Free chapter 路 Read without an account

.

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah 路 SARAUNIYAR KYAU (Book 1)

馃挀*SARAUNIYAR KYAU* 馃挀

      

馃憫 _(The Glam Queen)_ 馃憫

      

  


Sanye yake cikin 茩ananan kaya T-shirt fara da wando crazy Jeans ash color, kansa ba hula, kunnensa 蓷aya manne da 蓷an kunnen barima irin wannan wanda maza suke sakawa na gayu, shi 蓷in cikakken gaye ne mai ji da kuruciya da gayu ga kuma naira.

Cikin sakanin da ba za su wuce uku zuwa hu蓷u ba, ta gama 茩are mishi kallo ta cikin glashin dake fuskarta, kai ba za ka ce shi take kallo ba saboda yadda ta tsare gida. Shekarun shi baza su wuce ashirin da hu蓷u zuwa da biyar ba a iya lissafinta.

Muryarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.

"Hey babe am Sabbir Salis Mai Naira, amma an fi kira na da S.S Gidan Naira."

Ya fa蓷i hakan yana mi茩a mata hannu alamar su gaisa. Hannun nasa take bi da kallo ita ba ta ba shi nata ba, kuma ba ta masa magana.

茒an sosa sumar kansa ya yi ganin ba ta kulashi ba. Sannan ya cusa hannunsa 蓷aya cikin aljihun wando, ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce, "Please beautiful! A ta茩aice dai za mu iya zama abokai?" Ya fa蓷a yana wani kanne mata ido 蓷aya irin na tatattun 拼an duniya.

"Oh da gaske amma saboda me za mu zama abokai?" Ta tambaya ba tare da ta bari sun ha蓷a ido ba, don kuwa sai ya sa ta ba shi eleven 蓷inta ba tare da ta sani ba, da wadnnan shegun idanun nasa.

Murmushi ya yi, "Because you are so beautiful!" Ya ba ta amsa yana 茩ara kashe murya.

Za ta iya cewa ya ba ta dariya wannan kashe murya haka, haka ko mace albarka. Ba tare da ta kuma kallon shi ba ta ce, "Hmmm! I'm Lailah Abubakar Mai Kyau!"

Ta fa蓷a tana yamutsa fuska don ya ta kura mata shi ya sa ta fa蓷a masa sunan Lailah komai ta fanjma fanjam.

"Lailah, wow nice name! Am so Amazed meeting you."

"Me too!" Ta ba shi amsa tana kokarin barin gurin domin kuwa ta gaji da tsayuwar, da sauri ya sha gabanta sannan ya ce, "Sorry ba ki ba ni eleven naki ba?" Ya fa蓷a yana marairaicewa tamkar maraya.

Ganin dai zai tara mata mutane ne ya sa ta ba shi lambar Lailah da yake duka wayoyin har da ma na Haleesarth suna hannunta.

Da sauri ya kwashe lambar data karanto masa cikin dankareriyar wayarsa, don bala'i saboda ya tabbatar sai da ya kira ya ji ko tatan ce ko kuwa, 蓷auko wayar ta yi a handbag 蓷inta ta nuna masa sannan ta ce,"Shi ke nan ko da wani abu?"

Murmushi ya yi ganin ya sama lambarta, ita kuwa Afeefarh ba ta tsaya jin surutun da yake koarin yi mata ba tabar gurin.

Jin an dafa shoulder 蓷insa ne yasa shi jujowa, "Ah Haydar, kai ne ashe."

Murmushi Hydar ya yi sannan ya ce, "To ya an samu nasara ko kuwa?" Ya tambaya yana kallon Sabbir da fuskarsa take 蓷auke da 茩ayataccen murmushi.

"An samu da 茩yar amma fa..." Ya fa蓷a yana dafe saitin zuciyarsa.

"To kai Shar Shar, tunda ka samu Haydar." Ya fa蓷a cikin murmushi sannan ya ci gaba da cewa, "Amma na ji kamar 拼ar uwarta ka ce kana so fa, to ya haka?"

