Free chapter · Read without an account
04
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐️
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
*** page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
*BABI NA BAKWAI (7)*
“Meema event center zaka kaimu”
Muryar Anti Fati ta faɗi bayan sun fito daga gidan sun tsaya a bakin titi, sannan suka tsaida me napep.
“Ku shiga muje to”
Anti Fati ta juyo tana kallon Maryam wadda ke tsaye a bayanta sai gyara zaman gyalen dake jikinta take, ita jinta take kamar tsirara, gaba dayanta a takure take dan bata saba ba.
“Muje”
Tana ta jajjan mayafin daga baya ta shiga adaidaitar, ta kar6i Imran daga hannun Anti Fati, sai waige-waige take kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.
Da haka suka isa katafaren sabon event center din da aka bude a hadejia kwanannan, tun daga bakin gate Maryam ta tabbatar da ba bikin ƙananun mutane suka zuba, dan tun daga maka makan motocin dake parker a harabar wajen, zuwaga mutanen dake kaikawo a wajen da yanayin suturunsu zaka tabbatar da ba ƙananun mutane bane, Maryam ta kama kanta tana bin Anti Fati a baya.
TAFIDAH POV.
_🎶If this is a dream babe i don't wanna wake up ooh yeeh !_
_This is too sweet to be real babe i don't wanna wake up oooo yeeeh!_
_You give me life you give me vibe ooh, you be my energy i can't deny oh_
_Super man you will be my hero what is love if you not there ?_
A hankali wakar Sweet wadda Rayvanny tareda Guchi suka rera take tashi daga cikin home theater ɗin dake katafaren falon gidan Tafida.
Daga can kan wata kujera ta zaman mutum uku kuma shine kwance, idonsa a lumshe yana bin wakar a hankali, yayi nisa a abunda yake, har Muktar ya buɗe ƙofar bema sani ba, dan hankalinsa gaba daya yana kan sauraron waƙar, saida muktar din ya ɗan daki ƙafarsa sannan ya bude idonsa, har yanzu kalar idon nasa tana nan yanda ya tashi da ita tun safe, ja har yanzu bata sauya kala ba.
Miƙewa yayi ya zauna, yayinda Muktar ya ƙarasa ya kashe waƙar, ya dawo kusa dashi ya zauna.
“Ba hakane ya kamata ba, kamata yayi ace ka kunna karatu ba waka ba, kallifa idonka har yanzu bai sauya ba”
Tafida ya yi murmushi me ciwo, ba sai ya faɗa masa ba cewa a duk lokacin dayaji karatu ji yake kamar ruhinsa zai fita tareda baƙin ruhin nan ba, shima da kansa ya san da hakan, sai kawai ya juya ga wayarsa ya dauki ɗaya daga ciki ya shiga dannawa.
“Abincine Madam ta turo maka”
Wani murmushi ya su6ucewa Tafida, a gaba ɗaya cikin abokansa babu wanda bashi da aure harda yara, amma shi banda shi, dan koda wasa bashida tsarin yin aure a yanzu.
“Ina lil me ?” (yana nufin me sunansa dan gidan Muktar ɗin)
ya faɗi yana aje wayar dake hannunsa
“Yana nan, zasuje gidan kamun ai, wata ƙila ku hadu”
Muktar ya bashi amsa yana zuba masa abincin, shi sai yanzuma da yaga abinci sannan ya tuna ashe baici abincin ba tun safe, dan yana fita daga fada gidansa ya wuto aka fito masa da dokunansa sbd hawan angwancen, ya shirya suka tafi hawan kuma basu dawo ba sai dazu, shine yayi sallah ya kwanta yana hutawa har Muktar ɗin yazo ya sameshi a haka.
“Zakaje wajen kamun ne ?”
“Shi ya zama dole, su Mairama zasu zo fa, kuma da mahaifiyar Amina ne bama shiri ba wai da ita ba”
Tafida ya faɗi yana kaiwa abincin bakinsa, kuma daga haka babu wanda yaƙara cewa komai a cikinsu har ya gama cin abincin, ya tashi ya shiga dakinsa ya shirya sannan ya fito, cikin wata baƙar shadda wadda tayiwa farar fatarsa kyau, sai sheki take cikin hasken fitulin parlon, hannunsa rike da hular da zai saka, ya tako har cikin parlon sai baza kamshi yake.
Muktar ya miƙe yana kallonsa hannunsa na dama yakai ya tura gashinsa baya, wani abu daya zame masa al'ada, sannan ya saka hular a kansa
“Idanka ya dawo daidai”
Muktar ya faɗi ganin ƙwayar idon nasa ta dawo dai-dai, ma'ana ta dawo ainahin kalarta wato blue. Tafida yayi murmushi kawai, sannan ya buɗe tafin hannunsa ya mika shi saitin inda wayarsa take, nan take wayar ta taso ta sauko a kan hannunsa, wannan ba wani sabon abu bane a wajen Muktar, dan tun suna yara yasan wannan side ɗin na Tafidah.
“Muje ko ?”
Muktar ya gyada kai suka fita, saida suka fara zuwa asibitinsa wadda ya buɗeta a hadejia wato CROWN HOSPITAL, kuma Muktar ne yake kula da ita, bayan sun gama abinda zasuyi suka wuce meema event center.
Tunda ya isa wajen ƴan uwansa suka masa caa, kowa da nasa kalar ƙorafin, wannan yazo ya tafi wancan yazo, masu ƙorafi akan baya xuwa gidansu su sukafi yawa, shide nasa bada haƙuri ne kawai.
A wata kujera dake kusa da ta Mairama wadda take ƙanwa a wajen mahaifinsa ya zauna.
Itama saida tayi nata ƙorafin, kuma kamar sauran itama dai haƙurin ya bata. Daga nan ya shiga hira da yaranta ƴan mata dake wajen, Mairama kam kallonsa kawai take cike da tausayawa, dan abinda ya faru jiyama Fulani ta kirata ta sanar mata.
“Hamma ga ƙawar tawa”
Muryar Nadra ta faɗi daga bayansu, a hankali ya juya yana kallonsu, bama shi kaɗai ba harda mairama da yaranta, girarsa ta haɗe waje guda alamun rashin fahimta, yana kallon ƙawar tata wadda take ta washe baki, murna fal ranta yau taga Tafida kusa da kusa.
“Ƙawata da na faɗa maka jiya”
Nadra ta faɗi ganin kamar hamman nata ya manta da zancen da sukayi jiya, kuma hakaɗin ne ya manta ɗin, dan shi ba komai yake sakawa a ƙwaƙwalwarsa ba, a daidai lokacin ne kuma Muktar da matarsa da kuma ɗansa suka ƙaraso wajen, dan da tare suke kuma bayan zuwan matar tasa ya fita yace zaije ya shigo dasu.
Nan take Tafida ya manta da Nadra da kuma ƙawarta, ya miƙe yanawa me sunan nasa murmushi, yaron ɗan kimanin shekaru uku ya kar6a a hannun Muktar, yana gaisawa da matar Muktar ɗin.
“ Lil me ykk”
Yaron me tsantsar kama da ubansa ya kalli Tafidah
“Lafiya”
“wai ni da me kuke kiransa ne ?”
Muryar Mairama dake bayansu ta tambaya.
“Tafida”
Muktar ya bats amsa
“Gaskiya kun cuce shi, menene wani Tafidah?, da Eshaan ɗinsa ma kuke kiransa dashi”
Cewar Mairama, tana dubansu.
“Wallahi ranki ya daɗe baban ne yake kiransa da haka, kuma sunan sai yabi bakin mutane”.
“Ai kema da lefinki, sunan da uwa take kiran ɗa dashi ai shine suna”.
“Yanzu ranki ya daɗe menene aibun Tafida ?, nagade sunan ɗan uwanki ne”
“sunan ɗan uwan nawa, amma kuma ai shi yarone ƙarami, sunan ya masa girma”.
Sai maganar ta bawa Tafida dariya, shi tun yanada shekara uku suke kiransa da Tafidan, amma bai musu girma ba a lokacin, sai yanzu.
*
Maryam ta kalli Anti Fati dake ta faman hira itada dangin mijinta, zaune suke a kan wasu kujerun dake wajen, ta juya tana kallon amarya da angon da basu jima da shigowa ba, ita kwalliyar amaryace tafi birgeta, itama ta tsara abubuwa da yawa wanda za tayi idan bikin ta ya zo.
Abinda bata sani ba shine, wasu kaddararorin basa zuwama ɗan adam kamar yanda ya so, suna zuwane kamar yanda suka so.
Ita duk sai tajima wajen ya isheta, yanayin kallon da samari ke mata, ga kidan wajen dake hawa mata kai, dan haka ta ɗauki Imran ta miƙe daga wajen, ta ɗan taba kafaɗar Anti Fati.
“zamu ɗan fita waje”
Ta faɗi bayan Anti Fatin ta juyo ta kalleta
“Ina xakuje ?”
“Waje zamu fita”
“To kada kuyi nisa”
“Umhm”
Maryam ta amsa ranta fari tas, dan zata fita waje ta huta da kallon da samari ke binta dashi, gaba ɗaya a takure take, gyalen nan kwata kwata bata jin daɗinsa, tana tafiya tana gyara gyalen.Alokacin ne kuma abun ya faru, matakin farko na sauya kaddararta.
Bata ankara ba taci karo da wata tsohuwa, mayafin da take ta famar gyarawa ya faɗi kasa, kuma ɗaurin ɗankwalin dake kanta ya zame yayi baya, ta ruƙo imran dake barazanar faɗuwa batamabi ta kan gyalen nata ba ta dubi tsohuwar.
“Fan Allah kiyi haƙuri Iya, ban lura da ke bane”
Tsohuwar data tsaya tana mata kallon ƙurilla ta kasa cewa komai, ta tsirawa tawadar Allahn dake goshinta ido, da zirin farin gashin daya Dan leko ta ƙasan ɗankwalin kanta , sai kuma ta kalli wadda take wuyanta, gabanta ya buga, amma sai tayi dauriyar kallon fuskarta.
“A'a babu komai jeki kawai”
“To iya, sannu kinji”
Maryam ta faɗi tana gyara ɗaurin ɗankwalin dake kanta, tareda janyo mayafinta tafita daga wajen.
A hankali tsohuwar ta juya ga teburin da taga yarinyar ta taso, taga wata Karima wadda ta sani a cikinsu, ta kira sunan Kariman, sannan ta yafitota da hannu, Karima ta taso tazo tana gaisheta.
“Wayece waccan wadda ta taso daga teburin ku ?”
Tsohuwar ta tambaya bayan ta amsa gaisuwar Karima
“Iya jakadiya, sunanta Maryam, ƙanwar Fatice matar habib”.
Jakadiya tayi shiru tana nazarin maganar
“Karima a ganinki za tayi shekaru nawa haka ?”
Karima ta tabe baki cikin tunani
“Eh banajin zata wuce ashirin da ɗaya.... zuwa da biyu”
Zuciyar jakadiya ta buga wani tsallen murna, dan da alama watan yin arziƙintane ya kama.
“Inace unguwarsu kuma waye mahaifinta ?”
“Iya jakadiya kode ɗanki zaki nemawa aurenta ne ?, naga sai tambayoyi kike jero min”
Jakadiya tayi mata wani kallo, wanda yake nuna mata cewar da gaske take ba da wasa ba, hakan yasa Karima ta tara yaɗonta gu ɗaya tace.
“Aiko da ɗan naki zaki nemawa aurenta da ya dace da mata, yar garko ce, kusa da kan matoya, sunan babanta Tijjani direba”
Wani murmushi ya subuce daga leben jakadiya, tana ƙara bin hanyar da Maryam tabi da kallo.
An ce komai yanada sila, komai yanada mafari, wannan shine mafarin wasu ƙaddararorin, mafarin faruwar abubuwa da dama, silar gyaruwa wasu abubuwa, silar 6qcin wasunsu.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©By Sai Kaska
*** page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
*TAURARI WRITTER'S ASSOCIATION*
*BABI NA TAKWAS (8)*
Maryam tana fita daga wajen ta samu wani wari can nesa da mutane, kusa da inda ake ajebmotoci, ta zauna a kan wani dakali, tana ta mitar ƙaran kiɗan da yayi yawa a ciki, Imran ta zaunar gefe tareda kunna masa cartoon a waya, sai kuma ta ɗago tanata bin motocin dake parker kusa da inda take da kallo, wato su masu kuɗin nan basu da wata matsala a rayuwa, ta faɗi hakan a ranta.
Tafida ya fito daga cikin wajen taron, sbd ya gaji da mitar da ake masa, ga jikinsa dake ɗaukar zafi, kuma kansa na masa ciwo, alamun baƙin ruhinsa na kusa, yazo ya tsaya kusa da motarsa yana ƙoƙarin shiga ya tsinkayi wata murya a bayansa.
“Barka dai”
Sai kawai ya fasa buɗe motar ya juyo yana kallon ma abociyar murya, wata budurwa ce, matse cikin dikin staright gown, kai da ganin farinta kasan na mai ne, ga wata b'ular hanci tayi, mayafinta riƙe a hannu, baice mata komai ba sai tsaiwarsa da ya gyara yana binta da kallo, kuma ko bata faɗa ba yasan me zaisa tazo ta masa magana.
“Idan bazaka damuba dan Allah lambarka nake so, ina sanka da soyyaya”
Ba itace ta farkon masa irin wannan abunba, mata da yawa sun masa irin haka, sbd yasani a karan kansa ba sai an faɗa ba shi kyakyawa ne, amma kuma bayan wannan kyakyawar fuskar akwai wani duhu, duhun da babu wata ƴa mace da zata iya juyashi zuwa haske, wannan fuskar tasa kawai suka sani, basu san ainahin shi ɗin ba.
Eshaan Auwal Tafida bai san cewa akwai mace ɗaya da zata sauya tarin duhun dake cikin rayuwarsa ba, zuwa haske.
Kafin ya samu damar bata amsa, kunnensa ya jiyo masa wata magana a bayan wasu motoci, da farko tsaki akayi kafin yaji ance.
“Aikin banza, wallahi wasu matan basu da kamun kai.....”
Ko ba'a faɗa masa ba yasan cewa abinda yake faruwa tsakaninsu taji, shi yasa take faɗin hakan, dan haka ya mosta kunnensa na dama, wanda yake kusa da inda maganar take fitowa, tayanda yana iya jiyo bugin zuciyar me maganar, ga kuma wani ƴar ƙara kamar ta cartoon, muryarce taci gaba da cewa.
“In banda rashin kamun kai ma me zaisa kazo kana wani cewa namiji kana san sa da soyyaya?”
Aka kuma jan wani tsakin, a hankali take maganar, dan idan ba me ƙarfin ji irin nasa ba babu me iya jiyowa maganar, kuma bayan ta gama maganar sai ya meda hankali wurin sauraron bugun zuciyarta, a hankali take bugawa, sai yaji sautin yana masa daɗi, kamar wakar da yake yawan saurare.
Yayi nisa wajen sauraren bugun zuciyar tata, har baya iya jin abinda budurwa dake gabansa ke faɗi, gani tayi kamar yayi banza da ita, dan haka tayi tsaki ta bar wurin, tana ta mita a ranta na cewar gaskiyane abinda ake faɗi akan Tafida kan bashi da kirki, shi kuma ganin ta bashi damar shaƙar iska yasa ya shiga cikin motarsa yana ta sauraren wannan bugun zuciyar da baisan mamallakiyarsa ba.
*HAKUƊAU GROUP OF INDUSTIRIES, ABUJA*
*Da misalin karfe 10:00 am*
“Uallabai!, yallabai!, yallabai!!”
