Free chapter · Read without an account
End
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Sadaukarwa zuwa ga matar mijinta*
*BABI NA ARBA'IN (40)*
TAFIDA POV.
A hankali ya turo ƙofar office ɗin nasa, sannan ya shigo, mutum ya gani tsaye a balcony, kuma ko daga bayanta da ya gani, ya ganeta, sai ya yi murmushi, wato da tace masa zata fita nan zata zo kenan?.
Lap cort ɗinsa ya saƙala a jikin hook, sannan ya cire hular kansa. Ya shiga takawa a hankali ta yanda baza ta ji takunsa ba.
Bayan da nurse joke ta fice ta bar Maryam, sai ta shiga bin office ɗin da kallo, kafin ta zauna a kan wata sofa, data gaji ma da zaman sai ta fita balcony ɗin office ɗin, ta tsaya a wurin tana kallon dogayen gine-ginen dake wajen, babu wata iska sosai a wajen, amma kuma view ɗin yana da kyan gani.
Bata ankara ba ta ji hannaye sun kewayeta daga baya, cak!, iska ta ɗauke a maƙoshinta, kansa ya sako ta kafaɗarta, sannan kamshinsa ya ziyarci hancinta.
Kuma dama tasan babu me mata haka sai shi, hancinsa ya shiga goga mata a gefen kuncinta.
“Barka da zuwa matar mijinta”
Cikin raɗa ya mata maganar, Maryam ta ƙanƙame hijabinta da hannunta ke kai, wannan abun data saba ji yana yawatawa a kan fatar ta.
A hankali Tafida ya saketa, yana motsa kunnensa dan ya saurari abinda yake kewa a kullum idan basa tare, juyowa da ita ya yi ta fuskance shi.
“Ziyara ki ka kawo min?”
Maryam ta gyaɗa kanta, a lokaci guda kuma ta girgiza shi, Tafida ya yi murmushi me sauti.
“To kenan me ya kawo ki nan, ko allura ki ke so a miki, ai raunin naki ma ya warke”
Hannunta ta ɗora a kan nasa da ke shafa fuskarta da shi sannan ta zame hannun nasa tana matsawa baya.
“Abinci na kawo maka”
Tafida ya ƙara matsa kusa da ita yana kama fuskarta.
“Allah ya miki albarka, Dasso”
Ya ƙarashe yana sumbatar kanta, Maryam ta ƙara ture hannunsa.
“Abincin zai huce, muje kaci”
Ta faɗi tana dawo wa cikin office ɗin.
Bayanta ya biyo ya zauna a kan sofa yana kallonta, plate ta ɗauko a cikin basket ɗin, ta zuba masa dambun tana faɗin.
“Dambu na maka, amma ba zogale na saka ba, alayahu ne”
“Me yasa baki saka zogalen ba?”
Ta saka masa spoon a ciki tana miƙa masa.
“Babu mana, shi yasa ban saka ba, kuma ban san inda zan samu ba”
Ya karb'a yana 'yar dariya.
“Akwai bishiyar zogale a garden fa”
Ta ɗan tsaya, sannan ta ci gaba da zuba masa kunun aya a cikin glasa cup.
“Ban sani ba, kuma banma tab'a gani ba”
“Ni da kaina na shuka shi”
Ta gyaɗa kanta tana zama.
“Akwai chicken kibab, kana so?”
Ya miƙo mata plate ɗin yana faɗin.
“Me zai fito daga hannun ki nace bana so?”
Ta ɗan yi murmushi tana buɗe warmer ɗin chicken kibab, ta saka masa guda uku.
“Ke ba zaki ci ba?”
“Zan ci mana”
“Ok zo muci”
Sai ta miƙe ta dawo kusa da shi ta zauna, a kan cinyarta ya ɗora mata plate ɗin, sannan ya dunkule hannunsa na dama, ya buɗe, wata rose ce ta bayyana a hannun nasa, Maryam ta saki baki tana kallonsa, yanzu lamarin Eshaan ya dena bata mamaki.
“Abar ƙauna, ga tukwicinki”
Maryam ta kai hannu ta ɗauki rose ɗin.
“To mu ci”.
A tare suka ci abincin, bayan sun gama Maryam ta shiga haɗa kayan a cikin basket.
“Zan koma”
Tafida ya ɗan kalleta kaɗan, sannan ya mike.
“Ina zuwa”
Wata 'yar ƙaramar chest drawer ya buɗe, ya ɗauki wasu kaya, sannan ya shiga bathroom, Maryam na zaune tana jiran fitowarsa.
Jim kaɗan sai gashi ya fito, ya sauya kayan jikinsa zuwa ƙananu, wata ash T-shirt ce a jikin nasa, wadda ya ɗora mata baƙar hoodie a kai, sai track trouser fari.
Sumar kansa kwance a baya, duk da ta yi tsayi sosai.
“Taso muje ?”
Ya miƙa mata hannu, Maryam ta miƙe tana kallon hannun nasa kamar me shawarar kar ta riƙe.
“Ina ?”
“Chilling za muje”
Maryam ta yi dariya, wai chilling, ganin bazata kama hannun nasa ba yasa shi ya kamo nata da kansa, sannan ya fara janta zuwa ƙofa.
“Basket ɗin fa ?”
“Devid zai kawo miki”
Haka ta bi bayansa hannunta cikin nasa, duk inda suka ratsa a asibitin kallonsu ake, gaba ɗaya Maryam tabi ta takura, so take ya saki hannunta, amma yaƙi saki.
Da haka har suka sauƙa floor ɗin farko, a nan suka haɗu da Devid.
“Akwai basket a office, ka ɗauka ks kai mana gida”
Devid ya amsa masa, kuma daga haka suka fita farfajiyar asibitin, Maryam taga sun nufi gate gadan-gadan, da ƙyar ta samu ta zame hannunta daga nasa.
“Dr. Ina zuwa ne ?”
Suka ɗan dakata daga tafiyar, daga ita har shi suka kalli Dr. Damilola.
“Chilling zamu je”
Dr. Damilola ya yi dariya.
“Kuma a ƙafa zaku tafi ?”
Cikin pegin English ya yi maganar.
“A'a blue rail line zamu hau”
“To a dawo lafiya”
Tafida ya amsa suna ci gaba da tafiya.
Bakin titi suka fita, sannan suka hau Taxi, wadda ta sauƙe su a Marine station, wato tashar da ake hawa blue rail line, sabon jirgin ƙasa me yawo unguwa unguwa.
Tafida ya siya musu cowry card guda biyu, wato katin da ake amfani da shi wajen hawa jirgin, kamar tiket.
Daga haka kuma suka shiga jirgin, inda suka yi sa'a suka samu wajen zama.
Maryam ta shiga bin wajen da kallo.
“Wai ina zamuje ne ?”
“Chilling!”
Yanzun ma Dariya ta yi, ita idan ya faɗi kalmar ma har dariya ta ke bata.
“Ina nufin inda zamuje chilling ɗin”
Sai ya gyara zamansa, ya fito da hannunsa daga cikin aljihun hoodie ɗin jikinsa, ya tura sumar kansa baya sannan ya shiga lissafo mata inda zasu je.
“Farko Zamu fara zuwa siyyaya, daga nan sai muje jara beach, sai nike art gallery, sai Nok by Alara, za muje National museum of Lagos, sai lufasi nature park, sai mu koma gida”
Maryam ta rage girman idonta tana kallonsa, to duk yaushe ya tsara wannan ita bata sani ba?, ko a iyaka wannan zuwan nata ya shirya zuwa wajen.
A national theatre suka sauƙa. Bayan sun fito suƙa, suka hauTaxi zuwa wani mall da ake seda kayan indians na sakawa.
“Kaya zaka siya ?”
Maryam ta tambaya yayin da Tafida ya buɗe mata ƙofar shiga mall ɗin. Sai da ta shiga sannan shima ya shigo.
“Ke de, ai ni inada kayan sakawa, baki gansu a wardrobe ɗina ba ?”
“Ni kuma?, me zan yi da kaya ?”
Ta yi tambayar ba tare da ta san sanda ta furtata ba, sai kawa ya tsaya da tafiyar da yake, Maryam ta ci gaba da kallonsa tana jiran amsa, sai taga ya gyaɗa mata kai.
“Idan ina nigeria bana saka kayan india, duk da ko a indian ma ba saka su nake ba sai idan ana biki ko wani shagalin, amma ina martaba al'aduna duka biyu, idan ina nigeria ko hindi bana yi, zan saka kayan hausawa, naci abincinsu na yi komai kalar nasu, idan kuma naje india bana komai na hausawa, bana saka kayan hausawa, bana magana da hausa, bare naci abincin su, zan yi komai kamar ba'indiye, Na karb'i al'aduna duka biyu, dan haka kema hakan za ki yi, za ki je ƙasarmu sai ki saka kaya irin na matan ƙasar mu”
Maryam ta haɗiye wani abu, ita fa ba zata iya naɗa wannan saree ɗin ba, ba sanin yanda ake ɗaurashi ta yi ba, kuma ma ai ita be kamata ta saka saree ba, sbd rigarsa ta yi gajarta.
“Nifa bana san saree”
“Eh akwai wasu kayan ai, ba saree bane kawai kayan matan india, akwai chickankari da kuke cewa Pakistan, akwai lehenga wato riga da skirt da mayafi, akwai kurti na mata, sai ki zab'i wanda kike so.....”
“ Excuse me please”
Muryar wata mata ta faɗi tana kallon Tafida da ya tare mata hanya, Tafida ya matsa matar ta wuce, ya dawo ya kamo hannun Maryam.
“Muje ko ?”
Ta zame hannun nata daga nasa, sannan suka ƙarasa shiga ciki, Maryam ta ga yana gaisawa da ma'aikatan wurin, da harshen hindi, bisa ga dukkan alamu dai sun saba.
“Ye mere biwi hai bhai”
(Wannan matata ce ɗan uwa)
Mutumin da ke tsalleken wani teburi da ya raba tsakaninsu da shi ya kalli Maryam.
“Ai naga 'yar nigeria ce”
Mutumin ya faɗi cikin wani irin turanci, da Maryam a film kawai take iya jinsa, turanci indiyawa, wanda suke fitar da 'R' da kuma 'T', Maryam ta kusa tintsirewa da dariya, amma sai dariyar tata tab'ata, a sanda Tafida yake amsa shima, kuma cikin irin turancin nasa.
“Eh 'yar garinmi ce ai”
Wato shima ya iya kenan ?, to amma me yasa idan zai mata magana baya mata da irin wannan?. Maryam bata ce komai ba ta bishi da kallo kawai.
“Sunansa Vellamkonda, ɗan telugu ne, yana jin hindi amma baya iya mayarwa”
Yanzu ma bata ce komai ba, sai shima ya jiya ya kalli Vellamkonda.
“Chickankari muke so...... Ko kina san Lehenga ?”
Ya ƙarashe yana tambayarta, ita bata wani san lehenga ba, chickankari ɗinma ba dan ya faɗa mata ba da bata sani ba, kawai sai tace.
“A'a chickankari ɗin kawai”
Sai ya gyaɗa kansa yana juyawa wajen vellamkonda.
“Chikankari kawai”
“Size ɗinta fa?”
“Sai de ta gwada...”
Kusan guda ashirin ya siya mata, kuma kowanne saida ta gwada a jikinta, daga masu plane yadi sai masu ado.
Bayan sun fito daga mall ɗin suka shiga yawo a gari, duk inda ya lissafa babu inda suka tsallake, sai da suka je ɗin.
Ba su su ka dawo Alaro city ba sai bayan isha, sallalon magriba dana ishar ma a masallaci su ka yi, A ƙofar block ɗin su taxi ta sauƙe su.
Tafida ya fito daga cikin motar hannunsa riƙe da ledojin kayan da suka siyo, dan ko ɗaya bai bari Maryam ta ɗauka ba.
Unguwar tsit, babu kowa sai yan jifa-jifan mutane, duk da dare ne amma ko ina haske dau.
“Gobe zanje saloon”
Tafida ya ɗan juyo ya kalleta
“Duka ki bari sai munje can sai a miki”
Bata ƙara cewa komai ba, dan bata ga amfanin maganar ba, tunda ya riga yace haka ai shike nan.
Ji ta yi yana rera waƙa a hakali yana ɗan kaɗa kansa.
Ta juya ta kalle shi, kode bashi da lafi ?, yo in ba mara lafiya ba waye zai dinga rawa babu kiɗa ?.
Sai de kuma tunaninta ya wargaje, sanda suka shawo kwanar gidansu, ta ji sak waƙar da yake rerawa tana tashi daga wani gida a hankali, ta san gidan dama samari ne a ciki, wata ƙila sune suka kunna.
_🎶What if i say?_
_i know, you know_
_What if i told you i liked you?_
_We stay, we go what if i like you?🎶_
Iko sai Allah, wato tun daga can yake iya jiyo waƙar dake tashi a nan, waƙar da ba dan ma dare ne ba, da baza ta yi volume haka ba, dan a hankali take tashi.
“Bani abinci naci”
Muryar Tafida ta faɗa, a sanda suka koma gida, har ta shiga ɗakinta ta yi wanka, kuma bayan ta gama ne ta fito ta same shi zaune a wurin, shima ya sauya kaya, ga gashin kansa dake a jike.
Mamaki take wai yaushe ma suka ci aninci ?, a Nok by Alara ma saida suka ci abinci, amma yace yunwa yake ji yanzu ?, ita kam wata ƙila ko gobe da safe ballale ta ci wani abu ba, dan ta ƙoshi sosai.
Ta gyaɗa masa kai tana zama a kusa da shi, ta ja ladojin da suka yi siyyaya, ta ɗauki wadda aka saka musu abincin da suka yi take a way a Nok by Alara.
Ta ɗauko take a way ɗaya ta bashi, ya karb'a sannan ta miƙe ta shiga kitchen ta ɗauko masa ruwa da kunun aya.
“Ke ba za ki ci ba ?”
Maryam ta girgiza kai.
“Na ƙoshi”
Sai ya gyaɗa mata kai yana ci gaba da cin abincinsa.
Maryam ta shiga fitar da da kayan da suka siyo, tana ta yaba kyan kayan, ai gwara chickankari ɗin, me za ta wani yi da saree.
________________
_Hello!, tafiya india fa ta kankama_
_To kubiyo ni a babin mu na gaba, dan ganin yanda tafiya india zata kaya, na saiwa mutum huɗu ma ticket, waɗan da suka fara comments sune zasu bimu_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Na sadaukar da babin yau gareki daughter Ilham*
*BABI NA ARBA'IN DA 'DAYA (41)*
*Da misalin 02:40am*
Maryam na kwance a ɗakinta, ta shiga jin gurnanin da fisge-fisge, ga ƙarar abubuwa na fashewa, ba shiri ta miƙe zaune a kan gadon, dan baccin da take ji ta neme shi ta rasa.
Gurnanin Tafida take ji, da ƙarar da ya ke, kamar yanda ya saba a duk sanda abun nasa ya tashi, ita kam har ga Allah ta gaji, ta gaji da ganinsa cikin wannan halin.
Bata da wata dabara, sai kawai ta miƙe ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, ta zo ta tayar da sallah, tana yi ta na ta zuba masa Addu'a, dan bata jin zata iya wani abu bayanta.
TAFIDA POV.
_ “Eshaan sauƙo daga kan wurin mana”_
Muryar Roshni ta faɗi tana duban Ehsaan dake tsaye a kan coffee table, ya saka lap cort ɗin babansa, ga stethoscope ya rataya a wuyansa, har da saka wani glasses, shi a dole ga likita.
_“Nahi Maa(No Maa), baki ganni ba ne?, nine likita” _
Roshni ta yi dariya tana girgiza kai.
_ “Kana so ka zama likita ?” _
Ya gyaɗa mata kai.
_ “To ka dena ƙin jin magana, kullum da safe idan Maa ta baka madara ka shanye cup ɗin duka, ka riƙa zuwa makaranta, kuma kana yin homeworks ɗinka, banda yawam guje-gije ko hawa sama”_
Daga ita har shi suka waiga dan kallon Auwal dake masa wannan bayani, Eshaan ya sauƙo da ga kan coffee table, sannan ya yi wurin Auwal da gudu, ga lap cort ɗin jikinsa sai sharar ƙasa take, sbd yawan da ta masa.
Yana zuwa dab da Auwal ya yi tsalle ya faɗa jikinsa. Auwal ya yi dariya yana ɗago shi.
_“Idan na yi haka zan zama likita?” _
_ “Ɗari bisa ɗari”_
Eshaan ya yiwa Auwal peck a kumatu, sannan ya maƙalƙale masa wuya.
_“I love you Appa” _
Auwal ma ya yi masa peck ɗin a ka.
_ “I love you too son”_
_ “Ni kuma fa ?”_
Auwal na dariya ya ƙarasa inda Roshni take, sannan ya haɗesu su duka ya rungume.
_ “I love you all.....”_.
Sai suka yi dariya, wannan sautin dariyar ya shiga maimaita kansa cikin kunnen Tafida.
A hankali ya shiga buɗe idonsa, kafin ya buɗe shi gaba ɗaya, ya bi ɗakin da kallo, yanda ya hargitsa komai na ciki, dama kuma ya saba, hakan tasa baya san cika tarkace a ɗakinsa.
Da ƙyar ya iya miƙewa zaune, Abun mamaki yanzu ake kiran sallar asuba, miƙewa ya yi tsaye, a lokacin kuma ya yi arba da wutar hannunsa na ci.
Ya dunƙule hannun sannan ya buɗe, kasancewar babu curtains a ɗakin shi yasa ya fahimci cewa har yanzu a duhun asuba ake.
Hannayensa biyu duka ya ɗaga, sannan ya shiga meda kayan da suka faɗi ba tare da ya tab'a koda ɗayansu ba.
Kafin ya shiga banɗaki, ya yi wanka ya fito ya sauya kaya, kana ya wuce masallaci. Bai dawo ba sai shida.
Kuma yana dawowa kaitsaye ya wuce ɗakin Maryam, yasan cewa dole ta ji abinda ya faru jiya, wata ƙilama ya hanata bacci, dan haka zai je ya dubata.
Karatun ƙur'ani ne ya fara shiga kunnewansa yana buɗe ƙofar.
Daga can cikin wani rami kuma, wani abu da aka ƙulle a cikin kwalba ya girgiza, baƙin hayaƙin da ke ciki ya shiga yawo a cikin kwalbar.
Kan Tafida ya sara, dan haka ya dafe shi, yana tura ƙofar ɗakin, ji yake kamar ana raba kan nasa gida biyu, kamar guduma aka ɗauka ake buga masa a kan.
