Free chapter · Read without an account
25
Ina shigowa ɗaki na fara ƙoƙarin yin wanka saboda ɗan gudun nan da nayi ya sa na fara jin zafi, sannan ina jiyo alamar al'ada ta za ta zo, ban wuce wata uku da farawa ba, ni ban da wahalar da take ba ni ma har yanzu ban gane kanta ba.
Tuni na tara ruwa a kwamin wanka na zuba turarrukan wankan kala-kala sannan na shiga nayi kwanciya don su ratsa jikina gabaɗaya. Maganganun Yaya ne kawai suke dawo mun ina ta murmushin da ya ƙi barin leɓe na. Sai da naji ruwan ya fara sanyi, sannan na zubar na sake haɗa sabo amma ban sa turare ba. Tawul na ɗaura na fito da sauri domin ɗauko madara a kicin, don babu a firij ɗin ɗakinmu, da sauri saurina dawo bana son na haɗu da wani a hakan da nake. A ruwan wankan na zuba madarar peak ta gwangwani da na ɗauko, na kan yi irin wannan wankan lokaci zuwa lokaci, na koya ne a ire-iren jaridun kwalliya da muke karantawa a gida, sun ce nutrition na fata ne sannan yana taimakawa wurin cire stress musamman ga masu yawaita zirga-zirga.
Bayan na kammala wankan na tsaya gaban madubi ina ƙarewa kaina kallo, ni kaina yanzu na yarda na cika ɗin domin har na fi Rufaida cika ido. Mawuyaci ne ka gan mu tare ka yi zaton ta girme ni sai dai ka yi zaton mu ƙawaye ne kawai.
Kiran sallar da ake yi yasa na tashi domin yin alwala amma sai na ga al'adar tawa ma ta zo, don haka kaina kawai na shirya. Na shirya cikin doguwar riga me ƙaramin hannu kamar na shimi amma da faɗi sosai, ta kama ni ta ƙirji sannan ta buɗe ƙwarai ta ƙasa. Kalaba ce a kaina na kama da ribbon duk da ni ba wani gashi gare ni ba amma ina da na zaman falo, su Rufaida masu gashi, barin ma Anty Aysha da na ta har gota dokin wuya.
Anan falon suka zo suka iske ni bayan sun idar da sallah. TV a kunne take amma ban san me ake yi a ciki ba, haka kuma bana sa baki a maganar su don ban fahimci me suke faɗa ba ma. Kawai dai na san hannuna na ɗauke da lemo kuma sha kawai nake hankalina baya kan shi. Shigowa da zaman Ya Buhari gefe na ne ya katse mun yanayin da nake ciki.
Tun da ya fara tambayar me ya faru bayan ba ya nan, hira ta buɗe a tsakanin su ni da ban sa baki ba sam. Abin da bai gane ba sai ya nemi ƙarin bayani su kuma su yi masa.
Ya juya wurin Rufaida ya ce "Sarakan yawo, ana yawon da aka saba ko? Balle an ga bana nan tunda kun san Mommy ba za ta juri yawan magiya ba, kuna fara yi za ta ce Allah kiyaye hanya ko?"
Tana murmushi ta ce "Kuma ka ga wallahi yau......(Ta daga kanta kamar tana lissafi), yau kwanan mu huɗu ba mu je ba."
Yana duba agogon hannun sa ya ce "To me ya hana ku? Rashin kuɗi ko me?"
"A'a fa, kawai kasa fita muke yi a kwanakin nan zuwa can, kawai yanzu muna gama abinda muke yi sai mu bi Anty Aysha makaranta."
"Watau dai zaman gidan ne ba za'a yi ba kenan? To ku tashi na kai ku yanzu, ko ni ma naji me kuke ji a can ɗin da kuke ta nacin zuwa."
Sai da muka ɗauki sakwanni kafin ƙwaƙwalwarmu ta gane da gaske yake yi ba gatse ba ne, muka miƙe tsaye muna tsallen murna kafin muka kwasa zuwa ɗaki da gudu don ɗauko mayafi. Anty Aysha kam ba ta yarda ta bi mu ba, ta ce karatu za tayi.
***************
Tunda muka shiga wurin na ga alamar yau kam a cike wurin ya ke. Sa'ar da muka yi muna shiga wasu gungun mutane na tashi, na san da ba haka ba wurin zaman da yayi mana wahalar samu.
Zaman mu ba wuya na ga 'yan mata suna ɗan kallo ɓangaren da muke zaune, kó kuma a zo a gifta mu ba gaira babu dalili. Mts! Kai jama'a! Ina amfani kyau ga ɗa namiji. Shi kuma da ake wannan abubuwan saboda shi ko ɗaga ido bai yi ya kalli mutum ɗaya daga cikinsu ba sai ma ƙoƙarin jan mu da hira yake a game da wurin.
Ni taƙaicin hakan ne yasa na ƙi yin abinda ya kamata na kuma ƙi sa baki a maganar da suke da Rufaida. Shi ne ya gaji ya ce "Wai ku haka ake zuwa a wajen ba'a siyan komai?"
