Free chapter · Read without an account
Chapter 4
by Fatima Zara Alhassan · JOƊA
📚JOƊA📚
NA
FATIMA ZARA ALHASSAN
ƳAR MUTAN ARGUNGU
GARGAƊI!!!
WANNAN LITTAFI ƘAGAGGE NE, SABO DA HAKA BAN YADDA WANI KO WATA SU YI AMFANI DA KALMA ƊAYA DAGA CIKIN SHI BA. YIN HAKAN LAIFINE. A KIYAYE!!!
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
Can sai su ka ga an shuro kyauren bukkar da su ke cikin ta. Tamkar an jeho mutum haka su ka shigo cikin bukkar...
Matsattsun kaya ne sanye a jikinta, blue jeans da body hug fara, sai suman kanta wadda ta raba ta gida biyu two baby's, ta daureta da black ribbons, kunnenta na dauke da manyan yan kunne masu ruwan zinari, bakinta ya sha jambaki marun.
Cingam take taunawa kamar tana tausayinsa.
Ba namiji ba, ko mace idan ta kalleta sai ta sake kallo. Sai ka rantse da Allah ita din balarabiya ce ba daga Najeriya ta fito ba.
Kai ko acikin larabawa ita din kyakkyawa ce.
Ahankali ta dauki rimot din tibi ta kamo tashar labarai, sabo da babu tashar da take sauraro tamkarta(News).
ƙafa daya kan daya ta daura kafarta tana me ci gaba da taunar cingam dinta hankali kwance, tamkar ba ta da damuwar komai a rayuwarta.
Amma can kasan zuciyarta cinkushe
take da tarin baƙin ciki marar misaltuwa .
A zahirin gaskiya idan ka kalleta za kayi tunanin kallon tibi take yi, amma a gareta a kasin haka ne.
Firgigit! ta dawo daga duniyar tunanin da ya kasance jiki a gareta. Idanunta masu ruwan madara ta zubawa Tibi tana kallon mutumin dake yin jawabi wanda aka tsayar a matsayin sabon gwamna na Lardin Zamfara.
Jin kalamansa ta ke yi tamkar irin waɗanda sauran shuwagabannin da suka shuɗe ke ambatawa bayan sun karɓi mulki!
Haushi ya sa ta ɗauki rimot za ta canza zuwa wata tasha...
Maganganun sa taji tamkar saukar aradu aka.
Fasa canzawa tayi ta zubawa akwatin Tibi idanunta tana son ta sake jin abun da ya faɗa.
Tamkar ya san akwai me son maimaicin magana Shi, sake furtawa yayi yana cewa;
"Ba za a samu zaman lafiya ba har sai fulani da Hausawa sun haɗa kansu tamkar tsintsiya maɗaurinki ɗaya, kamar yadda suke ada can baya.
Bahaushe da Bafullace su ɗin Hassan da Husaini ne, kamar yadda wasu ke kallon su a matsayin Ɗan jumma ne da Dan jummai haka su ke.
Duk inda ka ga manomi to za ka tarar da makiyayi a bayansa. Haka suke su yi faɗa su shirya.
A lokacin Da, idan aka ce za a kai wani zamani wanda makiyaya za su kai farmaki wa manoma har su kashe su, wallahi ba za a yarda ba.
To amma gashi yanzu mun shiga ƙarnin da sai dai muce Lahaula wala kuwwati illabillah!
Wanda kwata-kwata babu ɗigon imani a cikin zuciyan wasu fulani kai harma da Hausawa. Ya kamata musan ta ina wannan ƙiyayyar ta kutso kai?
To wallahi kusani, matukar ina zaune akan wannan kujera ta gwamna ba zamu yi sulhu ga duk wani dan ta'adda ba!
Abu na biyu da nake son na faɗa muku shi ne; matukar aka kama ɗan leken asiri masu ɗaukan bayanai na mutanan kirki su na kaiwa ɓata -gari , to kusani hukuncin su ɗaya da wanda yayyi kisa.
Abu na uku: Muddin muka kama masu fatauci da miyagun ƙwayoyi, muna me tabbatar muku su ma hukuncin kisa ya hau kansu, sabo da sune ummul-aba-isin duk matsalolin mu a Arewa! Barin su a doron ƙasa masifa ne.