AFEEFARH

苼angaren Afeefarh fita waje ta yi wajen da suka parker motocinsu, tana jiran su Haleesarth.

A ta茩aice dai su Afeefarh ba su suka bar gurin Birthday 蓷in ba sai wajen takwas na dare.

Burin su bai wuce ace daddy bai dawo ba,dan sunsan idan ya dawo kashin su ya bushe..

"Oh my God !! Rashin sa`a cewar Haleesarth Lokacin da security gate man ya wangale musu wagameman gate 蓷in katafaren Gidan nasu,idansu bai sauka Ko`ina ba sai a parking space...

Da Jerin Motocin MISTER MAI 茦YAU da suke a pake suka yi arba. Ko gama daidaita parking haleesarth datayi driving nasu yanzu batayi ba suka fito dukansu.

Palo suka shiga da Mister mai kyau suka fara cin karo yana kaikawa da qaton palon hankali a tashe....

A hankali suka fara taku sa蓷an sa蓷ab kamar mara sa gaskiya cikin palon aikuwa kamar ance mister mai 茩yau juyo sukayi four eyes da afeefarh dama itace a gaba.

Da sauri ya qariso gurin hannunta dake rawa kamar mazari ya kamo.

A hankali ya fara magana kamar mai jin tsoron wani abu ya raba shi da ita shalelensa.

"Shalelena ba abin da ya same ki please tell me. Gaba蓷aya na shiga damuwa na dawo gida bakunan".

Murmushi Afeefarh ta yi tana kara jin 茩aunar mahaifin nata da wannan 茩auna da yake nuna mata da kulawa.

"Ah Daddy karka damu indai ni ce babu abin da zai same ni muddin kana tare da ni lovely daddy, yanzu birthday party 蓷in zahrah classmate 蓷inmu muka je mun yi tunanin bazaka barmu bane shi yasa muka yi satar hanya amma muna ba da ha茩uri our apologize."

"To amma shalele mai ya sa ba ku tafi da guards ba, kun fa san yadda 茩asar nan ta lalace." Mister mai Kyau ya kuma fa蓷a.

"Dad! Mu fa ba ma son hayaniya ne shi yasa ba mu tafi da escort ba."

Tun kafin ya kuma cewa komai ta riga shi da kara fa蓷in, "I need to take shower, na gaji sosai daddy."

Murmushi Mister Mai Kyau ya yi sannan ya ce, "To shi ke nan shalelena, yi sauri ki je ki yi wanka ki huta kin ji?" Ya fa蓷a yana duban inda su Haleesarth suke sai dai me? Wayam babu ba su sun gudu, ya girgiza kai cikin murmushi irin na manya.

Dariya Afeefarh ta yi ta ce "Daddy ke nan ai tun 蓷azu suka shige bedroom nasu ta fa蓷a tana kuma murmushi.

Daddy Bai kuma cewa komai ba ya wuce dining table wajen Matar Gidan Haj. Rafi'at {Mrs Mai Kyau}Sai dai yaranta sun fi kiran ta da Momy Ko kuma Momy Rafi'at, musamman Zaynerb da Afeefarh sun fi kiran ta da haka a matsayinta na kishiyar mahaifiyarsu Hajara da ta da蓷e da rasuwa tun haihuwar Afeefarh.