Cak ya tsaya yana kallonta, zaune take a kan darduma, bayanta jingine da jikin gado, idonta a lumshe, kamar me jin bacci, yanda muryarta ta ke fita cikin karatun kaɗai zai nuna maka cewar bacci take ji.
Duk da yana cikin wani hali na azaba, amma sai da tausayinta ya kama shi, baiwar Allah yanzu haka bata samu bacci ba.
Yaci gaba da takawa zuwa cikin ɗakin, amma hannunsa riƙe a kansa.
Dif!, ya ji karatun nata ya tsaya, numfashinta ya yi nauyi, alamun dai bacci ta fara.
A lokacin kuma wannan bajin hayaƙin da ke cikin kwalba ya dena motsi, kwalbar ma ta dena jijjiga.
Tsayawar karatun nata ya tsaya tare da sarawar da kansa ke yi. A hankali ya zauna a kusa da ita, kuma har lokacin bata farka ba, kanta ya kama tare da ɗorashi a kan kirjinsa, ya rungumeta a jikinsa tsam.
Cikin bacci Maryam ta ji kamshinsa a hancinta, sai kuma ta ji kamar an riƙeta, hakan yasa a wahalce ta buɗe idonta, ai ko ta yi kyakyawan gani, dan ƙur suka haɗa ido da shi, da ƙwayar idonsa wadda take ja.
Maryam ta razana zata fice daga jikinsa, amma yaƙi ya saketa.
“Ki yi baccin ki kawai ”
“A... abinci zanje na yi, yau ak...akwai aiki...”
“Ki kwanta nace ko ?”
Maryam ta yi shiru, amma kuma baccin ya gudu da ga idonta, kuma bata jin zai dawo, dan bazata iya bacci a haka ba, a cikin hannayensa ?, cab ɗi jam!!.
UCHENNA POV.
Yana dawowa gidan ya shiga neman Hanam, ɗakinta ya fara zuwa bai ganta ba, dan haka ya shiga ɗakin Arya, yasan cewa baza ta wuce nan ba.
Tsaye ya sameta a jikin baby cradle ɗin Arya, ta bashi baya, be san me take ba.
Da alama ma bata san cewa ya dawo ba, zuciyarta ta cilla cikin kogi tunanin, ji take kamar za'a rabata da Aryaan ne.
Bata ankara ba ta ji an kewaye ƙugunta ta baya, saida ta ɗan ja iska a maƙogwaronta sannan ta gane cewa shi ne.
“Nagode Hanam, ban tab'a tunanin cewa mafarkin da nake zai zama gaskiya ba, ban tab'a tunanin cewa zan shiga studio na yi waƙa ba, a koda yaushe mafarkina a nesa nake hangoshi, can nesa sosai, amma sanadiyyar ki, yau ya zo kusa, na ganshi a kusa”
Hanam ta yi ajiyar zuciya, Tun bayan rasuwar Abba ta yanke cewa za ta yi magana da Falaƙ, a kan fara waƙar Haris ɗin, yana san waƙa, kuma yana da talent ɗin waƙar. Kuma tasan cewa tun da yanzu ba Abba aikin a ƙarƙashin Kamal ba ze iyu ba.
A hankali ta juyo ta kalle shi, ba tare da ta ce masa komai ba.
Ta shiga ƙoƙarin fita daga hannunsa, amma yaƙi ya saketa.
“Waye Gabriel ?”
Tambayar ta doka wani abu me sauti kamar ganga a kan Hanam, duk da tasan cewa zai buƙaci sanin hakan, yana buƙatar sanin waye Gabriel!!.
*Room 330, Presbyterian hospital, New york*
Hanam ce kwance a kan gadon marasa lafiya, gefen fuskarta rufe da bandage, yayinda idanuwanta suka kumbura har bata iya buɗe su da kyau, a hankali siriryar ƙwalla ke zubowa ta gefen idonta.
A jiya kawai rayuwarta ta yi wani irin sauyi, sauyin da ba zai tab'a gogewa ba, a jiyan kawai Gabriel ya ɗan-ɗana mata azabar da tun da uwarta ta kawota duniya bata tab'a shan makamanciyar ta ba, a jiya Gebriel ya haike mata, ya haike mata cikin rashin imani da rashin tausayi.
Ta yi zaton cewa bayan rashin uwa da ta yi shikenan wahalarta ta yanke, ashe ba haka ba ne, ashe akwai wata wahala da azaba dake jiranta a gaba.
Ta tabbatar da yanzu rayuwarta ta gama wargajewa, babu na mijin da zai iya aurenta a haka, kimarta ta gama zubewa a idon kowa.
Ƙofar ɗakince ta buɗe, maƙociyarta Banedita ta shigo, wadda itace ta temaketa ta kawota a aibitin a jiya.
Kuma itace ta sanar da 'yan sanda, hannuta riƙe da leda ta shigo cikin ɗakin. Cike da tausayawa take kallon Hanam, dan likitan da ya karb'eta jiya yace ba ƙaramin azaba aka bata ba, ta wahala sosai.
“Sannu kinji, sunce zaki iya cin wani abu tashi na baki”
Hanam ta kawar da kanta gefe, alamun bata so, kuma itama Beneditan ta faɗa ne kawai, dan tasan wannan abun akwai ciwo ga 'ya mace, bayan haka kuma ita harda raunika a jikinta.
Haka Hanam ta yi jinya kusan sati uku a asibitin, amma bata faɗawa Abba ba, kuma yansanda sunyi bincike a kan bayanan da ta basu sunce basu samo wanda ta faɗa ba.
Kuma itama sai ta share komai ta karb'i sauyin da rayuwa ta zo mata da shi, inde har Allah zai ci gaba da ɗora mata ƙaddararo kala-kala ta shirya karb'ar su, kuma tana fatan Allah yasa ta iya jurewa.
Kuma bayan sati ukun ne ta koma aikinta, saide ta rage abubuwa da yawa, ta dena kwalliya, ta dena yawan fara'a da surutu, duk da dama can ba wani sosai take hakan ba, amma na yanzu ya ragu sosai. Kullum idan ka ganta kamar mara kafiya.
Bayan wata biyu ta soma jinya, tana laulayi irin na masu ciki, kuma tun kafin ta je asibiti Benedita ta faɗa mata cewar tana da juna biyu.
Abun ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba, amma haka ta je asibiti aka gwadata, sannan aka sanar mata da tabbacin shigar ciki a jikinta.
A ranar ta yi kuka kamar ranta zai fita, amma koda wasa bata ji san ta cire abinda ke cikin ta ba, ta ɗauke shi a matsayin ɗaya da ga cikin ƙaddarorinta na duniya, kuma tasan a ranta cewar Allah zai bata Ikon cinyewa.
Haka ta yi ta renon cikin dake jikinta, kuma ko da second ɗaya, bata tab'a jin sansa cikin ragu a cikin zuciyarta ba. Ita da Benedita suke kula da cikin.
Ga kuma su Camilla suma da suke tausaya mata, duk da cikin dake jikinta baya hanata zuwa aiki. Dan Hanam bata haɗa aiki da komai. Haka kuma duk wannan badaƙalar cikin da take bata tab'a faɗawa Abba komai a kan cikin ba.
Ana haka har ranar haihuwarta tazo, kuma daga ita sai Benedita da Camilla ne kwai a asibitin.
Sannan ko a wurin haihuwar taci baƙar azaba, dan har an afara shirin mata tiyata, Allah ya temaketa ta haifo yaron, kuma cikin ƙoshin lafiya. Amma taci azaba sosai. Dan sai da likitan da ya karb'i haihuwar ya sanar musu da cewa ba lalle ta sake samun wani cikin ba, sbd mahaifarta da ta samu matsala.
Tun da ta ɗora idonta a kan yaron, ta ji duk duniya bata da abun so da ya wuce Abba da shi, ta ji bayan Abba wani ya samu matsugunni a zuciyarta.
A da bata da wani wanda take so sama da Abba, amma a yanzu, ta samu wani, wani wanda ta ji har ƙahon zuciyarta zata iya komai dominsa.
Kuma wani abun mamaki sai yaron ya iyo kamarta gaba ɗaya, abu biyu ya rabata da shi, farin fatar da ya fita da kuma shuɗayen idanuwan da yake dasu.
Ita da Benedita suka ci gaba da kula da jararin da ta raɗawa Muhammad Aryaan, Har zuwa lokacin da aikinta ya ƙare a The House of Sofia couture .
Ta tattara komai ta koma Nigeria, babu abinda ta yi kewa a USA sai Benedita da Camilla, dan sune waɗanda suka rakota har zuwa airport, Benedita har da ƙwallarta.
Ƙalubale na farko da Hanam ta fara samu bayan ta dawo gida shi ne, 'yan gidansu da suka kira Aryaan da shege. Dama can ba shiri suke da ita ba, kullum cikin faɗa suke, duk da bata kula kowa a cikin su.
Amma a ranar sai da akayi fito na fito ita da su, ta shafawa idonta toka ta tsigesu tas, haɗi da kakkauran warning a kan kada su ƙara kiran ɗanta da shege.
Abba kansa abun ya ɗaure masa kai, yana san ya san wannan wani yaro ne 'yarsa ke ɗauke da shi tana kirarin itace uwarsa da ubansa, bayan yasan ba ta yi aure ba, kuma bata faɗa masa za ta yi aure ba.
Duk da yana waya sosai da ita sanda tana USA ɗin, amma bata tab'a masa wani batu a kan wani yaro ba.
Dan haka tana da sati ɗaya da dawo nigeria ya kirata babban parlonsa.
“Bannute waye wannan yaron ?”
Hanam ta sunkuya ta kalli kyakyawan jaririn da take ganin fuskarta a kan tasa, sannan ta ɗago ta kalli Abba.
“Ɗana ne Abba”
Abba ya girgiza kansa.
“Maman babanta ni ban miki Aure ba, kuma nasan ba ki yi aure ba, yaya aka yi ki ka samu yaro ?”
Cikin murmushi ta tsara masa komai, ta faɗa masa duk abinda ya faru, kamar labarin baya ƙona mata rai, kamar ba a kanta abun ya faru ba, kuma kamar wadda ta zauce.
Shi kansa Abba sai da yabyi kuka, dan shi yasan irin halin da take ciki a yanzu ma, amma kuma ga wata ƙaddarar Allah ya ƙara ɗoro mata.
“Abba ka dena kuka, nahan ma'anna kayal, yalli sha'atulul ƙadar huwa yalli rah yisir”
(Bamu da zabi Abba, YADDA ƘADDARA TA SO haka zata kansace”
An wuce lokacin da zata zauna ta yi kuka, a baya ne ta sha kulle kanta a ɗaki ta risgi kukan rashin uwa, a baya ne ta sha zubar da hawaye a kan abinda 'yan uwanta suke mata.
Amma yanzu komai ya sauya, an wuce wannan lokacin da zata zauna tana kuka kamar ƙaramar yarinya, yanzu ta girma, ita uwace, wadda take jin zata iya kula da nauyin ɗanta da Allah ya bata, ji take zata iya kareshi daga duk wani abun ƙi, ji take zata iya sadaukar da komai nata domin ya samu farin ciki.
Dan haka zata ta sadaukar da lokacin ta, ta sadaukar da auren da take shirin yi, ta sadaukar da duk abin da tasan zata iya duka domin Aryaan, ba zata gudu ta bar shi ba, domin ita uwa ce.
Abba ya miƙo mata hannu, alamun ta bashi Arya, Hanam ta yi murmushi tana miƙa masa shi.
“Kamar ke sanda kina ƙarama, amma kuma ke baki da blue eyes, kuma shi ya fiki farar fata”
Kusan a tare su ka yi dariya da Abba, tana kallonsu su duka, Haka Allah ya so su kasance ita da Arya, shi ita ce zata rene shi, yayin da ita kuma Abba ne ya renata.
Sai kuma ta godewa Allah, domin ya mata ni'imar da wasu basu da ita, wasu gaba ɗaya iyayen ma basu da su, tun tasowarta bata rasa komai ba, dawammamen farin ciki ne kawai ta rasa.
Kuma ta dan gana, domin babu wani abu me dawwama a duniya, komai me ƙarewa ne.
“Menene suna sa ?”
“Muhammad, Aryaan”
Abba ya kalli yaron sannan ya kalleta.
“Sunana ?”
Ta gyaɗa masa kai tana murmushi.
“Bani da kamar kai Abba”.
____________
_Na ƙarar da toilet paper kusan tara🤧,, kuka nake sosai, rayuwar Hanam abar a tausayawa ce_
_To ashe wanga fikafiki(munafiki) yana nan lab'e be gudu ba, bakin ruhi nake magana a kai😁_
_Naga addu'o'in ku masoya, ina me godiya a gare ku_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Wannan babin naki ne Khadeeja*
*BABI NA ARBA'IN DA BIYU (42)*
HANAM & HARIS.
Zaune suka a kasan carpet, yayin da Hanam ta jingina da jikin baby cradle ɗin Arya, shiru ɗakin kamar ruwa ya cinye komai.
Shi Uchenna yana mamakin yanda ta iya haɗiye baƙin ciki kala-kala a rayuwarta, amma sam bata nunawa.
Yayin da Hanam ke ƙoƙarin danne famun ciwon da ta yiwa zuciyarta.
“Gebriel shina mahaifin Aryaan, kaga nan?”
Ta faɗi tana nuna masa gefen fuskarta, Uchenna ya kalli tabon dake wurin.
“A sanda ya shigo gidan ya buga mun wani ƙarfe a wurin, kalli nan ma”
Ta nuna masa goshinta.
“Da bango ya buga kai na, saida ya dake ni sosai, kafin ya haike min, cikin rashin imani da rashin tausayi”
Uchenna ya rintse idanunsa, yana jin maganganun nata kamar tana watsa masa ruwan zafi ne, yana jin me yasa ɗazu da suka zo be kama Gebriel ɗin ya dake shi ba.
Babu ko ɗison hawaye a idon Hanam, babu komai sai hotunan abinda ya faru da ita ɗayan bayan ɗaya da suke haskawa a ciki.
“Na ci azaba sosai a sanda zan haifi Arya, kuma bayan na haife shi na tabbatar da cewa rayuwata ta sauya, na tabbatar da cewa na samu sauyi, matsayina ya ƙaru na zama uwa, uwa wadda zata zama katanga wurin faɗa da duk wani abun cutarwa ga ɗanta, bayan na sameka kuma sai na ƙara jin duniyata ta cika, a da ina ganin kamar duniyar duhu gareta, babu komai a ciki sai tashin hankali da b'acin rai, ina ganin kamar duniyar b'_an gare uku gareta, wanda ko wanne yake da duhu banda guda ɗaya, kuma wannan b'angaren na farko Abba ne, bayan zuwan Arya sai ɗayan b'angaren ma ya yi haske. Daga baya kuma sai gaka, wanda ka gama cike hasken gaba ɗaya, amma kuma bayan rasa Abba sai ɗayan b'angaren ya yi duhu, zuwan Masarrat da Mom ɗinka sai ya haske min wurin. Na ji ni a cikin duniya me ɗauke da hasken da zai iya haska min ko ina”
A hankali Uchenna ya jata jikinsa ya rungume, yana shafa bayanta.
“Bana cikin Damuwa Harees, damuwata ta ƙare, da yardar Allah”
“Inshaallah”
“Bana san na sake ganin Gabriel a kusa da ɗana”
“Sshhhhh, Arya ɗan mu ne mu duka, ba naki bane ke ɗaya”.
Maganar da Abba ya yi masa a ranar da aka ɗaura aurensa da Hanam ta gifta cikin tunaninsa.
_“Harees, Be Hanam's place of peace. She is tired of pain”_
A lokacin bai fahimci komai ba da ga cikin maganar ba, amma yanzu da ya ji komai a kanta sai maganar ta dawo masa, gaskiya Abba ya faɗa, Hanam was tired of pain. A hankali ya furta.
“Allah yaji ƙanka Abba”
Be san cewa Hanam ta ji ba, sai kawai ya ji hannyenta sun ƙara kewaye shi tana faɗin.
“Ameen”.
A wannan daren.
*
Gabriel ya zauna a kusa da Alice matarsa.
Wurin da suke wani hotel ne da suka kama a lagos, kallon Alice kawai Gabriel yake, wadda ido da hanci suka mata ja, sakamakon kukan da ta yi.
“Kin tabbata Alice wannan ita kaɗaice mafitar mu ?”
Alice ta juyo ta kalleshi.
“Shin kana ga za ta bamu shi ne ?, tun da har ta furta cewa ba ma tasan ganin mu ba bamu yaron nan za ta yi ba, nigerians suna da taurin kai sosai, ina san na zama uwa, amma babu hali, to me zan zauna na yi a duniya Gebriel ?”
Janta ya yi jikinsa ya rungume yana shafa kanta.
“Tunda de har kina so mu kashe kan mu ne za mu yi, amma ba'a nigeri ba, mu bari sai mun koma New york”
A hankali ta gyaɗa masa kai tana jan hanci.
“Ya ya za mu yi?, guba zamu sha ko rataye kanmu za mu yi”
“Musha guba kawai”
“Shikenan, sai idan mun koma gida, na ɗaukar miki alƙawarin tare zamu mutu, ba zan tab'a barin ki ke ɗaya ba, raina fansa gareki Alice”.
(Allah mun gode maka da kasa muka zama daga cikin musulmai).
*Navi Mumbai International Airport, India*
*08:00am*
ESHAM POV.
Eshaan ne ke turo trolley ɗin kayan su, yayin da Maryam ke biye da shi a baya, yanayinta kawai zaka kalla kasan cewa a gajiye take.
Dan gaba ɗaya jikinta babu wata gab'a da bata mata ciwo, musamman ma ƙafarta, Jiya daddare jirginsu ya taso, dan haka kwanan jirgi su ka yi.
Tafida ya ɗan tsaya sbd wayarsa da ta yi ƙara, ya kai hannu cikin aljihun wandonsa ya zarota. 'NEHA' ya gani rubuce a kan screen ɗin.
“Ke 'yar ƙauye ina ki ka shiga ?”
“Bhai nifa ina india, yaushe zaku ƙaraso”
“Ni na fasa zuwa sai gobe”
“Kya ?!(me ?!)”
Ya ji yanda sautin ta ya fito a razane, ya kunshe dariyar sa yana faɗin.
“Sai an jima”
Ɗif!, ya katse kiran, sannan ya juyo ya kalli Miriam dake tsaye a gefensa.
