Free chapter · Read without an account
3
________Wallahi har gaba na ya faɗi na zaci wani abu ne ya sameta" ce war Humaira.Dariya Baba Delu tayi ta ce"oh-oh-oh Allah mai haɗa ƙauna,babu abinda zance muku wallahi sai godiya dan ni duk mai ƙaunar Lube to kuwa kaf duniya ba ni da kamarsa,Allah ya yi albarka ƴaƴan nan" amin Baba, kawo flask ɗin mu je gidan in haɗa miki tea ɗin" Humaira ta faɗa tana ware mayafin abayar da ke kanta.
Ƙarɓar flask ɗin tayi Baba Delu na ta faman sa musu albarka, suna fita Zayyad ya koma ya sauya kaya dan wandon police ne jikinsa da belt ɗinsa mai symbol ɗin .D.S.S.
Gidan Baba Delu a hargitse babu abinda tayi ,Humaira ta haɗa mata shayin ɗumamen tuwonta ta ɗauko tana faɗin "ni fa idan ba ɗumame na ci ba sai inji tamkar ban ƙarya ba, yo Allah na tuba daman ruwan kunu da ƙosai ina zai ɗauki bawa.
Humaira ta ce" ko dai ulcer ce da ke Baba kin karya kumallo ɗazu yanzu ma ki ce yunwa"
"Ke ƴar nan dakata banason wannan jaye-jayen naku na ƴan birni meye wani olsa kar ki ƙara jawo min cutarku ta zamani" dariya Humaira ta yi tana faɗin" an daina Baba" ta miƙe tana faɗin " na tafi sai anjima" Baba Delu ta ce" sauka lafiya a gaishe min da maigidan da babu awo ba cefane" Humaira ta ce" kai Baba baki ga aiken da ya kawo ba cikin trailer hahhhh" Baba ta ce "uhmm nagani kam" Humaira ta fita tana jin daɗin zama da su Baba Delu.
Turus tayi ganin Zayyad tsaye da alama fita zai yi ta ce" ba dai ka gama breakfast ɗin ba?" ya ce" shago zan je costumer's ne suke jirana,yanzu zan dawo" ta tsare ƙofar tana faɗin " ni bansan meyasa ka ɗauki wannan kantin da mahimmanci ba, abinda ko Mu'azu mai gadi ba zai yi ba sanin ya fi ƙarfin ƴar trader amma ka dage akanta abinci ma neman gagara ci yake maka" Ganin yanda ranta ya ɓaci yasa ya matsa gareta yana langwaɓar da wuya ya ce" to banda abinki ke da kike shirin tafiya Kano da kike ta faman wannan maganar idan yau kin matsa min na ci gobe waye zai matsamin?" Humaira ta ce"ni dai mayi maganar daga baya amma yanzu dan Allah mu je ko tea ne kasha please" ta faɗa tana mai haɗa hannuwa irin na Indian culture.
Dole ya koma sukayi breakfast din tare, sannan ya bar gidan, shagonsa ya bud'e bayan sun gaisa da mutanen da ke wajen.Wasu motoci ne guda biyu new design, black colors masu tinted windows suka wuce, tsawon wata bakwai da zuwansa Gulu bai taɓa ganin irin motar ba. Samarin da ke gurin ne suka fara magana akan wannan motocin "ina ga fa Musaddik ne ya kawo ziyara" ɗayan ya ce" shi ne ma kasan shekara ta yi, kasan kaf garin nan babu wanda ya kai shi noma shinkafa, ka rasa me yake a birni da ya zama haka lokaci guda malam, ka tuna satar agwagi fa yake shine Maigari ya kore shi,amma mutum bai tashi dawowa ba sai da ya zama wani hege a gari Allaji" Zayyad da ke tsaye yana jin hirarsu, sai ya kuma juyawa dan ganin motocin amma bai hango su ba,cikin shagon ya shiga yana ɗauko wayarsa ya shiga buncike da sauri-sauri.
"Akwai katin waya Malam Zayyanu?" da sauri ya ɗago yana sakin fuskarsa ya ce"akwai Ɗanliti ya garin?" Ɗanliti ya ce" alhamdulillah da alama yau akwai sa'a tunda naji ana Musaddik ya shigo" Zayyad ya ce" waye haka kuma?' Ɗanliti ya dara yana jinjina kai sannan ya ɗan jingina ya ce" ai Malam Zayyanu tare muke da Musaddik tun yarinta, sai ya fara sace-sace yana haura gidaje, ga satar agwagi da kaji ba dama kiwonka ya fito sai ya sace ya kai kasuwa ya siyar, ya addabi jama'a shi ne aka koreshi daga garin, bai tashi dawowa ba Malam sai da ya zama mai kuɗin birni, kasan gonar nan ta can wajen gangare?" Zayyad ya ce" eh nagane ta wacce baa hango kunyar ƙarshe ko wannan mai duhu-duhun ko?" yauwa ita to kaf sai mun nome masa ita da shinkafa kuma ba zai ƙara zuwa ba sai angama girbi ya zo ya gani ya sallame mu wasu motoci manya su zo su kwashe akai kamfaninsa a gyarata ya yi kuɗi sosai fa" ce war Ɗanliti.
