Free chapter · Read without an account

Chapter 67-68

by Maryam Abdul'aziz · HAFSATUL-KIRAM

HAFSATUL-KIRAM


 

 ©Mai kosai


      FCW



Babi Na 67-68



   Bayan Kwana Biyu



Yau ta kama ranar asabar, ranar hutu babu aiki. Tana zaune gaban sistem(system) na ta, yayin da ta duƙufa kan ganin yadda zata saita al'amuranta na takun sakar da take yi tsakaninta da waɗancan mutanen da sam basu da tunani balle hankali.



Dija ce ta shigo ɗajin, hankalinta a tashi. Kwananta biyu a gida, kasancewar tafiyar gaggawa ta kama mijinta wato barista Jahid.


 "Lafiya dai Dija?" Hafsa ta tambayeta, bayan ta ɗago kanta daga dunƙufen da ta yi.


 "Ina fa lafiya, yanzu ina kwance ƙawata ta kirani wai na hau shafina na fezbuk(facebook) na ga abin da ke faruwa. Da na tambayeta mene ne? Sai ta ce na hau kawai, banƙi tata ba, don kin san an ce mutum bayaƙin ta mutane an ce da ɓarawo gudu! Amma sam shafin yaƙi buɗewa ko da na hau, sai na sake kiranta shi ne take ce mini hotunan batsa ake ta ɗorawa a shafin nawa, don haka na hanzarta na cire, kada masu ganin ƙimata su gani mutuncina ya zube a idanunsu. Wallahi hankalina ya tashi sosai."


 "Subhanallahi! Mu ga wayar, mene ne mabuɗin sirrin?"


 Hafsa ta ce, tana amsar wayar daga hannun Dija. Daidai nan Nisha ta shigo, tana waya.



 "To ai mabuɗin sirrin ba daidai ba ne, an ya kin riƙe mabuɗan sirrin kuwa?"



 "Wallahi su ne Hafsa, ni ban taɓa sauya su ba."



 "Me ke faruwa?" Nisha ta tambaye su, bayan ta yanke kiran.



Nan Hafsa ta hau kora mata bayanin komai. Murmushi ta yi, kafin ta ce,


 "Wannan ai ba zai wuce aikin masu madatsin shafi ba wato (hacker)."



  "Innalillahi! Yanzu mene ne abin yi?" Cewar Dija, hankalinta duk a tashe, zufa na wanke mata saman goshi.



 "Ka da ki damu, zan shiga na datse shi, shi ma." Cewar Nisha tana wani murmushin mugunta, haɗi da janyo kwamfiyutarta.



Nan ta shiga taɓe-taɓe a kwamfiyutar, tana yi tana yi wa Dija tambaya game da shafin nata. Ta jima kafin ta kalli Dija ta ce,


 "Za'a turo wasu lambobi, ki yi maza ki sanar da ni."


 Bata daɗe da rufe baki ba, aka turo, nan Dija ta shiga gaya mata. nan ta shiga shigar da su, bayan ta saita komai ne ta sanar da Dija wasu sababbin lambobin sirrin nata, tare da umartarta da ta hau shafin. Ai kuwa tana hawa ya buɗe, bayan ta saka lambobin da ta bata. Murna suka yi sosai, ganin komai ya yi daidai.



 "Wallahi na tsorota da sosai, bari na yi maza naje na bayar da haƙuri, na gayawa masu bibiyata ba ni ba ce." Cewar Dija.



 "Ai a duniyar nan akwai abubuwa kala-kala. Wannan al'amari na kuste cikin asusun mutane da shafuka na yanar gizo ya zama ruwan dare gami duniya, domin abu ne da yake sananne da aka jima da saninsa. Sai dai mu ce Allah ya shiryi masu yi." Cewar Nisha.


  "Amin." Suka amsa a tare.



Dija ta fice daga ɗakin cije da murnar da ta cika mata zuciya, wanda a daidai nan ne kuma taga shigowar kiran mijinta barista hajid cikin wayarta, tasan ba zai wuce tatsuniyar gizo, yayin Nisha ta kwanta kan gado, ta ɗau wayarta tana danne-danne, Hafsa kuwa ta ci gaba da abin da take yi.

Suna haka Afna ta sigo ɗakin, ganin anti nan nata su biyu ya sata gaisar da su a tare. Kusa da Hafsa ta zauna, tare da furta,


 "Anti sarkin aiki. Wai bakya gajiya ne?"



 "Ina na ga hutu, ni da ke tara kuɗi, tun da dai ina da 'yan mata kamarki."



Dariya suka yi a tare, kafin Afna ta ce,

 "Anti kin san jiya me kuwa malamin da yake yi mana kemistiri(chemistry) ya sanar da mu kuwa?"


  "A'a sai kin faɗa."



 "Ilimin kimiyya, da yadda yake, da rabe-rabensa, da wasu bayanan ma ya baje mana a fai-fai wai duk mu san su."


 "Lallai kun caɓa. To ni ma a sanar da ni." Hafsa ta ce.



Afna ta tanƙwashe ƙafa, har da gyaran murya kafin ta ce,

 "Wato dai shi ilimin kimiyar nan, ilimi ne na nazartar abubuwa, ɗabi'a da suke kewaye da mu 'yan adam. Amma shi ilimin ya dogara kan wasu matakan gano haƙiƙar abubuwa, ta hanyar gwaje-gwaje da ake kira "experiment" a turance, ɗakin da ake gwaje-gwajen kuma shi ne ake kira "Laboratory". Akwai masu kimiya na lura da yadda ɗabi'a ke tafiya a sararin duniya ta hanyar ɗanɗano, ji, gani, ko shinshina.

Sannan ita kanta kimiyar ta rabu gida daban-daban waɗanda ya haɗa da: ilimin kimiyyar rayuwa(Biology), da ilimin kimiyar duniya(earth science), ilimin kimiyar na'urar kwamfiyuta(Computer science), ilimin kimiyar sinadarai(Chemistry) da kuma ilimin fiziya(physics)."


Ta ɗan zuki iska kafin ta ɗora,

 "Akwai kuma wasu ilimin da yawa bayan waɗannan da suka fita ƙarƙashin kimiya, duk da su ma na kimiyar akwai wasu bayan waɗanda na zayyano miki. Kamar ilimin sararin subhana da ake kira da "cusmology", na taurari(Astronomy), na ƙananun abubuwa da ake kira "Quantum mechanics" su duk sun fice daga na kimiya da dai sauransu.

Bayan su kuma, akwai wasu ilimin su ma waɗanda su suna kwatanta yadda kimiya take a tsarin bincikensu. Irin su kimiyar jama'a(social science), kimiyar tattalin arziƙi(wacca take daban a ayyukan tattalin arziƙi), sai kimiyar siyasa(political science) da kuma na halayyar jama'a(sociology). Saboda suna ƙoƙarin nazartar ɗan ada ko jama'a, kuma su fitar da nazura da suke ƙoƙarin sharhi na musamman kan dalilin da ya sanya ani ke faruwa a cikin jama'a.

Shi ilimin kimiya, fanni ne mai kula da abubuwa kamar ruwa, iska, daskararren abu da sauransu. Wanda kimiya na sarrafa waɗannan abubuwan don ƙera waɗansu, yawancin duk abubuwan da muke amfani da su kamar lantarki, roba, mai, takalmi, mota, keke, jirgi duk sarrafa su ake yi daga kimiya."


Mai kosai✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.