A firgice Alhaji Muhammad Hakuɗau ya ɗago yana kallon PA ɗinsa, wanda ke ta ƙwala masa ƙira, sai kuma ya kawar da kansa gefe, PA ya samu kujera ya zauna yana kallon ogan nasa.
“Abba me yake damunka ?”
Ya tambaya a matsayinsa na ɗa a wajensa ba wai shugaba da na ƙasan sa ba, Alhaji Muhammad Hakuɗau yayi ajiyar zuciya yana jingina da kujerar da yake zauna a kai.
“Abba ka manta that we are friends, we do'nt use to hide komai wa junan mu”
Maganar taso ta saka Abban murmushi, sai kawai ya gyara zamansa yana kallon PA ɗin nasa.
“Haris abinda ke damuna da yawa, ba duk kai zai iya ɗauka ba”
“Try me”
Abba yayi murmushi
“Matsalar ƴata ce Hanam”
Haris yayi murmushi shima, dama yasan zance gizo baya wuce na ƙoƙi, shi bai taba ganin ƴar me gidan nasa ba, amma a koda yaushe abban bashida abun faɗi ko abun magana akai sai Hanam, hakan yasa shi san ganinta koda sau ɗaya ne.
“Abba a matsayinka na mahaifin ta, addu'a ya kamata ace kana mata, duk da bansan abinda ya faru da ita ba, kuma ka kasance a kusa da ita domin ƙwarara mata gwuwa, ba kazo ka zauna kana tunani ba”.
“Haris Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi”
“Ban gane ba”
“Ina nufin akwai mutuwa, akwai jinya dole wata rana zan zo na rabu da ita, hakan yasa nake san nayi mata aure kowa ma ya huta, amma kuma sam taƙi yarda da auren”.
“A'a abba bai kamata kace haka ba, kamar yanda na faɗa maka kayi mata addu'a just pray for her”
Ya ƙarashe yana murmushi, shima Abban murmushin yayi, Allah ya sani cewa yana matuƙar san Haris, da ace Hanam zata amince da ya saka ya aureta.
Abinda bai sani ba shine, wasu ƙaddarorin suna faruwa kamar yanda muka so.
“To meke faruwa ?”
Sai kuma ya dawo serious, ya miƙa masa file ɗin daya shigo da shi.
“file ne daga office ɗin manager”
Alhaji Muhammad Hakuɗau ya kar6a, ya buɗe file ɗin yana gyaɗa kai.
“Zaka iya tafiya”
“Ok sir”
Ya faɗi yana ƙoƙarin fita, a bakin ƙofa yaci karo da Kamal, babban ɗa a wajen shugaban nasu, wani banzan kallo Kamal ɗin ya watsa masa, dan Allah ya sani cewar ya tsani UCHENNA, dan a kullum mahaifinsu yana fifitashi akansa. Uchenna kam ko kallon Kamal ɗin beyi ba, ya rab'ashi ya wuce.
Ko ina ya wuce sai an kirashi, dan babu wanda bai san shi a kamfanin ba, dan Uchenna akwai raha, barkwanci da kuma haba-haba da mutane.
Office ɗinsa ya shiga ya zauna, tareda ɗora ɗaya akan ɗaya, ya janyo wayarsa ya kira ƙaninsa a waya, suka shiga waya, kuma bai kashe ba saida suka jima suna wayar.
Sai wajejen ƙarfe tara na dare ya tashi daga aiki, ya fito daga cikin ginin kamfanin nasu ya isa parking lot ɗin kamfanin, ya buɗe motarsa ƙirar Honda Accord, ya shiga ya tayar sannan ya wuce gidansa dake Cosgrove Estate Wuse.
Yana shiga cikin kyakywan gidan nasa wuta ya fara kunnawa, sannan ya ya haura sama ya shiga ɗakinsa yayi wanka sannan yayi sallahr isha'i da bai samu yayi ba, ya sauƙo ƙasa ya Shiga kitchen domin ya samawa kansa abinda zaici.
Duk da kyau da tsaftar gidan shi kaɗai yake rayuwa a ciki, babu kowa nasa tare da shi, shi ɗaya yake rayuwarsa.
*Hadejia Emirates*
Mai martaba Abdullahi Abubakar Masu ya tsaya tsirawa matarsa ido, wadda ta gama shaida masa da ta samo yarinyar da ake buƙatar Tafida ya aureta, bawai be yarda da ita bane, saide yana san ya san taya akayi ta samo yarinyar. Suna zaune ne a babban falonsa wanda yake cikin turakarsa, kuma babu me ikon shigowa wajen idan bashi ba ko matansa, sai kuma amintattunsa da suke zuwa su gyara wurin.
“Fulani, taya kika samo yarinyar?” Maganar tasa ta fito cikin ƙasaita kuma a hankali.
“ Bayan abinda ya faru jiya..... Na saka an kiramin Ɗan Masani, kuma ya ƙara faɗamin alamomin yarinyar kamar yanda ya shaida mana a wancan lokacin, kuma na ƙira jakadiya babba mun ƙara tattauna maganar da ita...... Kuma bayan ta dawo daga gidan kamu ne tazo take shaida min da taga yarinyar kuma tayimin bincike akan yarinyar..... Sannan babu alama ɗaya da yarinyar ta rage wadda ake nema”.
Me mai martaba ya sauƙe wani gwauron numfashi
“Na roƙeka ranka ya daɗe....dan Allah ka aura masa yarinyar nan, na gaji da ganin ɗana cikin wannan halin, ina so naga ɗana nima ya warke, na ganshi cikin farin ciki, naga ya tara iyali....”
Sai kuma ta kasa ƙarasawa, sbd kukan daya ci ƙarfinta, me martaba ya rungumeta a jikinsa cikin sigar lallashi
“Amma kinyi bin cike sosai akan yafinyar ?, dan bana so muje mu kawo wadda bata dace ba cikin ahalin mu, garin gyaran gira a rasa ido”.
Fulani taja hanci
“Eh na ƙara sawa an min bincike akanta, yarinyar tanada tarbiyya sosai, kuma daga gareta babu wani aibi, mahaifin ta ne ba mutumin kirki ba”
Me martaba ya gyara riƙon da ya mata a cikin jikinsa sannan ya furta abinda ya zama sannadiyar sauyawar ƙaddarorin Tafida da wannan yarinyar da suke magana akai.
“Yarinyar ce zata zauna da ɗanmu ba mahaifin ta ba, dan haka na ɗauka miki alƙawarin a gobe goben nan za'a ɗaura auren Tafida da wannan yarinya, kamar yanda za'a ɗaura auren Amina da Adam, wannan alƙawari na miki”.
**
A daidai wannan lokaci, a wani ban garen na masarautar Tafida ne yake tafiya cikin nitsuwa izza da ƙasaita, wayoyinsa ne guda biyu riƙe a hannunsa na dama, hannunsa na hagu kuma key ɗin motarsa ne yana tafe yana ɗan kaɗa key ɗin.
Bayace ga dalili ba, amma wannan bugun zuciyar daya saurare ya kawar da abubuwa da yawa a cikin kansa, ya mantar dashi sign ɗin zuwan baƙin ruhinsa, ya mantar dashi komai, sautin ne kawai ke bashi nishaɗi, kamar kaɗawar igiyar teku, yayinda yake tsaye a gab'ar tekun, iskar da tekun ke busowa me ciki da daɗi da ni'ima tana busawa akan fatarsa.
Haka yake jin bugun zuciyar tata, kuma kamar wata waƙa me daɗi daga bakin babban mawaƙinsa, yaso ace ya dawwama yana sauraron bugun zuciyar nan, dan bayan daya shiga motarsa bai fito ba, kuma baiga yarinyar ba.
Kawai de ya zauna yana jin bugun zuciyar tata ne, kuma jifa-jifa yake ji tanayiwa wani ƙaramin yaro magana, alamun ba ita kaɗai bace a wajen, kusan minti goma sha, sannan sai wata murya ta kira sunanta 'MARYAM' a lokacin ne kuma ta tashi ta bar wurin.
Kuma bai dena sauraron bugun zuciyar tata ba har suka fita daga wajen. Sunanta da kuma muryarta dama bugun zuciyar tata baki ɗaya sunyi gaba da zuciyarsa, har cikin ransa yake fatan sake ganinta......
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
©-By Sai Kaska
*** page @Sai_Kaska
*Proud of my first novel*
★TAUTARI WRITTER'S ASSOCIATION★
*BABI NA TARA (9)*
.....Idansa ne ya kai kan Galadima wanda yake tafe Dogarai na take masa baya, kallo ɗaya ya masa ya sheƙar, banda shi Galadima ɗin da bai ko kalli Tafidan ba, dan wata iriyar tsanarsa yake kamar idan aka bashi wuƙa yau akace ya kasheshi zai iya, bayasan Tafida ko kaɗan.
Babban abun haushin ma Tafid shine ya san sirrinsa da babu wanda ya sani kaf duniya, ciki kuwa harda Fulani Sadiya, haka suka zo suka wuce opposite, amma babu wanda yakula wani.
Tafida na shiga turakar Fulani, a parlo na uku ya samu Nadra tana kallo, gaishe da shi tayi sannan ta bishi da ƙorafin ƙin tsayawa ya gaisa da ƙawarta da beyi ba, daga nan tai mishi tayin abinci, kuma bai ƙiba amma sai yace bari yaje yayi wanka.
Bayan yaje yayi wankan ya sauya kaya zuwa farar T-shirt da baƙin jogger pants, ya saka baƙaƙen slide sandales a ƙafarsa, ya riƙo wayarsa ɗaya ya fito.
Yana wannan takun nasa na izza da jan aji, har ya ƙaraso parlo na ukun, dan shi bangarensa na parlo na huɗu, yayinda ɗakunan Fulani da na Nadra yake parlo wajen na shida, kuma akwai wani dogon corridor dake haɗa ɗakunan nasu.
Abincin ta zuba masa, shinkafa ce fara wadda aka dafata da green beans da kuma carrot, sai kuma miyar kifi da daffafen kwai, ta zuba masa pineapple juice ɗin da ke aje a wajen, ya kar'ba yana ci yana ɗan danna wayarsa.
Itama sai ta koma gefe tana kallo, bai tambayeta ina Fulani ba, dan yasan tunda baiganta ba to yau itace keda turaka, ya kai hannu ya tura sumar kansa baya, wadda daga ƙasa wajen fade ɗin ta dan taru, alamar yana bukatar aski, gashi kuma a haɗejia babu me iya askin sumarsa, ko a lagos ɗinma yana manege ne kawai.
Babu inda ake masa aski me kyau, irin wanda yake so kamar a india, idan de yaje shi to dama sumarsa ƙalau zai dawo da ita, kuma cio8 kalar askin da yake SO.
“Canza mana wanna tashar mana”
Nadra ta juyo ta kalleshi kamar zata fasa ihu, dan serice ɗin da take so ake haskawa a mbc bollywood, yau suna hidimar biki bata samu ta kalla ba, shine yanzu take ganin maimaici.
“Ayya mana hamma, ban gani bafa da yamma”
“shikenan ci gaba dakallon ki”
Ya faɗi yana ci gaba da cin abincinsa, dan dama kallon ba damunsa yayi ba, kawaide harufan larabcin ne suka ishi kunnensa.
“Lokaci na ƙurewa kije ki kwanta”
Muryarsa ta fito bayan wani lokaci
“Bari to a gama......”
Wani kallo da ya mata ne yasa ta haɗiye maganar a cikinta, gashi ya kafeta da shuɗayen idonsa, dan haka ƙafarta a likafa ta ɗauki wayarta zata tafi ɗaki, sai ta tsinkayi muryarsa.
“Ki dawo ki kashe kallon”
Tafida bawai a fuskarsa yake da kwarjini ba kawai, hatta da muryarsa kwarjini gareta, da wuya yayi maka magana ka musa masa, dan haka ta dawo ta kashe sannan ta nufi ɗakinta tana masa mu kwana lafiya.
“Sleep tight”
Daga haka shima ya miƙe yabi bayanta, ta wuce parlon ta shiga na gabansa, yayinda shi kuma ya buɗe ɗaya daga cikin ƙofofin dake parlon, wanda shine ɗakinsa.
A bakin gado ya zauna yanajin wani abu na taso masa, jin abun na neman fin ƙarfinsa Yasa ya cilla wayarsa kan gado inda ɗayar ma take, ya dafe kansa yanajin maganganu na yawo a kan nasa kamar kullum, sai yaji gaba ɗaya ɗakin na juya masa.
Sai kawai ya rintse idonsa yana san yayi addu'a kamar kullum, saide ya kasa kamar Kullum ɗin, da wani irin sauri ya buɗe idonsa, tuni ya sauya kala zuwa ja, wata iriyar ƙara ya saki, wanda ta saka bakinsa buɗewa.
A hankali wannan doguwar fiƙar take sauƙowa daga haƙwaransa na sama, ya fita a hayyacinsa, sam baya ƙarƙashin ikon kansa, ya dawo under control ɗin baƙin ruhin nan, miƙewa yayi da sauri, Nan take ƙafafuwansa suka rabu da ƙasa yayi sama, sai kuma aka bugashi da bangon gabar, aka dawo da shi na yamma, kansa duka ya fashe sai zubar jini, wani irin ƙara da kururuwa yake, gaba ɗaya ya sauya ya zama dodo.
Nadra dake zaune a ɗaki ta fashi da kuka, ta tashi ta kulle ɗakinta, gudun kada ya shigo ya illa tata.
Yau abun nasa yayi ƙamari, dan glass ɗin balcony ɗin ɗakin ya fasa ya fita cikin wani irin tsalle wanda yafi ƙarfin ace normal mutum yayi shi, ya ɗale saman rufin turakar Fulani khadija, ya saki wata iriyar ƙara, kamar wani zakin da yayi nasara akan wata dabbar daya farauta, kuma haka sautin ƙarar tasa yake fita, kamar na kura ko zaki kuma kamar na gwagwan biri, yana yi yana yakushin jikinsa.
Fulani sadiya dake maƙale a jikin tagar ɗakinta ta saki wani miskilin murmushi, ta tako ta juyo zuwa cikin ɗakin nata tana kallon Galadima.
“Shi ɗin ne ko ?”
Muryar galadima ta tambaya
“Shi ne, da waye dodo a masarautarnan idan ba shi ba ?”
Tayi maganar a sigar tambaya, amma kuma ba tambayar bace, dan daga ita har Dan nata sun san cewa Tafidan ne
“Ai bazan taba barin Tafida ya zauna lafiya ba, sai naga bayan Tafida da duk abinda yake taƙama dashi”
Ta ƙarashe da wani bussashen murmushi a fuskarta.
“Ɗaxuma na ganshi, sai wani faɗi yake yana taƙama kamar wani ubansa shi ne sarki”
Fulani tayi wani kasaittacen murmushi
“Ko ubansa Tafida bai isa ba, bare shi karan ƙaɗa miya”
“hakane mama, nasan zaki iya”
“dole ne gobe na aika jakadiya taje ta amsomin wannan laƙanin, dan ba a bori da sanyin jiki”
“shi yasa a kaf duniya bani da wata kamar ki”
Fulani tayi dariya cike da nishaɗi.
MARYAM POV.
Tunda suka baro event center ɗin kai tsaye gidan Anti Fati suka wuce, ta ɗauki hijabinta ta mayar, har wata ajiyar zuciya tayi ta nutsuwa bayan da hijabin ya rufe jikinta ruf.