Sanye take cikin wani maroon chickankari, wanda akayiwa wuyan adon embroidery, wandon da rigar kalar su ɗaya, rigar ta sauƙo mata har ƙasan guwa. Ta yafa mayafin chickankari ɗin a kanta, ta ratayoshi ta kafaɗarta.
Bawai kama ta masa da indians ba, dan bata da kamarsu, amma kayan sun amshi jikinta sosai.
“Ko na goyeki?”
Ta zaro ido tana kallon tarin jama'ar dake wajen terminal ɗin.
“Ke, nan ba nigeria bace, nan ƙasar martaba soyyayace, ba'a wasa da soyyaya a india, hasali ma ita kanta ƙasar soyyaya ce”
Ita de bata ce masa komai ba, sai bin mutanen dake wajen take da kallo, ba zata ce bata tab'a ganin irin su ba, dan ga Tafida nan, shi kaɗai ma ya isa misali, amma ita ko da a mafarki bata tab'a zaton ganin kanta koda a abuja ba ne, bare kuma lagos, daga nan ma sai ta wuto india. Allah ƙadirun ala man ya sha'u.
Duk taxi ɗin da ta zo wucewa sai Maryam ta shiga ɗaga musu hannu alamun su tsaya, amma ko kallonta basa yi.
Dariyar Eshaan ta ni a bayanta, hakan yasa ta juya ta kalle shi.
“'Yan matan Tafida kenan, nan basa taxi basa tsayawa a haka, bari kiga ikon Allah”
Hannunsa ya ɗaga,ya haɗe babban ɗan yatsansa da manuniyarsa, suka bada shape ɗin circle, ya kai ya saka a bakinsa sannan ya hura.
Ya bada sautin fito, kiiii!, ka ke ji taxi har biyu sunci birki. Maryam ta bisu da kallo, Tabbas wannan shine ikon Allah,wato ikon gaske.
Tafida ya sallami ɗaya, sannan aka saka musu kayan su a booth ɗin ɗayar, suka shiga.
Kuma suna shiga Tafida ya janyo Maryam jikinsa, tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa.
“Nasan kin gaji, ki kwanta kawai”
Bata ƙara ce masa komai ba, sai ta yi shiru, dan da gasken ne ta gaji, ita bata ƙi a ce ta samu gado ta kwanta ba ma.
*Survey NO. 1433, Shiv Mandir Talo St, Chikoli, Mumbai, India*
Mutum biyu ne tsaye a filin cricket, ɗayar macace, kuma wadda za'a iya kira da budurwa, ta riƙe ƙaramar ball ɗin cricket, wadda take shirin wurga ta.
Shi kuma ɗaya na miji ne, wanda ba zai wuce 15 yrs ba, shi kuma ya riƙe cricket bat a hannunsa, ya ɗau matsayarsa yana jiran ta cillo ball ɗin.
Daga can gefe kuma wata farar dattijiwa ce sanye cikin Saree fari, tana zaune a kan garden chair, hannunta riƙe da sandar dogaronta.
Daga gefenta kuma wani magidanci ne, yana zaune suna ɗan hira da shi, amma gaba ɗaya rabin hankalinta na kan wasan cricket ɗin da jikokinta ke bugawa.
Budurwar ta cilla ball ɗin, yayin da yaron ya daketa da bat ɗin hannunsa, kwallon ta ta shi sama, kowa ya bita da kallo yana san yaga inda zata tsaya.
Sai dai me ?, cak, suka ga ta tsaya a iska, kuma ko ba'a faɗa ba sun san waye me wannan aikin.
Dan haka gaba ɗaya su huɗun suka juyo suka kalli hanyar shigowa garden ɗin.
Kuma kamar yanda suka zata shine, ya ɗaga hannunsa setin ball ɗin. Matashin yaron ne ya rugo da gudu ya yi kansa yana faɗin.
“Bhaiyya!”
Yana ƙarsawa kusa da shi su ka rungume juna suna dariya, a lokacin kuma ya saki ƙwallon ta faɗo a kan budurwar.
Ta dafe wurin tana sosawa, tare da sakin 'yar ƙara.
“Kefa soja ce, ai ba kya ji zafi ba”
Cikin yaran hindi ya mata maganar, ta ɗauki bat ɗin da yaron ya jefar, ta yi kansa, sai ko ya fita a guja, itama ta saka gudun tana bin bayansa.
Dattijuwar nan ta miƙe ta na kallonsu, yarintarsu kaf tana dawowa sabuwa a idonta, sanda suna yara kamar haka suke daren gudu a lambun.
Da ƙyar ya iya samu ya ƙaraso wajen dattijiwar, yana zuwa zai rungumeta ta ja baya, haɗi da kawar da kanta.
Sai ya yi murmushi tare da kama kunnuwansa.
“Sorry Daadi, mujh maaf kardo”
(i am so sorry)
Taƙi ko kallonsa, sai ya kalli magidancin dake tsaye a kusa da ita
“Aree Chacha, kaise ho tum ?”
(iyee kawu, to ya kake ?)
Ya yi maganar yayin da suke yin side hug.
“Ina lafiya Eshaan, ya aiki ?”
“Kawu aiki ba daɗi, ka saka baki wannan tsohuwar ta yafe min mana.....”
A dai-dai lokacin wani duka me ƙarfi ya sauƙa a gadon bayansa, ji kake b'ass!, abu na karyewa.
Budurwar ta cillar da sauran bat ɗin da ta rage a hannunta, dan rabin bat ɗin ya karye, amma shi wanda ta bigawan ko a jikinsa, dan ko motsawa be yi ba, ta saba ganin hakan, dan ko ƙarfe zata buga masa sede ya lanƙwashe.
“Daadi pls, ai de na cika alƙawari, kalli sumar dana tara a kaina, kuma ma ai Bikin holi ɗin jibi ne”
“Gaskiya Eshaan baka kyauta ba, kafi shekara rabonka da india, ko bikin Neha ma fa baka zo ba”
“Na sani kawu, amma ka shawo min kan 'yar tsohuwar nan”
Daadi ta juyo ta kalleshi, sannan ta kai hannu ta mirɗe masa kunne.
“Kai baka ji ko ?”
“Aaahhh, Daadi za ki cire min kunne”
Sakin kunnen nasa ta yi tana wurga masa harara.
“Zonan my boo, kinsan ai ina sanki ko ?”
Ya faɗi yayin da yake rungumeta, Daadi ta yi dariya, Allah ya saka mata tausayin jikokinta, musamman Eshaan da Neha da kuma Gulzar, dan sune marayu a ciki.
“Ke kuma na dawo kanki”
Ya saki Daadi yana kallon Neha, hannunsa ya dunƙule sannan ya buɗe, kyankyanso ya bayyana a tafin hannun nasa, kuma daga haka ya cilla mata jikinta. Neha ta fita da gudu ta koma cikin gidan ta ƙofar kitchen.
“Kai ina matar taka ?, ko banda ita ka zo?”
“Mts, shiiiiii!!”
Ya faɗi yana dafe goshinsa, alamun mantuwa, shaf ya mance da Maryam dake bakin ƙofar garden ɗin.
“Ek minit Daadi”
(one minutes Kaka).
Ya nufi ƙofar Garden ɗin, kuma suma sai a sannan suka lura da ƙofar garden ɗin.
Tun da me taxi ɗin ya sauƙe su a cikin gidan, Eshaan ya saka masu aikin gidan su shiga da jakukunansu ciki, yasan cewa duk yanda akayi war haka suna garden, kuma ya yi sa'a, dan suna garden ɗin.
Da suka ƙaraso bakin garden ɗin sai yace wa Maryam ta jira shi a nan, ta jingina da jikin ƙofar shiga tana kallon irin farin cikin da yake da 'yan uwansa.
Kamar yanda ya faɗa mata ne, yafi farin ciki idan yana india, dan a nigeria ya cika kame kai, ba shi da surutu sosai, amna kuma a nan ta ga ba haka bane.
Hannunta ya kama bayan da ya ƙaraso kusa da ita, Maryam ta kalleshi a tsorace, zuciyarta na bugawa, yayin da shi kuma yake saurarin sautinta.
Ta kalleshi ta kalli su Daadi, wannan sai a ce basu da kunya ai, be saketa ba haka ya shiga janta har zuwa gaban Daadi, tana tirjewa amma sai da ya kaita.
Daadi ta kalleta na 'yan sakkani, Maryam ta rasa wace irin gaisuwa zata mata, ita ba wani hindi take ji sosai ba, kawai sai ta yanke shawarar cewa.
“Namaste!”
“Kace tana jin hindi ?, dama akwai indians a nigeria?”
Bisa ga mamakinta sai ta ji tsohuwar ta mata hausa, duk da ba ta fita da kyau, Eshaan ya yi dariya.
“Ba haushiya ce Daadi, bata san cewa kina jin hausa ba shi yasa”
“Maryam ko ?”
A hankali Maryam ta gyaɗa mata kai. Daadi ta rungume ta tare da faɗin.
“Barka da shigowa ahalin Iqbal Khan”
*Da Misalin 05:04pm*
Maryam ta tako da ga kan stairs a hankali, ita tun ɗazu ta je ta kwanta ta ke hutawa, sallah ce kawai ke tashin ta, kuma har abinci an aiko mata, abincin da kwata-kwata ta kasa cinsa, dan ita bata cika cin baƙon abinci ba, cikinta baya san baƙon abu.
Ta ɗan tsaya da tafiyar, tana kallon mutanen dake falo, Daadi ce da kawu Irfan, sai xan kawu Irfan ɗin da a ɗazu ya ce mata sunan Atif, amma kuma akwai karin wasu mata biyu da bata samu ta gansu ɗazu ba, sai kuma Eshaan, wanda rabonta da shi tun zuwansu.
Wadda ta saba gani a hoton nan ce ta taso harda gudunta ta rungume ta.
“Oyoyo Yayata!”
Da ga muryarta Maryam ta fahimci cewa Neha ce, ita sai ta yi murmushi a sanda Neha ɗin ke sakinta.
Murmushin da Neha ɗin ke yi ne ya ƙara bayyana mata kamarta da Eshaan, amma kuma duk da haka Eshaan ɗin ya fita kyau, hasken fata kawai ta fishi, a yanda ta lura ma kowa na gidan ya fishi fari, ita da take ganin ya fita fari sosai, ashe shi ma 'yan uwansa sun fishi fari.
Neha ta ja hannunta zuwa cikin falon, inda Maryam ta ƙara gaida su Daadi. Maryam Kawai binsu take da kallo musamman Neha, babu abinda ke bata mamaki irin yawan gashin Neha ɗin.
“Bhabi (sirikata) wannan itace Anti Saffah, matar kawu Irfan ce, kuma itace babar Atif”
Maryam ta gaishe da matar da hausa, amma sai ta amsa mata da turanci.
“Tana jin hausa, amma bata iya mayarwa”
Maryam ta gyaɗa kanta tana ci gaba da kallonsu, ashe Tafida so yake ya mayar da ita kalar 'yan ƙasarsu, wata ƙila shi ya ga cewar hakan zata iyu, amma ita a ba ta ga iyuwar hakan ba, dan babu yanda za'ayi ta zama kamar su, sai dai ta kwatanta.
“Ke!, kin isheta da surutu, wai ni ina mijinki ne ?, me yasa ya barki ki ka taho ?”
“Kai kuma ka fita idona Bhai, da de kafin ka zo ina kewarka, amma yanzu duk ka isheni Allah”
Haka Neha da Eshaan suka ci gaba da faɗa, Su Daadi kuma suna ta hira, inda suke ɗan sakota a ciki jifa-jifa.
______________
_Wayyo Allah Hanam😭😭😭, waye ya taya ni kuka?_
_And Hey!, mun iso india fa😁😁_
_Ina godiya gare ku masoya a sali_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Wannan naki ne Ummu Sabir*
*BABI NA ARBA'IN DA UKU (43)*
HARIS POV.
“Da da na tsaya a gaban microphone $in, sai na ji gaba na yana faɗuwa, na ji kamar bazan iya ba, dana kalli yanda Falaƙ da Djn nata suke kallo na sai na ji na ƙara tsorata, na sare gaba ɗaya. Amma a hankali dana rufe idona, sai na fsra jin ina rera waƙar haɗe da sautin kiɗan dake tashi”
Cewar Haris, yayin da suke zaune a falon gidansu, Hanam ce kwance a jikinsa, shi kuma yana shafa kanta haɗi da bata labari.
Wayar Hanam ɗince ta yi ringing hakan yasa ta ta shi daga jikin nasa ta miƙa hannunta ɗauko 'Y Kamal'.
Ɗaga kiran ta yi sannan ta kai kunnenta.
“Hanam gaskiya baki kyauta ba, ai na yi tunanin bayan rasuwar Abba komai zai wuce, mu haɗa kanmu waje ɗaya, mu manta da baya mu rungumi sabuwar rayuwa, ashe ke ba haka ki ka ɗauka ba!”
Hanam ta sunkuyar da kanta ƙasa, dan yanzu ji take kamar Abba ne ke mata faɗa, dan an riga an bashi matsayin Abba a gidan, yanzu haka shirye-shiryen bikinsa suke.
Kums tasan faɗan ba a kan komai bane face Haris da ya aje aiki a kamfanin Abba, kuma ita A ganinta hakan yafi mata daɗi, dan ko ba komai mijinta zai fita daga cikin danginta, ita bata san guntsiri tsoma, a zo ana ta kace nace a kan dukiya.
“Ka yi haƙuri Yaya, ba wai dan baku isa ba ne yasa ya bar aiki, burinsa ne ya cika, ya samu aikin da ya fi wannan shi yasa”
“Nide duk da haka banji daɗi ba wallahi, amma Allah ya sanya da alkairi”
Daga haka kuma suka ɗan tab'a hira a kan tsare-tsare bikin nasa kafin suka yi sallama.
“Kamal ba?”
Ta gyaɗa masa kai tana ƙara kwanciya a jikinsa.
“Yaushe za'a yi recording ɗin vedion?”
“Inaga nan da jibi za'a fara”
“Kunyi magana da Falaƙ ɗin ?”
“Eh”
A yanzu haka waƙar da Haris ɗin suka yi shi da falaƙ ita ce ke trending a ko wani social media, duk da audio ce ba vedio ba.
Wakar ta ɗaukaka sosai, sbd record label ɗin Falaq ɗin shaharrare ne, dan tana da ɗaukaka sosai. Duk da ma tafi ƙamari a nollywood, kuma shima ba waƙar hausa suka yi ba.
“Hairs, zaka iya tunawa a wattanin da suja wuce, a parking lot ɗin wani shopping mall ka temaki wata mata me yaro?”
Ta tambaya tana kallonsa, sai ta ga ya ɗagota daga jikinsa, yana mata kaallon mamaki.
“Wai kece ?”
Ta gyaɗa masa kai tana kwanciya a jiki nasa.
“Ni ce, a time ɗin ai Ya Kamal ne yasa a sato Arya”
Sai ta ji yana dariya, ta ɗago ta kalle shi.
“Miye na dariyar ?”
“Kawai na tuno yanda kike ta kuka kin ihu'Help!, help!, wani zai sace min jaririna’”
Ya yi maganar yana kwatanta muryarta, Hanam ta ɗaka masa duka a kafaɗa tana turo baki.
“Ni wallahi ban yi ihu ba, kuma ko kuma banyi ba”
Sai ya riƙeda da kyau a jikinsa.
“Wasa bake miki ai, nasan ke jaruma ce, me zuciyar ƙarfe”
Ta yi murmushin jib daɗi, tana gyara zamanta, yayinda shi kuma ya ci gaba da bata labarin da ya fara.
MARYAM POV.
Taye take a ɗakin da aka basu, wanda Eshaan ya faɗa mata cewar ɗakinsa ne tun yana gidan.
Kayan sakawarsu take jerawa a cikin wardrobe, Allah ne kaɗai yasan kalar yunwar da ta ke ji, dan har yanzu ita ta kasa cin abincin su.
Sai yatsina fuska ta ke yayin da cikinta ke ƙullewa. Hannunta ya aje riga ta ƙarshe, kafin ta rufe ƙofar wardrobe ɗin.
Ƙofar ɗakin a ka turo, hakan yasa ta klli ƙofar.
Eshaan ya shigo yana kallon Maryam, wadda itama shi take kallo.
“Me ki ke ne ?”
“Kaya na saka a loka”
Ta bashi amsa a sanda take zama a bakin gado, idon Eshaan ya kai kan abincin dake aje a kan coffee table.
“Wai baki ci abinci ba Miriam ?”
Ta yi shiru bata ce masa komai ba.
“Ba zaki iya ci bane ?”
A hankali ta gyaɗa masa kai. Shima sai ya gyaɗa nasa kan, sannan ya ɗauke abinci ya fita da shi.
Har bacci ya soma ɗaukar Maryam bai dawo ba, tana gyangyaɗi ta ji an turo ƙofa, hakan yasa ta buɗe idonta.
“Gashi noodles ce, ai zaki iya ci ?”
Ta gyaɗa masa kai tana karb'ar plate ɗin hannunsa.
“Nagode”
Shima kuma yana batan, ya yi jikin wardrobe yana tambayarta inda ta aje masa kayansa, tana cin abincin abincin ta bashi amsa.
Sweat trouser da T-shirt ya ɗauka, sannan ya shiga bathroom.
Sanda ya fito Maryam har ta gama cin abincin ta aje plate ɗin a kan coffee table.
Maryam ta bi shi da kallo, sumar kansa a jiƙe take, kuma duka ta barbaje a kan goshinsa, daga baya kuma a kan wuyansa.
Ta yi saurin kauda idonta a sanda ya juyo, sai kawai ta waske da cewa.
“A ina zan kwanta ?”
Ya ɗanyi jim, yana kallonta, hijabine a jikinta kamar yanda ta saba.
“Ga gado nan”
Sai ta kalli gadon sannan ta kalle shi.
“Kai kuma fa a ina zaka kwanta ?”
“A gadon mana ”
Ya amsa mata, yana taje sumarsa.
Maryam ta zoro ido, yayin da gabanta ya shiga bugu, ai ta yi tuanin cewa tsoronta ya barta, bata san cewa har yanzu yana tare da ita ba, wai me ?, a gado ɗaya zasu kwanta ?.
Juyowa ya yi ya ƙaraso jikin gadon yana sauraron bugun zuciyarta. Dariya ta so ta ba shi yanda take a tsorace.
“Ki kwanta mana, ko sai na kwantar da ke...”
Ba shiri Maryam ta kwanta a kan gadon, tare da juya masa baya, ta naɗe waje guda kamar curin nakiya.