Ban amsa har sai da na miƙe tsaye sannan na ce "To ka tashi mu je, ta ɓangaren daman ka ne." A ka cigaba da kallon shi, ni wata ce ma na ga tana ƙare mun kallon, muna haɗa ido ta ja tsaki ta juyar da kanta gefe, a take kuma na ji raina ya ɓaci har gumi na tsattsafo mun. A raina na dinga jin kamar na ce mu fasa mu tafi gida kawai amma dai na daure. Dukkan abinda muka siyo shi ya kwaso su wai bai kamata ya bar ni na wahala ba, murmushin yaƙe kawai nake yi.
Rufaida tun da ta hango ni ina dawowa wurin zaman mu raina a ɓace ta fara dariya ƙasa-ƙasa. Ina zama ta fakaici idon Yaya ta yi mun raɗa a kunne "Ke fa ki ka ce za ki iya, meye na ɓacin rai a ciki? Ko kin ga ya kula wata?" Hararar da nayi mata ne ya lura, ya ce "Kai, kai, kai! Ƙanwa na hararar yayarta?"
Ɗan jimawa kaɗan ya ce "Wai me ye abun daɗi wurin zama a wurin nan? Ba gara mutum yayi kwanciyar shi a gida ba?"
Rufaida tayi magana bakin ta cike fal "Uhn uhn Yaya, ƙila saboda yau jama'a sun yi yawa ne amma hirar mu muke sha, mu ci abinda ranmu ke so. Let your guard down, you will enjoy it, i promise."
Kallon ta kawai yake yi yana murmushi yana kuma tauna chocolate (kamar daga aljihunsa n ga ya fito da shi, don na san ba sa saida irinta a wurin). Hannu na miƙa masa na ce "Ba ni nawa chocolate ɗin."
"Ai kuwa babu wani, sai dai mu raba wannan." Ya ƙarasa maganar tare da kawo chocolate ɗin saitin baki na a nufin sa na gutsura, ai kuwa deep na ja chocolate ɗin don na gutsire sama da rabin ta. Ya janye da sauri yana kallon ragowan yana kallon baki na ya ce "La'ila! Ta cinye, ta cinye mun ragowan chocolate." Ya ajiye ragowan chocolate ɗin hannun shi ya kaiwa robar Robo ɗina chafka (ita kenan ta yi saura a wurin na siye, ya kuma san yanda nake matukar son Robo), da sauri na dafe hannun shi ya riga nawa sauka kan robar, don gara ya kwashe komai na gaba na da ya ɗauke ta.
Da ƙyar na samu sararin magana saboda na cika bakina da chocolate ɗin shi, na ce "Don Allah Yaya ka yi haƙuri ba zan ƙara ba, please please please Yaya, ka ji?" Juyowar nan da zan yi wurin Rufaida sai na ga tana ƙarasa cinye ragowan chocolate ɗin da ya ajiye kafin ya chafki robar Robo ɗina, sannan hannunta na rufe da favorite snack ɗin ta. Ni don tsananin dariya har sakar masa Robo ɗin nayi, shi ma dariyar yake yi yana jaddada "Yaran nan kun maida ni kakan ku."
Ya karkace yana zaro abu a aljihu ya ce "Wannan fashin da kuka yi mun kun sha naku, da niyyata na ba ku idan mun je gida amma inaaa." Ya ƙarasa tare da fiddo chocolates guda uku daga aljihunsa. Ihun murna muka sa ni da Rufaida saboda son da muke yi wa chocolate ɗin, kuma shi yasan a ina yake siyowa, ina ga ma mun manta a wurin da muke don sai da ihun ya jawo hankalin jama'a da dama zuwa kanmu.
Ya ce "Ai ba baku zan yi ba...." Katse maganar sa aka yi da faɗin "Ni ma a bani nawa." Daga bayanmu. Gabaɗaya muka juya wurin da muka ji maganar, wannan ƙawar Ya Buhari ce da muka haɗu da ita a Al-Abiyad stores can da daɗewa, sunan ta ne ya kwanta mun.
Fara'arsa ta ƙaru ya ce "Hamida! Yaushe wace rana? Last time na gan ki was a year ago, right?"
Ta ƙaraso tare da miƙa masa hannu don su yi musabaha. Da ta juyo kan mu kuma da ni ta fara magana "Halima ko? Mun taɓa haɗuwa, wannan kuma Aysha ko Rufaida ce, saboda kun yi kama sosai daga hotunan ku."
Chocolates ɗin hannun shi ta amsa lokacin tana amsa gaisuwar mu,ta ɗau ɗaya ta miƙa mana ragowan, kuma har lokacin a tsaye take ba ta da niyyar zama sai ma ɓare ledar da take yi. Ta kai bakin ta ta gutsura chocolate ɗin sannan ta janyo hannun Yaya ta na faɗin "Zo mu je ku gaisa da..." Ban ji me ta ce a ƙarshen maganar ba.
Rufaida cike da mamaki ta ce "Wai wace ce wannan ɗin mai shegen rawar kan tsiya?" Na faɗa mata.
