Free chapter · Read without an account

23

by Fareeda Aliyu · Taƙaitaccen Tunani

"Ƙwarai da gaske. Su uku ne Mommy ta haifa. Duk ranar ki ka zo zan kai ki ku gaisa." Na amsa ta. Wai ita duk a zaton ta shi Ya Buhari ɗan uwanmu ne kawai shi yasa har soyayya ta shiga tsakani na da shi. Tunda shi ne kamar shi daban da mu.


Muna tasowa daga makaranta kai tsaye ɗakin baccin Yaya naje na duba shi, bacci na iske yana yi. Amma Mommy tace hutawa yake yi don shine ya raka Daddy airport ɗazun.


Lokacin da na dawo daga islamiyya daidai lokacin Rufaida ma ta gama na ta, don haka a falonmu muka zauna kowa na yi abun da ya dame shi. A haka Yaya ya iske mu, ni fatana kawai Allah ya sa kar yayi mun maganar abinda na yi jiya na tafiya gidan Inna sai kuma na ji daɗi bai ɗaga maganar ba.


A haka Anty Aysha ta dawo daga makaranta ta iske mu amma ba ta zauna ba sai da tayi wanka ta ɗebo abinci sannan. Tunda ta zauna cin abincin da ta zuba sai ya zama kamar absent mindedly take ci. Duk maganar da muke yi da Rufaida ko Yaya ba ta sa mana baki ba don da alama hankalin ta yayi nisa. Hakan ya sa gabaɗaya muka juya muka zuba mata ido.


"Anty Aysha!" Duk kiran sunan ta da muka yi bata san ana yi ba sai da Rufaida ta taɓo kafaɗarta sannan ta yi firgigit ta farga ta ɗago ta kalle mu, har da yi mana murmushin ƙarfin hali.


"Me ya same ki?" A tare muka tambaye ta. Ta zuba mana ido sai kuma ta nisa ta ce "Ba komai, gajiya ce kawai."


Yaya ya koma kusa da ita ya zauna, ya sa hannuwansa ya juyo ta gabaɗaya ta fuskance shi sannan ya riƙo hannayenta ya ce "Kalle ni ki ga, me ye damuwar ki? Ko kina da wanda za ki faɗi ma damuwar ki sama da mu? I'm your brother and these are your sisters. Idan ma ba kya son faɗa a gabansu tashi mu je ki faɗa mu ni kaɗai." Yayi shiru yana ƙara nazarin ta yana kuma jiran ta yanke shawara, ya ƙara da "Pleaaaaaaaase?!"


Ta ɗan ja numfashi ta ce "Ni wallahi...mts! Yusuf ne! He's been pestering me har ban san ya ya zan yi da shi ba?"


Ya Buhari ya zuba mata ido da alama abubuwa da yawa ne suke zuwar masa a zuciya, kafin ya ce "Yi mun magana Aysha, kar ki ji tsoro, i'm here for you, we all are."


Ni da Rufaida muka sauko ƙasa duk jikinmu yayi sanyi, muka sa su ita da Yaya a tsakiya muka zabga tagumi. Ta kalle mu sannan ta mayar da ganinta kan 'yan yatsun ta ta ce "Rigimar Yusuf mana, wai babanshi ya dame shi da maganar aure domin yanzu yana shekara ta uku da fara aiki. Ya ce masa idan har bai kawo mata ba, to shi da kansa zai zaɓo masa a dangin su. Tun kwanaki yake damu na, ina cewa ya ɗan ba ni time shine ɗazu ya je makaranta ya same ni yayi mun hayaniya, wai idan bana son shi gara na faɗa mashi ya san me zai yi don yanzu haka Baba ya ba shi sati biyu ne, idan bai kawo ya gama ƙarar da damarsa kuma ba zai saurare shi daga baya ba. Wallahi Yaya har hawaye yayi mun ko tunanin mutane na wucewa suna kallonmu bai yi ba." Ta ƙarasa maganar cikin matsananciyar damuwa.


Yaya ya fara murmushi yana matsa yantsunta da suke hannun shi ya ce "To meye damuwar a ciki? Ba kya son shi ne?"


