Free chapter · Read without an account
Page 4
ALƘALAMIN SO
BY
DIJAHAM(OUM AMANI)
Page 4
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Dan ture ni Ya Kausar tayi ta ce “Allah y shirye ki, kuma gidan wa ɗin zaki zauna ba dai nawa ba ni kam don ni ban iya wa da wannan halin naki sam sam”.
Hannu na sa a baki na na rufe Ina zaro manyan ido na nace “lalalalala yanzu a gaban su Abba din kike cewa ba zan zauna miki a gida ba tabbas duniya ta soma lalace wa da zafi zafi”.
Yunƙuro wa tayi kamar zata dake ni na mike da sauri na nufi bayan Ya Haidar Ina mata gwalo.
Dariya su Mami kawai suke mana don su kam tuni sun sa ba da yadda ni da Ya Kausar muke kamar Tom and Jerry in har zamu zauna guri daya to fa sai mun raba hali duk kuwa da cewa ta bani shekara 5 amma ganin ta nake kamar sa’a ta. Ban sani ba ko dan dana fara wayo ita ce kadai macen da nake gani a part din mu ne?.
Sai wajen 11 Sultan ya bar part din mu bayan na basa System din da kyar don ya saka min gaba daya Chinese and Korean series din da yake tasa system din.
Sai da safe muka yiwa su Abba ni da Ya Kausar kowa ya nufi dakin sa don kwanta wa.
Ina shiga daki na toilet na fara nufa nayi fitsarin daya matse ni amma naki yin sa tun dazun, sannan nayi alwala na fito, sai da na karasa assignment din da ban gama ba sannan na saka book din a school bag dita na kwanta.
Next week zamu fara exam In sha Allah Ina so na yi bacci da wuri don na tashi da asuba nayi karatu duk kuwa da cewa kaf subjects din da muke ba wanda ban iya ba, sbd Allah yayi min baiwar basira da saurin fahimtar abu, daɗin daɗa wa kuma daga wannan term din zamu wuce SS 2 mun fara zama yan mata muma.
Kamar yadda nasan wasun ku da yawa suna son sanın asalin ni wace da kuma dalili na na kiran Ya Aliyu Uncle bana kiran sa da Ya Aliyu kamar yadda duka ahalin gidan suke, bara na baku takaitaccen tarihin rayuwa ta.
Suna na A’isha sunan mahaifiya ta naci wacce ta rasu wajen haihuwa ta kamar yadda aka fada min.
Sunan mahaifina Muhammad Ina kıran sa da Dada, Ina matukar kaunar mahaifina kamar yadda shima yake bani kula wa, duk abinda nake so siya min yake ya bar ni dai a wajen Mami ne tunda tun Ina jinjira ita ta rike ni. Hajja(kakata wacce ta haifi Dada) taso kwace ni lokuta da yawa amma Dada na tausar ta da bata hakuri tun da bawai bana zuwar mata hutu bane.
Ina da shekara hudu aka ce Dada ya sake aure ya auri Maama da kanne na su uku Humaira 10yrs
İsmail 6yrs, Hisham 2yrs.
Ba sosai nake zuwa gidan ba din ni kam sai sallah sallah ma nake zuwa nayi kwana biyu zuwa daya na dawo sai dai in har Dada ya matsa min ne nake zuwa shima bana dade wa nake dawo wa, kar kuyi tunanin ko Maama tana min wani abun ne ko daya kawai dai ni ce bana son zuwa nafi son naje gidan Hajja.
Wannan gidan da nake zaune gidan su Mamana ne, Abba mahaifin mamana su biyar mahaifiyar su ta haifa, Abubakar (Baaba ),Salisu (Abba), Khadija (Maman KD), Zuwaira (Aunty Zuwaira), Usman (Daddy).
Gidan Baaba matan sa biyu Umma ita ce uwar gidan sa tana da yara 4 ALIYU 32yrs, Hafsa 28yrs, Hamza 25yrs, Usaina 20yrs. Ya Hafsa tayi aure amma a Abuja take da zama da yaran ta, Ya Aliyu(Uncle) pilot ne shi har ynxu bai yi aure ba duk kuwa da yadda Baaba yake matsa masa akan maganar auren yaki mai da hankali har yanzu don shi in aka takura masa ma barin kasar yake gaba daya, Ya Hamza kuma NYSC yake sai Ya Usaina ita kuma tana level 2 a BUK.
Umma mace ce mai hakurin gaske da kau da kai a kan duk abinda za’a mata sau da yawa Mama kishiyar ta tasha hada mata sharri a gurin Baaba amma sai dai kawai ta kalle su ta kawar da kai, wannan hakurin na ta da sanyin hali yasa Mama take ƙwarar ta sosai.
