Free chapter Β· Read without an account
Page 1
π« π π¨π₯πππ π‘π ππ π«
An Imaginary Love Storyβ€οΈ
πππΎππ π°π½π³ πππΈπππ΄π½
π±π π΅π°ππ΄πππ°π°π·ππ°π·
Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah SWT da ya bani ikon fara rubuta wannan littafin Allah yasa yadda na fara rubuta wa lafiya in ga ma lafiya.
ΖirΖiraren labari ne.
Na Chanja masa suna daga MURADIN ZUCIYATA zuwa MURADI NA CE
π ππππ¬π πͺπ₯ππ§ππ₯'π¦ ππ¦π¦π’ππππ§ππ’π‘
Follow My WhatsApp Channel
***
Ψ¨Ψ³Ω Ψ§ΩΩΩ Ψ§ΩΨ±ΨΩ Ω Ψ§ΩΨ±ΨΩΩ
π΅π°ππ΄πππ°π°π·ππ°π·βοΈ
ππππ 1π¦
π³πππππ πΊπππππ, π«ππππ, π±πππππ πΊππππ.
TuΖi yake a hankali kamar baya son yi a bakin wani tangamemen Gida ya tsaya Horn yayi gate man ne ya leΖo ganin motar yasa ya koma ciki ya buΙe gate Ιin shiga ciki yayi tare da yin parking zaman sa yayi a cikin motar bai fito ba ya Ιauki gurin minti talatin a ciki sannan ya fito tsayawa yayi yana Ζare wa compound Ιin gidan kallo Ζaton gida ne dan daga ciki yafi girma Part-Part ne gurin guda Shabiyar daga can gefe garden ne mai kyau cigaba yayi da tsaiwa a gurin jikin motar sa. Babban Mutum ne ya shigo gidan kai tsaye gurin sa ya nufo Bata fuska yayi sannan yace masa
"Daga ina kake Fawzan?" Da Sauri ya juya yana kallon sa baiyi tsammanin zai haΙu da kowa yanzu ba Ko takwas bata yi ba ya dawo Shiru yayi masa yana Ιauke Kansa daga kallon sa, cigaba da yi masa magana yayi
"Yau ma baka kwana a gidan ba kenan?" Ζauke shi da mari yayi "a ina ka kwana nace maka" nan ma shiru ya Ζara yi masa yana cin magani da Ζunkuni Ζasa-Ζasa sai kuma ya ce masa
"Malam ka dame ni da surutun tsiya kai ba haifa ta kayi ba amma kana mari na, Ιaga maka Ζafa kawai nake amma wallahi da sai na rama"
"Rashin Kunyar taka har ta kai kace zaka mare ni Dan na maka faΙa, to zoka rama marin mara tarbiyya kawai"
"Na rasa inda ka samo wannan banzan halin mu dai duk zuri'ar mu babu Ιan iska sai kai maybe a Gurin Uwarka ka kwaso wannan mummunan halin"
"Kaga rashin tarbiyya a Ζ΄aΖ΄an ka tsohon banza kawai, kuma ba Mahaifiya ta ka zaga ba Tsohuwar ciki ka zaga kaji, mtwssssss" ya faΙa yana shige wa Part Ιin da yake kallon sa. Masifa ya cigaba da yi a gurin ba jima wa sai ga Tsohuwa ta fito itama daga Part Ιin ta "Kabiru kai da wane haka da sanyin safiyar nan?, Yawanci duk ba'a tashi ba kar hayaniyar ka taja hankali"
"Hajiya kema kin san wanene zai saka mutane magana iyanzu ai"
"Sai yanzu ya ga damar dawowa gidan Kenan, na rasa me yake damun Fawzan baya son kwana a gidan nan yanzu, Kabiru kira min shi yanzu ku same ni a palour na da Iyayen sa"
"Allah ya Kyauta dai Insha Allah yanzu zaki ganmu"
β§ο½₯οΎ: *β§ο½₯οΎ:*
π«πππππππ, ππππ, πΊππππ.
Palour ne kato an yalwata shi da kujeru masu kyau kirar Italy set Uku daga Ιayan side Ιin kuwa katon Dinning ne ba kowa a cikin palour Ζofofine gurin guda shida sai Stairs daga tsakiyar Palour'n daga gurin Dinning Ιin Ζofa ce a buΙe da alamu kitchen ne.
