Free chapter · Read without an account
34
A makaranta ma ina son nayi magana da Rukky amma har zuwa wannan lokaci ba ta yarda magana mai tsawo ta haɗa mu, tsakani na da ita sallama sai wani abin da ya danganci aikin aji. A raina har cewa nake yi ji Rukky da feleƙe tsiya, to idan ba feleƙe ba ina ruwan ta? Ko su 'yan uwan Ya Buharin ba su ɗauke mun wutar da ta ɗaule mun ba, ina ce rayuwa ta ce? Kawai na sa a raina da bala'i ma sai ta kula ni.
Don hakan gab da za mu yi hutu na hange ta can ƙarƙashin bishiya da alama littafin ta take karantawa. Hamdala na yi ganin ita kaɗai ce na je na same ta. Ban yi mata magana ba sam sai ma juya mata baya da nayi na zauna kamar abun duniya ya dame ni ɗin nan. Da ta share can kuma kamar an yi mata dole ta ce "Wai me ne ya dame ki ne?" Sai ta ɗauke kanta kamar ba ita ce ta yi magana ba.
Ni ban ma san zan iya cin galaba haka da wuri a kan ta ba, ashe tana lura da ni ta san abu na damu take wani share ni. Na ce "To ni me ye ba ya damu na? Kin share ni kin yi banza da ni sai ka ce sanin shanu ki ka yi mun. Ni ce har da ɗaukar Yallaɓai na kai maki shi gida don ya taya ni ba ki haƙuri, duk da cewa na gaza fahimtar ainihin abin da ya sa ki fushin nan, maimakon kuma ki haƙura sai kawai ki ka daɗa botsarewa. Yanzu ma haƙuri nake ƙara ba ki, Allah ya huci zuciyar ki."
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "It's okay, kar ki damu, komai ya wuce. Bari na yi karatu yanzu idan mun fito daga jarabawa an jima ma haɗu."
Da muka taso ta yarda ta bi ni kuma kai tsaye gidan su Inna direba ya sauke mu. Rukky kam mamakin ganin su a wani wuri daban ta yi tunda ba ta da labarin gyaran gidan mu balle gaskiyar al'amari. Sai da Inna ta shiga kicin ɗora girki sannan na warwarewa Rukky komai da ya faru har zuwa kan abin da Ya Buhari ya yi da na ɗauka a matsayin cin zarafi da wulaƙanci.
Sai ta ce kar na zargi Ya Buhari akan zantuttukan shi domin yana da damar faɗin dukkan abin da ran shi ya raya masa bare yanzu da yake ganin yana da hujja a hannu. Kawai na sauƙaƙa wa kaina ta hanyar cire hankali na daga gare shi sannan ta yi mun addu'ar ɗorewar alkhairi tsakani na da Yallaɓai.
Bayan kwana biyu Yallaɓai ya dawo, ba'a wani ɓata lokaci ba aka fara filasta sannan aka yi fenti, kuma cikin ƙanƙanin lokaci gida ya haska kuma ya yi kyau ƙwarai da gaske. An yi mun banɗakin zamani a gidan kamar yanda na buƙata sannan aka sanya mun sahiba t AC a ɗaki na, Wayyo ɗadi!
Ka san mun yi magana da shi kafin fara ginin akan zan yi amfani da kuɗaɗen hannu na na gyara ɗaki na, amma ranar da na zo sai na iske har an sanya mun gado da madubi kuma a ranar ya ba ni makullan gidan.
Lokacin da na ɗauko Inna don ta zo ta gani kafin su dawo, ta daɗe tana yi wa Yallaɓai addu'a tana ta zagayen gidan cike da jin daɗi. Kuɗin da su Mommy suka ba su gudunmawa ne ta fiddo ta kuma yi amfani da su wurin yin furnishing gidan, kuma tana kammala wa zasu dawo. Ta ɓangarena ma na ciro kaɗan daga ajiya ta na ƙarasa saka abubuwan da nasan ina buƙata barin ma kayan kallo. Kai! Maa shaa Allah!
Ranar da Gwaggo Safiya ta zo bayan dawowar su Inna ta kira ni gefe guda tana yi mun nasihar ya kamata na yi hankali da Yallaɓai domin ita a ganin ta gara mun Ya Buhari. Kuma ko ba komai an san shi, an san iyayensa da halayyarsa. A faɗar ta shi Yallaɓai fa? Me aka sani game da shi? Shin kullum shi ba a tafiye ya ke ba? Shin an tabbatar mun da cewa ba ya haɗuwa da mata kala-kala a tafiyar ta sa ne? Ta ya ya zan tabbatar ni kaɗai ya ke so? Ta daɗa nanata wa kar a yi gudun gidan gara a faɗawa na zago fa.
