Free chapter · Read without an account
Page 10
ALƘALAMIN SO
DIJAHAM(OUM AMANI)
Page 10
🎤🎤🎤🎺 ALBISHIRINKU
Amarya da💃💃💃💃uwar gida da masu taron biki ko suna ko taron birthday, basai kin wahalar d kanku wajen siyan kayan fitar bikiba kizo UMMU SUDAIS tashare muku hawaye. Zatabaku hayar duk abunda kuke bukata akan farashi me sauki
i€¥^
Muna bada wedding gowns, alkebbar kai amarya, kayan Fulani nayara d manya farare dakuma blue black,, Muna d abun dauri head & shoulders, Muna d kayan kamshi kala kala sai Wanda kikeso,sai angwada akansan na kwarai💃💃
********
Slm jama a Muna d Zumar nono d kibbah da duwawo jadidan inkikasha Bata Mikiba kizo abaki kudinki,
Kiyi kyau kalar Yan gayu,kiba maikyau ba da kwayaba
Haba hajiyata kina zaune
Oga najin haushinki jiki duk kasusuwa Dan Allah kidaure kisiya ki gwada kigani batada Wani side effects. Sai angwada akansan na kwarai
Muna da Sabulun tsarki (liquid soap) inganttacce yana mgnin kyakayin gaba zafin saduwa yana ciko d mace ga kuma y matseta yana Kara dadi d gardi,yana Kara ni’ima yana dauke warin gaba, dade sauran matsalolin mu na mata
Munada turaren tsugono
Dakuma na kaya
Muna bada renting duka a wajen Ummu SUDAIS
Zaku iya tuntubar mu ta wannan numbern
***
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
A gaban wata shegiyar bakar Lamborghini Huracan ya gan sa a tsaye hannun sa rike da Samsung fold 5 ita ma baka, danna wa yake yi a nutse yadda yke danna wayar zaka san abu ne mai muhimmanci yake.
Shi dai Khalil bai masa magana ba sai seat din gaba da yaje ya ajiye shopping bag din anan sannan ya dawo in da yake tsaye ya bude masa seat din baya, bai shiga ba sai da ya gama abinda yake yi sannan na shiga a hankali ya zauna.
Tafiya suke a hankali har suka isa wani gida mai masifar kyau, da sauri gate man yazo ya bude musu gate din suka shiga. Wato tsaya wa fadar muku kyaun gidan bata baki ne kawai amma tabbas gidan nan ya hadu, gashi yanayin sa kamar irin gidajen turawan nan.
Ynxun ma Khalil ne ya bude masa kofar motor ya fito, cikin gidan ya nufa kawai bai tsaya ko ina ba sai a cikin dakin sa, uhmmm dole ne wasu su dinga ce masa Mr Black komai da yake cikin dakin black ne in ka cire white paint din da aka yi wa dakin.
Dan kallon ko ina yake yi kafin ya sa hannu ya zare face mask din sa a hankali, tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan halittar🥹(Hmmm abinda kawai na iya fada kenan ina sake ware ido don na kalle sa da kyau🫣)
Dogo ne sosai kuma tsayayyen gaske, yana da dan jiki wanda ko da yanayin tsayuwar sa zaka gane yana horar da kan sa a gym, doguwar fuska ce da shi mai dauke da wasu lumsassun idonu tubarkallah, komai dai kawai yaji ga dogon hancin sa daya dace da madaidaitan jajayen lips din sa(eh wato da yake ban ga laifin sa ba da yake saka face mask sbd irin wannan kyaun tsaf su Mom Imam, Asmau Tukur, Nenneee da Maryama zasu iya samun karamin hatsari a zuciyoyin su😉😂).
Kamar wanda aka ma dole ya shige cikin closet din sa, anan kam sakin baki nayi ina jinjina kaunar da yake ma black, kusan kayan nasa ma gaba daya black ne ai sai dai dai ku ne da aka ware musu waje kawai suke dauke da wasu colors din, Kayan sa ya cire ya daura towel a waist din sa ya nufi toilet bayan ya saka kayan daya cire a laundry basket.
Kusan 30mins sannan ya fito yana goge sumar kan sa daya kwanta, yadda yake gogen ta tana hargitsewa ba karamin kara masa kyau yayi ba.
Gaban mirror din da yake a jikin dakin ya isa ya shiga wa jikin sa barın turare, sbd tsabar son black color kusan gaba daya turaren da yake a kan mirror din kwalbar turaren black ne.