Yanzu kam murmushi ya yi.Ya koma jikin wardrobe ɗin ya ɗauko chargers, ya dawo ya saka keypad ɗinsa a chargy, sannan shima ya kwanta a ɗayan bangaren.
Maryam tana jin gadon ya yi motsi ta ƙara ƙanƙamewa waje guda, zuciyarta kamar zata fito da ga ƙirjinta.
Kuma hakan be ishi Tafida ya gama da ita ba, saida ya saka hannayensa duka biyu, ya juyo da ita ta fuskanshi, sannan ya janyota jikinsa sosai.
Maryam ta ji komai ya tsaya mata cak, duniyar ma kamar bata juyawa, wata ƙila inner earth core ɗin ne ya samu matsala, abinda take ji ma a halin yanzu earth ɗin ba zata iya ɗauka ba, tana buƙatar ƙarin mars, wata ƙila ma sai dai Jupiter.
Eshaan ya saki murmushi yana jin yanda zuciyarta tata ke bugawa kamar a kunnensa.
“Miriam mu yi hira”
“Ummm ?”
“Nace mu yi hira, muyi hirar yanda bikin holi zai kasance”
Bakin Maryam ya mutu murus, ba zata iya cewa komai ba, dan a yanayin da take ciki, numfashinta ma da ƙyar ya ke fita.
Eshaan ya ƙara matseta a jikinsa
“Kin yi shiru cutie”
Yanxun ma bata iya cewa komai ba.
“Ok to ki yi bacci, nasan kin gaji”
Ya yi mata peck a kai, sannan ya ƙara gyara ruƙon da ya yi mata, ya sunkuyo da kansa kaɗan, yana kallon idonta ta cikin hasken ɗakin da bai kashe ba.
“Can i kiss you ?”
Maryam bata san sanda ta sunkuyar da kanta ƙasa ba, sannan ta ƙara shigar da kanta kirjinsa.
Ya yi dariya har jikinsu na jijjiga a tare.
“Yanzu baza'a ban ɗani ba?, guda ɗaya fa zan yi”
Bata ɗago ba sai ma hannunta da ta saka ta maƙalƙale shi.
Ya kuma yin dariya, dama hakan yake so. Yanzu da cewa ya yi ta riƙe shi haka bazata iya ba, amma da ya mata haka ai gashi ta yi.
Hannunsa ya ɗaga ya yi nuna da switch sannan ya motsa hannunsa, hasken ya ɗauke, ɗakin ya yi duhu.
Wanda ya ƙara tsorata Maryam ta maƙalƙale Tafida jikinta na ƙara yin rawa, tsabar tsoro bata san sanda tace.
“Sundar bana san duhu, tsoro nake ji”
Tafida ya tsira mata ido duk da babu wani haske sosai a ɗakin ss sanda yake shigowa ta taga, shi kam yanzu mamakinta ya fara kama shi, shi bata tsoronsa duk irin halin da zai shiga, amma kuma tana tsoron abubuwa da dama, bacin shi ne ya kamata ace ya zama abin tsoronta. Wato shi yasa kullum yake ganin wutar ɗakinta a kunne da daddare.
A hankali ya lalubo kunnenta sannan ya ɗora a hannunsa akanta, yayin da ɗayan hannun nasa ke sakale a ƙugunta.
“Ssshhhhh, kada ki ji tsoro ina nan tare da ke, kin ji ?”
Ta gyaɗa masa kai, kuma ta ji ɗin, tama ji abinda yafi hakan, dan yanda ya mata maganar cikin raɗa yasa ta dawo cikin hayyacinta ta gano abinda take shirin yi.
Eshaan ya cigaba da shafa kanta kamar wata ƙaramar yarinya.
“To ka kunna hasken”
“Ni bana bacci a cikin haske, ki kwantar da hankalin ki fa, ina nan, babu abinda zai sameki”
Yanzunma kanta ta gyaɗa masa, peck ya kuma mata a ka, sannan ya furta abinda bai tab'a faɗa mata ba.
“I love you Miriam, i love you”
Maryam ta ji zuciyarta ta narke nan take, kamar yanda butter ke narkewa a cikin pan, kamar ba a kan gadon take a kwance ba, kamar tana kwance a kan wani gajimare me laushi ne, taji wani sa shi na zuciyarta ya rufta.
Tunda take da shi bai tab'a faɗa mata yana santa ba sai yau, yana faɗa mata amma ba a irin wannan sigar ba, sai dai yace he is nust about her, ko she complete him, amma bai tab'a furta mata haka kai tsaye ba.
Maryam ta ƙara riƙe shi, tana jin kamar itama tace masa tana sansa, tana san fiye ma da yanda shi yake santa wata ƙila.
Eshaan be rintsa ba saida ya battara da Maryam ta yi bacci, sannan ya kuma Pecking kanta, ya dawo kan lips ɗinta ya yi pecking, sannan shima ya rufe idonsa. Yana rayawa ransa cewa ko da shuɗin ruhi ne ke jikinsa bai isa ya tashi yau ba, dan ba zai bari ya lalata masa wannan moment ɗin ba, for the first time yana kwance gado ɗaya da Miriam.
*Washe gari*
*Da 08:00pm*
Eshan ya sauƙo daga kan stairs, cikin wannan takun nasa na aji da ƙasaita, sanye yake da farin chinos trouser, da baƙar printed shirt, sai denim jacket baƙa da ya ɗora a samman T-shirt ɗin.
Ya tsaya yana kallon mutanen dake falon, Daadi da neha ne suke magana da masu decorating gida idan anaa biki ko shagali. Sun zube musu hotuna kala-kala, suna zab'ar irin wanda suke so a musu.
Yayin da Maryam ke zaune a kan kujera, wayarta riƙe a hanunta tana dannawa. Anti Saffah ce zaune a gefenta, ita kuma tana waya.
Daadi ce ta lura da shi, ta juyo ta kalleshi da kyau.
“Ina zuwa ?”
Ta tambaya cikin yaren hindi, Eshaan ya kai hannu ya tab'a sumar kansa.
“Aski zanje sumar nan ta min yawa, kuma zanje na haɗu da Arjit ta can”
“In zo muje ?”
Cewar Neha, Eshaan ya wurga mata harara.
“Inje ina da ke ?, da matata zan tafi”
Sai a lokacin Maryam ta ɗago da kanta ta kallesu, dama tun da ta tashi take jin zaman ɗakin babu daɗi, Neha ce ta zo ta kirata a kan ta zo zasu ci abinci.
Kuma ko da suka zo cin abinci yau ta iya cin abincin nasu, dan tikka masala ce da plate bread, haka ta ɗan ci kaɗan. kuma bayan sun ci abinci shine suka dawo falo suka zauna, har waɗanan mutanen suka zo.
Wayarta ta ɗauka ta shiga buɗe comments, kuma taga duk magana ce akan me yasa jiya da yau bata saki recipe ba.
“Eh ya kamata kuje, kaga sai ka kaita ta zaga garin namu”
“Yauwwa Daadi zanje na duba ƙanin nan nawa a asibiti”
“To sai kun dawo..... Maryam ki tashi ku je”
Su je ?, ina za su je ?, Bata de ce komai ba sai ta miƙe, mayafinta yafe a kanta.
“Ba dan halinki ba zo muje”
Neha ta miƙe tana faɗin.
“Ai ko baka ce na zo ba zan zo”
Mayafinta ta yafa a kanta, sannan suka fita a tare.
Daadi ta kalle su tana murmushi, a lokacin kawu Irfan ya sauƙo daga sama, fitar su Eshaan ɗin kawai yaga.
“Waɗanan ƙafar yawon ina zasu je ?”
“Zaga gari za su je”
“Maa yaron nan ya sauya sosai”
Ya yi maganar yana zama a gefen ta.
“Ya sauya sosai, gashi har ƙiba ya yi, kuma ya faɗa min abun nasa baya tashi sosai, saide mu godewa Allah”
“Hakane kam”
“Ka yi waya da yayan naka ne?”
Tana nufin Imran, mahaifin Neha, kawu Irfan ya gyaɗa mata kai.
“Eh na faɗa masa, yace ba zai samu zuwa ba, amma Mahima zata zo(Matar Imran ɗin da ya aura bayan rasuwar mahaifiyar su Neha)”
“Ta yi zamanta bama buƙata”
Kawu Irfan ya yi dariya, yasan me yasa tace haka, sam Daadi bata san Mahima, sbd itama bata nunawa Neha da ƙanwarta Gulzar kulawa.
MARYAM POV.
Suna fita daga gidan Taxi suka hau, Eshaan da Neha ne suka ce yawo a ƙafa yafi daɗi.
Wani babban wajen gyaran gashi suka fara zuwa, Eshaan ya shiga b'angaren maza, yayin da Neha da Maryam suka yi b'angaren mata.
Irin gyaran kan da akayiwa Maryam ba kallarsa aka mata a lagos ba, dan na yau yafi kyau, gashinta ya ƙara miƙewa, yayi laushi sai sheƙi yake, kuma Neha ta sa a mata kala a gashin nata, daga ƙasa aka saka mata maroon color.
Yayinda ita Neha ɗin aka saka mata purple color.
Bayan an gama musu sun fito suna 'yar hira, suka iske Eshaan tsaye a reception yana waya, kansa sanye da hular sanyi, wadda a samanta aka rubuta 'ESHAAN'.
“Kiga wai fa duk dan kada muga kalar askin da aka masa, shi yasa ya saka hular”
Neha ta faɗa mata murya can ƙasa, sai suka yi dariya a tare.
“Kun gama ?”
“Eh mun gama muje”
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Wannan babin naki ne Amina Maikudi*
*BABI NA ARBA'IN DA HUƊU (44)*
*No. 45, Janjira St, Mumbai, india*
“Yanzu ina zamu je ne ?”
Cewar Neha lokacin da suka fito daga shagon da aka musu gyaran kai, suna tsaye a bakin titi.
“Muje muci pani puri”
Eshaan ya bata amsa.
“Kai wallahi bhai ka haɗu!, nayi kewarsa dama, to kaga mu ɗan ƙara gaba, akwai wani me siyarwa a can”
Ita de Maryam ba ta saka musu baki, kuma daga haka suka yi gaban. Tun ɗazu Maryam ta ƙi yarda su haɗa ido da Eshaan, dan da ga zarar ta kalli fuskarsa zata tuna cewa jiyafa a tsakiyar hannayensa ta kwana, sai kunya ta lullb'eta har ƙafa.
“Lefi na miki Piya (lover)?”
Jiya cutie!, yau kuma Piya ?, sunaye biyu kenan tsakanin jiya da yau, sai kawai ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da suka tsaya da tafiyar, Dan sun iso wurin, Neha ce ta ƙarasa wajen me pani puri ɗin tana siyo musu.
Tafida yaci gaba da kallonta, daren jiya na ƙara dawo masa cikin tunaninsa, yanda Maryam ta ƙanƙame shi bayan da ya faɗa mata cewar yana santa.
“Kinyi shiru”
“Babu komai”
Saumar hannunsa ta ji a kan kumatun ta, ta yi saurin ɗagowa tana kallon wajen da suke, akwai mutane dan bakin hanya ne wurin, amma kuma kowa harkar gabansa yake, babuma wanda ya ko lura da su.
“Ko kissing ɗinki zan yi a nan babu me ce mana ƙala”
Maryam ta zaro ido tana zame fuskarta daga cikin hannunsa.
“Baki yarda ba na gwada miki ?”
Da sauri ta girgiza masa kai, tana mayar da bakin mayafin da ya sauƙo mata kan kafaɗarta.
“To faɗa min me na yi ake hukunta ni ?, or you are shy of me ?....”
“Ga pani puri”
Muryar Neha ta dakatar da abinda yake san faɗi, shi ya kai hannu ya karb'i ɗan ƙaramin kwanon dake hannun Neha ɗin, yayin da ita Neha ɗin ta ƙara komawa wajen me pani puri ɗin.
“Miriam akwai yaji, zaki ci ?”
Ta kalli abun da ke riƙe a hannunsa, ita fa cikinta ba ya san baƙon abu, yanzu sai ta yi amai, dan haka ta yi saurin girgiza masa kai.
“Good, bana san ki ci yajinsa ya dame ki”
Tana kallo suka ci shi da Neha, har santi suke.
Bayan sun gama da wajen suka wuce gate way of india, suka bawa barayen dake wajen abinci harma sukayi hotuna a wajen. Sun ɗan jima a wurin, Eshaan nawa Maryam bayani a kan tarihin wurin.
Kafin suka wuce marine drive, tekun dake gefen titi, kuma a tsakiyar garin mumbai, nan kuma hotuna kawai su ka yi.
Daga nan suka wuce Victoria terminus railway station, sun yiwa Maryam bayanin tarihin wajen, kafin suka si yi tiket ɗin jirgin ƙasa wanda zai kaisu byculla, dan jj hospital suka nufa.
*
Eshaan ne ya fara shiga bakinsa ɗauke sa sallama, sannan Neha da Maryam suka shiga.
Me martaba, Fulani Sadiya, Maimun sune suka amsa. Fulani Sadiya tabi wanda ya shigo da kallo, zata iya cewa kusan shekararta uku rabon da ta ganshi, dan ba sashenta yake shiga ba, ita kuma ba ko ina take fita ba balle har su haɗu.
Kuma ganin ta da shi na ƙarshe tun sanda Me martaba ya tarasu gaba ɗaya a kan bikin ƴar gidan Chiroma da za'ayi. Kuma duk da ta jima bata ganshi ba tasan ya sauya, ya yi ƙiba, ya ƙara haske.
Shi ɗin da take duk wani ƙoƙarin ganin bayansa, yau shine ya zo yake duba ɗanta da bashi da lafiya, shi ɗin da take so taga ya faɗi ƙasa shine Allah ya ɗaukaka, sannan ɗan nata da take ji da shi shine ya faɗi ƙasan.
Tafida ya gaida Me martaba, Harda Fulanin da bata son haɗa ido da shi, kuma baisan dalili ba, yasan cewa sam matar bata san sa, tun yana ƙarami take nuna masa ƙyama, sannan itace mutum ta farko data fara faɗa masa cewar shi ba mutum bane.
Amma ko daga yanayinta yau yasan cewa ta yi laushi, kuma wata ƙila sbd jinyar ɗan nata ne, ko kuma shi ta yiwa abun ya dawo kan ɗanta, dan yasani, kuma yana gani a mafarkinsa, duk sanda zata masa wani asirin.
Wannan karon ne Allah be sa ya gani ba, wani abu da ya ƙara bashi mamaki shine gaida shi da Maimun ta yi, yarinyar da ko ganin inuwarsa bata san yi.
Ya amsa yana kallon Galadima dake kwance a kan gado.
Sai a lokacin su Maryam suka gaidasu baki ɗaya, Me Martaba yana ta kallonta, dan shi bai tab'a ganinta ba ma, yau ya fara ganinta, sannan Fulani Khadija ta faɗa masa yanda Tafida yace mata jikinsa ya yi sauƙi.
Kuma shima yaga hakan da idonsa, dan ba ƙaramin sauyawa ya yi ba. Fulani sadiya ta shiga kallon ƴan matan biyu, ta gane ɗayar de, dan ta tab'a zuwa haɗejia, kuma tana kama da Tafidan, kenan ɗayarce matar Tafidan.
Tafida ya ɗauki file ɗin Habibu yana dubawa, sannan yace da Me martaba.
“Ranka ya daɗe ai babu abinda aka rubuta a nan, bayanai sun nuna cewa babu abinda ke damunsa”
Me martaba ya gyaɗa kansa.
“Haka suka ce”.
“Amma ina da shawara, sam wannan jinyar tasa bata kama da ta asibiti, kamar aikin aisiri haka ko jinni”
Ƙulululu!, cikin Fulani Sadiya ya yi, ta haɗiye wani abu da bata san sunansa ba, kuma dama Tafida da biyu ya faɗi hakan, dan yaga reaction ɗinta.
“Nima haka nake zato”
Cewar Maimun tana kallon ɗan uwan nata cike da tausayawa.
“To bari likitocin su zo, sai muyi magana da su”
cewar Me Martaba.
Su Tafida sun ɗan jima a asibitin, kafin suka yi sallama a kan Tafidan zai dawo gobe. Daga nan kuma shopping suka wuce, inda suka yi da Arjit kan zazu haɗu a can.
“Wannan ya yi bhai?”
Cewar Neha tana gwada wata sarƙar ƙafa, ya girgiza mata kai.
“Ko kaɗan ki sauya”
“Ok to...... sauya min”
Ta ƙarashe tana miƙawa me sarƙar wadda ta gwada ɗin, tun da har yace ba ta yi ba to ba ta yin ba, tun suna yara shine yake zab'a mata sarƙar ƙafa.
“Kefa Miriam ba kyasan sarƙar ƙafa ?”
Maryam ta ɗago daga danna wayarta da take ta kalli Eshaan dake maganar.
“Na zab'o miki ?”
Ta gyaɗa masa kai. Shi da kansa ya zab'o mata, sanna yace ta gwada, gwadawar ta yi kuma ta karb'i ƙafar tata.
“Wow sirikita amma fa ta miki kyau, kina ji ?, ki riƙa saka sarƙar ƙafa da waist beads bhai yana sonsu”
Maryam ta juyo ta kalleshi, shi ba su yake kallo ba, dan waya ce kare a kunnensa yana magana da wani Arjit.
Suna tsaye a wajen Arjit ɗin da ake waya da shi ya zo, inda ya gabatar mata da shi a matsayin abokinsa. Arjit ɗin baya jin hausa, sai da turanci suka gaisa, wannan turancin nasu dake bawa Maryam dariya, dan ascent ɗin akwai ban dariya.
Sai da suka yi siyyayar kayan sakawa sosai sannan suka bar mall ɗin, ko da wasa Maryam taƙi ta ɗauki saree, hatta da lehenga ma ƙin ɗauka ta yi, chickankari ɗin da take gani shine dai-dai ita su ta ƙara ɗauka.
UCHENNA POV.
Wayarsa ce ta yi ringing hakan yasa ya dakata da kaiwa abincin da ya ɗebo bakinsa, ya kalli screen ɗin wayar 'JUDE'.
Ya ɗanyi murmushi, dan sun kwana biyu ba su yi waya ba, dan yanzu makaranta Jude ɗin ke zuwa, ya ansa wayar da faɗin.
“Ɗan makaranta!, to ya school ɗin ?”
“Lafiya, Baba ne yake san ganin ka”.
Second ɗaya.....biyu......uku.