Da sauri ta kalle shi ta ce "Taɓ! Ai ni shi kaɗai ma nasan ina so, kawai ina shakkar me Daddy zai ce ne, saboda ya ce na mayar da hankali akan karatu na sosai banda distractions. Tsoro nake ji na zo na kawo Yusuf ya ce ba zan yi aure yanzu ba, shi kuma ga abinda yake fama da shi a gidan su."


Rufaida ta ce "Wait! Idan Daddy ya yarda, za ki auri yayanmu ne?" Ta gyaɗa mana kai alamar 'eh' don haka ba mu jira ta faɗi da bakinta ba muka miƙe tsaye mun tsallen murna.


"Mommy" na faɗa, kai tsaye da gudu muka kwasa muna ƙwala mata kira za mu je mu kai mata jarida. Anty Aysha na ta ƙwala mana kira babu wanda ya saurare ta.


Mommy kam bakinta ya ƙi rufuwa da ta ji labarin da muka kawo mata, ta ce "Au, toh! Ashe lokacin surukuta ya kama, Alhamdulillah! Maa shaa Allah! Yau ɗin nan Daddy zai ji da zarar ya kira waya kuwa. Allah ya sa albarka, Allah ya sa a yi da mu. Kai kai kai, Alhamdulillah."

**********************


A satin Ya Yusuf ya zo har gida ya gaishe da Mommy, ita ce ma ta faɗa masa Daddy ya ce idan ya dawo su baban shi za su iya zuwa.


Ita kanta Anty Aysha tunda ta ga kowa murna ake yi ba wanda ya ce mata komai akan makaranta sai ta sake baki ɗaya, hakan ya sa ta ba wa Yusuf dama kusan koyaushe yana gidanmu da daddare. Shi kuma ba ya yarda ya ɓamɓaru, domin duk roƙon da za mu yi masa na ya kaimu yawo ya kan ce mu bari a mallaka masa Anty Aysha tukunna sannan sai ya ji da mu.


Bayan dawowar Daddy da kwana kaɗan aka faɗa masa ya turo, shi ma kwanakin saboda ya sa a yi bincike ne kuma da alama ba'a samu wata matsala ba.


Sai kuma a daidai wannan lokacin ne wani abu ya bayyana a gare ni game da dangin Daddy da da ban sani ba. Saboda sun zo akan baƙin Anty Aysha da zasu zo.


Abinda na lura kamar ba sa ƙaunar Mommy sam, idan kuma ba gizo idona yayi mun ba to tabbas ko da Yaya babu sakewa a tsakanin su. Haka ina kicin an aike ni ɗauko lemo na hango ƙanin Daddy da suke kira da Baba Sagir yana hantarar Yaya.


Kashegarin karɓar kuɗin gaisuwa, suna shirye-shiryen tafiya a lokacin ma suna karin kumallo ne, Mommy ta ba ni quacker oats a babban flask ta ce na kai mashi can babban falo. Na zo zan shiga na jiyo su da Daddy suna zancen filin da ya siya a Kano domin buɗe kamfani (daga yanda ake maganar filin ba na wasa ba ne). Na ji Daddy yana daɗa yi masu bayani ai ba'a Kano ba ne kawai, a arewa dai da shi zai yi gwajin farko kafin a buɗe wasu rassan (kila a yanzu haka yana da kamfanin a wani wuri da alama), amma dai a ra'ayin Buhari yana ganin kamar ba za su sami matsala ba cewar Daddy kenan kafin a katse shi.


Baba Usman ya katse shi da "Abdallah wai me kake nufi ne? Mu nan 'yan uwanka ba mu isheka ba sai ka wani sako yaro kamar Buhari? To yaushe ya girma yayi hankalin da za'a dinga sa shi a cikin shawarwarin kasuwanci saboda Allah? Wauta ake son gani ko sakamako?"


Ni dai ban shiga ba, ban koma ba kuma, ina sauraron abinda bai shafe ni ba.


Cikin murmushi mai sauti na ji Daddy ya ce "Haba Yaya, ai Buhari da kake ganin shi basirar shi ta fi shekarun shi, kuma Allah ya ba shi baiwa in dai a harkar business ne, domin zai matuƙar ba ka mamaki idan ka ga irin taimakon da na dinga samu daga gare shi akan kasuwanci na. Bari dai na kira shi yayi maku bayani akan sabon kamfanin nan da ake ginawa za ku fahimci me nake nufi." 