Sai da ya gama wa kan sa barın turare sanan ya nufi cikin closet din sa ya shirya cikin wasu black pajama masu bala’in taushi, suna bin bayan ya saka sai da ya feshe su da turaruka sanna y zira black slippers ya nufi palon.
Khalil da yake zaune yana danna waya ganin fitowar Ogan nasa yasa shi mike wa da dan sauri yana murmushi, a ran sa kuma yana kara jinjina irin kaunar da yake wa black color.
Zama yayi akan kujera, Khalil yayi serving din sa tea din daya dafa masa wanda bai saka sugar ba sai zuma.
A hankali yake sipping tea din yana sauraren Khalil da yake masa magana akan wani abokin kasuwancin su daya yaudare su a lokacin da suka damka masa kudade masu yawa ya gudu da su.
Sai da ya gama jin sa tsaf sannan ya Lumshe idon sa yana jinjina wauta irin ta mutunin, bai san waye ASAD ABUBAKAR LIMAN ba da yasan shi da kuma hatsarin da yake dashi da bai fara ko tunanin yaudarar sa ba.
Bude idon sa yayi ya kalli Khalil wanda kan sa yake a kasa don baya iya hada ido da Ogan nasa ko dan wani irin kwarjinin da Ubangiji ya masa, kamar wanda aka ma dole ya bude bakin sa ya ce “ka sa yaran nan su kama sa daga nan zuwa kwana biyu, su dan fara fahimtar dashi waye ASAD kafin na samu time din sa”
Da sauri Khalil ya ce “angama Boss”
Mike wa yayi ya nufi bedroom din sa don a gajiye yake sosai gashi gobe yake so ya wuce Canada…
Khalil yana ganin shigewar sa ya dauki wayar sa ya danna wa Tukur waya, bata dade tana ringing ba aka dauka.
Kofar kitchen ya nufa hannun sa rike da flask din tea din da Ogan nasa ya gama sha ya kara wayar a kunnen sa ya ce “mu hadu a goron dutse Boss ya bada aiki”
MARYAMA
A tsaye take tun lokacin daya shiga cikin part din Mami, yayi wajen 20mins sannan taga ya fito shi da Aisha daga shigar su tasan fita zasu yi, kuka take sosai tana kallon su har zuwa lokacin da Aisha ta shiga motar suka bar gidan, kifa kan ta tayi a jikin windown tana wani irin kuka mai dan sauti.
Me yasa ita komai take so shi Aisha take samu, tun suna kananu a school kowa Aisha kowa Aisha in aka gan ta ma cewa ake wannan yar gidan su A’isha ce ai.
Ga Ya Aliyun ta tun da ta fara wayo take matukar kaunar sa amma shi bata gaban sa gaba daya, sbd shi take shige wa Aisha wai duk sbd ya dinga kallon ta amma ina har ynxu dai ta gaji Wallahi ta gaji, don ta fara fahimtar wani abu game da shi Ya Aliyun.
Rintse ido tayi wani irin tsanar Aisha na kara mamaye zuciyar ta, ko yaushe ita ce a saman ta ko QSA duk yadda ta dage tana shiga cikin friends wai sbd afi sanin ta akan Aishan amma a banza don har a can din juniors in zasu gaishe ta da murna suke gaishe ta sbd ita yar gidan su A’isha ce.
Wani ihu ta kurma tana zubewa a kasa kan tiles, da sauri Mummy ta shigo dakin tana nufo gurin Maryam din da sauri.
Tsugunna wa tayi ta riko kafadun ta ta ce “meye haka kike kuka kamar wacce aka ce miki Daddy ko ni mun mutu”
Cikin kuka ta ce “Mummy baxan iya daure wa ba wallahi, ynxu fa suka fita tare kamar ma zance zasu yi ne ko me ni ban sani ba amma sun ci kwalliya”
Tsaki Mummy tayi ta ce “ynxu don wannan ne yasa kike kukan?”
Fada wa jikin Mummyn tayi tana rike ta sosai ta ce “wallahi in har ban aure sa ba mutuwa kawai zan yi, Mummy ina son sa tun ina karama amma shi hankalin sa gaba daya yana kan A’isha, me Aishan tafi ni da shi da baxai so ni ba?”
