗakin mu fa, so kake tace zazzagawa ba su iya karɓar ɓaki ba?"


Zaman hirar da muka yi a ɗakin su Auntie har ba mu lura lokaci ya tafi ba sai da ƙarfe tara tayi. Ai kuwa da sauri muka fito yin sallama da su Hajiya, sai kuma muka ci sa'a an zo ɗaukar Ya Khadija sai ta rage mana hanya, har gida suka sauke mu tukunna.

*****************

Washegari kam da muka karɓo result ɗina, WAEC ina da 7 credit, Hausa da IRS ne nake da pass. NECO credit takwas gare ni, Hausa ce pass (dama ban ba wa kaina wahalar karatun su ba, so ban yi mamakin abinda na samu ba).


Farin cikin da nake ciki har bansan yanda zan kwatanta ba, kawai tsintar kaina nayi ina faɗin "Alhamdulillah lazi bi ni'imatih tatimmus salihat".


Gwaggo ma bayan mun koma na kai mata sakamakon sai murna take ta tayi. Dama Baba ya ce idan na karɓo, idan yayi kyau sai a siya mun form na fara diploma a ABU ɗin tunda ban rubuta jamb ba, idan ma naso ina cin diplomar idan an fara sayarwa sai a siya mun.


Da yamma sai ga Abba ya zo, wai yasan hali na, a gida zan ƙunshe Rukky shi ya zo ya fita yawo da ita. Ya miƙo mun hannun shi yana cewa "Congratulations!" Ya sani bana so, shi yasa yake tsokana ta don haka da jakar hannu na na doke hannunsa, shi da Rukky suka fara dariya.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.