Abu na hudu; kusani mutum daya ba zai iya magance duk wasu matsaloli da suke addabar wannan Lardi namu ba, sai da taimakon ku, hadi da taimakon makwabtan mu( sauran jahohi) dama talakawanmu baki daya, kuzo mu hada hannu da ku, mu gudu tare mu tsira tare.
Abu na gaba mu cire hassada da kyashi ga junanmu. Mu sani duk abun da Ubangiji ya nufe mu da samu, zamu same shi ba sai munbi ta gurbatacciyar hanya ba.
Sai abu na biya shi ne; ina son al'umma su sani cewa, mun bude hanyar sirri ga talakawa domin cin zarafi da wasu sojoji da yan - sanda su ke yiwa jama'a.
Duk wani kaki wanda jama'a su ka nema wajen su kai musu dauki, amma su kayi biris da batunsu, alhalin mun basu isassun kayan aiki, su ka ce ba zasuyi ba, sai am basu cin - hanci a hannun su kafin su taimake ku, to kuyi ma za ku tuntubi akwatin sirrinmu.
Mu kuma in sha Allahu zamu karbi korafe- korafen ku.
San nan abu na shida...
Fadowar Li. (Halima) cikin falon ya sa ta dauke kanta daga kallon Tibi ta mayar gefen da Li ta ke.
Take Li ta sare mata yadda ake yiwa soja.
Zama tayi a gefen ta, tana kallonta, nan take idanunsu suka kada ja-jawur sabo da bacin rai.
Ko da ace Li. ba ta bude baki tayi ma ta magana ba ita kanta tasan me za ta furta ma ta.
", sun shigo. Yanzu nan na samu sako daga mutanan sirrin mu.
San nan kuma a iya bincikenmu, mun gano cewa akwai sa hannun Alhaji Yusuf , Haka zalika mun sake bincikowa akwai wasu yara guda hudu su na zaune a unguwan mareri, su na daya daga cikin yaran sirri na Alhaji Yusuf
su wadan nan yara a ko da yaushe ba su da aiki saina yawon unguwanni domin leken sirrin al'umma su kaiwa barayi."
Runtse idanunta tayi, bayan ta gama jin dogon jawabin Li.
"Ina son ganin Yaran.
Joɗa ta fada a hankali.
Sune kalmomin da suka fito daga bakinta.
Daga nan ta tsuke baki, ba tare da ta sake furta komai ba.
Sanin tayi ko da za takai shekara ba za ta sake cewa ci- kanki ba.
Fahimtar hakan ya sa Li. tashi ta bar falon.
Ganin tashinta ya sa tabi Yarinyar da kallo tana kara jinjinawa Li. akan kokarin da take yi.
Ajiyar zuciya ta sauke, kaddararsu kusan iri daya ce ita da Li.
Li(Halima) ta fito cikin zuri"ar masu kudi, kwata-kwata ba tasan wani abu wai shi wahala ba, amma aka samu azzalumai su ka ruguza mata a halinta.
Haduwar su ta farko shi ne lokacin da barayi su ka kaita maboyansu , a can ta hadu da Li.
kullum duk lokacin da ta tuna irin rayuwar da tayi a hannu barayi sai hankalinta ya tashi!
Ba ta san ya zauna kusa da ita ba , sai da taji hannunsa na yawo akan fuskarta.
Kallonsa tayi tare da shimfida mishi murmushin karfin hali, " yaushe ka shigo? ta tambaye shi"
Shima murmushi ya mayar ma ta tare da sumbatan bakinta, san nan ya ce;. " Bandade da shigowa ba, sai kuma na tarar dake cikin duhun yanayi.
Babu abun da ke tadamin hankali kamar na ganki cikin tashin hankali Joɗa!
WACE JOƊA AKE MAGANA?
KUMA WAYE ME WANNAN MAGANA?
MENE NE MATSAYIN LI. A WAJENTA?
KARKU MANTA KU YI MIN...👇
**SHARE
**COMMENT
**LIKE
**VOTE
** FOLLOW
San nan ku garzaya #Arewabooks domin samu sauran littafai na.
ko kuma ku je #wattpad acan ma zaku samu.
ko kuma a YouTube channel di na
FATIMA ZARA ALHASSAN
***
NAGODE 🙏