Ni kuwa na amsa da cewa "To ai shi yasa Gwaggo na san yana so na, tunda ai yana haɗuwa da waɗanda suka fi ni amma bai ce sai su ba kamar Ya Buharin da ki ke yabo yanzu." Ba ta ƙara magana ba ta bar ni a wurin a tsaye, amma yanayin fuskar ta bai nuna kalamai na sun yi mata daɗi ba. Na ja ƙaramin tsaki ina cewa haka kawai mutane sun bi sun dame ni saboda na samu mai kuɗi? Wa yake son talaka da za'a dame ni? Aikin banza kawai!
A ranar da daddare na je na samu Mommy tare da nuna mata sha'awa ta na komawa gidan mu da zama, amma ba wai a take ba don zan dinga yin kwanaki a ɗakina na gidan nan sai kuma wasu kwanakin a can gida. Ƙwarai ta nuna damuwar ta don tsare ni da tambaya ta yi ko an yi mun wani abu da ban ji daɗin shi a gidan, na ce wallahi babu abin da aka yi mun amma idan haka take gani to na fasa komawa gidan Inna bari na ci gaba da zama na anan kamar yanda na saba. Ta ƙara tambaya akan tana fatan ba zancen Buhari a cikin dalilai na na son tafiya gida ko? Domin ƙaddara ce ta raba mu kuma ba wanda ya san gobe ban da Allah. Nan ma na tabbatar mata ko kaɗan babu shi a ciki, don haka sai ta ce ta yarje na dinga raba zaman nawa tsakanin gidaje biyun.
Ta ce "Ai kin san ɗiya ce ke ko Halimatu? Kuma zai kasance hakan a tare da ni har abada. Ɗakin ki na nan gidan da kayan ciki duka mallakin ki halak malak, duk abin da ki ke son ɗauka daga wannan ɗakin ki kai can ba sai kin tambaye ni ba, idan ma duka za ki kwashe to maza a bada himma 'yar Mommyn ta."
Kunyar Mommy ta kama ni sosai ganin da zuciya ɗaya ta riƙe ni baiwar Allah, don tuni tayi moving on akan abin da nayi duk kuwa da cewa bai yi mata daɗi ba. Allah ne kaɗai zai biya su abin da suka yi mun.
Rufaida ma jikin ta ya yi sanyi, tashin nawa bai yi mata daɗi ba sam. Ita ta taya ni ɗaukar abubuwan ƙawata ɗaki da na ɗauka daga ɗakina na gidansu zuwa sabon ɗaki na, har wanda ban damu na ɗauka ba ita ta ɗaukar mun domin a faɗar ta so take ta ga ɗakina tsaf-tsaf. Kuma kasancewar mun yi hutu don haka sai da na kwana uku a gidan Inna kafin na juyo gida wurin su Mommy. Ɗokin sabon wuri kawai nake yi amma ai gidan mu bai isa ya jera da na su Mommy ba don ko ɗakunan baƙin su ya kere gidan mu nesa ba kusa ba.
Ranar da na koma na samu labarin Ya Buhari ya zo, ashe tun ranar da na je gidan Inna shi ma ya duro gari, ɗazun nan ya koma kafin zuwa na. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mun ba domin babu abinda na ke tararrabi da rashin so irin haɗuwa ta da shi.
Na koma na iske Mommy na shirye-shiryen tafiya tare da Daddy sati mai kamawa. Rufaida ta ce a wurina za ta zauna har su dawo amma sai Anty Aysha ta dage akan ta dawo gidan ta tana taya ta abubuwa ko don albarkancin tsohon cikin da ke gare ta. Cewa ta yi mu zo ni da Rufaida amma har yanzu ina jin kunyar su don haka na ɗan cije na dinga zamewa har ta haƙura.
Ban ƙara komawa gidan Inna ba na bari sai ranar da za su tafi tukunna. Daddy ma ko a fuska bainuna ya san an yi wani abu a gidan ba game da ni da Ya Buhari, bai canza mun ko da na daƙiƙa ɗaya, kai an ya ma ya ji zancen?
