Free chapter · Read without an account

Page 14

by Khadija Muhammad · ALƘALAMIN SO

ALƘALAMIN SO



DIJAHAM(OUM AMANI)



Page 14



Saura 1 page In sha Allah free pages su kare😩 ku yi maza kuyi payment kar ayi tafiyar nan babu ku🤾‍♀️🤾‍♀️


In zaku yi payment zaku tura 500 ta wannan account din ***

Khadija Danasabe Adamu

OPay 


Sai ku tura shaidar biya ta wannan numbern

***




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM




  Hidimar biki ake sosai ynxu saura kwana hudu a fara biki, ni dama tun bikin saura sati biyu na dai na ganin Uncle, bana ma yadda mu hadu duk wata hanya da zata hada ni da shi guje wa hanyar nake sbd tsira da lafiya ta tunda ynxu ta kai ko maganar sa ake ji nake kamar numfashi na zai dauke.


Sai rame wa nake yi a tsaitsaye kowa tunanin yake zullumun aure ne kamar yadda dai aka san kusan kowacce amarya tana yi amma banda Sultan, shi kullum cikin magiya yake min akan na fada masa abinda yake damu na, bana iya magana sai dai kawai na ce masa kewar su da zanyi ne yake sani cikin tashin hankali.


Ynxu ma kamar ko yaushe nayi zurfi a tunanin da ban san ko na meye ba ni dai kawai nayi shiru ne ina tunani.


Ringing din da waya ta ta shiga yi ne yasa ni zabura da sauri, ganin sunan Sultan yasa na sauke ajiyar zuciya na dauki wayar na kara kunne na.


Maganar daya fada min ce tasa ni murmushi na mike da sauri na shiga toilet, wanka nayi na shirya cikin doguwar riga sannan na zira Hijab har kasa.


Sanin da nayi Mami baxa ta bari na fita ba sbd gyaran jikin da ake mun ysa na fita ta kofar kitchen, a guje na nufi compound din gidan ban tsaya ko ina ba sai cikin motar da nasan Sultan din ne a ciki.


Kallona yake yana dariya ganin yadda nake ta mayar da numfashi.

 Harara na sakar masa ina tabe baki na ce “baza ka gane bane, nasan in har Mami ta ga zan fita hana ni zata yi shiyasa nabi ta kitchen ma”


Murmushi yayi ya ce “kawai dai so kike ki taba rashin jin kafin rana ita yau tunda sati mai zuwa a irin wannan lokacin kina nan da igiyoyi har uku sun daure ki”


Shiru nayi masa ban ce komai ba gaba na yana faduwa da karfi.


Shima Sultan din bai sake cewa komai ba don ya fahimci tun da ya kawo maganar auren tayi shiru, shi fa kan sa hankalin sa a tashe yake don kwata kwata ya kasa gane kan Aishar tasa, da farko kusan ko yaushe suna tare tana fada masa irin shagalin da zata yi a bikin amma yncu shiru kake ji, ko ya fara mata magana ma sai dai kawai tai murmushi.


Supermarket din da muka shiga ne yasa ni dawowa hayyaci na, gaba nane ya fadi saboda tuno wa da nayi anan ne muka hadu da Mr Black kamar yadda na saka miki a rai na tun da ni dai sau biyu na taba haduwa da shi kuma ko yaushe cikin bakaken kaya yake.


Ban dai ce komai ba har muka fito Sultan yaja hannu na muka hau sama. Gurin da ake siyar da Kayan kitchen ya nufa da ni.


Murmushi yayi ya kalle ni ya ce “zabi flask din da kike so zan siya miki”


Kallon sa nayi da mamaki na ce “kai Sultan yaushe kake da kudin da zaka siya min flask?”