*
*Unguwar Rafin Cinnaka*
*Da 03:00pm*
Uchenna ne zaune a kan kujera, yayin da yake facing mutumin dake kwance a kan gado. Mutumin da ya shafe kwanakin rayuwarsa yana tsine masa, mutumin da ya koreshi daga gidansa yace ba ya buƙatarsa, wanan mutumin da ya ce ba zai tab'ayin albarka a rayuwarsa ba, kuma de shine wannan mutumin da tsawon shekaru goma da be yi a gidansa ba be nemeshi ba. Yau shine ya saka a nemo shi, ya sa a kirashi.
“Ya jikin naka ?”
Aja Johnson ya yi murmushi cikin raɗaɗin ciwo.
“Jiki babu daɗi Uchenna, ina shan wahala sosai, na saka Jude ya kiramin kai ne dan na nemi yafiyarka, ina so ka yafemin Uche, ban sani ba ko bazan ta shi ba, ka kuma roƙa min Rashidat da ta yafe min”
Uchenna ya rintse idonsa yana kawar da kansa gefe, yana jin wani abu me kama da allura na tsikarar zuciyarsa, yaji zuciyar tasa tana ɗaukar ɗumi, kamar da ake gasata a cikin oven. Bayan tsawon shekaru, Aja ya dawo yana neman yafiyarsu.
“Na yafe maka, kuma dama ni baka tab'a min komai ba, nide kawai ina so ka musulunta ne”
Aja ya kuma yin murmushi.
“Kada ka damu da wannan, tun wata huɗu da suka wuce na musulunta, wannan karon ba dan Rashidat ko dan soyyayarta ba, ba dan kai ko ƴan uwanka ba, tuba na yi tsakanin da ubangiji, sakamakon nasihar da Jude ke min a kullum ”
Ƙwalla ta zubo daga idon Uche, ya sha jiran irin wannan ranar, ya sha mafarkin ranar, ranar da mahaifinsu zai musulunta, ranar da zai ce su yafe masa.
Miƙewa ya yi ya ƙarasa kan gadon kusa da shi ya zauna, kuma bai jira komai ba ya rungume shi, ya saki kukan da ya jima be yi irinsa ba, hasali ma shi rabonsa da ya yi kuka tun rabar da Ajan ya kore shi daga gidan, sai a mutuwar Abba.
Jude ne shima ya ƙaraso ya kwanta a bayansu yana sakin nasa kukan.
Aja ya yi murmushi yana shafa kan ƴaƴan nasa gaba ɗaya.
“Allah ya muku Albarka“
Hausawa sunce komai ya yi farko yana da ƙarshe, a sanda za'a b'ata maka za ace ka yi haƙurui, sai dai a lokacin gani za ka yi kamar an cuce ne, amma kuma ai ance haƙuri me tadda rabo, idan aka haƙura za'a dace.
Uchenna ya ja hanci, wannan bakin da a kullum cikin tsine masa ya ke, yau shine ke saka masa albarka, yau Aja ne yace Allah ya masa albarka.
“Ameen”
*Survey NO 1433 Shiv Mandir Talo St, Chikoli Mumbai, India*
*08:40*
MARYAM POV.
Fitowa ta yi daga banɗaki, bayan da ta saka farin chickankari ɗin da suka siyo ji ya, daga wandon har rigar duka farare ne, rigar ta kai guwarta, wandon kuma yanada faɗi.
Eshaan da kansa ke sanye da wannan hular sanyin tun jiya ya juyo yana kallonta, ita ta rasa me yasa yake saka wannan hular, kuma tun jiya bai cireta ba, da itama ya kwana.
Yau tun safe suka tashi da kai kawon mutane a gidan, da ta tambayi Neha sai tace mata ƴan uwansu ne, sun zo su yi bikin Holi ne tare.
Kuma tun jiya daddare akewa gidan decoration, kuma taga kowa sai farin kaya yake sakawa, dan kuwa harda Eshaan shima farin kayan ya saka. Kamar yanda yake kallon nata itama shi take kallo.
Riga da wandon kurta ne a jikinsa, rigar ta kawo masa guwa, daga gefe da gefen rigar akwai tsaga. Kayan sun amsheshi sosai, sai ya fito mata a matsayin Eshaan ɗinsa.
A hankali ƙafafun Maryam suka ci gaba da takowa zuwa cikin ɗakin, yayin da idon Eshaan ɗin ke kanta. Dressing mirror ta ƙarasa sannan ta zauna a kan stool ɗin, kuma shi har yanzu yana kallonta.
“Wai me yasa baka cire hular nan ba”
Ta tambaya a sanda take ɗaure sumarta me laushi da ribbon.
Memakon ya amsa mata sai ya tako inda take, yana motsa kunnensa, ya dafa kafaɗarta a sanda ya ƙarasa kusa da ita, sai kuma ya ɗauke hannun nasa daga kafaɗarta ta, ya cire ribbon din da ta saka, ya kama ƙarshen gashin nata ya mata braid (kalaba) guda ɗaya.
Sannan ya saka mata ribbon a ƙarshen gashin, ya ɗaga hannunsa na dama sama, ya dunƙule sannan ya buɗe, wasu ƙanan stars masu sheƙi suka bayyana, ya shiga jera mata su a gaban gashin nata. Style ɗin ya yiwa Maryam kyau sosai, kuma duk abinda yake ta cikin mirror take ganinsa.
Yasan ba kwalliya take ba shi yasa ya ɗauki gyalenta dake kan kafaɗarta ya ɗora mata a kanta.
Da hannu ya mata alama da ta yi kyau, Maryam ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Sannan ta miƙe tsaye ta juyo tana kallonsa.
“Naga wata da wuri zata tsufa”
Sai kawai ta yi dariya, dan tasan me ya gani, wannan silin farin gashin na kanta ya gani.
“Kuma dan mutum yana da furfura sai akace zai tsufa da wuri?”
Ya kai hannunsa ya tallafo fuskarta yana kallon cikin idanuwanta.
“Kinyi kyau Cutie, kamar kullum”
Yanzunma murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta, sai kuma ta ɗago da kanta ta dube shi, da alama bazai cire hular kansa ba, sai kawai ta yi tattage, kamar me san kissing ɗinsa ta kai hannunta ta fisge hular sanyin nasa.
Sannan taja baya tana dariya, a lokaci guda tana kallon kan nasa. Eshaan ya kai hannu ya shafa kansa yan murmushi.
Askin da ya saba yi shi aka masa, wato high fade ga kuma razor part daga gefe, da aka aske masa gashin sai ta ga ya sauya, yanayin kyan fuskar tasa ya ƙara fitowa, kammaninsa suka ƙara bayyan.
Sai kuma kunnuwansa da suka ƙara fitowa, dan an aske gashin dake musu rumfa. Bisa ga dukkan alamu su yake b'oyewa.
“Baki ga yanda na koma ba, bani hular pls”
Maryam na ja da baya tana girgiza masa kai a lokaci guda tana masa dariya.
Shima bin nata yake amma taƙi ta tsaya, bata ankara ba ta ji an rabata da ƙasa, an ɗagata sama duka, ta shiga yawo a iska, tana dariya ta kalli Eshaan da ya ɗaga hannayensa a setinta, alamun de shine ya ɗagata.
Kafin kuma a hankali ya sauƙeta ƙasa, kusa da shi, kuma be jira komai ba, ya kai hannunsa na dama ya riƙo waist ɗinta, ɗayan kuma ya tallafo fuskar ta, kafin ya aika Maryam duniyar da ya saba turata a duk sanda zai yi kissing ɗinta.
Ba shiri Maryam ta damƙe hular dake hannunta, yanda ya motsa harahensa cikin bakinta ne yasa ta saki hular, itama bata san sanda ta ɗago hannayenta duka biyu ba, ta ratayasu a wuyansa.
Tana jin kamar komai ya tsaya a duniyar, kamar babu kowa sai su, su biyu kawai, daga ita sai shi.
Ƙwan,ƙwan,ƙwan!.
________________
_Aja Johnson de ya saduda, ya kuma nemi yafiyar Uche da Jude, To!, bari mu ci gaba da zuba ido, dan ganin yanda zata kaya_
🌸SAI KASKA CE✍🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Na sadaukar da wannan babin gareki; Maman Nana*
*BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI (45)*
*11:30am*
“Sirikata ga laddu”
Cewar Neha, yayin da suke tsaye a garden ɗin gidan, kuma ba su kaɗai ba ne a wajen, kowa na gidan dama baƙin da suka zo suna garden ɗin.
Daadi dama sauran mutanen sai gabatar da ita suke a wurin baƙin, duk wanda ya zo sai an nuna masa matar Eshaan.
A hankali Maryam ta gyaɗa mata kai, sannan ta kai hannu ta ɗauka.
“Ki ƙara mana”
Ta kai hanni zata ƙara Daadi ta ƙwalawa Neha kira, Neha ta amsa tare da damƙawa maryam kwalin laddu ɗin, sannan ta tafi.
Maryam ta zauna a kan wata kujera tana kallon yanda suke ta nishaɗi, suna guje-guje, ga kalolin da suke watsawa junansu.
A hankali ta ƙara kai dunƙulen laddu guda ɗaya bakinta, kalmar kala data ayyana na ƙara maimaita kanta, a cikin ƙwaƙwalwarta.
_ “Kada ki yarda ki saka shafa kala da yawa a fuskarki, idan ya kama fuskar mutum baya fita da daɗin rai”_
Ɗazun bayan an ƙwanƙwasa ƙofar nan, a hankali Eshaan ya janye bakinsa daga cikin nata, ama kuma fuskarsa haɗe take da tata, suna sauƙe numfashi a tare, yana kalon idanuwanta dake a lumshe.
A hankali Maryam ta shiga ƙoƙarin janye hannunta daga bayan wuyansa, amma sai ya kai hannayensa ya riƙe nata, hakan yasa ta buɗe idonta itama.
A lokacin ya faɗamata waɗanan kalaman, ƙofar aka ƙara ƙwaƙwasawa, hakan yasa ya yi pecking kanta, sannan ya juya dan ya buɗe ƙofar, yayin da ita kuma ta yi saurin juyawa. Neha ce ta shigo a taime ɗin, shine suka fito tare.
Murmushi ta yi tana saka wani laddu ɗin a bakinta. Kamar daga sama ta ji muryarsa suna magana da Neha.
“Bhai wallahi Holi ɗinma ni lami nake jinsa, babu kiɗa babu komai”
“Na sani choti (ƙanwata), amma bari kiga”
Ya ƙarashe yana saka hannyensa a baki ya saki fito me ƙarfi, nan take wasu masu kiɗa suka shigo garden ɗin. Neha ta ɗagawa Eshaan hannu shima ya ɗago mata suka tafa.
“Ku sakar mana ganguna!!”
Masu kiɗan suka fara, kowa ya fara rawa, Maryam ta yi dariya tana kallonsu daga inda take.
Allah ɗaya gari banban, da ace a nigeria ne da yanzu ana ta maganganu, amma kalli yandasu suke rawa abunsu, har da Daadi, a cikinsu ta hangi shi Eshaan, shi ma yana taka tasa rawar.
Ta tintsire da dariya tana ci gaba da cin laddu ɗin, hannu ta kai zata ƙara ɗaukar wani ta ji wayam!, a cikin kwalin, hakan yasa ta kalli kwalin, babu ko ɗaya, ta cinye duka.
Ta rufe ƙaramin kwalin tana murmushi, sannan ta ɗago tana kallon inda su Eshaan suke, sai dai kuma babu shi a ciki, sune kawai.
Tasan kurɗakurɗarsa, yanzu haka wani wajen ya yi, sai kawai ta goge hannunta da tissue ɗin da taga a kan table ɗin gabanta, sannan ta ɗauki wayarta ta shiga tiktok.
Yau ta rantse kan sai ta yi posting hoton da suka yi jiya, in yaso matan da suke yawan damunta a comment section kan mijinta, yau su ganshi, kuma ta musu ƙwalele.
Bim!, saƙo ya faɗo wayarta, Daga lambar Sundar, dan haka ta buɗe tana murmushi.
_'Ki fito waje'_
Abun ya ɗaure mata kai, waje ?.
_'Waje ina ?'_
Ta tambaya.
_'Ƙofar gate'_
Sai kawai ta miƙe tana gyara zaman gyalen kanta, sannan ta fita daga garden d'in.
A kusa da babban gate d'in gidan ta hange shi, babu kowa a wajen, dan hatta da masu gadi ma suna cikin garden.
Shima yana hangonta sai ya gyara tsayuwa, sannan ya buɗe hannunsa d'aya, yana mata alama da ta taho, sai kawai ta yi dariya tana ƙara duba farfajiyar wajen, kamar me neman wani abu.
Sai da ta kusa ƙarsa kusa da shi, sannan ta taka da ɗan gudunta ta isa gabansa, ta kuma kama hannunsa da ya mika mata, kanta a ƙasa tanaa murmushi.
“Muje ko?”
Ta ɗan ɗago ta kalleshi, idanunta na haskawa da mamaki.
“Ina zamu je”
“Unguwa”
Ya ƙarashe yana jan hannunta, bata ƙara cewa komai ba, haka suka fita daga gidan.
A ƙafa suke takawa, wani layi suke bi wanda yake a makekeyar unguwar, kuma unguwar tsit! take babu wata hayaniya, saide kana ɗan jiyo hayaniyar mutane a cikin gidajensu.
Sun yi 'yar doguwar tafiya, kafain suka shiga wani layi.
A ƙofar wani madaidaicin gida taga sun tsaya, akwai securities biyu a ƙofar gidan, kuma bisa ga dukkan alamu sune masu gadin gidan, dan saida suka sara masa sannan suka buɗe musu gate ɗin gidan.
A sanda gate ɗin gidan ya buɗe a gaban Eshaan, sai wajen ya shiga juyawa a idonsa, hoton ya sauya i zuwa wani lokaci can baya, sanda yana ƙarami, lokacin ya dawo daga makaranta ne, bayan school bus ta sauƙe shi.
Ya fito daga cikin motar da gudu, yayin da Roshni ke tsaye a kan balcony ɗin shiga cikin gidan, sanye take cikin chickankari, gashin kanta kwance a bayanta.
Ta yi dariya a sanda ya kira sunanta, sai itama ta taho da gudun tana su kuyawa dai-dai setinsa, yana zuwa kusa da ita ta ɗauke shi tare da cilla shi sama.
_ “Yeeeeee!, Eshaan”_
_ “I love you Maa”_
_“ I love you tooooo Eshaan”_
Yaci gaba da jin sautin dariyarta a cikin kunnuwansa, a dai-dai lokacin da suka ƙaraso ƙofar shiga cikin falon, shi ne ya tura ƙofar sannan suka shiga.
Komai na cikin gidan irin na da ne, bisa ga dukkan alamu ba'a sauya komai ba, komai yana nan yanda yake, sede a na kula da gidan sosai, kamar akwai mutane a ciki.
“Ina ne nan ?”
“Gidan mu ne, a nan na fara yarinta ta, a nan aka haifeni, ko wani memories ɗina yana nan gidan”
Maryam ta ci gaba da kallon wurin, kafin idonta ya sauƙa a kan wani bango dake cike da hotuna, kuma mafiya yawan hotunan nasa ne.
Eshaan ya ƙarasa jikin bangon da hotunan suke, sannan ya shiga nuna mata hotunansa yana bata labarin sanda aka ɗauke su, wasu kuma ma baisan sanda aka ɗauke su ba, dan yana ƙarami sosai. A cikin hotunan akwai na iyayensa ranar da aka ɗaura musu aure.
Bayan ya gama bata labarin sai ya dawo inda take tsaye, yana kallonta, Maryam bata ankara da sanda ya ɗago hannunsa ba, sai jin sauƙar tafukan hannunsa ta yi a kan kumatun ta, yana shafa mata kala, a hankali ta lunshe idonta, sannan ta buɗe a kansa.
“Happy Holi Piya!”
Ya faɗi a sanda yake shafa mata a ɗayan kumatun nata, sannan ya sauƙe hannunsa yana sunkuya setinta, a hankali ya juyar da fuskar tata bayan ya riƙo hab'arta, sannan ya kai tasa fuskar ya gogi kalar dake fuskarta ta.
Haka ya yi a ɗayan ban garen ma, kafin ya haɗa goshinsa da nata yana lumshe idonsa.
“I love you”
Ya furta maganar haɗi da sauƙe numfashi, wannan yanayin da Maryam ta saba shiga ya ƙara dawo mata, kafin ta yi ƙarfin halin kai hannunta ta riƙe gaban rigarsa, sannan itama ta furta.
“I love you too...”
Kuma tun kafin ta gama faɗi, ya haɗe bakinsa da nata, sannan a hankali ya shiga kissing ɗinta.
HANAM POV.
“Cut!...”
Muryar director ta karaɗe wajen. Kuma bayan bada umarnin nasa masu ɗaukar sauti da masu ɗaukar hoto da kuma masu haska fitulu suka dakata.
Uchenna dake tsaye a tsakiyar fituluvda kuma gaban cameras ya bar wajen, ya tafi zuwa wurin Hanam dake zaune a can gefe kan wasu kujeru. Har ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita ta na kallonsa.
Bottle watter ta miƙa masa, ya karb'a yana mata godiya.
“Aikin da wahala ne?”
“Akwai mana, sai anyi ace be yi ba a sake, gaba ɗaya na gaji”
Sai ta kai hannunta ta ɗan bubbuga kafaɗarsa.
“Idan ka yi haƙuri zaka ga sakamokansa a gaba, yanzu yanda audio ɗin tayi treding ai vedion sai ta fita trending”
Ya aje bottle ɗin yana gyaɗa mata kai, sannan ya kamo hannunta na dama ya yi kissing.
“Inde kina tare da ni babu wani abun da zai tsorata ni, zan dage na yi duk yanda zan yi ganin na yi abinda ya dace”
*Nisa premier hospotal, abuja*
“Mu shiga”
Cewar Uchenna yana duban Hanam da ta tsaya ta a ƙofar ɗakin, ta ɗago ta kalle shi, sannan ta tura ƙofar suka shiga.
Tun jiya ya faɗa mata cewa an kwantar da mahaifinsa a asibiti, ita kuma tace tana so ta zo ta duba shi.
Iko sai Allah, shine abin da ta faɗi, a sanda ta ɗora idonta kan mutumin dake kwance a kan gadon mara lafiya, badan furfurar dake fuskarsa da kuma tsufan da ya yi ba, babu abinda zai hana tace wannan Uchenna ne, babu wani banbanci a kammaninsu, baƙar fatarsa da tsayinsa da komai irin na mahaifinsa ne.