Ta ce "Au! Na tuna, wacce ta ba ki scrunchie ko? Ni sai na ganta kamar balarabiya."
Na amsa "A naki idon ba, ni kam tafi mun kama da half-caste. Kuma kin sani wani abu? Duk wannan kyan na ta, ba ƙaramin ganin na Yaya take yi ba."
Rufaida ta fara murmushi da alama tsokana ta za tayi, ta ce " Ni fa shi yasa kika ga nafi son zaman lafiya ta. Ni kam ko da wasa ba na son farin namiji, abun shi ya fi fita a ganshi nan da nan, barin ma a zamanin nan da mata sun zama marasa kunya. Gara mun irin kala ta, ko yana da azabar kyau zan samu sauƙi akan masu irin kalar Yaya. Kuma ni ba sage maki gwiwa nake yi ba." Ban tanka ba amma ina nazari dai.
Na ɗaga idona ina bin wurin da kallo a ƙoƙarin lalubo Yaya don son sanin ina yake. Can na hange shi tare da wasu mutane da ko mutun ɗaya ban shaida a cikin su ba. Shi ma hankalinsa yana kanmu, domin muna haɗa ido yayi mun murmushi tare da ɗaga mun hannu da alamar yana zuwa.
Hakan da yayi ne ya ja hankalin abokan zaman nasa zuwa gare ni, na kuma hango ɗaya daga cikinsu tana yi masa magana yana amsawa, sai kuma gabaɗayan su suka juyo suka kalle mu. Ina ganin sun taso da alama wurin zaman mu za su zo, na ɗauke idona na ce "Ga wasu bataliyar friends ɗin Yaya nan, ina ce dai ya fi sanin mata akan maza ko?"
Ba ta samu damar amsawa ba suka ƙaraso, ta kuma ɗaga ido tana masu kallon ƙurilla. Hamida ce kawai ba ta sake biyo su ba, tana can teburinsu tare da wani yaro da bai wuce shekara goma sha biyu ba.
Yaya ya ɗaga hannun yana magana ya ce "Wannan ce Halima sannan ga Rufaida." Kafin ya juya kan su yana faɗa mana sunayen su "Wannan Rufaida ce, ina kiranta my sister saboda sunan su ɗaya da Rufaidarmu. This Nabila, (ya tsallake wata ya nuna ta gaban ta), ga Zara, (sannan ya koma kan wadda ya tsallake) wannan kuma Hasina. Lokacin da muna Yola ba ma rabuwa da su, mutane na ne na kusa."
Ya duƙo wurin kunne na tare da katse mun tunanin da nake yi akan Hasinar, saboda na ga gabaɗaya hankalin ta yana kan shi, da kuma me ye dalilin da yasa ya tsallake ta? Ya ce "My ex. Kin tuna da tun farkon alaƙa ta da ke? That's her."
Na ƙara ɗago kaina na ƙara kallon ta, har lokacin hannunshi na zuɓe saman kafaɗa ta suna magana da Nabila. Ashe ita ma Hasinar ni take kallo kamar fuskar ta akwai yanayi na rashin jin daɗi. Katse maganar kowa tayi da faɗi "Buhari mu kima wurin su Hamida, yanzu za mu tafi don mun daɗe a nan ɗin ba laifi."
Suna barin wurin na barin wurin, Rufaida ta ci gaba da tsokanarda ta saba "Wai! Ai ɗazun tsokanar ki nake yi, sai yanzu daga waɗannan sannan na san girman halin da ki ke ciki." Sai ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Wasa nake Malama! Nasan tare suka yi karatu a Yola. Amma wannan Hasinar ce dai bangane mata ba, sai wani shan ƙamshi take yi wa jama'a."
"Ai dole tayi tunda Ex ɗin shi ai."
"No wonder! Haba! Ko da naji! Ke rabu da su, your ice cream is melting." Muka kama sabgar gabanmu don ban ƙara wai wayawa wurinsu ba bare na ga me suke yi.
Can ba babu daɗewa na hango wasu ƙawayen mu da su ma regular ne a Hangout irin mu, don ta dalilin haka ne ma muka saba da su sosai. Su uku ne, Zainab, Shukura da Rabi'a (ƙawaye ne ba wai gidan su ɗaya ba). Rufaida na cewa "Bari na ƙarasa wurin su shukura, ina zuwa."
Ba su lura da ni ba sai da na rufewa Zainab ido don ita ce ta farko da na fara riska. Duk muka gama hayaniyar mu ta kwana biyu ba sa ganin mu ko lafiya.
Sai da na zauna sosai sannan Zainab ta zaburo irin ta tuna wani abu ta ce "Yauwa! Gara da na gan ki yau. Yau kwana biyar kenan kullum sai an ba ni saƙo na ba ki. Wani ne ya zo yana ta tambaya wai ko lafiya ƙalau kike don ya kwana biyu ba ya ganin ki a nan. Ɗazun nan ma aka ba nu wani saƙon wai na baƙi." Ta miƙo mun takarda da ragowar wasu katina. Ya ci gaba da magana "Ya damu sosai, kaman sunan shi Yallaɓai ko wa? Ga shi nan dai ki duba."