Anti Fati tace mata ta zauna taci abincin dare amma sai taƙi, tace yau dambu sukayi a gida dan haka shi za taje taci, Anti Fati tayi ƙorafi akan me yasa bata kawo mata dambun ba, dan inde Maryam ce tayi abinci to baya kwantai a gidansu, kamar wani abune a cikin hannunta idande tayi girki to babu makawa zaiyyi daɗi.
Da zata tafi Anti Fati ta bata kuɗi da wasu kayan abinci wanda ta tambayi mijinta akan zata bawa Maryam ta kaiwa Maanmu idan tazo, kuma ya amince hardama ƙara mata da kuɗi.
Ta rakota har bakin titi ta hau adaidaita, Imran sai kuka yake akan sai ya bita, dan wata ƙauna Allah ya saka a tsakanin ita dashi, wasu lokutan ma Anti Fati ɗin kance da ace Maryam tayi aure to da cewa zatayi Imran ɗanta ne, yaron yana bala'in kama da ita.
A bakin ƙofar gidansu ta iske Sanata, tana ganinsa ta haɗe rai ta ƙarasa ƙofar gidan, shi kuma tunda ya hangota yake washe baki, dama ya aika yaro ance bata nan, shi ne ya tsaya yana jiran dawowarta, dan yasan bazata wuce magariba ba zata dawo.
Ciki-ciki ta gaisheshi, ya amsa mata da fara'a.
“Rannan kinga ban zo ba ko ?”
Taƙi tace komai ta kawar da kanta gefe
“Maryam ya kamata ace kin faɗa min wani abun ko hankalina zai kwanta, ki faɗamin ra'ayinki a kaina dan Allah”
Maryam tayi ajiyar zuciya
“Sanata inaso kayi haƙuri, a gaskiya yanzu banjin zan iya aure ko kuma sarmunta, kayi haƙuri burina shine na gama karatuna, so dan Allah kayi haƙuri ”
Sanata baiji komai a ransa ba, dan tayi masa magana ne cikin lallashi da kuma nutsuwa irin tata.
“Shikenan Maryam, babu komai zan jiraki har zuwa lokacin da Allah zai sa ki fara tunanin aure”
“nagode daka fahimceni”
“kada ki damu Maryam, ni a koda yaushe me fahimtar ki ne, na barki lafiya”
Maryam ta gyaɗa masa kai, yayinda yake barin ƙofar gidan nasu, Allah ya sani bawai san Santane batayi ba, ita kawai yanzu bata da niyyar yin auren ne, burinta shine ta gama karatu, ta nemi aiki sannan ta ɗauki nauyin mahaifiyarta da kuma ƙannenta, amma ba dan baka ba babu abinda zai hana taso Sanata, domin bashida wani aibu.
Ta ayyana hakan a rantane ba tareda ta san ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta a gobe ba, kaddarar da zata sauya rayuwarta har ƙarshe.
Da sallama a bakinta tashiga gidan, kuma tun daga soro take jin hayaniya da yawa, hakan ke nuna mata cewar baƙi sukayi, ta saka kai cikin gidan tana bin mutanen gidan dake zaune akan tabarma a tsakar gidan da kallo, Maanmu ce itada Muhsin, Hassan, Hussain sai wani Abbalele, ɗan ƙanwar Maanmu wanda yake sa'an su Hassan, kuma dama yana zuwa gidan jifa-jifa.
Ta ƙaraso tana amsa gaisuwar da Abbalelen ke mata, ledojin dake hannunta ta aje a gaban Maanmu tana faɗin
“Maanmu gashi wai injin ya habib” Maanmu ta buɗe tana ta saka masa albarka
“aa yaya kwalliya kikayi ne?”
Maryam taja ta tsaya tayi tunanin da tayi alwala kwalliyar ta koɗe, ashe bata fita ba, banza tayi da Hussain dake mata tambayar ta shiga ɗaki ta saka wata doguwar rigar atamfa mara nauyi ta fito tayi alwala.
Dan zuwa lokacin an fara ƙiran sallar isha ta koma ɗakinta tayi sallah, tana zaune akan sallaya aka ɗauke nefa, bata ko gamayin addu'o'in data saba ba, ta fito daga ɗakin a guje, Allah ya sani tana da bala'in jin tsoro, musamman ma na duhu.
“Ke Maryam lafiya?”
Maanmu ta faɗi tana kunna fitilar dake aje a gefenta, kamar da tasan za'a ɗauke wuta, ta fito waje da ita, sannan ta aje ta a gefenta.
“Babu komai”
Muryarta ta fito cikin ƙoƙarin seta kanta
“Bari naje gidan Iya” (Wato kakar Badar).
Ta faɗi tana saka takalmanta
“Kada ki daɗe fa! ”
“To”
Ta amsa lokacin da ta kai ƙofa
“Tsorata fa tayi”
Hussain ya faɗi yana dariya ƙasa-ƙasa
“Nasani ai, ban san yushe Maryam zata dena jin tsoro ba, ita tsoron nata yayi yawa”.
*
“Ke wallahi kallo yayi kyau, da kika ƙi zuwa in faɗa miki anyi ba ke, Tafida yayi hawa kuma na ganshi dan ma ya rufe idonsa da sun glasses shi yasa ban samu damar ganin his beautifull blue eyes ba”
Maryam taja tsaki, tana mitar ita ko fidar yarane ma ina ruwanta ballan tana wani can waishi Tafida.
“Baki ce komai ba”
Badar ta faɗi tana ta'bata ganin tayi shiru
“Me kike so nace ?”
“say something mana”
Sai ta girgiza kai “I have nothing to say”
“Ai shikenan”
“Ke mu ki kunna mana vedion mana”
“Wallahi kuwa harda yanda ake biryani na ɗauko”
cewar Badar tana buɗe wayarta kirar sumsung.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐️
⭐️ شاء القدر⭐️
©-By Sai Kaska
*** page@Sai_Kaska
*proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*BABI NA GOMA (10)
*washe gari, juma'a*
*Titin barikin sarki, hadejia emirates*
* Da misalin 10:00am*
Ga duk wanda yasan bayan tsohuwar perison, dai-dai kan titin bariki yasan cewa wajen zaman ƴan cacane, mutane masu shekaru harda waɗan da suka fara furfura ne ke zaune a wajen ana kalander, ga kuma masu buga karta, sai hayaniya suke ga warin sigari na tashi a wajen dan ɗaiɗaikune basa busa hayaƙin a wajen, cikin masu busa hayaƙin harda Tijjani direba.
“Tijjani bani kuɗina!”
a hankali Tijjani ya ɗago da kansa ya kalli Wasila, ƴar da batako kai sa'ar yarsa ta biyu a haife ba, amma kalli yanda take wani ƙifi-ƙifi da ido dan tsabar rashin kunya, kuma babu wani baba gatsal ta kira sunansa.
“Haba ƴar Wasil-Wasil, kinsan idan na sam.....”
“Wallahi baka isa ba, kuɗina zaka bani yanzu”
Ta katseshi tun kafin ya ƙarasa maganar, Tijjani ya miƙe ya shiga bata haƙuri, harde ya samu ya kashe bakinta da nera ɗari ta haƙuri ta koma rumfar da take saida abincinta tana aiko masa harara.
Kafin ya zauna wata mota tazo tayi parking a daidai inda suka, gaba ɗayan su suka bi motar da kallo, dogarai suka ga sun fito daga motar har su Uku, gaba ɗaya kowa ya miƙe yana kwasar gaisuwa, dan da gani babu tambaya kasan cewa daga fada suke
“Waye Tijjani anan?”
Wani dogari ya tambaya cikin wata garjejiyar murya, cikin Tijjani ya tsure ƴan hanjinsa suka kaɗa, kadafa ace sarki yayiwa laifi.
“Gashi nan”
Muryar Lautai ta fito yana nuna shi, abokin cin mushen nasa, Tijjani yayi tsilli-tsilli da ido yana binsu da kallo.
“Zaka biyomu muje fada, sarki yana nemanka”
Cikin Tijjani ya ƙara kadawa, har ɗan wani guntun fitsari na suɓuce masa, shiko me zaisa sarki ya nemeshi ?.
“Ko bakaji bane!, ance kada mu maka dole, dan haka salin alin ka biyomu”
“Lautai bari naje na dawo”
Tijjani ya faɗi yana kallon su Lautai, suka gyaɗa masa kai, haka Tijjani ya nufi motar, suka buɗe masa gidan baya ya shiga, ɗaya dogarin ma ya shiga ya zauna, ɗaya ya zauna a mazaunin driver ɗaya kuma yana gefen drivern.
Suka tada motar suka miƙi titi ɗoɗar dan daga wajen da suke zaune zuwa fada wani dogon titine ya haɗa, babu ko kwana ɗaya har suka iso ƙofar fada.
*
Tijjani direba ne durƙushe gaban, Turaki, Ciroma da sarki, dukansu sun kasance ƴaƴan sarkin haɗejia Abubakar Masu na da, kuma sarki Abdullahi shine babba a cikinsu, kaf ƴaƴan sarki abubakar ɗin Tafida da Mairama ne kawai babu a ciki, kasan cewar shi Tafida ya rasu, ita kuma Mairama macace, dan wannan maganar bata mata bace.
Tijjani sai juya maganar da Ciroma ya faɗa masa yake, to tayama akayi suka ga ƴar tasa?, kuma me yasa suke san aurawa ɗansu ita ?, kuma wai a yau, yau ɗin nan fa ?, duk waɗannan tambayoyin kansa yakewa, dan bai isa ya furta musu ba.
“Malam Tijjani kayi shiru?”
Tijjani ya ƙara gyara zamansa, ya kuma durkusawa kamar zaiyyi musu sujjada sannan ya furta abinda ya zama sanadin sauyawar rayuwar mutum biyu.
“Shikenan Malam Tijjani, ga wasu kuɗaɗe nan, tunda an saka lokacin auren a ƙurarren lokaci sai ayiwa yarinya abinda ya kamata”
Da rarrafe tijjani ya isa ga Turaki ya karɓi kuɗin, sannan Ciroma ya faɗa masa daidai lokacin da zaizo masallaci.
Haka ya tashi ya fice suna binsa da kallo.
“Yanzu mai martaba kanaga wannan ita kaɗaice mafita ?”
Mai martaba da tun zuwan Tijjani beyi magana ba sai yanxu ya kalli turaki
“Ita kaɗaice mafita Turaki, ita kaɗaice hanyar da zan iya ceto rayuwar ɗan ɗan uwana”
“Hakane, to yanxu shi Tafida yasan halin da ake ciki ?”.
TAFIDA POV.
_“Eshaan”_ muryar ta fito cikin dariyarta, fiskokinta daya saba gani a kullum sune suke giftawa a hankali, a hankali kuma cikin mabanbantan lokuta. Sai kuma hoton wani lokaci da sam baima san ya auku ba, wata mota ƙirar honda civic ta wancan zamani tana juyawa akan titi, tareda wasu mutum biyu a ciki mace da na miji.
_“Eshaan”_ ita ce kalma ta ƙarshe da ta fita daga bakin macen, har ranta ya fita daga gangar jikinta. Daga can wani kogo kuma wani mutum ne, kansa duk ya tara gashi ga wani farin gari zane a gaoshinsa da ɗugon ja a tsakiya yana ta watsa wani abu a cikin wutar dake ci a gabansa.
Sai kuma fuskarta ta dawo tana dariya tareda faɗin _“Eshaan”_*
“Maa!!, Maa!!!”
Sai kuma ya buɗe idonsa, ya kalli inda yake, a cikin ɗakinsa ne na turakar Fulani Khadija, kamar de kullum mafarkine kamar yanda ya saba, a hankali ya fara ƙoƙarin miƙewa, sai yaji wuyansa ya ƙage, hannu ya kai zai taba wuyan nasa, sai yaga wutar nan, daya saba gani a kullum tana ci a tafin hannunsa, hannun ya dunƙule sannan ya buɗe nan take wutar ta b'ace k'arasa miƙewa yayi, dan yashe yake a tsakar ɗakin, yabi ɗakin da kallo.
Gaba ɗaya yau ɗakin a hargutse yake, wasu kayan ma sun farfashe, mikewa tsaye yayi sannan ya ɗaga hannayensa ya shiga meda kayan da suka faɗo ma ajinsu kuma ba tareda ya ta6a komai a cikinsu ba, yana amfani da ƙarfinsa ne, har ya maida komai inda yake sannan yaje gaban mirror ya tsaya yana kallon kansa, sumar kansa duka ta sauƙo kan goshinsa ta barbaje, gabrigar jikinsa duk ta faffarke, ga raunikan dake jikinsa, hannu ya kai ya cire rigar, a hankali ya lumshe idonsa, gaba ɗaya raunukan dake jikinsa suka fara haɗewa da kansu, kamar bai taba rauniba, sai kuma ya buɗe idonsa, wani abun mamaki yau idonsa beyi ja ba yana nan a blue ɗinsa.
Banɗaki ya shiga yayi wanka haɗi da alwala ya fito yayi sallah sannan ya samu ya sauya kaya, yau juma'a kuma yau za'a ɗaura aure, dan haka ya saka wata farar shadda ƙal, kuma sabuwace dan bai ta6a sakawa ba, ya kawo falmara zabuni maroon color ya ɗora rigar an mata aiki da milk ɗin zare, ya saka hula dara itama maroon, ya saka wani farin takalmi halp cover, ya fito a ainahinsa na jinin sarauta, ya feshi jikinsa da turare, ya tsaya yana kallon kansa, kamar shine angon, sai kuma yaji gabansa ya faɗi, amma me yasa ?, kai ba wannan zancen, wani bangare na zuciyarsa ya ayyana ma sa, ya ɗaura digital watch ɗinsa sannan ya ɗauki wayoyinsa ya fita.
A parlo na biyu ya iske Fulani tana tsaye tana bada umarnin yanda za'a gyara mata parlon, sai kace itace take auren ƴar ba Fulani sadiya ba, ya ayyana hakan a ransa, ƙarasawa yayi ya gaisheta ta amsa tana masa ya jiki, dan Nadra ta faɗa mata komai.
“Baki zakiyi ne ?”
“Ba biki muke a gidan ba?”
Ya gyaɗa kansa a hankali
“Hakane”
Ta ɗan juyo tana kallonsa, a kullum Tafida ƙara girma yake haɗi da kyau, ga wani kwarjini da yake ƙarawa saide kuma a bayan wannan kyan, girman da kwarjinin akwai wata fuska, fuskar da babu wanda ya santa sai makusantasa, idanta ne ya kai kan wani rauni dake gefen kansa.
“Akwai rauni a gefen kan ka”
Ta faɗi a hankali kamar ba ita tayi maganar ba, kuma yaji ɗin, dan a zuciya ne kawai mutum zeyi magana in har kana kusa da shi bai ji ba, a hankali ya lumshe idonsa, nan take raunin ya haɗe jikinsa, kamar wajen bai taba fashewa ba, dama haka yake inde har yaji rauni lokacin da baƙin ruhin ke jikinsa to da zarar ya dawo hayyacinsa yana haɗewa inde har rauni bai haɗe ba a jikinsa to ainahin jikinsa ne yaji raunin.
“Ina zaka je baka ci abinci ba? ”
“Asibiti, zanci a can”
Ta gyaɗa kanta
“Kada ka makara sbd ɗaurin auren da za ayi”
Bai san dalili ba, amma tana maganar auren gabansa ya faɗi, hakan yasa ya ɗigawa maganar auren ayar tambaya amma sai ya gyaɗa mata kai, ya kaɗa kai ya fice bayin dake wajen sai gaisheshi suke yana amsawa.