Harara ta yayi ya ce “amma yarinyar nan Wallahi kin rai na ni, to kinga flask din nan daga na 50k har na 80k ki dauka zan biya”


Kara waro ido nayi sosai ina kallon sa da mamaki, murmushi yayi ya ce “ba sata nayi ba atoh kudi nane da nake ta Adashi ynxu na karba ban san irin flask din da kike so bane shiyasa nace zan kawo ki da kan ki sai ki zaba kin ga duk lokacin da kika zuba abinci a ciki zaki ce Allah sarki Sultan shi y siya min wannan flask din”


Dariya nayi sbd yadda ya karashe maganar yana wani lumshe ido, kallon ta kawai Sultan yake ganin yadda take dariya, murmushi ya saki cike da Jin dadi don rabon da ya ga dariyar ta haka an kwana biyu.


Ni da shi muka shiga duba flask din, in na dauko wani sai yace yayi kalar kauyawa mu chanja wani.


Kallon sa nayi na ce “wai Sultan ba kace na zabi abinda rai na yake so ba? To me ysa in na dauki wanda nake so sai ka ce a chanja”


Murmushi yayi ya ce “Aisha ni na ce miki fa ina da kudi, na fada miki adashi na shiga kuma nayi niyya, amma sai dauko wanda suke da karamin kudi kike, ki zage ki dauki wanda kike so yarinya kar daga baya kizo kika cizar yatsa”


Murmushi nayi kawai ban ce komai ba, a haka muka tsaya a kan wani flask guda uku ne golden masu shegen kyau 72k, kallona yayi ya ce “ko ke fah ynxu saura 8k muje na siya miki chocolates da ywa kiyi ya sha har a kai ki dakin Ya Aliyu”


Ban ce masa komai ba sai murmushi da nake masa, first floor muka sauka anan kuwa zage wa nayi na zabi irin wadanda nake so da snacks da yawa ni da snacks akwai amana.


Dauko wata katuwar chocolate nayi na juyo don na wa Sultan magana idona ya sauka a cikin na Zarah.


Ware manyan ido na nayi cike da mamaki da kuma farin ciki na ce “wa nake gani kamar Zarah”


Da gudu ta zo ta rungume ni tana dariya ta ce “ni ce Aunty”


Nima rungume ta nayi ina Murmushi kafin na dago ta ina kallon ta, bawai bamu haduwa bane amma mun dade bamu hadu ba sosai last year ta gama QSA ita ma.


Murmushi nayi na ce “oh su Zarah an zama yan mata irin wannan kyau haka”


Dariya tayi tana dan rufe fuskar ta da mayafin abayar ta tace “kai don Allah Aunty har kin sa naji kunya”


Murmushi nayi mata kawai na ce “kin san dazu da safe nake maganar ku ke da Amina, katin ku yana waje na yau nayi niyyar na bawa Sultan ya kawo miki”


Kallon Sultan nayi da yake ta kallon Zarah yana murmushi, dariya ya bani Ai kuwa na dage iya karfi na na dala masa duka a kafada.


A zabure ya dago yana kallona, harara ya zabga min yayi tsaki ya ce “ke dai Aisha baa abin kirki da ke, ai kin gane mai nake nufi amma don mugunta shine zaki dake ni”


Dariya muka yi ni da Zarah din sai kuma ta saki hannu na ta nufi wajen wasu da ke tsaye.


Gaba na ne ya fadi da karfi hada ido da muka yi da Mr Black, yau ma dai kayan bakake yana sanye da face mask din ka’ida.


Shi ya fara janye idon sa yana tabe baki, ni kuwa bakın ciki da haushin sa kawai naji ina ji wanda ni kai na bansan dalili ba.


Hannun sa Zarah ta kama tana Jan sa ta ce “Uncle ga Auntyn tawa da nake fada maka da QSA, ranar Friday daurin auren ta zan karbo ma kati don Allah ka je”


Zuba mata lumsassun idon sa yayi yana kallon ta, ita kuwa sai marairaice fuska take ita a dole yaji tausayin ta ya ce zai je.


Kau da kan sa kawai yayi ya kika wa Sultan hannun sa don su gaisa, da sauri Sultan ya mika masa nasa yana cewa “ina wuni”


A hankali ya ce “lafiya qalau” yana daura idon sa akan A’isha dake faman hararar gefe, tabe baki Ya’u ya ce gata dai kamar mai hankali amma da alama kan ta da motsi Allah Sarki.



DIJAHAM

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.