Shiru Mummyn tayi kawai bata ce komai ba sai shafa bayan ta da take yi, sai da taga ta dan dawo nutsuwar ta sanna ta ce “na fada miki kar ki damu Maryam, in har Aliyu ne ki sa a ran ki kawai kin gama zama matar sa ke dai kar ki kuskura ki bata mana plan ni da Hajiya, komai a tsare yke ai muma muna da hankali kuma mun san mai shi Aliyun yake nufi, kar ki damu ki cigaba da shigewa ita Shegiyar sbd kar lokacin da komai zai wakana a zarge ki kin ji koh?” Ta kare maganar cike da nuna wani irin yanayi dake bayyanar da dacin da take ji a zuciyar ta.
Cikin farin ciki Maryam ta rungume Mummyn tana sauke ajiyar zuciya.
AISHA
Uncle ya biya kayan muka nufi mota, zama nayi a motar ban ce komai na sai tabe baki da nake yi kawai, abinda kuma yke sani tabe bakın sai kokari nake naga ban tuno shi ba.
Ko da muka isa gida ledojin na dauka nawa Uncle sallama na nufi part din mu da dan sauri.
Sai da na tsaya muka sha hira da Mami da Abba har wajen 11 kafin na shiga daki na don gobe ina da duty da safe.
Da wuri na kimtsa na shirya cikin kayan mu nurses da muke sawa, dogon Hijab na daura akan kayan sannan na dauki jaka ta da key din mota ta na fito, dakin Mami na fara shiga na mata sallama sannan na wuce.
Sai bayan la’asar na fito daga hospital din sanye da Hijab dina dogo da nake sawa in zan je asibitin da kuma in zan tafi gida wannan dokar Uncle ce daya kafa min ita.
Kallon sama nayi ganin hadari ya hadu sosai gashi dazu da nake taho wa mota ta ta samu matsala sai da na kira Sultan yazo ya tare da mai gyara suka wuce da motar don duba mai ya same ta.
Ruwan da naji yana duka na ne ya sani saurin dagowa na kalli jikina, ruwa ake sosai gashi na riga na fito daga asibitin na kuma dan yi tafiya mai nisa don na samu abin hawa, kamar zanyi kuka nake kallon jikina daya kusan gama jike wa sosai hijab din yana manne min a jiki ina dan jajjan sa.
Horn din da aka mun ta baya na wasa ni juyawa, Dr Munnir neh tun da nazo asibitin ya takura mun akan na basa number na shi so na yake da aure, bana kula shi din tun da Uncle ya hana ni kula samari balle ni din bana bukatar su tun da dai zuciya ta a kulle take.
Horn din daya Kara min yasa ni dawowa daga karamin tunanin dana tafi, kallon sa nayi shima kallon nawa yake cikin marairaice wa ya ce “ki shigo na Kai ki gida please Aisha kin ga ruwa ake gashi abin hawan suna wahala a irin area dinnan”
Murmushi na masa kadan na ce “Ngd Dr in na kara gaba wata kila na samu din”
Kallona yayi ya ce “kin ga jikin ki sake jike wa kike kuma is not safe ki dinga tafiya a haka”
Kallon jikin nawa nayi nima, ajiyar zuciya na sauke kawai kafin na nufi motar tasa, kamar na bude back seat na zauna sai dai rashin dacewar hakan dana gani yasa kawai na bude front seat din na zauna.
Gaishe sa nayi ya amsa yana murmushi yana tambaya ta unguwar mu, fada masa nayi sannan naja baki na nayi shiru a zuciya ta ina addu’a Allah yasa Uncle baya gidan.
Har kofar gidan mu ya tsaya, da sauri na kalle sa na ce “Ngd sosai bara na shiga daga nan”
Murmushi ya min yana kallon gate din ya ce “no please ki bari na karasa da ke ynxu in kina fita anan kafin ki shiga daki ma kin gama jike wa gaba daya, bana son kiyi mura”
Kamar zan yi kuka nake kallon sa amma haka ina ji ina gani sai da ya shiga cikin compound din, ido na bai sauka akan kowa ba sai Uncle dake zaune a kan farar kujera daga corridor din dakunan su, gefen sa Sultan ne yana danna waya, amma suna ganin shigowar motar gaba dayan su suka zuba mata ido.
Ji nayi kamar kar na fito, ban san na dau lokaci bama a motar sai da Dr Munnir ya Kira suna na, da sauri na kalle sa ina dan yake daure wa nayi na masa godiya na bude motar na fito.