Kamar yanda ya faɗi ɗin asibitin ya tafi yaje sukayi abinda za suyi shida Muktar sannan suka haɗu gaba ɗaya suka wuce babban masallacin juma'a na garin haɗejia, dan duka ƴaƴan sarki a nan ake ɗaura musu aure.
Tsabar cikar da masallacin yayi kwata-kwata basu samu damar shiga ciki ba, a waje suka samu, can kusa da tsohuwar kotu a nan sukayi sallar juma'ar tasu kafin aka sannar da cewa za'a ɗaura auren, sai suka koma kan motocinsu, suna ɗan hira shida Muktar jifa-jifa samari na wucewa suna miƙo gaisuwa, dan Tafida akwaI farin jini matasa.
An ɗaura aure na farko, wanda ya kasance shine auren Amina Abdullahi Abubakar da angonta Adam Isma'il, su Tafida sun samu sunji sanarwar ɗaurin auren ta hanyar lasifikokin dake manne a kowani b'angare na titin masallacin.
Sai kuma akace akwai wani na gaba, kowa ya kasa kunne yana jiran yaji wani aure za'a ɗaura.
Sunan da aka sanar shine ya saka kowa a shock, an ɗaura auren Eshaan Auwal Tafida da amaryarsa Maryam Tijjani Muhammad.
Damm!, gaban Tafida ya faɗi, a hankali ya sauƙo daga kan motar da yake, wasu abubuwa na masa yawo a akai, shifa kansa ya kulle, kamar ma baya ji da kyau, kuma kamar ya kurmance, aure ?, wai aure aka ɗaura masa ?, to waima da wa aka ɗura masa auren ?.
MARYAM POV.
Yau suka tashi da abun mamaki, dan da wajejen ƙarfe sha ɗaya saiga Abba ya dawo, yazo yana ta wata fara'a da suka kasa gane mata, yau rabonsa da kwana a gidan wajen kwana huɗu kenan.
Ya shiga ɗakinsa ya ɗauko kaya yayi wanka ya saka kayan daya sama ɗin rabonsa da ya saka su tun auren Fati, farar shaddace hadda babbar riga (malum-malum), Maanmu da Maryam dai kawai binsa suke da kallo har ya gama ya fice. Har maanmu na zaton kode aure zai ƙara to in ba baka b me zaisa yana wannan abubuwan ?.
Bayan fitarsa saiga Hassan da Hussain sun dawo tareda muhsin ɗin da suka kaɗo shi a waje yana wasa, suma shiryawa sukayi har Maanmu na basu labarin Abbansu yazo ya fita, suma shirin zuwa masallacin juma'a su kayi, kasan cewar babu nisa sosai daga unguwarsu zuwa masallacin fada, domin titine kawai ya taba fadar da masallacin.
Bayan an sauƙo daga masallaci Maryam na alwalal sallar azhar, yayinda Maanmu ke zaune a rumfar gidan nasu tanajin radio, dan ana rahotone na musanman akan bikin ƴar me martaba, Maryam ta gama alwalar ta zo zata shiga ɗaki Maanmu ta tambayeta ƙarfe nawa, ta tsaya ta ɗauki wayar tata akan window tana faɗo mata lokacin sai wani magana da ake a radio ya ɗauki hankalinta, dan haka tayi shuru tana saurare.
_“Bayan an ɗaura auren gimbiya Amina da angonta Adam sai kuma aka ɗaura wani aure me ban mamaki, saurayin da ƴan matan haɗejia ke ribibi, samarin haɗejia ke ƙaunarsa an ɗaura masa aure a yau ɗin nan bayan na ƴar uwarsa, a da mutane suna tunanin auren ɗaya za'a ɗaura amma kuma sai gashi an ɗaura biyu, haƙiƙa wannan aure ya bawa mutane da yawa mamaki, wannan aure de ba kowani aure bane face auren Eshaan Auwal Tafida, wanda akafi sani da Tafida, ɗa a wajen tsohon Tafidan hadejia, da amaryarsa Maryam Tijjani Muhammad, ƴa a wajen Tijjani driver......._
Iyaka abinda ta iya tsinkayi kenan, wayar hannunta ta sub'uce ta faɗo a dandaryar ƙasa, sabon screen gard ɗin da hassan ya sako mata ya fashe har screen din wayar ma.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*BABI NA GOMA SHA DAYA (11)*
*Bayan Shuɗewar Awa ɗaya*
Malam Tijjani yayi sallama a ƙofar gidansa, kuma ba tareda ya jira an amsa masa ba ya sa kai. Da kallo yabisu ɗaya bayan ɗaya, Maanmu ce sai hassan da hussain da suka zo suka ƙara tabbatar musu da gaskiyar batun ɗaurin auren.
Maanmu ta ɗaga kai ta kalleshi, hannunsa riƙe da huhun goro da kwalin alawa a kai, tunda Maanmu taga haka ta san cewa Shikenan, ta faru ta ƙare. Hawayen da ba ta samu tayi ɗazuba sune suka sulalo mata, alawa da goron ya aje sannan yace.
“Ku shiryata, anjima za'a zo a ɗauketa, kuma gobe zasu wuce lagos”.
“Wai dan Allah malam me kake nema ?, anya ma kuwa kaine ka haifemu?, me yasa zaka siyar mana da ƴar uwar mu ?, dan na tabbatar da siyara mana da ita kayi, dan wannan sunansa kasuwanci ba aure ba, kum.....”
“Ya isa hassan!”
Tsawar da Maanmu ta daka masa ce tasa yayi shiru da maganar da yake, sai aka koma kallon-kallon tsakaninsa da mahaifin nasu, hussain ne ya miƙe shima ya ja hannunsa zuwa ɗakinsu, dan yana ganin hakan itace mafita, dan idan ba hakan yayi ba a yanda hussain yake ji zai iya kaiwa abban nasu duka.
Maanmu ta tsaya tana kallon cikin idon Tijjani.
“Allah ba azzalumin sarki bane, ka riƙe wannan Tijjani”
Tana kaiwa nan ta shige dakinta, shime rigarsa ya kaɗe ya fice daga cikin gidan, ai yau ganima ta samu.
Maryam da ke zaune a ɗaki itada Anti Fati wadda bayan an ɗaura auren kai tsaye mijinta ya wuce gida ya sanar mata kuma bata jira komai ba ta taho gidan ta rushe da kuka, Anti Fati ta riƙota.
“Maryam wai miye na kukan ?, inde har Tafidan da kowa ya sani ne to bakya bina bashin rantsuwa kan zai kula dake, Tafida ba irin ko wani na miji bane, kawai kiyi haƙuri ki ɗau haka a matsayin YADDA ƘADDARA TA SO ”
Maryam taja hanci, daga ɗazu zuwa yanzu har idonta yayi ja tsabar kukan da ta sha.
“Anti Fati ba wannan bane abunda ke damuna, taya za'ayi a aura maka mijin da baka sanshi ba?, wanda baka tab'a ganinsa ba, kuma Anti Fati ko kaffara bazanyi ba kan kuɗi suka bawa Abba ya aura musu ni, Anti Fati me yasa Abba zai min haka ?, me yasa ?”
Ta faɗi tana nuna kanta, cikin muryar kuka, sai kuma ta share hawayen dake zubo mata.
“Anti Fati kinsan de yanda gidan sarauta yake, yanzu daga na shiga gidan ganina zasu dingayi da wannan tabon da Abba yayi min, zasu dinga min kallo ƙasƙanci, above all ƴan matan dake haɗejia sai ni?, Anti Fati why me ?, why ?, shikenan rayuwata ta zo ƙarshe anti fati, garinma zan bari zan bar kowa nawa na bar karatuna na barku, mutafi can ta yanda zaiji daɗin min gori”
Anti Fati ta rungume ƙanwar tata, ta san Maryam kamar yunwar cikinta, Maryam tanada haƙuri da kuma b'oye abinda ke ranta, tunda kuwa take faɗin hakan lalle abin ya kai ta ƙarshe.
“Ina imanin ki ya tafi Maryam ?, kiyi haƙuri ki ɗau hakan a matsayin ƙaddara...”
Guɗarn Badarce ta tsayar da Anti Fati daga ban bakin da take ma Maryam ɗin, ta shigo ɗakin sai wani fara'a take kamar itace amaryar.
“Iskanci, miye na wani kuka ?, ai ƙawata farin ciki zakiyi ba kuka ba, Tafida ?, hmmm Tafida fa kika aura Maryam”
Ta ƙarasa shigowa ɗakin tana wannan batu, batun da ya ƙara karyar da zuciyar Maryam ta fashe da wani sabon kuka, hakan yasa Badar ta fuskanci cewa abun ba na wasa bane, dan haka ta zauna itama aka ɗora sabon shafin rarrashin da ita.
Kan kace kwabo har gidan yacika da ƴan uwan Maanmu dana Abba, Anti Fati ce ta saka Badar ta tsefe mata kai, ira kuma ta mata kitso, zuwa lokacin ta dena kuka dan taga koma me zatayi ba fasa auren za'ayi ba, tunda an riga an ɗaura, wai itace ta auri Tafida, abun ya tsaya mata a rai. Gaba ɗaya ta rasa takamemen tunanin da za tayi.
*Hadejia emirates*
"Wai Tafida yayi aure ?”
Muryar Fulani ta fito cikin wani irin nishaɗi da bazaka iya musaltawa ba, ƴaƴanta ne biyu zaune a gabanta cikin dakinta da babu wanda yake shiga sai ita da yaran nata, Galadima da Maimun, Galadima yayi murmushi.
“Ai ni abun ya min daɗi, duk irin wannan so da ƙauna da ake nuna masa amma haka akayi aurensa lami”
“To ni so nakema na san dalilin yin auren” cewar Maimun
“Zai wuce so suke su halaka ƴar mutane, yau in ba haka ba sa aura mata Dodo”
Gaba ɗayansu suka saka dariya, Fulani Sadiya tana cikin farin ciki domin yau an ɗaura auren ƴarta ga kuma maƙiyin ɗanta anyi masa aure irin wanda ba kowani ɗan sarauta za'ayiwa ba.
A daidai wannan lokacin da suke wannan dariyar a wani b'angare na fadar, Tafida ne zaune a ƙasan lallausan carpet ɗin dake falon Me Martaba, wanda yake ganawa da iyalansa, a zaune akan kujera kuma Sarki ne, da Turaki, Ciroma da kuma Mairama sai Fulani Khadija.
“Eshaan”
Ciroma ya kira sunansa, chikakken sunansa, a hankali ya ɗago da kansa ya kalli iyayen nasa, sannan ya amsa.
“Na'am”
Gaba ɗaya ya sauya a cikin yinin nan kawai, ya cire zabunin dake jikinsa ɗazu, kansa babu hula gaba ɗaya gashin kansa ya sauƙo ya baje a goshinsa dan har ya rufe girarsa sai idonsa kawai ake gani.
“Munsan cewa mun isa da kai, shiyasa ma muka yanke wannan hukuncin ba tareda munji ra'ayinka ba, munsan cewa kanada hankali da kuma biyyaya, munsan cewa kai ba kamar ɗan uwanka Habibu kake ba, kana mana biyyaya a koda wani lokaci, bamu tab'a aje kara munce kada ka tsallaka ka tsallaka ba, kana binmu sauda ƙafa, to dan hakama a wannan karon muna so kayi mana biyyaya kamar yanda ka saba, muna so ka kakarb'i auren nan hannu bibbiyu, ka riƙe yarinyar nan da amana, munsan ka san cewa aure ba abun wasa bane, inshaallah idan kayi biyyaya a gaba sai kayi alfahari da wannan auren, ka ɗauki wannan auren a matsayin YADDA ƘADDARA TA SO ”.
A lokacin shi kaɗai yasan abinda yake ji, sam ya kasa wani tunani me kyau, ya rasa a wani matsayi zai saka wannan auren.
“Inshaallah zaku sameni a matsayin me bin umarninku kamar yanda na saba”.
Masomin kaddarar kenan, Daga haka aka soma.
*Da misalin 09:00pm*
Tafida ne zaune a parlon gidansa, tunanuka barkatai a kansa, shi ya rasa inda kansa yake, baya gane komai tun bayan da amace an daura musa aure.
“Me yasa baka san auren nan ?”
Muryar Muktar ta tambaya, wanda yake zaune a gefensa, Tafida ya gyara zamansa, tareda kai hannu ya tura sumar kansa baya, dan yau ta sauƙo masa kan goshi.
“Muktar su Me Martaba sun tafka babban kuskura, ni sam ban cancanci zama da kowa ba, kaɗaici shine abinda ya kamaceni, bai kamata ace ina rayuwa da wani a kusa dani ba, yarinya tana can tana rayuwarta suka rabota da danginta da farin cikinta suka aura mata ni, ni bancanci zama da kowa ba Muktar, sun lalata rayuwar ƴar mutane a banza”.
“A'a Tafida ba haka bane, tunda de har kaga hakan ta faru to tabbas akwai abinda Allah ya hukunta a ciki, kuma Tafida duk wadda ta sameka a matsayin miji itace tayi sa'a ba kai ba”.
Tafida yayi wani bussashen murmushi yana tura sumar kansa baya, sai kuma ya dawo da hannun nasa ya dunƙule ya ɗora a bakinsa.
“Inaso ka nemo min bayanai akan yariyar me suna Maryam ”
“Me yasa ?”
Sai ya ɗago ya kalli Muktar
“A tsarin gidanmu babu saki da na saketa taci gaba da rayuwarta kamar yanda ta saba, amma tunda har hakan ba zata samuba zan yi yanda zanyi na temaki rayuwarta bazan bari wani ya cutu sbd ni ba”.
MARYAM POV.
Zaune take a bakin makeken gadon da aka bata, babu abinda take tunawa sai yanda aka rabota da gida, tana kuka tana komai, wani abu daya tsaya mata a rai shine maganar da sukayi da Maanmu ta ƙarshe.
_“Maryam, bance kada kiyiwa mijinki biyyaya ba, kiyi masa biyyaya iyaka bakin iyawarki, ni misalice a wajenki, kinga yanda naci tarin baƙin cikin mahaifinki, kada ki duba sigar da aurenki ya faru kawai kiyiwa mijinki biyyaya, wannan shine kaɗai abinda zan iya faɗa miki” _
Sai taji wata sabuwar kwalla na zubo mata, daga wannan magana ta Maanmu wasu manyan mata da aka aiko daga fada wanda suka shiryata cikin alkyabba suka fita da ita daga gidan, suka sakata a cikin mota suka kawota fadar haɗejia, tunda take a rayuwarta bata tab'a shigowa cikin fada ba, dan bataga dalilin da zaisa ta shiga fadar ba, kuma suna kawota ne kaitsaye akayi turakar Fulani da ita, duk da tanajin fadar babu hayaniya sosai alamun ƴan wancan bikin suna gidan dinner, kuma tunda aka kawota bangaren da take ciki kai tsaye wannan ɗakin da take ciki aka kawota, daga ita sai jakar kayanta guda ɗaya, kuma yawancin kayan ciki Anti Fati da Badar ne suka bata shi, dan gaba ɗaya nata cewa sukayi bazata tafi da suba, hijabanta kawai suka bar mata.
Tunda tayi sallar isha har yanzu hawaye bai yanke a idonta ba.
Jin kamar ana motsa kofar ɗakin ne yasa gabanta yayi wata wawuyar yankewa ya faɗi, ta tsirawa kofar ido sai taga Fulani ta shigo, a sirrance ta sauƙe a jiyar zuciya, Fulani na mata murmushi ta ƙaraso har cikin ɗakin tana zama a kusa da ita, Maryam ta zabura zata sauƙa kasa Fulani tayi saurin riƙota tana girgiza mata kai.