Tunda na ji ya ɗaga intercom sai na yanke shawarar nayi sallama a daidai lokacin na miƙa saƙon kawai. Hakan kuma yayi daidai da maganar Baba Sagir ya ce "Duk ba wannan ba, ya dai kamata ka jawo wani daga cikinmu yake taimaka maka, kafin Buharin ya gama kai munzalin da za'a sakar masa ragamar komai."


Ni dai nayi sallama tare da gaishe su kafin na ajiye abinda aka aiko ni da shi na fita ina mamaki a raina ta yanda suke nuna sun fi Yaya mahimmanci a wurin mahaifinsa. Kai duniya! Anya ma waɗannan suna ƙaunar Daddy da iyalansa kuwa? Don na tuna irin wulaƙancin da suka yi wa Mommy jiya. Anya ba sa yi masa yankar baya? Allah ka tsare ahalin nan. Shi ne addu'ar da nayi masu.


Da suka fito za su tafi, suna tsattsaye jikin motocin da zasu mayar da su, mu kuma duk mun fito wurin domin yi masu sallama kamar yanda Mommy ta tattaro kanmu barin ma ni da Rufaida, don mun fi ɗaukar zafi.


Hankalina gabaɗaya yana kan Ya Buhari, domin tsabar tausayin shi da nake ji yana ta ƙaruwa a zuciya ta. Zallar ɓacin rai ne ɓaro-ɓaro bisa fuskarsa, irin wanda ban taɓa gani ba. Abinka da farin mutum, tuni fuskarsa ta koma jawur kamar jini zai fito, idon shi kam ban ma gani ba bare na kwatanta saboda ƙasa kawai yake kalla.


Suna barin gidan na hango shi cikin sauri yayi ɓangaren ɗakunan baƙi, anya ba kuka na ga kamar yana yi ba? Gaba na ya faɗi dum! Ban tsaya wata-wata ba na bi hanyar da naga yayi. Jikin kowa na gidan a sanyaye gabaɗaya, ba wani mai walwala.


Zaune na iske shi ya haɗa kai da gwiwa a tantagaryar ƙasa bisa ciyawa. Har na zo kusa da shi na zauna bai nuna alamar ya ji mutum a kusa da shi ba sai da na dafa kafaɗarsa.


Ban san ya aka yiba sai kawai na ga yasa kanshi akan kafaɗa ta ya zagaye ni hannayensa, kafin na yi wani abu ma naji gefen da ya ɗora fuskarsa ya fara jiƙewa da alama kuka yake yi, yana jan numfashi na ji gabaɗaya tsigar jikina ta tashi. Ni dai a gigice nake a lokacin don bai taɓa mun irin haka ba tunda muke da shi.


Mun ɗauki lokacin a haka kafin nutsuwa ta fara zuwar masa kafin ya fara mun magana a hankali. Ya ce "Me yasa family ɗin Abba suka tsane ni Sadiya? Me yasa ne? Zan ƙi taimakon Daddy ne? Kuma ba sai ana ɗor mutum akan abu ya ke gwanancewa ba? Daga na yi zan mayar da martani sai Daddy ya dinga lallaɓa ni akan nayi haƙuri, wai ɗan uwa ɗan uwa ne, ko da yana yankar naman ka kullum. Wannan ba shi yasa kullum suke ƙara ƙarfi akan yi mun yanda suka ga dama ba?"


Ya yi shiru ya ƙara matse ni ya ce "Thank you for being here for me, i appreciate it Sadiya na." Sannan ya sake ni ya gyara zamansa yana kallo na, sai kuma ya sa hannu ya juyo da fuskata.


Hawaye ya gani face-face a fuskata (to ni kaina ban san lokacin da nayi kukan ba). Ya ce "Sadiya kuka? Kalle ni ki gani, kin gani na daina kukan ni ma (ya nuna fuskar shi) oya share idon ki, ko so kike yi na sake wani sabon kukan?"


Cikin sanyin jiki na girgiza kaina alamar a'a, shi ne kuma ya share mun hawaye tare da goge mun fuska da hannayenshi. Muka ci gaba da zama shiru.


Sai kuma cikin murmushi ya ce "Yanzu saboda nayi kuka ne ke ma kika yi? Ya kamata fa idan na weak for us lokacin ya zama shine lokacin da za ki zama strong for us.....amma....."

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.