Momy Rafi'at ta kasance kyakyawar Bafulatana ce kyakyawar 茩arshe ajin farko, ta kasance mace mai son a girmama ta na 蓷aya, ta kasance mace mai son mijinta Mister Mai Kyau fiye da komai a rayuwarta na biyu, ta kasance mace mai bala'in saurin fushi da gaza fahimta kuma ita tana so a fahimce ta na uku, ta kasance mace mai Bala`in iya 蓷aukar wanka da shiga na kece raini domin kuwa sometimes idan ta 蓷auki wanka ta saka mayafi da glass kai ba za ka yi tunanin shekatunta Hamsin da 蓷auriya a duniya ba, tunani za ka yi ba ta wuce 30yrs ba, na hu蓷u ta kasance babu wasu wadnda ta ta蓳a tsana a duniya ko na ce ta tsana sama da Zainab da kanwarta Afeefarh ta tsane su, sama da mutuwarta, sai dai ba ta ta蓳a nunawa ko a fuska ba, tun shekaru goma sha daya" baya da ta yi kuskuren yi wa Zaynerb da Afeefarh dukan mutuwa a kan dalilin da bai kai ya kawo ba, ai kuwa lokacin ta ga masifa da bala'i domin sai da mijinta ya sake ta a lokacin, kuma ya 蓷auki yaransa Zaynerb da Afeefarh ya bar 茩asar da su tsawon shekaru shida sannan da 茩yar aka samu ya dawo, tun lokacin ba ta 茩ara yun茩uri ko gigin sake dukan su ba, sai dai ba wai don tsanar su ta bar zuciyarta ba, a'a sai dai don ba ta so mijinta ya 茩ara sakin ta, domin wancan lokacin da ya sake ta ta sha matukar wahala kafin ya dawo da ita don sai da ta shekara guda cur sannan aka samu ya ha茩ura aka mayar da aurensu.

Shi ya sa take danne tsanar tasu a zuciyarta ba wai don ta 茩yale su ba, a'a 蓷aurin talala ta yi musu ya gama nuna musu 茩aunar.

Da yake tana da katafaren asibiti nata na 茩ashin kanta a tsakiyar garin Abuja, tana aiki a can shi ya sa mafi yawan lokuta take cikin busy da yake asibitin nata Pediaric ne.

Yau ma around 6:pm ta dawo asibiti a gajiye ta sama mijinta Mister Mai Kyau cikin tashin hankali wai ya dawo gida bai ga shalelensa ba hankalin shi ya tashi yake fa蓷a mata.

Abin ba 茩aramim sosa mata rai da ba ta haushi ya yi ba, kawai ba yadda ta iya ne ta danne 蓳acin ranta ta ki kula shi, sai dai abin yana nu茩ur茩usar ta 茩asan rai. To ban da latsinsa ma da rashin son gaskiya, Afeefarh ce ka蓷ai ba ta gidan, ai har da su Lailah da Haleesarth amma Afeefarh ya tuna saboda ita ce 拼ar gold sauran ko oho.

Da ta gaji da abin nasa bayan ta yi wanka ta shirya cikin jallabiya ruwan madara da mayafi shi ne fa ta fito palon 茩asa inda yake tsaye har yanzu, ba ta kula shi ba ta karasa ha蓷a蓷蓷en dining room ma'aikata suka yi serving nata ta fara cin abinci hankali kwance.

Tana nan zaune Afeefarh suka shigo palon kuma tana jin duka abin da suka tattauna sai dai ba ta kula su ba, har Mister Mai Kyau ya dawo dining room 蓷in ya zauna cikin washe baki.

Ma'aikaciyar ce cikin rawar jiki ta fara kici-kicin serving 蓷insa, ai kuwa cikin zafin nama Momy Rafi'at ta yi saurin mi茩ewa tana mai daka wa 'yar aikin tsawa a kan za ta yi serving mijinta abinci abin da ko da gigin wasa ba su ta蓳a ba, tana mata tsiya dan bala'i gefe guda kuma tana antayawa Afeefarh da za ta wuce ta side 蓷in hararar tsana.

Ita ma Afeefarh ba ta kuma magana ba ta nufi bedroom 蓷inta ko kula momy Rafi'at da ke antaya mata harara ta gefan ido ba ta yi ba.

KANO

Da gudu ta shigo bedroom 蓷in tana 茩wala wa Jieddarh kira, "Jieddarh, Jieddarh. Ke Jieddarh!" Hango ta ta yi saman gado ta yi 蓷ai-蓷ai tana 茩wasar barci.

Da sauri ta hau kan bed 蓷in tana kiran sunanta, "Jieddarh ki tashi takardar ki ta fito nan da wata 蓷aya za ki fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin Jaha.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.