“Haba!, haba! Maryam ai yanzu kin zama ƴar gida”
Maryam ta share hawaye tana zama amma a ɗarare ta zauna sai kama jikinta take, zama kusa da matar sarki ai abun azimun ne.
“Maryam, inasan nayi miki magana a matsayina na uwa wadda take fatan samawa ɗanta lafiya, ba a matsayin Fulani Khadija matar sarki ba”
Sai Maryam taji abun banbarkwai, itafa dama tasan cewa dole dai wanna auren na manufa akayi, in ba haka ba taya za'ayi a zab'ota ita ɗaya kaf cikin tarin ƴaƴan masu kuɗi da mulki na garin nan ace sai ita, ita kaɗai, Fulani ta kamo hannayen Maryam.
“Maryam, Tafida ya taso ne cikin wata hautsinnaniyar rayuwa, tun yana yaro ya rasa iyayensa, Raruwarsa gaba ɗaya lillub'e take da wani baƙin duhu, Kuma a yanda aka sanar mana babu me iya kawar da wannan duhun na rayuwarsa sai ke”.
Sai kuma tayi shiru, hawayen da Maryam taga a idonta shi yafi ruɗata fiye da maganganun da ta faɗi.
“Ina me roƙonki Maryam, dan Allah ki temaki ɗana, ki ceto shi daga cikin wannan kogin da yake ciki, Nasan zakimin kallon me san kai, amma ina roƙonki dan Allah....”
Maryam ta shiga girgiza mata kai, ita bakinta ma ya kulle, ta kasa cewa komai, maganganun sunwa ƙwaƙwalwata nauyi. Ta masa fahimtar maganganun nata gaba daya, da kyar ta iya lalubo muryarta.
“Ni ban isa na warkar da kowa ba, Allah shine me waraka, kuma shine me warkar da kowa”.
_ya ne ?, my people, garifa ya kama da wuta, kamar wani abu yana ƙauri a nan, labari ya dauki zafi🔥_
_To ki biyoni domin jin karashen labarin, a har kullum nice taku Salma Ahmad Isah, wato SAI, Ina miƙa godiyata zuwa gare ku🙏_.
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*BABI NA GOMA SHA BIYU (12)*
*Washe gari*
*Malam Aminu international airport*
*Da misalin 10:00am*
Tafida ya fito daga wani shagon snakes, inda ya saba kaiwa ajiyar key kafin Muktar yazo ya karb'a, wasu lokutan ma tare suke tahowa idan ya aje shi sai ya juya da motar, to yau sun taho da wata shi yasa bai biyo shi ba, tun jiyama da sukayi sallama bai ƙara ganinsa ba, kawai de da zasu taho ya kirashi akan zai bayar a aje masa keyn inyaso sai yaje ya karb'i motar.
Inda yasan ya bar Maryam ya dawo, zaune take akan daya daga cikin wasu kujerun dake wajen, ga jakukunansu a kusa da ita, sai yanxu ya samu damar ƙare mata kallo, dan yau da safe da yaje fada sarki ya fara zuwa ya gaisar,sannan yayi masa sallama sai ya fita yaje ya yiwa Fulani sallamar itama, kuma itace tace masa yaje ya jira Maryam ɗin a mota, yana zaune a motar suka ƙaraso ita da Nadra.
Kuma har ta shiga motar bai kalleta ba, gaisuwar da ta masa ma da ƙyar ya samu ya amsa, kuma bai kalleta da kyau ba sai yanzu.
Bata cika fari ba, amma kuma farar ce, bata da wani kyau na tashin hankali, saide bata da muni kyanta daidai ita, kuma bata da jiki duk da abayar dake jikinta tanada faɗi, amma hakan bai hanshi ganin sirirantar ta ba, wani abu dayafi komai kyau game da ita shine idanunta, farare tar, duk da sun ɗanyi ja, alamun tayi kuka, wani irin innocent face gareta, kuma akwai nutsuwa da kamewa a tareda ita, Kuma daga ganinta kasan cewa akwai ƙarancin shekaru a tareda ita, sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi.
"Muje ko ?”
A hankali Maryam ta ɗago ta kalleshi, gabanta yayi wata iriyar muguwar faɗuwa, taji kamar tana nitsewa a cikin wani abu, kamar yanda shima bai kalleta ba itama bata kalleshi ba sai yanzu, ta saba jin hirar Tafida a bakin mutane da yawa bata san ashe haka Tafidan yake ba, lalle kuwa Tafida, ai wannan bai dace da wannan sunan na Tafida ba, wannan sunansa Eshaan, dan shine yafi dacewa da shi, ashe duk abunda Badar ke faɗa mata gaskiyane.
Kuma tana kallon fuskar tasa sai maganganun da sukayi da Fulani yau da safe suka faɗo a cikin ƙwaƙwalwarta.
_“Maryam, nasan da cewa Allah shine me temakon kowa da komai, amma ke kece sanadiyyar temakon Tafida, akwai wani abu dake damun rayuwarsa da bayasan karatun alqur'ani ko addu'a, nasan cewa ke me ilimice dan haka ki riƙi addu'a, ga wannan qur'an ɗin ki lazimci karantashi a kullum, na tabbatar da Allah zai temakeku, ya kuma baku zaman lafiya, Allah ya miki albarka”_
A ɗazun sai ta kar6i qur'an ɗin ta kuma mata godiya, bayan fitar Fulani wata ta shigo wadda ta bayyana mata kanta a matsayin Nadra, ta bata wata brown abaya, kuma itace bayan tayi wanka ta saka dan har yanzu ma itace a jikinta, saida suka fitone taga tarin wasu akwaituna guda shida, Fulani ta sheda mata da kayan aurenta ne da aka mata, a lokacin ma saida tayi hawaye, kuma wasu bayine da Nadra suka rakata har motar da akace Tafida na ciki, suka saka kayan a baya, sannan ita ta shiga motar.
Kuma tun bayan gaishe shi da tayi bata ƙara cewa komai ba, shima kuma baice ɗinba, sannan batayi gigin kallonsa ba har suka iso kano, amma kuma gaba ɗaya a takure take a cikin motar.
Kuma bayan sun zo ne ya saka aka shiga musu da kayansu ciki yace ta zauna ta jirashi yaje ya dawo shine har yanzu yake tsaye a gabanta.
*
Kamar yanda a mota sukayi tafiyar kurame yanzuma haka ita sukeyi, zaune take a gefensa, cikin wani irin kusanci, kusancin ma har yafi na ɗazu, gaba ɗaya sai taji wani iri, ta takur fiye da ɗazu.
A hankali ta ɗan waigo ta kalli fuskarsa, ba ita yake kalloba idonsa na kan wayarsa yana dannawa, ga wani sun glasses wanda yake idonsa tun tahowarsu daga haɗejia, wani abun mamaki ta gani a gefen fuskarsa, ƴar haɗejia ta gani a kusa da sajensa, gefen kunnensa, abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba.
Ashe shima yanada ita kamar yanda itama take da?, ai ita tunaninta su basayin irin wannan abubuwan. Da sauri ta juya ta kalli window domin itace a window seat, wani abu da bata tab'a kawoshi koda a mafarkinta ba, shine hawa jirgi, yau sai gata a cikin jirgi, tana iya hango gajimaren dake ƙasa, abun gwanin ban sha'awa. Hankalinta gaba ɗaya ta maida akan kallon windown, dan yafiye mata alkairi, dan da taci gaba da kallonsa gwara ta kalli windown.
Tunda ta juyo ta kallishi, Tafida ya ankara da ita amma bai ko nuna mata ba, sai kuma wata hira da wasu ƴan mata dake tsallakensu ta dauki hankalinsa.
“Yanzu dan Allah hafsa idan na samu wannan guy ɗin ban more ba?”
Sai kawai ya motsa kunnensa ta yanda zai samu damar jin abinda suke faɗi da kyau, sai kuma ya tsinto abinda beyi zato ba, wannan bugun zuciyar, bugun zuciyar da yake kwana yake tashi da shi akwana kin nan, wannan bugun zuciyar da yake kwantar masa da hankali ya saka masa nutsuwa.
A hankali ya juya ga inda sautin ke fita, ita ɗince zaune a gefensa gaba ɗaya ta maida hankalinta kan kallon window, iko sai Allah, ashe itace ?, tabbas itace domin sunanta Maryam, amma sam beyi tunanin sake haɗuwa da ita bama, balle har ya sake sauraren bugun zuciyar tata.
“Hello handsome!”
Maganar ɗaya daga cikin ƴan matan dake tsallaken nasu ta katse masa hanzari, a hankali ya zuyo ya kalleta da idonsa dake cikin sun glasses.
“ya akayi ?”
Mamaki ya kamata dan ba tayi zaton yanajin hausa ba, ita kallon indian take masa, zuciyar Maryam ta matse a ƙirjinta, itafa shi yasa bata san kyakyawan namiji, yanzu ƴan mata zasuyi caa akansa. Gara taso mummuna duk kuwa muninsa, inde har yana sanya kuma itama tana sansa hakan ya wadatar.
“Ammm.....da...dan Allah lambar wayarka zaka bani ”
Amsar da ta fito daga bakinsa ba ƙaramin basu mamaki tayi ba, bama su kaɗai ba, harda Maryam dake zaune a gefensa.
“I am sorry maam, but i am married, kinga matata ma”
Ya ƙarashe yana ɗan kaucewa dan su samu damar ganin Maryam ɗin dake rakub'e a gefensa.
“Oh sorry”
“Never mind”
Maryam ta haɗiye wani abu, ahse har zai iya nunata a waje yace ita matarsa ce ?, kode yayi hakan ne dan ƴan matan su ƙyaleshi ?, itafa tunda ta ɗora idanta akansa wani abu yaxo ya tokare mata maƙoshi.
Tana hango ɗumbun tazarar dake tsakanin ta dashi, sam ko kaɗan basu dace ba, basu dace da juna ba, a da tana neman dalilin da yasa aka aura masa ita, amma bayan maganar da sukayi da Fulani jiya ta samu amsar tambayarta, an aura masa itane sbd itace maganin wani ciwo a rayuwarsa ba dan yana santa ko yana ra'ayinta ba, amma me yasa ?, me yasa rayuwa zata mata haka ?.
Har jirginsu ya sauƙa a lagos Maryam nata saƙe-saƙe a ranta, shi kuma Tafida ya bada himma wajen sauraren bugun zuciyarta ne, shi abun har mamaki yake bashi, ya rasa me yake tsinta a bugun zuciyar tata.
Drivernsa na asibitine yazo ya ɗauke su zuwa ALARO CITY, Tunda Maryam tazo duniya gari uku ta ta6a zuwa bayan haɗejia, daga ƙauyen su Abbansu sai kano sai kuma malam madori da ta tab'a raka Badar wani biki, amma kuma bayan su bata tab'a zuwa ko ina ba.
Ita manyan gine-gine irin wanda take gani a yanzu sai a waya ko a tv, suma ɗin dan ta kasance ma'abociyar kallon finafinan india ne, amma da bazata tab'a sanin akwai kalar wannan abinda take gani ba, kuma irin waɗan nan ɗinma tana ganinsu a tiktok, dan akwai wani a tiktok wanda yake posting kyawawan wurare a nigeria.
Ta tuna yanda suke ta musu itada Badar akan wasu wajejen ba nigeria bace, amma kuma a yau, sai gata a gaban waɗannan manya-manyan gininnikan. Da ace bata san abinda take ba, kuma bata da wayewa da ta zuba ƙauyanci.
Ta lekki link bridge suka wuce, ita batama san akwai ta a nigeria ba, tasan de akwai irinta a mumbai, kuma itama ɗin a waya ko tv take kalla, wato inda ranka ka sha kallo, ta faɗi hakan a ranta.
Mamaki bai cinyetaba saida suka iso ALARO CITY, wani babban estate me kama da wani garin, a babban symbol ɗin dake manne a saman wajen ta karanta sunan estate ɗin, haka sukayi ta wuce blocks kala-kala, kuma ta lura da kowani block ginin gidajesu iri ɗaya ne.
Maryam taga kamar sun shiga wata duniya ne da ban ba earth ba, abun akwai ban mamaki ga wanda bai taba gani ba, gaba ɗaya tsarin estate ɗin irin ginin ƙasar turai ne.
Block 3, suka shiga, drivern yayi parking a kofar wani gida wanda yake shima gininsa iri ɗaya ne da sauran gidanjen cikin block d'in, ta waya Tafida ya buɗe musu gate ɗin, drivern ya shiga cikin gidan, yayi parking suka fito, ya kalli Maryam.
“Ki shiga ciki”
Ya faɗi cikin wannan muryar tasa me zurfi, da ƙyar maryam ta gyaɗa kai, sannan ta kama hanyar shiga cikin gidan, hannunta riƙe da hand bag ɗinta, hannunta na rawa ta kai ta buɗe kofar gidan, bakinta da sallama ta shiga cikin gidan.
Bazata iya cewa komai ba akan tsaruwar gidan, gidan ya haɗu ta ko wani fanni, shida drivern ne suka shigo ɗauke da jakukunansu, sannan taga sun haura sama, da hannu yayi mata alama da ta biyoshi, haka tabi bayansu har zuwa ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan dake saman, daga inda take tsaye a corridorn ta leƙa ƙasa ta kalli parlon, a ranta tana jinjina girman gidan, shida drivern ne suka fito daga ɗakin da suka shiga sannan yace mata.
“As from today this will be your permanent room”
Her permanent room ?, kenan yana nufin zai zauna da ita har abada ko me ?, itafa ta kasa ganewa, amma sai ta gyaɗa masa kai, ƙasan taga shima yayi yabi bayan drivern yayinda ya bar jakarsa a wajen, batayi gigin tab'a masa ba.
Tasa kai ta shiga ɗakin, Allahu ƙadirun ala man yasha'u, shine abinda Maryam ta ayyana a zuciyarta, bayan da tayi arba da ɗakin, ba wani me girma bane can, amma kuma ya ninka ɗakinta da take kwana na gidansu, gidansu ?, kalmar ta maimaita kanta a ƙwaƙwalwarta, yanzu ita ɗaya zata kwana a wannan katafaren ɗakin ?, ko a wani hali gidan nasu ke ciki ?.
Sai kuma tabi ɗakin da Kallo, komai na cikinsa ja ne da baƙi, babu abinda yafi ɗaukar hankalinta irin kofar balcony ɗin, wadda ta kasance ta glass ce, hand bag dinta ta aje a kan gadon sannan ta taja a hankali zuwa balcony ɗin ta kai hannu ta kawar da curtais ɗin sannan ta zuge kofar glass ɗin, ta taka zuwa balcony ɗin, wata iriyar iska me cike da ni'ima ta bigi ƙofofin hancinta dama na fatarta, kyakyawan garden ɗin gidan dake back yard yayi mata sallama, daga saman da take tana iya hango kyan garden ɗin. Ga wata kujera me kamar lilo a balcony ɗin, sai wasu flower vase masu kyau da aka jera a kasan wurin, wurin ya tafi da imaninta......
🌸-SAI KASKA CE-🌸
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*BABI NA GOMA SHA UKU (13)*
*Na sadaukar da wannan babin zuwa ga, mrs zak's*
......Tunawa da tayi batayi sallar magriba da ake ba yasa ta koma cikin ɗakin da sauri, sai kuma ta shiga toilet, duk jikinta a gajiye take jinsa dan haka ta yanke cewar harda wanka zatayi.