Ana gobe za su tafi ya kira mu falon shi ni da Rufaida lokacin suna tare da Mommy. Ya raba mana kuɗi kamar yanda ya saba idan zai yi tafiya, wannan karon har da ƙari saboda zai tafi backup plan (Mommy) ɗin mu. Ya yi mana faɗan ba ya son su dawo daga tafiya su samu labarin rashin kyautata wa daga gare mu ganin muna zaune a hannun yayar mu ba Mommy ba. Mu kasance ma su bin na gaba, kar ya ji labarin an ce mun raina wani ko wasu. Wata irin nasiha mai ratsa jiki ya yi mana, ni dai a raina cewa na yi don ya ɗauki Mommy za su tafi ne shi yasa hankalin sa ya ɗaga a kanmu tun da idan ya bar mu da ita ba ya taɓa damuwa. Kuma daga maganar shi bana tunanin ya san ni ba gidan Anty Aysha zan zauna ba.
Kashegari, Anty Aysha da mijinta suka zo yin sallama da tafiya da Rufaida. A falo muka haɗu ana ta hira har zuwa lokacin da Daddy ya kammala shirin sa ya fito da sauri. Muka haɗu muka yi masu rakiya bakin mota ni dai ina jin babu daɗi, Mommy saboda mu ba ta yin nisa ko kuma ta sa mu a gaba mu tafi, ga shi wata guda za su yi! Daddy ne zai tuƙa don ba da direba zasu tafi ba, a yayin da Mommy ke zaune a kujerar kusa da shi bayan ta rurrungume mu tana faɗin "ku kular mun da kan ku gimbiyoyi na."
Mun tsaya muka rurrufe ko'ina da kashe kayan lantarki na gidan gabaɗaya don ma'aikatan cikin gidan kowa ya tafi sai idan su Mommy sun dawo kuma, Iya Delu da ta rage da Kuku ne suka yi mana sallama suka wuce. Makullan motocin na hannun Anty Aysha bayan direba ya rufe komai da tampol ya ba ta.
Kammala rufe ko'ina ya sa su Anty Aysha suka fara haramar tafiya, ni kuma ta ce na jira maigadi ya taya ni mu rufe gidan gabaɗaya sai na tafi sannan sati ɗaya jal ta ba ni a gidan Inna, satin na ƙarewa na tabbata na zo gidanta kuma idan ban zo ba to na sani fushi za tayi da ni ba ɗan kaɗan ba. Haka na jira duk muka ƙarasa sannan na wuce gida, a can kuma Inna ta ce Anty Aysha ta kawo mijinta ya gaishe ta sannan sun faɗa mata zan je na same su nan da sati ɗaya.
Kasa zaman nutsuwa nayi a gidan Inna saboda kewar su da ta cika ni, sannan ga faɗuwar gaba ina ta jera ta kamar mai tasbihi da carbi. Na ji ba zan iya zama ba sai kawai na yi wanka na tafi gidan su Rukky don ta ɗebe mun kewa na yi zama na. Su Maryam ma ta yi mun hira amma na kasa fahimta, haka kawai nake zama distracted babu dalili kuma jiki na ya yi sanyi sosai.
A kuma wannan ranar ne na fara sabawa da Yaya Ahmad ɗin su domin shi ya yi ta damu na akan na faɗa masa me ye ya dame ni. Irin lallaɓanin da ya dinga yi har sai da hakan ya hana ni sakewa, to ni kaina ban san me ye yake damu na ba bare na faɗawa wani don haka sai kawai na dawo gida abu na.
Na koma na iske masu jona satellite suna aikin sakawa wai Yallaɓai ne ya turo su a sa. Ban daɗe da dawowa ba suka kammala kowa ya yi nasa wuri. Na zauna na fara gwada tashoshin, kowanne kuma yana yi. Maimakon hakan ya ɗauke mun rashin jin daɗin da ke tattare da ni amma sai na ji kaman takura ni ma ya ƙara yi.
Tashar ARTV na juya na kama, na yi tsaki na mayar zuwa NTA ni ban san me nake nema a wurin ba domin tasoshin nan biyu babu abinda ya ke haɗa ni da su. Ina ga an sa breaking news sai hankalina ya tattara akai, ƙila ma abin da ya jawo hankalina zuwa gare su kenan.
Ban san lokacin da na ƙwala ihu ba, a take na ji kaina ya amsa wani mugun ciwon kai da ban taɓa jin irin sa ba ya dirar mun a take sai kuma jiri ya ce salamu alaikum. Na kasa gasgata abin da idona ya ke gane mun, anya ba mafarki ba ne?