Daga gefen gadon kuma wani matashi ne da ta riga da ta sanshi, dan yana yawan bata labarin sa, Jude ne.
Zama ta yi a kan kujerar da Jude ɗin ya bata, a lokaci guda kuma yana gaisheta, ta amsa masa sannan ta gaida Baban Uchenna, ya amsa mata yana murmushin ƙarfin hali.
“Uche wannan itace matar taka”
“Eh Baba, itace ”
“To Allah ya muku albarka”
“Ameen”.
*Mumbai, India"
*08:00pm*
“To Daadi, sai bayan saduwa”
Cewar Maryam hannunta cikin na Daadi, yayin da suke tsaye a harabar gidan, me motar da zai sauƙesu a railway na jiransu, dan daga mumbai Eshaan ya faɗa mata cewa Ahmedabad(Amdavad) zasu wuce.
Daadi ta janyo Maryam ta rungume ta, sannan ta saketa tana shafa kanta dake sanye da gyalen chickankari ɗin jikinta.
“Allah ya miki albarka jikata”
Maryam ta yi murmushi, sannan ta juya kan Neha, itama ta rungumeta sunawa juna sallama, daga ita sai Anti Saffah, sai kuma Atif, Kawu Irfan ma ya saka mata albarka.
Mota ta shiga tana jin wani abu me kama da kewar mutanen da bata fi sati da su ba na kamata, suna da kirki sosai, basu duba tazarar dake tsakaninta da su ba, santa kawai suke sbd Allah da annabi.
Tana kallon yanda Eshaan ma ke sallama da su, kafin shi ma ya shigo cikin motar, har motarsu ta fita daga gidan su Daadi na ɗaga musu hannu.
Victoria Terminus Rail way suka nufa, dan a nan Eshaan yasai musu ticket, bayan tafiyar 'ƴan wasu awwani suka sauƙa a garin Ahmedabad wato Amdavad.
Amdabad ba wani babban gari bane, amma kuma garin a cike yake da mutane daga garuruwa da ban-da ban, kuma kamar yanda Tafida ya faɗa mata ne, sbd gasar world cup ɗin da za'ayi ne.
*Acasa mia, New cairo north house, 90 suez Rd, Cairo, Egypt*
A madaidaicin garden d'in gidan, wani ɗan ƙaramin yaro ne a kan encounter vehicle, yayin da ɗayan yaron ke turo shi ta baya, ƙaramin yaron yana sanye cikin farar hooded knitted jacket da ash jeans trouser.
“Khalil ta'al ila hina, al akli sar jahiz”
(Khalil kazo nan, abinci ya kammala).
Kyakyawar balarabiyar matar da ta fito daga cikin gidan ta faɗi, babban yaron ya waigo ya kalleta, sannan ya juya kan yaron dake kan car toy ɗin, ya kama hannunsa sannan ya sauƙeshi daga kan car ɗin.
Yaron ya shiga taku cikin tafiyarsa da bata gama nuna ba, haka ya ja shi har cikin kyakyawan falon gidan.
Kuma suna shiga babban wansu ya yi caraf ya ɗauke ƙaramin yaron yana juya shi sama. Yaron ya shiga dariya cikin gwalantunsa yace.
“Allamil”(Al-amin)
Al'amin ɗin ya haɗe rai.
“Ba Allamil ba, Baabaa zaka ce”
Cikin harshen larabci ya masa maganar, kuma kullum haka suke yi, shi yaron ba zai dene ce masa Allamil ba, shi kuma kullum yana cikin ce masa sede yace Baabaa, wata Baba.
Wani magidanci ne ya fito daga wata ƙofa yana dariya, ƙarasawa kusa da su ya yi ya karb'i yaron a hannun Al-amin yana masa wasa.
“Baabaa, Baabaaba!”
Magidancin ya ƙyalƙyale da dariya.
“Ka ji batu na Gaskiya, yaro nine Baabaan Aryaan ba kai ba, sai ka ɗau haƙuri”
Al-amin ya b'ata rai, wai shi a dole an b'ata masa.
“Wai zaku zo kuci abincin ne kokuwa ?”
Wannan matar ta ɗazu ta ƙara tambaya, a sanda ta fito daga wata ƙofa, wadda taksance ta kitchen.
“Yaro gwara muje muci abincin nan, kafin Ammin ku ta kawo duka”
Gaba ɗayan su suka dariya. Wata matashiyar yarinya ta taso dafa kan sofa tana fad'in.
“Aryaa?, Abuya kawo shi”
Abuya ya miƙa mata Aryaan din, sannan ya yi hanyar danning, gaba ɗaya kowa yazo ya zauna, Ammi ta zuba musu abincin da ta girka, suna ci suna hira yayinda Salwa da kanta take bawa Aryaan din.
__________________
_Kai to Mashaallah, Aryaan na morewa a Cairo, wa zai biyo ni mu tafi??_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Na sadaukar da wannan babin ga Aisha Haruna Salisu*
*BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS (46)*
*Abuja..*
HANAM POV.
“Kinga gaskiya wannan yayi duhu, dan wallahi mu baƙaƙe ba zai mana kyau ba”
Hafsi ƙanwar Kamal, wadda take yaya a wajen Hanam ta faɗa, suna zaune ne ita da Hanam, Na'ima, Zainab, Ummu kulsum, Mariya, Rahina, Firdaus, Hafsin kanta, Rafi'a, Nabila, Kamila, fatima da Aisha a babban falon gidansu, yayin da suke zab'ar kalar lace d'in da zasu saka ranar bikin Kamal dan shirye-shiryen bikin suke.
“Anti Hanam wallahi gaskiya yaya ta faɗa, duk gidan nan babu wanda blue color kewa kyau sai ke, tunda kinga mu gaba ɗayan mu baƙaƙe ne”
Cewar Nabila, Hanam ta tura hoton gaba, wani ya shigo a cikin ipad ɗin.
“Wannan fa ?”
Ta tambaya tana nuna musu.
“Yauwwa, ai gwara farin, shine zai hau da kalar jikin mu”
“Kema de Nabila da wani abu kike, yanda kike ta magana a kan baƙin fatar nan taku sai kace wani shuni”
Gaba ɗayansu suka saka dariya.
“Ai maganar gaskiya ce, kaf gidan nan waye me hasken fata ban da ke ?, sai wannan yarinyar da ta shiga shago ta siyo”
Rafi'a ta faɗi tana ɗakawa Mariya duka.
“Rafi'a bana san iskanci, ni na hana wata cikinku shiga shago ?, kuma idan kuna san farin ku shiga mana”
“Allah stirbiƙui inji kishiyar me doro, Allah tsare mu da shafa mai, ke baki san baƙin fatar mutum yafi kyau ba ?, me ake da wani mai”
Rafi'a ta bata amsa.
“Anti Hanam wai ina Aryaan ne ?”
Aisha ta tambaya, Hanam ta yi murmushi.
“Arya yana Cairo, jibi ma zanje na ɗauko shi, dan bana so a yi bikin nan baya nan”
“Ai kuwa gwara ya zo mu ganshi ”
Wayar Hanam ɗin ce ta yi ringing dan haka ta kai hannu ta ɗauka 'Benidita'.
Har da saurinta ta miƙe ta bar falon sbd hayaniyar da suke, a ƙofar shiga falon ta tsaya, sannan ta ɗaga wayar.
“Ya ya mijin ki?”
Benedita ta tambaya a sanda suke gaisawa, Hanam ta yi murmushi tunowa da shi da ta yi, shine da kansa ya kawota gida, sannan yace mata zai je ya karb'o musu visa ɗinsu.
“Yana lafiya”
“Kira na yi na sanar miki dama, kinsan Gebriel ya mutu....”
Duk da akwai hasken rana a wajen, Amma sai da Hanam taga kamar wata walkiya ce ta haskota daga sama, bakinta a sake kuma yana rawa ta furta.
“A garin ya ya ?”
“Guba suka sha shi da matarsa, wai dan sbd sun haihuwa, yanzu fa shine labarin dake tayawo a new york baki ɗaya”
Hanam ta damƙe ƙarfen balcony, dan ƙoƙarin faɗuwa da take, ba wai tausayinsa take ba, ba kuma haushi ta ji dan ya mutu ba, kawai de zafin rasa rai ne ya dake ta, haka kuma koda ta ruɗi kanta cewa shi ba baban Arya bane ta sani cewa shi ɗin ne baban nasa, amma, ba musulmi banr, bata san wata kalar addu'a zata masa ba. Sai kawai ta kashe wayar, dan wata ƙila hakan ne mafita.
*RNo.202,Taj Skyline Hotel, Ahmedabad, India*
*09:30am*
ESHAAN POV.
Zaune yake a kan wata sofa, hannunsa riƙe da littafin Aakhoki Gustakhi, wanda Saree ya rubuta, littafin yake karantawa, yayin da yake jiran fitowar Maryam da ga banɗaki, so yake ta yi sauro ta fito su tafi, dan yau za'ayi final, kuma wasa ne tsakanin India da Australia.
Sannan yana sa ran a gobe zasu wuce Delhi, dan jibi ne ɗaurin auren Mahesh abokinsu.
Tunaninsa ya katse tare da karatun da yake, a sanda Maryam ta fito daga banɗakin sanye cikin chickankari, rigar orange color ce, kuma ta sauƙo mata har kan guwa, yayinda wandon ya kasance fari, kuma wandon yana da faɗi, ta yafa farin mayafin kayan a kanta, ta rataya shi zuwa bayan kafaɗarta.
Ƙafarta sanye cikin fararen boots, kamar kullum fuskarta babu kwalliya, amma shi a hakan da take tafi masa kyau, dan yafi san ya ganta a yanda take, haka ɗin nan nata, dan hausawa sunce wai dai-dai ɗin wani, karkattaccen wani. Litafin ya rufe tare da aje shi a kan coffe table, ya miƙe yana shafa sumarsa.
“Kin shirya?”
A hankali ta gyaɗa masa kai.
*Narendra Modi stadium, Ahmedabad, India*
*12:00pm*
Hayaniyar masoya da kuma magoya bayace ke tashi, sai kuma masu bayyana yanda wasan ke kasancewa, gaba ɗaya stadium din cike take maƙil da mutane, daga tsakiyar fili kuma ƴan wasan india da na australia ne ke fafatawa, dan yanzu haka ana zagayen ƙarashe ne.
Daga cikin kujerun ƴan kallo, akwai ta Eshaan da Maryam, wanɗan da suka zuba ido suna so suga yanda wasan zai kaya, a farkon fara zuwansu wajen babu abunda Maryam take ganewa a wasan.
Amma a hankali a hankali ta fahimci kan wasan, kuma kamar Eshaan itama tana fatan ace india ce ta lashe wasan, dan yanda ta ga indiyawa nasan wasan cricket idan suka fad'i wata ƙila Ahmadabad ta kama da wuta.
Wajen ya yi wani irin shiruu, kamar mutuwa ta ratsa, kamar da ba wajen ne ake ta hayaniya ba, sun yi shirun ne saka makon Rohit Sharma babban ɗan wasa india, da ya riƙe bat a hannunsa ya ɗau matsayarsa yana jiran Jones ɗan wasan austrelia ya cillo ƙwallo.
Jones ya ɗan ja da baya kaɗan, kafin ya tako a guje, kuma yana zuwa tsakiyar filin ya cilla ƙwallon, wani irin duka da Roshi Sharma yayiwa ƙwallon saida ta fita daga ginin stadium ɗin.
Kamar magoya bayan india jura suke, sai suka saka ihu, ana tafi ana fito, india taci wasa, bakin Eshaan kamar ya rabe biyu dan tsabar murna, Maryam ma ta taya su murna sosai. Da a wajen su abun farin ciki ne sosai, dan indiawa na martaba wasan cricket.
*Cairo Internacional airport*
*05:40pm*
HARNAM(Harees and Hanma) POV.
A tare suka fito daga cikin terminal, yayin da Haris ke riƙe da jakukunansu, gaba ɗaya hanam ta ƙagu taje taga Arya, so take taga yanda ya sauya, dan tana da tabbacin ya sauya sosai.
Haris ne ya tsare muasu taxi, sannan suka shiga, kai tsaye Acasa Mia suka nufa.
Ta ta haddace address ɗin gidan, dan haka taxi na sauke su ita ta fara shiga gidan.
“Aryaan?!”
Shine abinda ta fara faɗi, a sanda idanuwanta suka gane mata shi suna wasa shi da Al-amin,Salwa da Khalil a garden ɗin gaban gidan.
Da gudu ta yi inda suke ta sure shi tana rungume shi, kafin ta dago shi daga jikinta tana kissing face ɗinsa, ta yi kewarsa sosai, fiye da yanda baki zai iya furtawa.
Jikinsa tabi da kallo tana ganin yanda ya sauya, bakinsa taf cike da haƙwara, girma ya ƙara bayyana a tare da shi.
“Arya Ammi ta yi kewarka”
“Ammi ?”
Cikin gwarancinsa ya furta hakan, Hanam ta yi dariya tana sake rungume shi.
“Eh Ammi, Amminka ta yi kewarka”
“Papi ma ya yi kewarka”
Ta juya ta kalli Uchenna dake bayansu, hannu ya kai ya karb'i Arya daga hannunta yana rungume shi shima, sai a sannan ta dawo kan ƴan ƙanenta data ga a wajen, ɗaya bayan ɗaya tabi ta rungume su suna gaisawa da ita.
*09:30pm*
“Bani ɗayan”
Muryar Masarrat ta faɗi, a sanda suke tsaye a kitchen ita da Hanam. Hanam ta ɗauko plate cike da cabbege ta miƙa mata.
Saida Masarrata ta juye cabbege ɗin, sannan ta rufe pot ɗin, ta jiyo ta kalli Hanma.
“Ana biddi ahki ma'ak bi maudu'u daruri”
(Ina so nayi magana da ke akan wani abu me muhimanci).
Hanam bata ce komai ba sai ci gaha da kallonta da ta yi alamu ina ji.
“Waye mahifin Arya ?, dan inada tabbacin cewa Harees ba shine mahaifinsa ba”
Bisa ga manakinta sai taga Hanam ɗin na murmushi. Dama sai da ta ayyana hakan a ranta, tasan cewa dole zata tambaya.
Sai kawai ta ɗago da hannayenta ta sunkiyar da kanta tana kallonsu, yayin da ta haɗesu waje guda tana wasa da su.
“A sanda naje New york wani aiki, na haɗu da wani, kuma shine yayimin fyaɗe, har na samu cikin Arya”
Kalaman basu da yawa, amma kuma sun yiwa Masarrat nauyi a ka, gani take kamar ko wani ƙunci da ya faru a rayuwar Hanam itace sila, kamar duk wata damuwa da Hanam ɗin ta shiga duk ita ta ja. Nan da nan ta fara hawaye, Hanam ta ƙarasa kusa da ita sannan ta rungumeta tana shafa bayanta.
“A'a Ammi, ba kuka za ki yi ba, komai ya wuce yanzu, dan Allah ki dena saka damuwa a ranki”
Kafin ta saketa, Masarrat ta kai hannu ta share hawayenta, sannan ta dafa kafaɗar ta.
“Allah ya miki albarka, muje muci abinci, zuwa gobe zaki zaga dangi”
Hanam na murmushi ta ɗauki wani bowl ta fita, a falo ta same su duka suna hira.
“Yauwwa abinci yakammala, wallahi yunwa muke ji, ya yi kyau yarinyata, Allah ya miki Albarka ”
Dr. Taiyyab Abu Al-aminya faɗi, Hanam ta yi dariya, dan mutumin yana da kirki, kamar Abbanta, Abbanta ?, a ranta ta yi masa addu'a kamar yanda ta saba a duk sanda zai shigo cikin tunaninta.
A hankali ta juya ta kallesu su duka, Abuya kamar yanda ta ji su Al-amin na faɗa masa, Harees, Arya, Al-amin, Salwa da Khalil dukan ninsu suna cikin farin ciki.
A da ita kaɗai take rayuwa, daga ita sai Abba, bayan Abba sai Arya ya zo, daga shi kuma sai ga Harees, wanda zuwansa ya zama sanadiyyar shiryawarta da mahaifiyarta, bayan kuma ta shirya da mahaifiyar tata sai ta samu ƙanne harda mahaifi.
A cikin ranta ta godewa Allah, a sanda ta tuna abinda Abba yake faɗa mata a kullum.
_ “Bayan wuya sai daɗi Bannute”_
Haƙiƙa baka ne, bayan wuya sai daɗi, dan a yanzu tajita a matsayin cikakkiyar ƴar adam, ta samu komai, babu abinda take nema, kewar Abba kaɗai ta dameta.
*No.803, Tolstoy Rd, New Delhi, India*
*05:00pm*
MARYAM POV.
Zaune take daga kan wata sofa, ta yi tagumi tana bin ƴan matan wajen da kallo ɗaya bayan ɗaya, yaren hindi suke wanda ita sam bata fahimta, ko magana za ta yi da su saide ta musu da turanci, su kuma su amsa mata da turancin nan nasu dake bata dariya.
Tun safe take tare da ƴan matan, waɗanda suka kasance ƙawayen amarya Komal, kamar yanda Eshaan ya faɗa mata sunanta.
Dan jiya suka sauƙa a delhi, kuma ya faɗa mata cewa yau za'a ɗaura auren abokin nasa, shi yasa suka taho tun safe, ya danƙata a hannun amaryar shi kuma tun bayan nan bata ƙara ganinsa ba.
Sai biryanin da ya aiko mata dan yasan ita ba komai take iya ci ba, sai laddu ɗin da sukai ta bata. Hayaniyar ƙawayen amaryar ta cika mata kunne, dan yanzu haka amarya suke shiryawa.
Sai kawai ta ɗauki wayarta ta buɗe ta shiga message, kusan jarin mesages uku tana turawa Eshaan amma ba ya replying.
Dan haka kawai sai ta fito daga wajen ta aika masa kira, amma de kamar ɗazu bai ɗaga ba.
“Mts, ina ya shiga ne?”
Babu me amsa mata dan haka kawai sai ta meda wayar cikin jakarta ta ci gaba da kallon ƴan matan, kyawawa wanda babu ɗaya da zaka iya cillarwa a cikinsu, domin babu baya a cikin.
“Wow...., a ina kika si yi wannan saree ɗin”
Maryam ta juyo ta kalli budurwar, sannan kuma ta kalli jikinta, nan take tunanin ta ya dawo mata da abinda ya faru a ɗazu.