A yau ta godewa Allah, social media da novels da take karanatawa, dan badan suba ba zata iya tab'uka komai ba, a ranta ta tuno da cewar da ace wata daga area ɗinsu aka kawo wannan gidan, wai da anga ƙauyanci, tayi murmushi a bayyane tana buɗe kofar shower stall ɗin.
Wankan tayi sannan ta fito tayi alwala ta maida kayan da ta cire ta fito, jakarta data zo da ita ta buɗe ta ɗauki hijabi ta saka, taji wani daɗi na ratsata, dan tayi kewar hijabinta, abayar ma ta yarda ta saka ta ne sbd tanada faɗi.
Sallar ta gabatar, sannan kamar yanda ta saba ta zauna tayi addu'o'inta ta shafa, sai kuma ta miƙe ta cire hijjabin ta ninke, jakarta ta kuma biɗewa ta ɗauki wata sabuwar dark navy midi prom dress wadda Anti Fatice ta bata, rigar bata da nauyi kuma hannun rigarma ba wani dogo bane.
Ta sakata sannan ta miƙe ta shiga bubbuɗe lokokin data tarar a ɗakin, bata samu komai a ciki ba, har ta buɗe doguwar drawer ɗin dake manne da wani bango, kuma wardrove ɗin yar bangoce, amma kuma kamar closet dan sai kayi taki ɗaya.... biyu.... Sannan zata tarar da inda zaka jera kaya a cikinta, nan ɗinma babu komai.
Goge lokar da tayi sbd ƴar kurar data gani a ciki, ta dawo kan akwatunanta ta shiga buɗewa, mamaki kawai take da ta'a jibin abinda take gani, gaba ɗaya kayan atamfofine da lesuka kuma duka an ɗiɗɗinka.
Wani abu daya ƙara bata mamaki shine data gwada su a jikinta duka daidai itane, daga tsayin har faɗi, akwati hud'u na tsaddadun kayan sakawa ne ɗinkakku sai abayas, sauran biyun kuma data buɗe ɗaya daga cikinsu takalma ne da jakukuna a ciki, ita kuma ɗayar kayan kwalliyane harda jewelleries.
Maryam ta rasa ma abunyi, data gaji da kallon kayan ta miƙe ta shiga naɗewa tana jerasu a wardrobe ɗin, har ta gama jeresu kaf, takalma da jakukunan kuma gaba ɗaya ta jeresu a lokokin kasa, wani ƙaramin flat kawai ta bari a cikinsu wanda zata dinga sakawa na zaman gida, tana shiryasu tana mamakin kayan, ga shi kuma harda gyalulluka, kuma ita ba ma'abkciyar saka gyale bace, duk da gyalullukan na matan aure ne, dan suna da girma sosai, daga can gefe ta jere wanda tazo dasu, har ta gama shirya kayan wardrobe ɗin bata cika ba, kuma batayi mamakin hakan ba, dan wardrobe ɗin ta kusa cinye faɗin bangon da take jiki.
Gaban drassing mirror ta dawo wanda babu komai a kai, ta jere kayan kwalliyar sannan ta dawo ta zauna a bakin gadon ta ɗauko hand bag din data zo da ita ta fito da qur'an ɗin dake ciki ta saka shi a bed side drawer, ta ɗauko wayarta da ear piece ɗinta harda charger ɗinta, sai kawai ta shiga jujjuya wayar a hannunta, gaba ɗaya screen ɗin wayar ya fashe daga sama, duk bata lura da hakan ba sai yau da safe.
Wayar ta kunna taga babu chargy, gashi tana san ƙiran Anti Fati ko Badar, dan a gidansu babu me waya, su Hussain dama basu da waya, dan dokace maanmu ta kafa musu akan bazasu tab'a riƙe waya ba sai sun gama secondary.
Kuma tun kan Anti Fati har zuwa kanta basu riƙe wayar ba sai da sukayi candyn, jiki a sab'ule ta miƙe ta saka wayar a chargy jikin wani socket dake kusa da bed side drawer, bata san lokaci ya ja ba saida taji ana kiran sallar isha, ta riƙe alwalarta dan haka kawai ta miƙe ta saka hijjabin data cire ɗazu ta gabatar da sallar ishar sannan ta zauna tana addu'o'in ta.
Ƙofa taji an ƙwanƙwasa dan haka tayi saurin shafa addu'ar ta miƙe a hankali ta buɗe kofar gabanta na wani irin bugu, sai de bataga kowa ba, har zata juya ciki idonta ya sauƙa a kan wasu ledoji guda biyu, ta tsugguna ta ɗauka sannan ta meda ƙofar ta rufe.
Tana ta mamaki, duk da tasan de babu me mata hakan sai shi, shi ɗin da a yanzu yake amsa sunan mijinta, mijinta ?!!, sunan ya maimaita kansa a ranta, shekaran jiya take faɗin cewa batada niyyar yin aure kwana kusa, amma cikin kwana ɗaya komai ya sauya, rayuwarta ta juya up side down, tana kaikawo a kan siraɗin rayuwa.
Ledar farko ta buɗe, kuma tun kafin ta gama buɗe take a way ɗin dataga a ciki ƙamshin wani abu da ɗumin abin ciki ya daki hancinta da fatarta, wani gasashen cat fish ne da kuma fried potatoes tun kafin ta kai abincin bakinta yawunta ya tsinke, ta ɗauko wata roba da itama take cikin ledar ita kuma tun kafin ta buɗe taga abin ciki kasan cewar rober is transparent, wani haɗin cake parfait ne a ciki, maryam ta aje shi shima gefe, ta buɗe ɗayar ledar kuma ita drinks ne a ciki.
Ƙasan carpet ta dawo ta zauna ta baje kayan abincin, sannan ta shiga toilet ta wanko hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin abincin, tabbas tasan ta iya girki, amma kuma bata saba cin irin wannan abincin ba idan har ba Badar ce ta kawo mata girki ba, ko kuma taje gidan Anti Fati ta tayata girki, amma a gidansu babu irin wannan cimakar.
Cikinta ta bawa hakkinsa sosai, dan bata ci abincin ranaba, rabonta da abinci tun na safe data ɗan caccakala, sannan ta rage wanda ta rage ta naɗe shi ta aje sai kuma da safe hannunta ta shiga toilet ta wanke.
Sannan ta ɗauro sabuwar alwala ta dawo ta kwanta akan lallausan gadon da zatace kusan a irinsa ta kwana jiya, duk da bata samu tayi wani baccin arziƙiba jiyan, dan tunani ne fal ranta.
Sai kuma ta kasa baccin, sbd wata sabuwar kewar gida da ta kamata, Allah ya sani tana kewarsu tun jiya, hannu ta kai ta kashe wuta amma kuma sai ta kasa kwanciya sbd wani tsoro daya kamata, dan haka ta kashe wasu ta bar wasu a kunne, tana tasbihi a ranta har bacci yayi gaba da ita.
HANAM POV.
Tashi tayi yau Arya baya jin daɗi dan haka saida ta kaishi asibi sannan taje wajen aiki, kuma a wajen aikin ne aka kawo musu kwangilar ɗinkin atamfofi na wani biki da za'ayi a villa.
Ita kuma ma'aikatanta basa ɗinka atamfofi, wanda yake ɗin ma baya gari,dan haka tana buƙatar wanda zai ɗinka mata atamfofin, da wannan tunanin ta dawo gida, yau ji tayi bazata iya zaman ɗaki ba, ai itama gidan gidan ubanta ne, dan haka zata iya zama a ko ina taso.
Dan haka bayan taje tayi wanka tayiwa Arya ma sai suka sauƙo parlon ƙasa, bata sakawa Arya riga ba sai ta barshi daga shi sai diapers, ta fito da system ɗinta dan akwai aikin da zatayi, ta zaunar da Arya a cikin baby floor seat ɗinsa, dan yanzu ya fara wayo ga ta'adi a cikinsa.
Ta tafi kitchen taje ta zubo abinci sannan ta dawo ta zauna kusa dashi a ƙasan, ta ɗora laptop dinta akan coffee table, farar shinkaface da Stew wadda taji naman sa, sai coslow, data tashi sai take bashi shinkafar da coslow ɗin kawai, dan tana so ya fara cin abinci tun yanzu, dan ya kusa shekara, kuma a yanda ta yanke yana cika shekara zata yayeshi.
Tana ci tana bashi tana masa wasa har suka cinye tas, sai ta kira ɗaya daga cikin masu aikinsu tazo ta kwashe plates ɗin, sannan ta cireshi daga cikin floor seat ɗin, ta koma kan kujera tana dudduba aikin nata.
Arya ya kama kujera ya miƙe ya fara rirriƙe kujerar yana tafiya.
“um um kace sai munyi tafiya zamuyi magana”
Ta faɗi tana masa dariya, ya juyo ya kalleta shima yana dariyar, sai kuma ya saki kujera ya koma rarrafe a tsakiyar parlon, duk inda yayi tana binsa da kallo.
Nabila ƴar Mero ce ta sauƙo, babbar mara kunya cikin ƴaƴan mero, ta sauƙo tana wani taunar chewing gum, sai wani kallon tara saura kwata take bin Hanam da shi.
Arya ya kai wajen da aka aje wasu kaya a leda Hanam bata lura dashi ba ya shiga janyo ledar daga ƙarƙashin kujera.
“kai !!, du**n uwarka zakayi da ledar da kake janyowa?”
Ta ɗura masa ashar ɗin tana finciko shi daga gaban kayan, tsawar da tai masa yasa Aryaan fasa kuka, 'dan ya tsorata, ta wancakalar dashi a gefe har ya kusa faɗuwa, duk abinda take Hanam na binta da kallo, sai kuma tazo ta tsaya a gaban Hanam tana wani girgiza irin ta tashen balagar nan.
“Ki jawa shegen ɗanki kunne, babu ruwansa da kayan mu a cikin gidan nan”
A hankali Hanam ta kai hannu ta aje system ɗin a gefen inda take zaune, ta miƙe tsaye kuma ba tayi wata-wata ba ta ɗauke Nabila da maruka har uku ƙwarara.
“Naga kamar ranar da nayiwa uwarki da yayanki warning akan ɗana ba kyanan, to kema ga naki warning ɗin, a da kunyi min rashin kunya na jure, kun zageni na jure, but now baku isa ba, kuma har yanzu idan rashin mutuncin ku akaina zai tsaya bazan ce muku komai ba, but if you dare touch my son, hmmm hmmm”
Tayi wani irin murmushi, tuni matan gidan suka fito sbd kukan da Nabila ta saka, Mero ta kamota tana faɗin
“Kede Hanam wallahi baki da mutunci, ki tab'a uwa ki tab'a ƴaƴanta, wannan ai wulaƙanci ne, dama ai barewa baza tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba, haka uwarki ma take”
Hanam ta ba banza ajiyarsu, ta kamo ɗanta ta shiga bashi mama, sannan taci gaba da aikinta.
Bayan abba ya dawo Mero ta sameshi da ƙorafi akan Haman kamar kullum, shima sai ya bata haƙuri kamar kullum ɗin, sannan kuma ya ƙira Hanam ɗin ya yi mata nasiha, bayan ya gama ne tace
“Abba an kawo mana kwangila na ɗinka atamfa daga villah, to kasan musa ya tafi garinsu, su kuma sauran ba iya ɗinka atamfa sukayi ba, shine nake so ka duba min wanda ya iya ɗinki”
Abba yayi shiru yana nazari
“Akwai amma ki bari sai nayi magana dashi gobe duk yanda mukayi zaki ji”
“To Abba Allah ya kaimu”
Abba ya shiga yiwa Arya dake kan cinyarsa wasa, Hanam ta tsaya kawai tana kallonsu, wani abu na yawata a ƙwaƙwalwarta.
Duk duniya bata da wani farin ciki bayan wannan abu biyun, sune rayuwarta, domin su take farin ciki, bata da komai bata da kowa sai su, a da tana addu'ar Allah ya ƙara bata wani sabon fata, sai kuma ta samu Arya a lokacin, sai ta ɗauki Arya a matsayin wannan sabon fata.
*ALARO CITY*
*Da misalin ƙarfe 09:00am*
Dogayen yatsun hannun Tafida suka ƙwanƙwasa kofar ɗakin da maryam ke ciki, yau lahadi amma dole yaje aiki, sbd kwanakin da yayi baije ba, duk da yana buƙatar ya huta, dan jiya bai samu yayi wani baccin arziƙi ba.
Dan yana aje mata kayan nan suka fita shida drivern nan, ya aike shi yaje ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya wuce masallacin block ɗinsu, kuma bai dawo gidan ba sai bayan isha, dan ya tsaya sunyi magana da maƙocinsa wanda shima ya kasance bahaushe ɗan arewa.
A lokacin daya dawo gidan har drivern ya dawo ya karb'i aiken da ya masa ya ware wanda zai bata sannan ya nufi ƙofar ɗakinta.
Kuma tun kafin ya ƙwanƙwasa ƙofar yaji bugun zuciyarta, yana buga ƙofar bugun zuciyar ta ya sauya, wani irin sauti dayafi na ainahin yanda zuciyar tata take bugawa daɗin saurare, idan zuciyarta tana bugawa a tsorace sautin yafi daɗin saurare.
“Ya Rab!!”
Shine abinda ya furta a lokacin, sai kuma yayi sauri ya aje mata ledar cikin wani irin sauri daya zarce na normal ɗan adam ya shige ɗakinsa.
Bai samu yayi bacci da wuri ba sbd bugun zuciyar tata dayaci gaba da saurare. Kuma yau da safe daya fita masallaci yaga wutar ɗakinta a kunne, alamun ta tashi, bayan ya dawo kuma bai fito ba sai yanzu, shine yake san ya sanar mata da zaije aiki..........
_Kamar kullum jama'a, ina miƙo godiya sinƙi-sinƙi, sannan gaisuwa ta musamman zuwa ga mrs Zak's, naga saƙonki, Maryam tana zuba ido😂_
_Ayi dropping comments dan Allah_
_And pls share it😚_
🌸-SAI KASKA CE-🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Arewabooks @18saikaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*BABI NA GOMA SHA HUƊU (14)*
*Babin mu na yau kuma naki ne, Badi'a Ahmad Sulaiman*
.........Tunaninsa ya katse a sanda Maryam ta buɗe ƙofar, abu na farko daya fara shiga ƙofofin kunnuwansa shine wannan bugun zuciyar, kuma a tsorace yake bugawa, kenan tsoransa take, tana tsoransa a matsayinsa na haka ina ga idan tasan waye shi, ainahin shi.
Sai kuma ya kalleta, hijabi ne a jikinta har ƙasa, hannunta da fuskarta ne kawai a bayyane, idonta ya kalla, wani abu dayafi komai kyau a fuskarta.
Maryam na haɗa ido dashi ta sunkuyar da kai, dan bata tab'a sanin haka kalar idonsa take blue ba sai yau, cikin tsoro da rawar murya ta sunkuya ƙasa tace
“Ina kwana”
“Lafiya”
Ya amsa mata cikin muryarsa me zurfi, kuma sautin muryar tasa kamar akwai gajiyab a ciki, Maryam ta miƙe kuma har yanzu kanta a ƙasa zuciyarta na tsere a ƙirjinta.
Shi kuma ya kasa kunnensa sai sauraren bugun zuciyarta yake, koda wuƙa za'a ɗora masa a wuya a tambayeshi me yake ji a bugun zuciyar tata bazai iya faɗar komai ba, dan baisan me yasa yake san sauraren sautin ba.