********************
Na ɗago idona na kalli Abban da ke zaune gaba na babu alamar ya gaji da saurare na. Sai a lokacin na lura da duhu ya fara domin ban ganin fuskar shi tar-tar. Hakan ya sanya ni kallon agogon waya ta domin sanin ko ƙarfe nawa ne yanzu, missed calls guda bakwai na gani a yayin da agogon ya nuna ƙarfe bakwai da minti ɗaya.
Na fara jujjuya wuya saboda riƙe war da naji ya yi na ce "Abba gara mu koma gida duhu ya riga ya fara, duk mutanen wajen nan sun watse. Mu je mu fara sallah tukunna sai na ƙarasa maka in shaa Allah."
Gidan Yaya Khadija muka wuce muka yi sallar a can. Ba yanda ba ta yi da mu na mu tsaya mu ci abinci ba, amma daga ni har Abban mun dage kan cewar mun ƙoshi ga shi kuma sauri muke yi na yi dare a waje kafin Baban Zaria ya fara faɗa. Marmarin abinci a dai-dai wannan lokacin bana yi, ko wanda ya siya ɗazun suna motarsa ba abin da muka ci a ciki.
Shi kuma saurin da yake na son mu baro gidan Yaya Khadija domin ya ji ƙarashen me ya faru ne. Can gida muka koma, na shiga na faɗawa Gwaggo Hafsatu na dawo amma ina ƙofar gida ko ana nema na. Kayan jiki na na sauya zuwa doguwar riga mara nauyi kafin na koma waje wurin Abban da ya ke jira na.
*********************
Abinda na gani da ya yi matuƙar girgiza ni a talabijin shine hoton hatsari da aka nuna, ba kuma hatsarin ne ya tsorata ni ba sai ganin motar da aka yi hatsarin da ita. Motar ta karya makarin gada sannan hancin motar yana kallon ruwa don kaɗan take jira ta gangara cikin ruwan. Motocin agaji sai tahowa suke yi domin ceton rai. Motar da su Daddy suka tafi a ciki ne, ko daga bacci na tashi zan gane ta balle kuma ga lambar motar a bayyane ina gani ƙuru-ƙuru.
Na fara ƙarya ta zuciya ta kan cewa ba su ba ne, kamar ana jira na sai na ji an ambaci cikakken sunan Daddy. Kalla nake na kasa kashewa ga shi gabaɗaya tunani ya rufe har ba na jin me suke faɗa a labaran. Jikina sai kaɗawa yake yi kaman mazari saboda kallon motar na daɗa sa wa ina tsinkewa da lamarin hakan ne kuma ya ja nayi ihun da na yi.
Na dafe kaina da ke azabar ciwo na zamo ƙasa na kwanta ban san me nake yi ba, ina dai tuna lokacin da Inna ta zo tana girgiza ni tana buƙatar jin me ya faru. A gigice nake nuna mata TV ina maimaita "Daddy. Mommy. Wayyo Allah. Mommy." Daga nan kuma sai komai ya ɓace mun ɓat!
Lokacin da Baba ya dawo daga kasuwa jikinsa a sanyaye ya shigo, haka ya riski Inna ita ma jikin ta a sanyaye. Ni ma cikin ikon Allah na samu nutsuwa a daidai lokacin domin ina iya gane me suke faɗa daga cikin ɗakin da nake kwance. Inna ce ta fara magana "Sannu da zuwa Malam. Sai kawai muka samu labari mai tayar da hankali."
Baba ya amsa "Ashe kuma kun ji rasuwar ta su kenan! Hmm! Allah Sarkin sarakuna, mai yin yanda ya so...."
Inna ta katse shi cikin rawar murya, a yayin da nayi zumbur na miƙe tsaye da wani ƙarfin da ban san a ina na same shi ba domin son jiyo gaskiyar abinda na jiyo, ta ce "Rasuwa ko dai hatsari Malam? Ɗazun nan aka nuna a talabijin, Halimatu tun ɗazun da ta faɗi bayan ta gani har yanzu ta na kwance a ɗaki ba ta da lafiya."
Baba ya ja numfashi ya amsa "Ƙwarai! Rasuwa ce domin labarin ya bazu a kasuwa na cewa Alhaji da Hajiya sun yi hatsari sun kuma rasa rayukansu. Waya aka bugo aka faɗawa wani mai gidana da ta hannunsa Alhajin ya samo rumfa, in taƙaita maki gaisuwa ya zo yi mun shi ne ni ma na samu labarin tun ina kasuwar....."
Bai ƙarasa zancen sa suka jiyo ni na yi wata firgitacciyar ƙara da ta sa suka zaburo zuwa ɗakin nawa, suna shigowa ina sumewa.