Tana zaune a bakin gado tana cin abinci, Eshaan ya shigo ɗakin hotel ɗin da suka sauƙa, hannunsa riƙe da wani kwali, yacemata saree ne a ciki, kuma nata ne, so yake ta saka.
Ta faɗa masa cewar ita fa bata iya ɗaura saree ba, shi kuma yace taje ta saka blouse da skirt ɗin tazo sai ya ɗaura mata.Yanda aka ɗaura saree ɗin nema bata san tunawa, dan yau d'an guntun hankalin da take ji Tafida ya bar mata shi seda ya zube, notukan kanta suka karasa kuncewa.
“Kin gane saree ɗin Krishan?, shine fa wannan wanda na taya a Metropolitan Mall, amma na fasa sbd tsadar da ya min”
Maryam ta kuma kallon ƴan matan, sannan ta ƙara kallon saree ɗin, jar kala ne, an masa ado da wasu golden stones, kuma yadin sa silk ne, hakan ke ƙara nuna mata tsadarsa, duk da ba wani sanin kan saree d'in tayi ba.
“Ba ni na siya ba, mijina ne ya siyo min”
“Aiko mijiniki yana sanki, saree ɗin ki kud'insa ɗaya da na amarya”
Maryam ta kalli sareen da ke jikin amaryar sannan ra kalli nata, kusan kallarau ɗaya ma, dan hatta da kalar blouse d'in iri ɗaya ce, kawai de yanda aka jera stones d'in jiki ne ya banbanta.
“...Kai ga tawagar ango sun iso...”
wata matashiyar budurwa da Maryam ta ji suna kira da Rakshi ta faɗi baki washe.
Ƙawayen amarya suka shiga gyarta, dan dama jama'a sun jima da fara taruwa, ita Maryam ba wannan ne ha dameta ba, duk da tasan cewa ba al-adarsu ɗaya ba, dole de ango idan zai zo wajen ya taho da abokansa, kenanan Eshaan na tare da su?.
Ba ta yi tunanin komai ba ta miƙe, ta ɗauki wayarta da wani golden mayafi ta yafa a kanta, dan bazata iya yawo kanta a buɗe ba haka.
Ta cikin tarin firmitsin jama'ar da suka taru a gidan tabi har zuwa bakin ƙofa inda take jiyowa kiɗe-kiɗe.
Waje ta ja ta tsaya tana kallon ikon Allah, ango da abokansa dama 'yan uwansa sun iso gidan, sai tiƙar rawa ake ana watsa kuɗi. Ga masu kiɗa suna aikinsu.
Cikin abokan ango ta hango Eshaan,sai daj shi ba rawar yake ba, tafi kawai yake yana fito.
Cikin tarin jama'ar wajen ya hangota a gefe, ba zai ce yasan daliliba, amma se yaga babu kowa a wajen, duk wannan hayaniyar da ke tashi a wajen babu ita.
Babu kowa sai itan da yake gani, sanye cikin red silk saree, me ratsin golden, wuyanta hannayenta da kanta dauke da jawellies, babu wata kwalliya da yawa a fuskarta. Amma kuma ta yi kyau, domin ta yafa wani golden ɗin viel a kanta.
A hankali ƙafafuwansa suka shiga takawa setin inda take, kallonsa take yayin da shima yake kallonta.
“Ina ka shiga Sundar ?” Muryar Maryan ta tambaya da ɗan ƙarfi ta cikin kiɗa da hayaniyar da ke tashi a wurin.
Eshaan ya lumshe ido sannan ya buɗe yana ci gaba da kallonta.
“Kinyi kyau Wifey”
Sai ya faɗi hakan me makon ya amsa mata tambayar da ta masa.
Me ?, ɗazuma fa sai da ya faɗamata hakan, me yasa yanzu ze sake ?.
“Mu shiga ciki, za'a fara gudanar da ɗaurun auren ”
Muryar sa ta faɗi, ta cikin hayaniya da kiɗan dake tashi a wajen, hannunta ya kama ya shiga janta har zuwa cikin farajiyar gidan inda za'a gudanar da ɗaurin auren.
A kijerun gaba suka zauna, har yanzu idonsa a kanta ya kasa janyesu, hannunsa ya kai ya gyara nata zaman veil ɗin.
A lokacin kuma ango da ƴan uwansa suka ƙaraso wajen, har yaje ya zauna a wajen da aka tana da domin shi, Suwami ya shiga jero addu'o'i.
Kafin aka kawo amarya, itama ta zauna a kusa da ango, aka ci gaba da yin addu'o'i, sannan aka bawa ango red Tikka (wannan jan garin da matan auren ƴan addinin hindu ke sakawa a tsakiyar gashinsu, alamun suna da aure).
Ango Mahesh ya sakawa Amarya Komal tikka a tsakiyar gashinta daga gaba, sannna aka maƙo mangalsutra, (sarƙar aure). Ango ya sakawa amarya, sannan suka miƙe, mahaifin amarya ya zo ya ɗaure mayafin amarya dana kafaɗar ango, sannan suka shiga zagaya wuta.
A lokacin kuma aka shiga rabawa jama'a fure suna watsawa amarya da ango, yayina da shima Swami ya miƙe yana karanto addu'ar aure.
“Mangalan fagbani bishnu mangalan madradda shar, mangalin gundari fakshar mangala yatarobari......” Har zuwa ƙarshe.
Eshaan da Maryam suka miƙe a sanda suma aka miƙa musu fure suka shiga watsawa amarya da ango.
Maryam na watsa kamar kowa sai ji ta yi ita kuma ana watso mata, ta juya ta kalli Eshaan, yayin da kowa ke watsawa amarya da ango shi kuma ita yake watsawa.
Ta saba ganin irin wannan auren a Tv, yau gashi a gaban idonta tana ganin yanda ake ɗaura shi.
🌸SAI KASKA CE✍️🌸
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Wannan naki ne Rahma Musa Hussaini*
*BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI (47)*
{ESHAM}
~~~
*R 78, TC Maurya Hotel, New Delhi, India*
*11:15pm*
“Dama Mahesh ba musulmi ba ne?”
Muryar Maryam ta tambaya, yayin da take shirya kayan sakarwarsu a cikin jaka.
Eshaan da ke zaune a kan gado yana danna system ya juyo ya kalleta.
“Eh, ɗan addinin hindu ne, ai ina jin kaf abokamu daga ni sai Arjit ne musulmai”
Ta gyaɗa kanta tana zipping ɗin jakar, sannan ta ajeta a ƙasa kusa da wardrobe.
Ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala, ta fito ta saka hijabinta, sannan ta kwanta a,kan gadon, tana kallon Eshaan dake gefen gadon har yanzu yana danna system.
“Yanzu gobe gida zamu koma ?”
Sai ta ga ya dakata da danna systen ɗin, kafin ya juyo yana kallonta ta cikin ɗan guntun hasken da ya rage a ɗakin.
“Indian ta isheki ne ?”
Sai ta gyara kwanciyarta tana girgiza masa kai.
“Naga mun gama komai ne, to me zamu jira ?, ko akwai inda zamu sake tafiya ?”
Sai ya girgiza kansa yana rufe laptop ɗin, sannan ya ajeta a kan bedside drawer.
Ya kwanta yana jan bargon, kansa na kallon sama yace.
“Mun gama zuwa ko ina, kawai de ina ga ya kamata a ce mun ɗan yi yawo a delhi”
Ya ƙarashe ya na juyowa ya kalleta, itama shi take kallo.
“Ina zamu je to?....”
Ta tambaya a sanda yake kashe sauran fitulun da suka rage a ɗakin, Maryam ta rintse idonta tana ƙanƙanme pillown da take kwance a kai, har yanzu bata dena tsoron duhu ba, kullum zai kashe wuta sai ta tsorata.
Hannunsa ta ji yana lalubar nata, kafin ya haɗe tazarar dake tsakaninsu ya janyota jikisa, kanta ya sauƙa a kan kafaɗarsa, hannayensa biyu duka suka kewaye waist ɗinta.
Maryam ta ƙara duƙunƙunewa a cikin jikinsa, a hankali ya lalubo kunnenta sannan yace.
“Akwai wurare da yawa da zamu iya zuwa a Delhi, Qutub Minar, India gate, safdarjung tomb, Humayun's tomb, lodhi art district suna da yawa sosai, ina so ki yi yawo sosai a india”
Maryam ta ƙara matse jikinta dake cikin nasa, har wa yau ta kasa sabawa da wannan yanayin.
“Yanzu de ki kwanta ki huta, dan a gobe zamuje mu zaga gari, kuma a goben jirgin mu zai koma nigeria, kinsan idan mun koma lagos kwana biyu za mu yi mu tafi haɗejia”.
*Chida Event Center, Jabi, Abuja, Nigeria*
*07:40pm*
HANAM POV.
Babban ɗakin taron a cike yake maƙil da jama maza da mata, daga can wajen zaman amaryam da ango kuwa Kamal Muhammd Hakuɗau ne da amaryarsa Kalisa Usman.
Daga b'angaren zaman dangin ango kuma gaba ɗaya ƴan uwansa ne maza da mata sai hira ake ana cin abinci, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci cewa suna cikin tsantsar farin ciki.
A cikin su kuma akwai Hanma. Wanda itama ke sanye cikin irin nasu kayan, kuma harda ita ake hirar.
“Ya Hanam wai ki zo inji Ya Harees!”
Nabila ta faɗa mata da ɗan ƙarfi, kasan cewar hayaniya da kiɗan dake tashi a wajen. Ta juya ta kalleta sannan ta miƙe tsaye.
“Hanam wai Ina Aryaan ne ?”
Ta juyo ta kalli Hafsi, sannan kuma ta shiga hange-hange ko zata hango shi, ita rabonta da shi tun da safe. Allah ya temaketa ta hango shi zaune a kan wani table.
Ƙanenta maza ne gaba ɗaya a kan table ɗin, hatta kayan da ke jikinsa ma irin na su ne. Ta nuna wajen da hannunta.
“Gashi can a wajen su Hafiz”
“Bari naje na karb'o shi, ai basu kaɗai suke san sa ba”
Hanam ta yi dariya tana tafiya, sai kuma ta tsaya ta juyo ta dawo wajen tana faɗin.
“Nabila yana ina ?”
“Ni dai a waje na ganshi, ki duba cikin motarsa”
Sai ta gyaɗa kanta, sannan ta fita daga wajen da ƙyar sbd tarin mutanen dake wurin.
A parking lot taga motarsa dan haka ta je ta buɗe zata shiga gaba, amma sai taga baya gaban, yana baya, ta rufe ƙofar gaban ta buɗe ta bayan sannan ta shiga. Kuma tana shiga ya janyota jikinsa ya rungume.
“Wai bakwa tausayi na ne?, kun barni daga ke har Arya ”
Hanam ta saƙala hannayenta ta wuyasa a sanda ya saketa.
“Kamar baka ci abinci ba ma”
Sai ya gyaɗamata kai.
“Tun safe banci komai ba, kinsan mu ne abokan ango, duk gwagwarmayar da akayi da mu akayi ta”
“Awwww, Alah sarki rex (king), sannu”
Ya kai hannunsa yana janyo wata leda dake gidan gaba na motar, ya aje mata ledar a kan cinyarta bayan ya ɗauko.
“Ga abincin nan, a bani na ci”
Ta ɗanyi dariya tana buɗe kayan dake cikin ledar. Sannan a lokaci guda ta ɗago ta kalleshi cikin hasken futulun waje dake shigowa cikin motar, farar shaddace sanye a jikinsa, kansa harda hula, kuma ta ga kayan da ke jikinsa irinsa ne a jikin ango, dan yanzu sun ɗiki, aminta suke shi da Kamal kamar waɗan da suka ta so tun yarinta.
“Ni fa na yi tunanin Mama zata zo”
Uchenna ya jingina da jikin kijerar motar yana cire hular kansa, sannan ya shafa kansa.
“Wai Zakiyya ce za ta yi graduate, shi yasa bazata zo ba”
Hanam ta buɗe wata roba tana saka spoon a ciki.
“Ai mu ma kuwa ya kamata a ce munje, ka je wurin Baba yau ?”
Ta kai masa lomar farko tana masa tambayar, ya haɗiye abicin da ya gama taunawa sannan yace.
“Da safe kawai naje, amma ban koma ba, wata ƙila kafin mu koma gida sai muje”
“Kaida wa ?”
“Ni da ke”
Ya amsa mata yana karb'ar abincin da take ba shi.
“A'a ni yau bazan kwana a gida ba”
“Da izinin wa ?”
Sai kuma ta yi shiru, dan ya kamata a ce shi sai da ta tambaye shi tukunna.
“A ina za ki kwana ?”
“A gida, su Ya Kamila ma duka a can zasu kwana”
“Shikenan tun da kina so bazance a'a ba, sai yaushe kenan?”
Spoon ɗin hannunta ta aje a cikin robar abincin sannan ta riƙe fuskarsa da duka hannunta biyu, ta yi pecking fuskarsa.
“Thank you mi rex (my king)”
Hannunsa ya kai ya kamo waist ɗinta ta baya, sannan ya shiga kissing ɗinta, da ƙyar ta samu ta ja baya da shi.
“Ka ci abincin”
Ta faɗi kanta a ƙasa, sai ya yi murmushi yana karb'ar abincin.
“Ina Arya ?”
“Yana wurin su Hafiz”
“Kwaliyarki ta yi kyau, me yasa kika dena kwalliya yanzu?, ba ki ga yanda ta miki kyau ba”
“Sanda na kusa zama uwa na dena, kuma har bayan da na zama uwar ma ban ci gaba ba”
Hannunta ya kama, sannan ya ƙara matsota cikin jikinsa sosai.
“Yanzu kuma kin zama mata, mijinki yana so, dan Allah dan shi ki riƙa yi”
A hankali kamar me raɗa ya furta hakan, yana yi yana shafa gefen fuskarta da ta ɗau heavy make-up.
Kafin ya kuma kissing ɗinta kaɗan, ya ɗan ja baya yana haɗe fuskarsa da tata, suka shiga musayar numfashi.
“I love you Rex”
Ya ɗan ja baya da fuskarsa kaɗan,sannan ya yi pecking gefen fuskarta.
“I love you too”.
*House No.122, B3, Alaro city lekki, Lagos*
*09:56pm*
MARYAM POV.
A hankali ta fitar da gaba ɗaya kayan da ta siyo na gujirin da zata kaiwa ƴan gidansu, jiya suka dawo daga India, kuma basu bar delhi ba sai da ya kaita duk inda ya lisaafa mata harma da inda be faɗi ba, kuma har kasuwa suka shiga, a nan taga takalma da ɗankunnaye ta tsaya ta si yi wanda zata kawowa ƴan uwanta, tun da yace gobe zasu wuce Haɗejia.
Jiya ta tambaye shi me yasa zasu je haɗejia.
_ “Kinga hutun dana ɗauka da saura be ƙare ba, kuma idan hutun nan ya ƙare bana jin za'a ƙara barina na ɗauki wani hutun kwana kusa, kuma kema kinga hutun ki da saura, kafin ya ƙare se muje mu dawo”_.
Idan aka bincika zuciyarta cike take fal da farin ciki a sanda ya bata wannan amsar. Bayan wasu watanni zata je ta haɗu da Maanmu, Hussain, Hassan da auta.
A cikin jakar da za ta yi tafiyar ta saka kayan, sannan ta ɗauki hijabinta ta saka ta fito ƙasa.
Tafida baya gidan, dan ya faɗa mata cewar zai je asibiti ya dawo, kitchen ta shiga dan ta sama masa abinda zai ci, dan ita bata jin yunwa, taci abincin da Maman Ilham ta aiko mata, duk da babu wasu kayan girki a gidan, dole ne bayan sun dawo da ga haɗejia su yi siyyaya.
TAFIDA POV.
Da sallama a bakinsa ya shigo parlon, amma be samu kowa ba kuma dama yasan cewa ba zata wuci kitchen ba, dan haka kai tsaye ya wuce kitchen ɗin.
Har ya buɗe ƙofar bata san ya shigo ba, sai ji ta yi anyi hugging ɗinta ta baya.
wata iriyar iska ta shaƙa, wadda ta taho mata da ƙamshinsa, a hankali ta ɗora hannunta a kan nasa, a sanda shi kuma yake saka kansa a cikin wuyanta.
Ba shiri ta yi saurin juyowa a cikin hannayensa ta riƙo gaban rigarsa, hannayenta da ke b'ace da fulawa suka b'ata gaban rigar, sai kuma ta janye hannun nata ganin ta b'ata masa jiki.
Sai ta ga yana dariya, hannayen nata biyu ya kamo ya ƙara meda su kan kirjinsa, sannan ya kara fuskarsa a tata.
“Borrow me a kiss Miriam”
Maryam ta zaro ido tana jan fuskarta baya, amma sai ya saka hannayensa yana dawowa da ita.
“To ba bashi, kiss me then”
Zaburar da ta yi yanzu tafi ta ɗazu. Kansa ya gyaɗa mata.
“Kiss me pls, i like your soft lips”
Roƙon da yake mata yasa bazata iya musawa ba, dan haka sai ta ɗago da hannayen ta ta kama fuskarsa har tana bata masa ita da garin fulawar dake hannun nata, ta ɗan yi kissing saman lips ɗin nasa kaɗan, sannan ta sake shi tana ja baya.
”Me ki ka yi wannan ?, wannnan ai ba kiss ba ne Miriam, bari na koy.....”
A guje ta zare ta fice da ga kitchen ɗin, Tafida na dariya ya juyo ya kalli fulawar da take kwabawa, be san me zata ta yi da ita ba, amma sai ransa ya ba shi kamar ɗan ƙwantalaka za ta yi, dan ga manja da yaji nan ta aje.
Da ƙarfinsa ya yi amfani ya yi girkin da kansa, bayan ya gama ya zuba mata a warmer, sannan ya zauna yaci nasa.
Har kusan sha ɗaya bai ganta ba, hakan ke nuna masa cewar wata ƙila ta yi bacci, shi kuma ta barshi gadin gida.
miƙewa ya yi da ga kan kujerar da yake, ya kashe duka wutar gidan, sannan ya koma ɗakinsa ya yi wanka ya saka kayan baccin sa ya kwanta.
Sai yaji baccin ya gagare shi, dan a kwanakin nan ya saba sai da ita yake bacci, ko jiyama da ya iya yin bacci shi ɗaya gajiya ce a jikinsa.
A zaune ya miƙe, sannan ya sab'a slide sandals ɗinsa, ya fita ta balcony ɗin ɗakinsa ya yi wani irin talle da ba duka ɗan adam ze iya ba, ya dira a balconyn ɗakinta.