Kawai de yana jin kamar akwai wani abu a cikin sautin bugun zuciyar tata na musanman, kamar yanda fuskarta take very Innocent hakama zuciyar tata ke bugawa, musamman ma idan tana bugawa da sauri.
“Zanje aiki ne, shine nace bari na faɗa miki, akwai kitchen a ƙasa, zaki iya shiga ki girka abinda zaki ci, ko idan na fita na aiko miki ?”
Ya bata zab'i biyu ne dan be san me ya kamata yayi a cikin biyun ba, idan yace sai ya fita ne lokaci zai ƙure, kuma bai sani ba ko bata makara wajen cin abinci, idan kuma yace ta girka wata ƙila bata iya girkin ba, dan haka ya yambayeta.
Kamar Maryam zata ce masa ta rage abincin jiya kuma shi zata ci sai kawai ta fasa tace.
“A'a zan girki”
Muryarta ta fito da irin innocent dinta, a hankali ya gyada mata kai.
“Sai na dawo”
“Allah ya tsare, Allah ya kiyaye hanya”
Maryam ta faɗi bayan ya juya, maganar tasa Tafida ɗan dakatawa da tafiyar da yake, addu'ar ta dakeshi sosai. A hankali yaci gaba da tafiya cikin takunsa na izza da ƙasaita, tausayin yarinyar na ƙara kama zuciyarsa.
Maryam tabi bayansa da kallo, tana kare masa kallon da bata samu damar masa ba jiya, bata san cewa dogo bane sai yanzu data tsaya a gabansa, kuma wani abu data lura dashi shine yana da rukon al'ada, dan daga jiya har yau duka kayan hausawa take ga yana sakawa, amma ita a ganinta sai take ga kamar kayan basu wani karb'e shi ba, da a ce zai saka kayan indiyawa sai yafi karb'arsa, dan gaba ɗaya kamar indawace dashi.
Ɗakinta ta koma ta cire hijabin jikinta dan dama sbd ya kwankwasa kofar ne yasa ta saka, wajen data saka wayarta a chargy ta koma ta cire wayar.
Da ƙyar ta samu ta lalubo lambar Anti Fati, dan wayar bata dannuwa da kyau, alamun taci sensor, gaisawa sukayi sannan ta tambayeta ya su maanmu suke, Anti Fati ta ƙara mata nasiha, sannan sukayi sallama ta nemo lambar Badar za ta kirata amma sai aka sannar da ita bata da isasshen kati.
Tayi tsaki sannan ta aje wayar miƙewa tayi ta ƙara saka hijabin data cire sannan ta fita daga ɗakin, ta tsaya a ƙofar ɗakin tana kallon corridor ɗin dakunan, daga karshen corridorn daga dama kuma balcony ne, wanda yake facin kofar gidan.
A hankali take takawa zuwa wurin, balcony ɗin yanada faɗi sosai, ga wasu flower vase da aka jera daga ƙasa, ga grass carpet shimfiɗe a kasan wurin, ga kuma wani lilo a wajen, sai wasu flower vase din rataye a sama.
Daga jikin bangoma wasu ne jere kala-kala, karfen balcony ɗin an masa ado da neon strip light, hakama wasu daga cikin flower vase ɗin, Maryam har ta hango yanda wajen zeyi kyau da daddare idan aka kumma neon strip light ɗin, daga ɗan sama kuma kejin aku ne kuma akwai akun a ciki.
Maryam taji wani abu na farinciki na ratsa mata zuciya, sai kuma ta kalli sauran gidajen dake tsallaken nasu da ma na kusa da su, ko wani gini iri ɗaya ne hatta da fenti, view ɗin kasan akwai ban sha'awa. Ta koma wajen akun nan, tana kallonta, can tace.
“ Barka”
Akun ma ta maimaita.
“Barka”
Dariyar farin ciki ta sub'uce daga bakin Maryam, gaba ɗaya wajen ya gama burgeta.
Fita tayi daga wurin ta ci gaba da tafiya a corridor ɗin, bata buɗe dakin da taga ya shiga jiya ba, dan bisa ga dukkan alamu nasa ne, sai ta bud'e na kusa dashi, shi ma kamar nata yake, amma kuma babu gado sai katifa kawai, kuma komai na dakin an lillibe da kyalle alamun ba'a amfani dashi, ta jawo ƙofar ta rife.
Amma kuma sai taji tana san taga ya nasa ɗakin yake, dan haka ta koma da baya ta bud'e kofar
“WOW”
Kawai ta iya furtawa da tayi arba da ɗakin, tsarin ɗakin kamar nata yake amma kuma yafi nata girma, a hankali ƙafafunta sukaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin, tana ta santin kyan ɗakin a zuciyarta.
Ta kalli inda yake aje cricket kit bag dinsa, ga Jersey dinsa rataye a saman jakar, a ranta tace ashe ɗan wasan cricket ne, dubanta yakai kan wani bango a ɗakin wanda yake cike taf da hotuna, kafafunta sukayo kwana zuwa jikin bangon, ta tsaya tana bin hotunan da kallo ɗaya bayan ɗaya, duka hotunansa ne, tun na yarinta har zuwa girmansa.
Idonta ya tsaya akan wani hoto guda ɗaya, kuma wanda yafi kowani hoto girma a cikinsu, wani baƙin fatane ɗan africa sanye cikin suit irin tasu ta lokacin, sai kuma wata ba'indiya fara tas da ita, sanye cikin sari hannun ta riƙe da wani yaro da ba zai wuce 3 yrs ba.
Abu ɗaya ne ya faɗo a tunaninta, tabbas wannan iyayensa ne, kenan babarsa ce ba indiya ?, ga zahiri kinga tunda kamarsu ɗaya da matar, wani sashi na zuciyarta ya amsa mata, Fulani ta faɗa mata cewa iyayensa sun rasu.
Sai kawai tayi musu addu'ar Allah gafarta musu, taci gaba da bin hotunan tana kalla, tun yana ƙarami suke hoto da wata budurwa itama kuma ba'indiyace, kode kanwarsa ce ?, to amma kuma ai bashi da ƙanwa a wannan hoton, wata ƙila yar uwarsace, dan suna kama hatta da kalar idonta irin nasa ne, amma ita nata idon ba light blue bane, nata dark blue ne, kuma duk da kasancewarta mace yafi ta kyau.
Ya samu gata sosai, ta faɗi a zuciyarta, sakamakon hotunansa da take gani na celebrating birthdays dinsa.
Saida ta gama masa tsurku akan hotunan nasa sannan ta bar ɗakin, ta sauƙo ƙasa. Kamar jiya, yauma ta tsaya tana ta kallon tsaruwar parlon, ƙofar farko da idonta ya sauƙa a kai ta fara shiga.
Sai taga store ne na a jiyar kayan amfanin gida, akwai irin su wheelbarrow, watering can, spade (shebur), hose (tiyo din ruwa), vacuum cleaner, pruner (abun yankan ciyawa), spenner, hammer, broom ɗinma wata doguwa ce, bucket, dustpan, squeegee mop(mofar goge glass), mop (mofa), scrubbing brush da dai sauransu.
Wasu abubuwan ma bata sansu ba, kuma komai a killace yake, akan kantoci, daga ƙarshen ɗakin kuma washing machine ne har guda biyu, wata chest drawer ta gani a gefen washing machine ɗin, ta bud'eta sai taga laundry detergent, bleach, pegs ( clips ɗin shanya ), ta mayar da rufe, sannan ta fita daga wurin.
Sai kuma ta shiga ɗayar ƙofar shi kuma bashi da girma dan guga kawai ake a ciki, daga ironing board sai wasu lokoki, ta shiga ta bubbuɗe lokokin, wasu kayane a ciki ba'a goge ba, wasu kuma an goge amma ba'a ɗauke ba, sai wasu iron guda biyu babba da ƙarami.
Ta fito daga ɗakin ta buɗe ɗayar ƙofar dake a tsalleken dakunan, shi kuma data buɗe gym ne kawai, katangu biyu da suka zagaye wajen gaba ɗayansu ɗauke suke da mirror, batama shiga ba taja ƙofar, dan a ganinta babu abinda za tayi a wani gym.
Ƴar wata kwana dake bayan ƙofar gym ɗin tayi, taja ta tsaya baki buɗe tana kallon danning table ɗin dake wurin, danning ɗin ya burgeta fiye da misali.
Ƙofar dake kusa da wajen tayi sbd ko tantama ba tayi ƙofar kitchen ce, abinda take ɗaukin gani kenan a gidan, kusan sumewa Maryam tayi, bayan tayi arba da kitchen ɗin.
A rayuwarta tana san kyakyawan kitchen, wasu lokutan kawai sai ta tafi gidan Anti Fati sbd kitchen ɗin gidan, yau sai gashi idonta na gane mata kitchen ɗin daya ninka na gidan Anti Fati girma da kyau, kuma wai na gidan mutumin da ake kira da mijinta ne, wani abu yazo ya tsaya mata a zuciya na murna, taji kamar tana yawo a gajimari, ita da ganin kitchen irin wannan sai a film, ko a social media.
kalar cabinet din kitchen din ash ne, ga wani kitchen island wanda aka kewaye shi da kujeru guda hudu, biyu daga kowani b'angare, wani abu da ya ɗauki zuciyar Maryam ya jefa a cikin ruwan sanyi shine.
Daga tsakiyar cabinet ɗin sama da na ƙasa wanda yake setin inda gas cooker take glass ne a wurin,a bayan wajen kuma garden din gidan ne, ga wasu flower vase da aka jera akan wajen, ga haske a cikin kitchen ɗin ta ko ina, kuma daga ƙasan cabinet ɗin sama akwai wasu led strip light dake haska kan cabinet ɗin ƙasan.
Maryam ta rasa ina zata saka kanta dan murna, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka shiga taka tiles ɗin kitchen ɗin, babu inda zuciyarta ke raya mata ta fara zuwa sai wurin glass ɗin nan.
Ta kai hannu ta zuge glass din zuwa gefe, daddaɗar iskar da bishiyoyin garden ɗin ke bayarwa ce ta silalo zuwa cikin kitchen ɗin, a hankali ta lumshe idonta, sannan ta buɗe, sai kuma tabi vase ɗin dake laye a wajen, green leafy vegetables ne dangin mint, coriander, rapini da dai sauransu, Maryam ta maida dogon glass ɗin ta rufe.
Sai kuma ta dawo ta shiga bud'e cabinet ɗin, gaba ɗaya dangin kayan aikin girki babu wanda bata gani ba, spoon, fork, knife , pot har set biyu kuma duka non stick ne, juicer, tray, tongs, bottle opener, blender, ladle, pestel and morter, choping board, plastic containers dama wadan da bata taba gani ba.
idonta sai ƙyallin murna ya ke, ga ba ɗaya kayan sauƙaƙawa mutum wajen aikin girki akwai a kitchen ɗin, tun daga toaster, coffee maker, oven har guda biyu, mixer, deep fryer, dish washer, microwave oven, hand blender hatta da dishwasher akwai.
Maryam kamar ta taka rawa dan daɗi, sbd wasu kayan ma ba'a ko buɗe su a ledar su ba, sabbabi dal, hakan ya nuna mata cewar ba sosai yake girki a kitchen ɗin ba, ta buɗe fridge ta ganshi cike da fruits da veggies, ga kayan miya ga kuma drinks amma komai a hargitse yake a ciki ga wasu kayan rober, shi kuma tasa kalar ƙazantar kenan ?.
Wata ƙofa ta gani a kusa da fridge ɗin ta buɗe ƙofar ta shiga taga store ne, kuma akwai kayan abinci amma ba da yawa ba, ta shiga cikin store ɗin ta shiga dudduba kayan ko zata ga abinda zata iya ci.
Aiko tayi kyakyawan gani, wata rice stick wadda tun sanda ta ganta a wani recipe na tiktok ta shiga santin taliyar, yau sai gata ga taliyar, a da kullum bata da zance saina idan tayi aure zata ce mijinta kullum ya dinga siyo mata ita, sosai taliyar ta tafi da ita, sbd a ido idan ka ganta kafin a dafata sai kace zarene ba taliya ba.
Maryam ta kai hannu tana ɗauko taliyar yayinda idonta ke cika da kwallar murna, sai kuma ta tuno gida, nan take murmushin fuskarta ya ɗauke, ko me suka dafa yau ?, ko waye yayi musu girki ?.
Sai kuma ta tuno makarantar ta, yanzu shikenan babu ita ba makaranta ?, Lalle rayuwarta ta sauya sosai a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ta samu abubuwa da dama kuma ta rasa abubuwa da dama.
A hankali wata ƙwalla ta sulalo mata, ta daure ta share, sannan ta dawo cikin Kitchen ɗin, ta shiga ƙoƙarin dafa taliyar rice stick ɗin.
Saida ta haɗa komai sannan ranta ya raya mata me zai hana ta duba garden ɗin ma, sai ta rage wutar gas ɗin.
Sannan ta buɗe ɗayar ƙofar kitchen ɗin wadda take da tabbacin garden ɗin zata kaita. Ƙam, ta ƙame tana kallon yanda wajen ya bala'in tsaruwa, shuke shuke ne fal wajen, ga wani water falls wanda aka kewaye shi da stones.
Maryam taji kamar ta nitse a gun dan daɗi, wajen ya haɗu, ya haɗu karshen haɗuwa, wata rumfa dake tsakiyar wurin ta shiga, wadda ke ɗauke da kujeru da kuma table a tsakiya, kamar de balcony ɗin saman nan, shima nan wajen akwai wannaan neon strip light ɗin, an ƙawata wurin dashi, shima dai nan ɗin kamar can ta hasaso yanda zeyi kyau da addare, aiko zata zo ta duba shi da daddaren.
Wani stairs ta gani wanda zai kaita can saman rufin gidan, a hankali ta juya zuwa wajen, tana takawa har ta kai saman gidan, nanma haɗuwarsa ba'a magana, kuma saman ma akwai jerin kujerun zama ga grass carpet ga iska me daɗi dake kaɗawa a wurin, ta shiga duba gidajen dake kusa da nasu dama wanda ke nesa da nasu, ita kam yau ta rasa abunyi dan murna.
Tunawa da tayi ta bar girki yasa ta koma ƙasan ta shiga kitchen ɗin bayan ta leka wani lungu da tagan shi a bayan kitchen ɗin, taga b'ulla gaban gidan ne.
Taliyar tata ta sauƙe ta haɗata da kayan haɗin da ta mata sannan ta komo kitchen din ta zauna ta saka taliyar a gaba tana kallo, sai kuma tayi bisimilla sannan ta kai bakinta, wasu lokutan burika na cika a gaske ba mafarki ba, yau gashi tana cin taliyar da take burin ci. Allah abun godiya.
TAFIDA POV.
Har ya kai ST NICHOLAS HOSPITAL, bai dena tunanin addu'ar da tayi masa ba, anya kuwa idan yaci gaba da zama da ita bai cuceta ba ?, anya kuwa ba zai zama me san kai ba ?, da haka ya fito daga motarsa har ya shiga floor na farko kuma kamar kullum yana gaisawa da mutane, a ƙofar elevator ya haɗu da Khabir.
“Ango, Ango”
Itace kalmar da khabir ɗin ya fara faɗi suna gaisawa, Tafida yayi murmushi, amma baice komai ba, suka shiga elevator ɗin zuwa hawa na 5 dan a nan office ɗinsu su dukan yake.
Khabir sai tambayarsa yake akan auren nasa amma Tafida yaƙi cewa komai sai da suka shiga har office ɗin Tafidan sannan ya bashi amsa.