Wata kyakkyawar budurwa ce tsaye a bakin sink ruwa take tara da alamu ta faΙa Duniyar tunani Wata Babbar Mace kana ganin ta kaga wadda Naira ta zauna a jikin ta cikin kitchen Ιin ta shigo a baΖin kofa ta tsaya tana kiran"Jaanan!, Jaanan!, Jaanan" jin shiru ne ya sata Ζara so wa kusa da ita "Jaanan! Jaanan" ta Ζara faΙa shiru bata answer ba Ιaka mata duka tayi a firgice ta Ιago "Yaushe kika Ζara so ne Ummu?" Ta tambaye ta
"Ban sani ba, bacin kina jina amma baki amsa ba sai da nazo dai-dai inda kike ke ga ishashiya" ta faΙa kamar ta rufe ta da duka
"A'a Ummu banji kina magana ba ne"
"Ai dama ba zaki ji ba, kin raina kowa a gidan nan musamman Ni"
"Kiyi haΖuri dan Allah" ta faΙa tana yin Ζasa da kanta kafin ta Ζara wani laifin. wata mace ce ta fito daga Ιaki daga ita sai sleeping dress tsayawa tayi tana kallon su tabe baki tayi Sannan ta Ζara so kitchen kusa da Ummu ta tsaya tana watsa wa Jaanan Mugun Kallo Ζasa tayi da kanta magana ta fara yi musu
"ummu ya Naji kina ta faΙa tun dazu?, Hayaniyar kice ta tashe ni daga bacci"
"Ba Dole kiji ina ta faΙa ba, Yarinyar nan nake ta kir amma tayi banza dani bata amsa ba, nasan har maΖota suna jiyo mu yanzu"
"Uhmmmmm, Indai Jaanan ce ai ta saba tana jin ka kana mata magana amma tayi maka banza, wallahi na tsani Yarinyar nan ji nake kamar na kashe ta, an auro mana wahala mtwsssss"
"Ban san me Yaya ya gani a jikin Yarinyar nan ba ya nace mata sai Wulakanta shi take amma ya nace mata" ta faΙa tana galla mata harara
"Bari yazo shima zai ci Ubansa, Sakin ta zai yi nan bada daΙewa ba na gaji da halin ta"
"Ummu dan Allah Kiyi haΖuri, me za'a yi miki yanzu?"
"In kinyi laifi kin san kice ayi haΖuri, wai Uban me kike ta zaman yi baki fara wanke-wanke nan ba, Da gani ko breakfast Baki haΙa mana ba kuma kin san Ιaki na yana jiran ki zan fita aiki Kizo yanzu ki gyara" cewar budurwar
"Na kusa gama breakfast Ιin, Bari in Ζara sa wanke-wanken Sai inzo"
"Auuuuuu Har sai na ma jira kin Ζara sa?, ai tashi zaki yi Kizo ki gama da shi kafin na fita, in kin gama kya dawo kiyi wanke-wanken" ta faΙa tana fice wa daga kitchen Ιin zuwa Ιakin ta.
Tashi tayi daga wanke-wanken ta bita zuwa Ιakin kafin ta Ζara yin wani laifin cikin Ιakin itama ta shiga katon Ιaki ne an cika shi da kayan alatu kala-kala, kaca-kaca yake kamar ba mace ce a ciki ba. Ko kallon wacce take cikin Ιakin bata yi ba ta wuce Toilet shima ba kyan gani haka ta fara gyara shi tassss ta gyara shi Sannan ta fito. Harara ta watsa mata sai kuma tace "sai nace ki fara aikin nan Ιin sannan zaki yi ne?"
"A'a ba sai Kince ba, amma ai sai kin tashi daga kan gadon sai in fara"
"Ki fara gyara kasan sai in tashi daga nan" Tom tace mata tana fara gyara wa tashi tayi ta koma kan kujera tana danna wayar ta bata daΙe ba ta tashi tana mata wani kallon banza tare da cewa
"saura in fito daga wanka in tarar Baki gama ba" tana shigewa Toilet Ιin. Da sauri sauri ta cigaba da yin aikin tana kuka hawayen daya zubo mata ta share...................βοΈ
# π΅π°ππ΄πππ°π°π·ππ°π·π―
***
WhatsApp Only
Comments & Share Fisabillahπ₯°π
π½πΈππΌπβ€πΈπΈββπΈββοΈ