Sai dakin Mama ita kuma yaran ta 3 Musa 22yrs, Fatima 20yr, Sultan 15yrs. Duk wani dai mugun hali ya tare a gurin Mama masifaffiya ce ta gaske ga gulma da rowa, don zaki iya shiga gaishe ta tana rabawa yaran ta abu kina kallo haka zata bisu daya bayan daya ta basu ke kuwa sai dai kallo don ko kadan baza ta baki ba, duk yaran ta kuma halin ta suka dauka ban da sultan wanda shi kam kamar ba ita bace ta haife sa bama.
Sai gidan Abba gidan mu Kenan😂 su Mamana su hudu Mami ta haifa, Late Aisha,Karima28yrs,Haidar 25yrs, Kausar 20yrs.
Maman KD a kaduna take aure mace ce mai hakuri da kawaici matuka yaran ta hudu duka maza Yusuf 32yrs,Bashir 28yrs, Mustapha 25yrs, Haruna 20yrs
Sai Aunty Zuwaira ita ma dai masifaffiyar ce kamar kuma yadda Mama ta tsani Mami da ni kai na haka ita ma Aunty Zuwairar ta tsani Mami da ni.
Ita a Kano take aure yaran ta biyar Halima 22yrs,İsmail 20yrs,Hanifa 15yrs, Bilkisu 10yrs, Usman 8yrs.
Ita Aunty Zuwaira zan iya cewa kusan tsanar da take min ita da Ya Halima sbd Uncle ne don kuwa kaf familyn mu ba wanda bai San yadda ta ke son sa ba shi kuwa ko kula ta baya yi, to ni dai dama ban ga wani abun da Uncle zai so a gare ta ba don sam bata dace da Uncle dina ba.
Mama ce dai ban san mai nayi mata ba akan shirin da muke da sultan ba kalar dukan da bata masa ba don ya dai na min magana ma gaba daya amma yaƙi yi dole haka ta hakura sai dai zagi da take aika masa kullum ta gan mu tare.
Nima kuma saboda Sultan din yasa name bata girma sosai duk da ban tsira daga zagin nata ba nima.
Sai auta Dady shi kuma matar sa daya Mummy da yaran su hudu Maryam 15yrs,Meenal 12yrs, Hassan 9yrs,Hussain 9yrs.
Wannan shine takaitaccen tarihi na, na fada muku shekaran kowa ne saboda kufi fahimtar labarin sosai.
Ɗan bubbuga fada ta da ake a hankali ya saka ni bude ido na Ina turo baki gaba hade da karanto addu’ar tashi daga bacci, cikin kasala na miƙe zaune Ina kallon Mami wacce ita ma ta zuba min ido tana so na tashi sosai.
A hankali na ce “Barka da asuba Mami”
Dan Murmushi tayi ta ce “an tashi lafiya Shatu?”
Gyada kai nayi nace "Alhamdulillah"
Toilet na shiga nayi alwala, lokacin dana fito Mami bata dakin don haka na shinfiɗa sallaya bayan na zura katon Hijab dina na sallah har kasa yake ja, raka’atainul fajr na fara yi sannan nayi sallar asuba dana idar ban tashi ba sai da nayi azkar dina sannan na miƙe bayan na cire Hijab din jiki na.
Fita nayi daga dakin gaba ɗaya zuwa palon Abba wanda duk bayan sallar asuba anan yake zama shi da Mami sai duk mun zo mun gaishe su sannan yake koma wa bedroom ya kwanta.
Da sallama ta na shiga bayan an bani izinin shiga, kujerar da Abba yake zaune naje na zauna a kasa kusa da kafar sa, a nutse na ce “Barka da asuba Abba”
Hannun sa ya dora a kai na yana dan shafa wa a hankali ya ce “an tashi lafiya Shatu, ni na dauka ma baki yi baccin ba sbd zumuɗi ai?”
Turo baki nayi Ina dora kai na akan cinyar sa cike da shagwaɓa na ce “ai Abba ba sosai zan ɗinga amfani da ita ba yanzu tun da mun kusa fara exam sai mun gama tukun sannan zan mai da hankali na kan ta sosai”
Murmushi ne har lokacin a kan kamilalliyar fuskar sa ya ce “Allah ya taimaka ya bada sa’a”
Murmushi nayi masa nima na ce “Ameen Abbana”
Yar ƙaramar dariya yayi kawai muna hira a nutse wanda kusan duka hirar nice nake basa labarin abubuwan da zan yi in muka gama exam, Mami ma da ta shigo palon zama tayi muna hirar da ita sai da gari ya dan yi haske sannan na musu sallama na koma daki na.
Karatu na nayi sosai sannan na kwanta bacci……….
DijahAM
***