“Khabir, yanzu bani da abin cewa akan auren nan, ka bari akwai wata waya da nake jira, daga baya sai muyi magana”
Kamar Khabir ɗin zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru.
“Allah kyauta, bari naje”
Tafida ya gyaɗa masa kai, wayarsa ce ta fara ringing tun kafin ya zauna, zaman yayi kamar yanda yayi niyya, ya cire hular dake kansa sannan ya daga kiran, suka gaisa da Muktar sannan dalilin kiran ya taso.
“Me ka samo ?”
Muryar tasa ta fito cikin wannan ajin nasa da kasaita, yanayi yana tura sumarsa baya, muryar Muktar ta fito daga cikin wayar yayinda yake faɗin.
“Komai ma na samo, sunanta Maryam Tijjani Muhammad, haifaffiyar hadejia unguwar garko, tanada yan uwa huɗu, babbar yayarta itace Fati matar Habib, nasan ka sanshi ai gidansa ma kusa da gidan ka ne”
Idanun Tafida a lumshe ya gyada kai, kuma shima Muktar ɗin kamar da yasan ya gyaɗa masa kan sai yaci gaba.
“Tanada ƙanne uku, Hassan da Hussain sai autansu Muhsin...... Wato Tafida abun mamakin shine ƙannen nata ƴan biyu a secondary school suke, kuma sune suke ciyar da gidan nasu, and a shekaru bazasu wuce 18 ba”
Da sauri Tafida ya buɗe idonsa
“Me ?, but ina babansu ?, ko ya rasu ?”
Ya jerowa Muktar tambayoyin, cikin wata iriyar murya da bazaka iya gano halin da yake ciki ba.
“Wallahi yana nan da ransa, da drivern tilera ne, ya riƙi kuɗi a da, amma kuma yana bin mata kasan shi kuma ƙarfe ba'a haɗashi da kazanta, sai me motar ma ya kwace kayarsa, daga nan kuma sai ya talauce, sai yake ganin kamar wai matarsa mahaifiyar su kenan itace me farar ƙafa, sai ya fara mata cin mutinci baya kula da ita da yaranta, wani yayanta ne wai Usman, Shine yake kula da ita har yaran suka taso sannan suka fara aiki a wani gareji, kuma har yanzu sune suke kula da gidan, and baban kuma har yanzu bai dena halin banzansa ba, ni wani labari da naji ma ance kuɗin auren Maryam ɗin da aka bashi zaije yayi aure dashi, abun de abun tausayi”
“umhm ina jinka”
Tafida ya faɗi hannunsa akan bakinsa
“Shi wanna kawun nasu yayan maman tasu shine yake ɗaukar nauyin karatun Maryam ɗin, dan poly take ma, ta gama level one zata fara level two, kuma kasan wani abu ?, wallahi yarinyar akwai kamun kai, ga tarbiyya bata da matsala ko kaɗan, ko saurayi ba ta da shi sai wani wai shi sanata, kuma shima ba kulashi take ba, dan yanda naji labari ma ance wai daga karshe ce masa tayi ita yanzu bata da ra'ayin aure, gaskiya kayi dace”
Ya sauke hannunsa daga kan bakinsa.
“Gaskiya kam nayi dace, nayi dace da su Fulani suka aura min ita, dan nasan idan ba ita bace ba lalle na karb'eta ba, saide kuma ita batayi dacen ba, su Fulani sun hargitsa rayuwarta da suka aura mata ni, amma babu komai, zan nema mata gun karatu a nan polytechnic din alaro, sai taci gaba kawai kaje poly din ka karbo min takardunta ka aiko min pls”
“Tafida yanzu baza kayi haƙuri da auren nan ba?”
“Yaya zanyi Muktar ?, nesanta kaina da zanyi da ita shine babban gatan da zan mata, idan har naci gaba da kusantar ta zan iya cutar da ita, and if that happens bazan tab'a yafewa kaina ba, bana san na zama silar rasa innocent soul kamarta”
Yana iya jiyo ajiyar zuciyar da Muktar yayi.
“Kuma hakane, Allah ya mana me kyau kawai”
“Ina asibiti idan ka karb'o takardun just let me know”
“Inshallah”
Daga haka kuma wayar ta ƙare, ya ƙira drivern sa ya aike shi siyyaya, sannan ya fara aikin da yake jiransa.
UCHENNA POV.
Dariya yayi bayan Abba ya gama roƙonsa akan wai yana so yayi aiki a ƙarƙashin ƴarsa, to shi a duniya me Abba zaice ya yayi,kuma ya masa musu, shi kuma Abba ganin yana dariya yasa yace.
“Kaga zan saka ta baka albashi fiye da wanda ake baka a nan....”
“Haba mana Abba, nifa bance komai ba, ni yanda kake roƙonane yake bani dariya, abba babu abinda zaka nema nayi maka naƙi, komai kake so wallahi ni me maka ne”
Ran Abba yayi tas, a kullum idan ya kalli Uchenna wani alfaharine ke cika zuciyarsa, yana jin inama ace dansa ne, dan ya fiye masa Kamal sau dubu.
“Haris.....”
Sai kuma yayi shiru.
“Na'am Abbana”
“God bless you”
“Abba God has already bless me, tunda ya bani kai a matsayin uba”
Abba ya miƙe daga kan executive chair ɗin da yake kai, ya zagaya zuwa tsallaken teburin nasa ya zauna a kujerar fake facing ta Uchenna.
“I am so proud of you Haris, Uchenna Franklin”
Uchenna na murmushin da baya rabuwa da fuskarsa ya kamo hannayen abba.
“Abba i am the one that will be proud of you, because you changed my life, Abba ka bani abinda babu wanda ya bani, ka bani kyakyawar rayuwa, Allah ya raya mana kai, Hanam ƙanwatace, zanje nayi mata aiki kyauta, ɗinki baiwata ce, laifine dan na baje basirar ɗinkina domin ƙanwata?”.
Abba ya shafa kansa, kalamansa sun ƙare, dan babu abinda zai iya cewa.
“Yaushe zan fara zuwa ?”
“Gobe”
“Allah ya kaimu”
Yana san yaje ya ga wannan ƙanwar tasa da a kullum abba bashi da magana da ta wuce tata.
TAFIDA POV.
Tare suka dawo gidan shida drivern sa, amma bai shiga gidan ba sai da suka zagaya ta baya yasa drivern ya jibge kayan da sukayi shopping, kuma tun daga kitchen ɗin yaga sauyin gidan, dan ko ina a gyare yake tsaf, dama shi baya bawa kitchen ɗin muhimanci idan ba girki zeyi ba, wasu kayanma ba tab'a amfani da su yayi ba.
Saida ya dawo ta kofar gidan ya sallami drivern sannan ya nufi gidan. Curtains ɗin falon wanda ke jikin katangar glass ɗin nan a sauƙe suke, dan haka bai samu damar ganin komai ba.
Abu na farko da idonsa ya fara gane masa a parlon bayan ya buɗe sogar shine, Maryam kwance a kan kujerar parlorn, tayi ɗai-ɗai, amma kuma lullub'e cikin hijabi, daga ganinta ba bacci take ba, duk da idonta a rufe yake,Sbd ga wani guntun murmushi a leb'enta, sai kawai ya motsa kunnensa.
Abu na farko daya fara saurara shine wannan sautin, wannan sautin daya sauya duniyarsa a kwanakin nan, ya shiga cikin irin yanayin da ya saba shiga idan yana sauraren bugun zuciyar tata, kamar igiyar ruwa na kaɗawa, kamar iska me daɗi wadda take busowa daga bishiyoyin garden ɗin gidan sa.
A tare da bugun zuciyar tata kuma sai ya tsinkayo wani abu, haka kamar magana, sai ya kara takowa cikin parlon, har ya kawo jikin kujerar da take kwance, sai a lokacin ya samu damar sauraren abinda itama take saurare.
Wato ear piece ta saka tana sauraren novels na ji. Yaji tausayinta ya ƙara cika zuciyarsa, nishaɗinta take hankali kwance, ba tareda tasan halin da rayuwarta ke ciki ba.
Kuma bisa ga dukkan alamu littafin na mata daɗi, a hasaso ya indonsa yanda zata tsorata idan ya tahseta, daga jiya zuwa yau ya fuskanci cewa tana da tsoro, kuma shi yafi jin dadin sauraron bugun zuciyar tata idan tana a tsorace.
*
Yau maryam yini tayi cikin nishaɗi, dan ko ina ta kalla a gidan wani daɗi ne ke lullub'eta, tanajin inama zata dawwama a haka, gidan ya mata fiye da zatonta, kyakyawan kitchen, kyakyawan ɗaki, ga kyakyawan garden.
Komai ma na gidan me kyau ne, haka ta yini ita kaɗai a gidan, amma kuma kaɗaicin bai dameta ba, dan akwai TV, ga kuma kitchen.
Haka ta shiga tayi abincin rana ma sannan tayi nadare dan harda shi ta dafa, bata sani ba wata ƙila zai ci.
Har tayi sallar la'asar amma babu alamar dawowar Ficar yara, to wai ita inama ya tafi ne ?, yace mata de aiki za shi, to wani aiki yake?, tayiwa kanta tambayar lokacin da take banɗaki tana wanka, sai kuma kwakwalwarta ta nuno mata hoto ɗaya daga cikin hotunansa da ta gani ɗazu, hotonsa sanye da lap cort, da kuma wani award da ta gani akan wata chest drawer.
Wato likita ne, bayan ta gama wankan ta fito ta zab'o wata riga ɗaya daga cikin kayan da tazo dasu, dan kayan da Fulani ta bata tace ba na sakawarta yanzu bane, sai ko idan fita ta kamata, fita ?, sai ta bawa kanta dariya, ko waye zai dauki mummuna yar ƙauye kamarta ya fita yawo da ita, kuma ma wai Tafida, Tafida fa?.
Da saƙe-saƙenta ta saka hijabi ta dauki wayarta ta sauƙo ƙasa, dama bata saba kwalliya ba, shi yasa ba tayi ba, kuma bawai dan bata iya ba, ta iya kwalliyar kawai de ba tayi ne.
A kan kujera ta zauna, sai taji tana san kwanciya, amma kuma ta san cewa baccin la'asar ba kyau, dan haka kawai ta yanke shawarar ƙarasa jin littafin wani gari da ta fara, dan haka ta saka ear piece ɗinta ta kamo na inda ta tsaya, dan tana ƙaunar littafi, na karantawa ko naji.
Tayi nisa a abinda take bata ko san mutum ya shigo ba, bare ta san sanda ya tsaya a kanta, sai ji tayi an ɗan bigi kujerar da take kwance akai.
A firgice ta mike zaune, tana dube-dube, sai ganin mutum tayi tsaye a kanta yana kallonta, kuma dai kamar yanda ta sanshi fuskarsa babu fara'a bare a kasinta sai kawai ta sa hannu ta zare ear piece ɗin ta cikin hijabinta, ta tsugunna ƙasa.
“Ba....barka da..... da zuwa”
Ta furta muryar ta na rawa, kamar wadda ta yi wa sarki ƙarya, gaba ɗaya ta tsorata jikinta har wata rawa yake, dama ita gata sarkin tsoro kamar farar kura, kanta sunkuye a ƙasa, ga kamshin turaren sa na barazanar fasa mata kai.
Tunda zuciyarta ta buga sau ɗaya yaji wani abu na ratsa shi tun daga saman kansa har tafukan kafarsa, yaji daɗin sautin ma ya fi na waƙar da ya ke saurare, ji ya ke kamar ya taka rawa dan dama shi gwaninta ne.
Wannan ladabin da take masa na ƙara burgeshi da ita, alƙawari yake ɗaukarwa kansa, na har Allah ya karb'i ransa ba zai tab'a cutar da wannan innocent soul ɗin ba, zeyi duk abinda zeyi ganin ya kyautata mata, ya sakata farin ciki, zai tabbatar bata nemi komai ta rasa ba, magana can ƙasan maƙoshi ya amsa sannu da zuwan da take masa, ta shiga ƙoƙarin miƙewa zata bar parlon.
“Maryam....”
Maryam taji wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan kafarta, idanuwanta ta runtse zuciyarta na tsere a kirjinta, Sunanta ya kira, cikin wata iriyar murya, ahse dama ya san sunanta?, gaba ɗaya ilahirin jikinta rawa yake har yanzu, ita bata ci gaba da tafiyar ba, kuma ita bata juyo ba.
“I want to talk to you”
Gabanta ya kuma bugawa, saida ya lumshe idanunsa a wannan karon.
'Hai fagban!'
(oh god)
ya fadi a zuciyarsa kuma cikin harshen indianci, A hankali ta juyo kuma har yanzu kanta a ƙasa, ya zauna a kan kujerar da ta tashi, ita kuma sai ta zauna a ƙasa, idanta a ƙasan tana kallon carpet, amma kuma sai idonta ya kai kan kafarsa ta dama, daga idon sawunsa, taga wani baƙin zare ɗaure a wurin, irin dai zaren da ta saba gani a ƙafar indians a filma, ashe de da gaske ma suna sakawa.
Shi kuma yayi shiru yana sauraren abinda ya zame masa kamar dole, can kuma sai yayi gyaran murya.
Ya fara magana cike da kasaita da kuma nutsuwa
“Maryam nida ke gaba ɗaya mun samu kanmu a cikin wata alaƙa me suna aure, kuma dagani harke ba tare da mun shirya ma sa ba, saide kuma dole mu karb'i hakan da hannu biyu, domin haka KADDARA TA SO, babu wanda ya isa ya ja da ita, saide dolene aurenmu ba zai kasance kamar auren kowa ba, bawai dan ban karb'eki a matsayin mata ba, sai dan wani dalili, Maryam dolene ni da ke mu nisanci juna, domin ni annoba ne, bai kamata ace wani ya rab'eni ba, Gashi an aura miki ni, kina rayuwarki aka rabaki da kowa naki aka sakaki a cikin wannan alaƙar, alaƙar da zata iya cutar da ke, Maryam da ace inada iko da na hutar dake daga wannan auren kinje kinci gabada da rayuwar da ki ka fara, amma hakan bazata samu ba, nayi bincike akanki, kuma an sanarmin da kina karatu dan haka na saka a karb'o min takardunki na can Binyaminu Usman Poly, inaso kiyi join a nan dan akwai polytechnic a cikin estate ɗin nan, inaso kici gaba da rayuwarki kamar yanda kika saba, duk da nasan kin rasa wasu abubuwan a rayuwarki, but i will try my best to make sure that baki rasa komai ba anan gaba, and one more thing, kullum da daddare ki riƙa kulle ƙofar ɗakinki, duk abinda za kiji kada ki kuskura ki fito ko ki buɗe ƙofar,kiyi haƙuri ki jure, ina san ki ɗauki zama dani a matsayin ƙaddara, Maryam”
Ya kira sunanta, mar3yam da kalamansa suka saka zuicyarta a cikin wani irin yanayi mara fassara ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai ganin shima kallonta yake, sam ta kasa gane inda zancen nasa ya dosa, farin ciki za ta yi ne ?,ko kuwa, ta rasa ma ƙwaƙƙwaran tunanin da za ta yi a kanta.
“Sbd ni.....”
Ya nuna kansa da ɗan yatsa
“Maryam i am a monster, i am a beast so, stay away from me....”
second daya..... biyu.......uku.
_Me 😱, wai Tafida yace shi monster ne, kai Daaso kiyi ta kanki🚴, dan ga dodo nan zuwa_
_Shin ya kuke ga Sarauniyar mu ta tsoro za ta yi ?_
_Ina godiya a gareku masoya_
_Share it, and ayi comments pls🙏_