Kamar yanda ta saba yau ma bata kashe wutar ɗakin ba, a kan gado ya ganta ta duƙunƙuna cikin bargo.
Kamar yanda shima ya kasa baccin haka itama ta kasa, ita ko jiyan ma ba ta iya yin baccin ba. Jin gadon yana motsi yasa ta yi saurin juyawa, aiko ta yi kyakyawan gani, dan tana juyawa Tafida ya janyota jikinsa ya ƙanƙame kamar me shirin medata ciki.
“Me yasa za ki tafi ki barni”
Ya faɗi yana ƙara ƙanƙameta, Maryam ma ta saka hannayenta biyu tana rike shi.
hannunsa ya ɗaga setin switch ɗin ɗakin ya motsa, wutar ta mutu, yau ɗinma sai da ta razana, amma kuma Tafida ya riƙeta da kyau, yana shafa kanta har sai da ta yi bacci.
Shi kuma se ya kasa baccin, kawai ya saka ta a gaba yana kallo, duk da babu wani wadataccen haske a ɗakin.
jinta a jikinsa da kuma kallonta da yake irin haka yafiye masa baccin.
______________
_To fa, daga India kuma Haɗejia zamu wuce, fuk me san zuwa ya min magana na aje masa ɗakin kwana, dan gida zasu dawo_
_Godiya nake🙏_
🌸SAI KASKA CE✍️🌸.
⭐️YADDA ƘADDARA TA SO⭐
⭐️ شاء القدر⭐️
*Magical love story*
©By Sai Kaska
Wattpad @Sai_Kaska
Phone number:***
Tiktok @SAI_KASKA
Arewabooks @18saikaska
Facebook fage: Salma Ahmad Isah Sai Kaska
_________________________________
*Proud of my first novel*
★TAURARI WRITER'S ASSOCIATION★
*Na sadaukar da wannan babin ga M. Hafsat*
*BABI NA ABA'IN DA TAKWAS (48)*
*Kano Road, Hadejia Emirates*
*05:20pm*
Wata kyakyawar mota ce fara sol take tafiya a nutse. Daga cikin motar kuma Tafida ne da Maryam zaune.
Jiya suka sauƙa a gidan baban Neha dake abuja, kuma a can suka kwana, a jiyan Maryam ta gano dalilin da yasa Neha da Eshaan suke kama, dan baban Neha ɗin kamarsa ɗaya da Tafidan.
Bayan gari ya waye suka yi shirin tafiya, kuma Baban Neha ɗin wanda Maryam ta ji Tafida na kira da Appa shi ya basu motarsa, har gidan Neha ɗin ma sunje, wani gida Me kama da fada inji Maryam.
Dan gidan ba ƙarami ba ne, sbd ba su kaɗai ke rayuwa a ciki ba, akwai ƴan uwan mijinta a gidan.
Duk da ta gaji amma waƙoƙin motar sunfi gajiyar mata da kunne, dan haka ta shiga daddana botton ɗin sauyawa.
_🎶Kuzo gidan Ahmen ku gani_
_Na Garba me nasara a Ruwa🎶......_
Maryam ta tintsire da dariya a sanda waƙar ta shiga playing, ita irin wannanƙoƙin a wurin Maanmu ko kakarsu Jaruwa ta saba jinsu, ashe shima yana jin irin su. Ta jiyo ta kalleshi a sanda ta ji yana rera waƙar shima, harda wani turo hula gaban goshi.
_🎶Mutum da ganin motar A ruwa..._
_Tilas yaka ba giwa hanya, yasan akwai manya a ciki_
_Na Garba me nasara A Ruwa, Kuzo gidan Ahamen mugani🎶...._
Maryam kam me za ta yi in ba dariya ba, Tafida ya juyo ya kalleta.
“Cikkaken ɗan gargajiya ake faɗa miki”
Tana girgiza kai ta kai hannu ta sauya waƙar.
_🎶Gadar gayan Mamman ɗan sha'aibu_
_Gadar Gayan Mamman ɗan sha'aibu_
_Mota ki dakata ki aje ni a birnin gadar Gayan...._
_Direba dan dakata kaɗan zan sauƙa a birnin gadar gayan...🎶_
Yanzun ma dariya ta yi tana kallonsa, yanda ya dage bilhaƙƙi da gaskiya ya na bin waƙar.Ta sauwa waƙar wata ta shigo.
_🎶Khadal yen khabiye, ni yen arugul ban dale_
_Fasi faga bai maride, ani bani yallem madu fogum🎶...._
“Wato har waƙoƙin Telugu kake saurare?, dan na san wannan ba hindi ba ne,yafi kama da Telugu”
Se ya tura hular kansa baya kaɗan, yana gyaɗa mata kai.
“Ai ina jin Talugu ɗin ma, sanda muna makaranta akwai wani abokin mu Srinivas, ɗan talugu ne, kuma Mahesh ma yana jin Telugu, dan Babarsa 'yar telugu ce”
Ta gyaɗa kanta tana sauya waƙar dan ita har yanzu bata samo wadda take nema ba.
“Yare nawa ka ke ji a India”
Ya ɗan ɗaga kansa sama kaɗan yana tunowa, can kuma sai ya sauƙe.
“Mts, ina jin kamar biyar ne, Kinga inajin Hindi, Talugu, tamil, urdu sai bengali”
Maryam ta gyaɗa kai tana sauya wata waƙar.
_🎶Wataran wata rana, za'a kaiki gidana_
_Matsayin matata, kece madarata..._
_Na matsu, na matsu, na matsu naga wannan rana,na matsu..._
_Allah kaimu, Allah kaimu, Allah kaimu ranar nan.....🎶_
Maryam ta kuma sauyawa.
_🎶You hit my heart, oh, hit it like a heart attack...._
_We talking all the time like insomniac....🎶_
“Mts!”
Eshaan ya juyo ya kalleta.
“Me ya faru ?”
“Ni ban samu waƙar da nake so ba”
Se ya yi murmushi.
“Mun shigo gari ai”
Maryam ta kalli inda suke, bakinta ya buɗe cikin dariya, ta yi missing gida, ta yi bala'in kewar komai na haɗejia.
Farin cikinta be ƙara ninkuwa ba sai sanda taga sun wuce ƙofar fada sun nufi Garko. A ƙofar lungunsu ya yi parkinga.
Se da Maryam ta riga shi fita daga motar, bakinta fal murna, ta tsaya a wajen tana ta bin unguwar tasu da kallo.
A sannan Tafida ya zagayo inda take tsaye bayan ya fito mata da jakarta dake booth. Matasan dake zaune a kan bencina suna ganinsa suka ta so suka rufe shi suna ta miƙo gaisuwa.
Tafida be iya shariya ga matasa ba, seda ya tsaya suka gaisa har ya musu ihsani, sannan suka barshi ya tafi, Maryam kam har ta yi gaba, saida ya haɗa da sauri sannan ya cin mata.
A ƙofar gida taga auta da abokasa suna wasa, tamanta da wani Tafida dake binta a baya ta ruga da gudu inda suke tana faɗin.
“Auta!”
Shima jin Muryar yayar tasa yasa ya miƙe da sauri, yana ganinta ya ruga inda take shima yana dariya, suna haɗewa suka rungume juna, Maryam ta ɗaga shi masa tana juyi da shi, tuni batun zuwan Maryam ya karaɗe unguwa.
Maƙota da ƴan mata duka aka loƙo ana ganin Maryam da Tafida.
Sai da Maryam da auta suka gama yarintar tasu sannan ta ja hannunsa suka shiga cikin gidan.
“Maanmu wata sabuwar Ps5 ce ta fito...”
Hussain be ko ƙarashe ba, Maanmu da wata mata dake zaune a kan tabarma suka saka dariya, harda Hassan da ya fito daga banɗaki.
Ya kalli kwanon dambun da ke gabansa sannan ya kallesu.
“Ni fa ba santi nake ba, labarine kawai nake san baku”
Matar da ke zaune kusa da Maanmu tace.
“Babu wanda yace kana santi ai, kawai de labarin naka ne abun dariya ”
Sai kawai shima ya yi dariya yana kai loma.
“Wato anti Hanne ai a gidan nan babu girkin da za kuyi ya saka ni santi, Yaya ce kawai take yin girkin da ke sakani santi”
Kamar daga sama suka ji sallamar Maryan da Muhsin.
Gaba ɗayansu suka sakawa bakin ƙofar ido, ko amsa sallamar an rasa wanda ze yi.
Ita ɗince kuwa ta shigo, sede wannan Maryam ɗin tana da banbanci da waccan, wannan Maryam ɗin tana da jiki, kuma tafi waccan fari, amma maganar da ta yi yasa suka fahimci cewa ita ɗin ce.
“Wai baku ji muna sallama ba ne ?”
Ta ƙarashe tana zama kusa da Maanmu tare da rungumeta, Anti Hanne ta miƙe tsaye tana faɗin.
“Ko wannan itace Yayan?”
Ihun da su Hussain suka saka shi ya tabbatar mata da maganarta. Gaba d'aya suka zauna a gaban Maanmu suna ta yi Maryam sannu da zuwa.
“Kuma ina Yaya ?”
Maryam ta kalli Hussain, tana so ta tuno waye Yaya, nan take ƙwaƙwalwarta ta hasko mata Tafida dake tsaye a bakin ƙofa riƙe da jakarta. Ita ɗaukin ganin ƴan uwanta ma ya mantar da ita shi. Ta dafe goshinta.
“Oh!, yana waje, kaje ka shigo da shi ”
“Auta bani hijabina gashi can”
Muhsin ya miƙe sannan ya ɗauko mata hijabin, Maanmu ta karb'a ta saka, sai bin Maryam take da kallo yanda ta ga tasauyamata, duk da dama Anti fati tana fad'a mata yanda Maryam d'in tace suna zaman lafiya da mijinta, amma ganin 'yarta ta ya k'ara tabbatat mata da waccan magana.
“Sirikin mu ne zai shigo ?”
Maryam ta juya ta kalli matar da kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa bafulatana ce.
“Eh Hanne, mijin Maryam ne“
“Ah to nima bari na je na saka hijabi“
Cike da kokwanto Maryam ta bita da kallo har ta shige ɗakinta na da. Ta juyo ta kalli Maanmu.
“Maanmu waye ce wanna ?”
“Husain ka ɗauko wannan dardumar ta ɗakina ka shimfiɗawa Tafida”
Maanmu ta faɗi memakon ta amsa mata, ita fa kanta ya kulle, ta kasa ganewa.
Sallamarsa ta ji daga waje shida Hassan, Hassan ɗin ne ya fara shigowa sannan shi, kansa a ƙasa har ya zauna a kan dardumar da Hussain ya shimfiɗa masa, suna gaisawa da Maanmu Hassan yace da Maryam.
“Yaya a ina zan aje miki jakar ?”
Ta kalli jakar da ke hannunsa se taga jaka ɗaya, bayan ita tasan da jaka biyu ta taho.
“Ka kaimin ɗakin na”
“Ai yanzu baki da ɗaki a gidan nan, sai dai na Maanmu ”
Maganar Hussain ta ƙara kulle mata kai, amma ba komai zata tambayesu tunda Maanmu taƙi amsa mata, sai kawai tace.
“Kai min ɗakin Maanmun to”
A lokacin Hanne ta fito daga ɗakin Maryam na da, ta ja kujera ta zauna itama suna gaisawa da Tafida.
Duk yanda ya kai da gujewa kada Maanmu ta masa godiya sai da ta masa, shi kuma sbd baya san yawan godiyar yasa koda su Hussain suka turo masa lambarsu be bawa Maryam d'in ba, dan bayama so ta san da abinda yama 'yan uwanta.
Har ruwa aka kawo masa amma yace tafiya ze yi, sai da ya tashi ya fita sannan Maanmu ta kalli Maryam.
“Kije ki taka masa mana”
Ita gaba ɗaya rudanin dake kanta ya hanata cewa komai, a kunyace ta miƙe ta fita.
Can ta hangoshi har ya kusa fita daga lungun, ta bi bayansa, sanda ta isa wurin har ya shiga mota.
Ita ma seat ɗin gaba ta buɗe ta shiga.
“Akwai jakata ɗaya”
Ya juyo ya kalleta.
“Na sani ai, amma ai wannan kayan sakawar ki ne”
“Eh kayan sakawar, dama su nake faɗa”
“Keda ba'a nan zaki kwana ba, anjima zan zo na ɗauke ki”
Bata san sada ta furta “Huh?”
“Eh mana, baki da wurin kwana a gidan Maanmu, baki san an bawa wata ɗakin ki a gidan ba?”
Zuwa yanzu kam abun ya gama kulle mata kai, kenan har Tafida ma ya san da zaman waccan matar amma ita bata sani ba ?, to me yake faruwa haka?.
“Kije ku gana da ƴan uwanki, nima zanje na ga nawa“
Ita de ba haka ta so ba, tana san ta kwana a gida yau, a cikin 'yan uwanta. Dan ta yi kewar kowa a cikin su.”
Ta juya jiki a sanyaye zata fita, caraf ta ji ya riƙe hannunta, ta juyo ta kalleshi, a kan lips ɗinsa ya furta.
“I love you”
Bata ce Komai ba, dan kanta cike yake da ruɗani.
Ya saki hannunta ta buɗe motar ta fita, sai yanzu take kallon yanda jama'a suke binta kallo, gaba ɗaya maƙota an leƙo ana san a ga ƙwaƙwaf.
Ko da ta shiga cikin gidansu se ta ga su Hussain na irga kuɗi.
Ta zauna a inda ta tashi ɗazu tana faɗin.
“Wannan ribar shagon wayar ce?”
“A'a mijinki ne ya bayar yace a bawa Maanmu da Anti Hanne”
Ta ɗanyi murmushi, ita de kam ta ƙagu ta san wacece wannan Anti Hannen, gashi kuma tana zaune a wajen, babu damar ta tambayi su Hussain.
“Hassan ɗauko min jakar nan”
Hassan ya miƙe ya shiga ɗakin Maanmu ya fito mata da jakar, se yanzu Maryam take ƙarewa gidan kallo, har sabon fenti suka sake, an gyara gidan sosai.
Bayan Hassan ya kawo mata jakar ta buɗe ta shiga raba musu kayan tsarabar da ta kawo musu, kowa se murna yake har da Abti Hannen da bata tsara kawo gujirin da ita ba itama ta samu, harda maƙotansu.
TAFIDA POV.
Kai tsaye fada ya wuce, sai da ya yi parking motarsa a babban parking lot ɗin katafariyar fadar, sannan ya buɗe motarsa ya fito.
Kamar yanda aka saba, dogarai da hadima dama bayi sai kirari ake masa da miƙo gaisuwa.
“Tafida ɗan Tafida, ruwan kogi tafi sannu sannu wanda ya yi wargi zai halaka, giwa ta gama da masu ƙarfi ta wuce......”
Haka wani dogari me kaifin murya ya ci gaba da rangaɗowa Tafida kirari har ya shige soron farko.
Ya ci gaba da taka sorayen fadar har ya isa inda yake san isa, wato b'angaren Fulani Khadija.Sai da aka masa iso da ita sannan ya samu ya ganta.
Yana zaune a falo na uku ta fito cikin wannan tafiyar tata ta ƙasaita. Tun da ta fito take binsa da kallo, ya sauya mata sauyi ba ɗan kaɗan ba. Ita a yanda me martaba me bata labarin ya sauya ma sai ta ga ya fi, ya yi ƙiba ya ƙara haske, kai da ganinsa kasan cewa hankalinsa ya kwanta.
Zama ta yi a kan kujera tana amsa gaisuwar da yake mata.
“Ina Nadra?”
Sai da wasu sakkani suka wuce kafin ta amsa da.
“Taje wani bikin ƙawayenta”
Ya gyaɗa kansa.
“Ina Maryam ?”
“Na kaita gidansu, inshaallah zata zo ku gaisa”
Itama kan nata ta gyaɗa.
“Bari na saka a kawo maka abinci”
Muryarta ta faɗi cikin shirun da falon ya ɗauka.
“A'a ranki ya daɗe, sauri nake, dan a can gidana zamu sauƙa, zan shiga na duba jikin Galadima sannan na wuce, kuma dama mun yi magana da me martaba kan sai gobe zamu gaisa“
“Babu matsala, Allah kai mu goben, zaka iya tafiya”
Ya miƙe yana mata sallama sannan ya fice.
Fulani Khadija ta ɗaga kanta tana godewa Allah, zuciyarta cike take fal da farin ciki da kuma murna, murnar ta sauƙe nauyin marayan Allahn da aka ɗora mata, murnar ganin tilon ɗan da zata iya kira da nata na cikin farin ciki bayan wani abu da ta yi a rayuwarsa.
Tafida ya yi sallama a falon Fulani Sadiya, jakadiyar da ta masa iso ce a kan gaba, yayinda shi kuma ke biye da ita.
A gaba ɗaya zamansa a fadar wannan shine karonsa na biyu da ya shiga b'angarenta, na farkoma da Fulani Khadija suka fara zuwa sanda ta haifi Amina, bayan nan bai sake shiga ba.
Bin mutanen dake falon ya yi da kallo kafin ya samu waje ya zauna. Fulani Sadiya, Maimun, Amina da Nabil.
Ɗaua bayan ɗayan suka gaida shi, kafin shi ya gaida Fulani.
“Ya Galadima da jiki ?”
Ya tambaya yayinda suke gaisawa, Fulani Sadiya ta jinjina kai.
“Jiki da dama, sai godiyar Allah”
“To Allah bashi lafiya, ni zan wuce”
Ya ƙrashe yana miƙewa.
Ya kuma musu sallama sannan wuce.
Gidansa ya koma, yaje ya yi wanka sannan ya ƙara fita ya tafi asibitinsa.
*Unguwar Garko*
*Da 08:15pm*
Suna zaune a kan babbar tabarma, abinci suke ci suna hira, Hassan, Hussain da Muhsin suna ci a kwano ɗaya, yayin da Maanmu da Anti Hanne da kuma Maryam suke ci a kwano ɗaya.
Zuwa yanzu Maryam ta saki jiki da matar dan tana da kirki, kuma wani abu ɗaya ne ya gifta a tunaninta kan matar, da alama Abbansu ne ya yi aure, dan ko girkin daren ma ita ta yi.
“Yanzu da bana nan waye yake shara da wanke-wanke ?”
“Da da bakyanan Ko ni ko Hussain, amma bayan zuwan Anti Hanne kullum ita take yi” Cewar Hassan.
Maryam ta kalli fuskar matar ta c…