Nayi taku wajen 5 naji Muryar Dr Munnir yana kira na, Innanillahi wa inna ilaihir Rajiun wallahi ji nayi kamar na kwasa a guje na bar gidan ma gaba daya, ba kallon inda Uncle yake ba nake amma ina jiyo idon sa a kai na.
Sake Kira na da Dr Munnir yayi ne yasa ni juyawa kamar wacce take ciwon wuya, jakata ya miko min yana murmushi ya ce “ko kin bar min ne”
Na ma kasa yi masa murmushi duk kuwa da yadda naso ko yake ne nayi, hannu nasa na karba na ce “Ngd sosai”
Murmushi ya sake min ya ce “sai gobe in Allah ya kai mu, ki kula kar ki yi mura please”
Ni ko kallon sa ma nayi da sauri sauri na karasa part din mu gashi gaba daya na jike hijab din sai manne min yake a jiki.
Rintse idon sa yayi kafin ya bude su ya mike da sauri ya shige dakin sa, Sultan da yke kallon sa tagumi ya buga shima a ran sa yana cewa “yau ba zaman lafiya a gidan nan kenan”
Ni kam jikina har rawa yake na shiga palon mu ban tsaya Jin abinda Mami take ce min ba na shiga toilet, wanka nayi na zira doguwar rigar atampa na daura dankwali har lokacin gaba na faduwa yake yi.
Fito wa nayi nufi wajen Mami, zama nai a kasa na dora Kai na akan cinyar ta kawai na fashe da kuka.
Hannu tasa tana shafa kai na ta ce “me ya faru Shatu?”
Cikin kuka na ce “Mami Uncle ne”
Da mamaki ta ce “mai ya samu Aliyun?”
A shagwabe na ce “Dr Munnir dinnan dana fada miki yana damuna ne ya dawo dani gıda sbd ruwan da ake yi, kuma lokacin da muka shigo Uncle yana zaune yana kallon mu ni ynxu ban san mai zan yi ba”
Murmushi Mami tayi irin nasu na manya ta ce “to sai me don Aliyun ya gan ki, ai yaşan in ba wani dalilin ba baxa ki hau motar wani ba, balle ma shi taimakon ki yayi kamata ma yayi ya je su gaisa ya gode masa”
Dagowa nayi na kalle ta na ce “shi Uncle din?”
Gyada min Kai tayi tana murmushi, bana sake magana ba don da alama Mami bata fahimci abinda nake nufi bane.
Bayan sallar Isha’i ina zaune ina kallo messages ya shigo waya ta, tsoro ne ya kama ni ganin daga uncle ne kamar kar na bude sai dai kuma baxan iya sharewar ba koda nayi niyyar hakan.
“Ki kawo min tea ynxu” abinda ya rubuta kenan a message din, ajiyar zuciya na sauke na mike na shiga kitchen.
Tea din na dafa masa na sannan na nufi dakin sa bayan na saka Hijab gaba na yana faduwa.
Knocking nayi har sau biyar kafin ya bani izinin shiga, da sallama na shiga dakin yana zaune akan kujera ya dafe kan sa da yake Jin yana barzanar fashe wa.
Ganin yadda yayi din yasa ni saurin nufar sa, ajiye flask din na fara yi sannan na zauna a gefen sa a hankali na dora hannu na akan nasa na ce “Uncle baka da lafiya”
Bai magana ba kuma bai kalle ni ba, kamar zan yi kuka na ce “Uncle kayi hakuri Allah ba kula sa nake ba ya dade yana min magana amma ba ruwana tun da kace kar na kula saurayi, yau din ma sbd ruwan da aka fara ne kuma sai da na ce baxan shiga ba amma ya ce is not safe na tsaya a gurin shiyasa”
Sai a lokacin ya dago idon sa da suka yi ja sosai ya zuba min su, kasa kallon sa nayi don haka na saukar da nasa idon hawaye suna wanke min fuska.
Cikin wata murya mai matukar sanyi ya ce “so kike na haukace little?”
Da sauri na girgiza kai ina fashe wa da kuka.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce “na daure iya daure wa, duk wata hanya da zan nuna miki abinda nake ji game da ke nabi amma kamar baki fahimta na, sai yaushe ne zaki gane cewa Ni Aliyu ina matukar kaunar ko Aisha?”
DijahAM
***