Zayyad ya ce "Allah sarki ya taimaka, na nawa zan baka recharge card din?" Bani Ɗan dari jan zaka ba ni" Zayyad ya ɗauko airtel ya ba shi, ya ci gaba da tura saƙonsa...
Washegari bayan an gama yi wa Amarya jere, kowa ya yaba da kayan amarya.Lube da Mara suka kamo hanya dan komawa gida "Zaki je allo yau?" Mara ta tambayi Lube,cikin hassala ta ce"ba zaa je ba ke wai dole sai kin ɓatawa mutum rai ne to ni na cire kaina" Mara ta ce"ni banason tahin hankali Allah ya baki haƙuri" Tusa Lube ta shiga bugawa, mai ƙara gami da wari.
Mara da suke tafe sai toshe hanci take tana faɗin Allah ya isa. Ba damar yi a fili yanzu sai Lube ra bata kashi dan angama morar junan tunda biki ya ƙare, Lube ta washe baki tana dafa kafaɗan Mara ta ce" kinsan me ni fa alkur'an auren nan nake so, dan Allah gidan yaya Sailuba bai burgeki ba?" Mara da tafi ta hankali ta ce" tab ni aradu babu wani abun burgewa iskanci fa ake a auren ko kin manta abinda su Aliya suka dinga faɗa da aka je da mu kai mata kayan gara?" Lube ta yi shiru tana tuno labarin da Aliya ta dinga bawa ƙawayenta sukai ta shewa gami da dariya.
Lube ta ce" ke dallacan ai ita ɗan iska ta aura shiyasa ni ko babban damuwata ma bansami wanda nake so ba tunda kinga Baba Delu ta damu nayi aure shi kuma Baban na yana son nayi karatun muhammadiyan nan dan Allah ba gara auren ba?" Mara ta kai mata duka tana faɗin" hegiya Lube ashe kina son auren idan Baba Delu tayi magana ki tura baki gaba wai irin baki ƙauna ɗin nan hahhhh" Lube ta yi dariya ta ce" bakiga yanda Sailuba tayi kyau ba a kwana ɗaya tal da aure ba, kinga fa kayan da aka kai mata ga robobin nan masu murfi da randunan birni kala ɗaya, ga katifarta sabuwa kuma anyi mata wankan inji ta zama fara" ta shafa fuskarta ta ce" nima ko dan na zama fara ai nayi auren nan dan natsani wannan fatar tawa baƙa mtsw" ta yi ƙwafa Mara ta ce" ke ba fa dole sai anyi wankan inji ake zama fara ba, ana sai da wani mai a burni ki tambayi wannan matar ta birni maƙotanku mana ta faɗa miki sunansa sai mu siyo, ƙila ita ma shi take sawa naganta fara tas kamar Balarabiya kuma nasan da ƙyar idan ba shafawa take ba" take kuwa aka yanke shawarar haka zaa yi.
A mararraba suka rabu Lube tayi kudu Mara tayi arewa dan komawa gidajen iyayensu.
Hango shagon Zayyad a buɗe tayi take zuciyarta ta raya mata zuwa fara tambayar shi ko yana da man fari. "Yaya Zayyad hannu dai" ta faɗa tana sosa kai tayi wujiga-wujiga da ita ko wanka ba su yi ba, ɗagowa ya yi yana kallonta cikin datti ya ce" ba ki iya gaisuwa ba ko Lubna?" kama baki tayi na ce"lahh na manta shaf alkur'an, Ina kwana,gidan ya kwan lahiya" Kai kawai ya girgiza ya ce" me za a baki?" Ta ce" uhm dama ko Mara ce ta ce min wai ana sai da Mai wanda zan zama fara nima shi ne na ce ko kana saidawa tunda kaima daga birni ka zo" Dalla yi min shiru, uban waye ya ce miki ana sa mai a yi fari?" cikin taɓara ta tura baki gaba ta ce" to ai Mara ta sani ita ta faɗi min fa" ganin ba ta da saiti ya sa ya sauko in a cold voice ya ce"ayya ba ki ji daidai ba, babu wani Mai da ake sawa a yi fari, banda abinki ma me zakiyi da fari?" Caraf ta d'auke maganar "Kai Yaya Zayyanu baka ga yanda Yaya Humaira ta koma ba kamar Balarabiya ba, Kuma ai Mara ma fara ce,ni ce kawai baƙa fa ai ta yi min dariya" ƙwalla ta cika idanunta.
Ta shi ya yi yana jin daɗin yanayin da suke murmushi ya yi yana zagayowa ya fito daga shagon ya ce" to ai skin ɗinki ita ce natural skin Kuma tafi kyau da tsada banda abinki ma kin fi su kwari da juriya, Kar ki ƙara bari wata ta ce ki shafa komai idan kuwa kika yi zaki koma Mai cutar kuturta" cikin razani ta dafe ƙirji ta ce"kuturta!? ya gyaɗa kai ya na mai ƙara tsoratar da ita akan hakan.
Unexpected ta ce" Amma ai Yaya Humaira ba kuturwa ba ce ba kuma Affan ma fari ne ba kuturu ba ne ba" haɗe rai ya yi ya ce" fitar min daga shago sokuwa kawai angaya miki su irinki ne Baƙa da ke zaki fita ko sai na buge ki?" tsawar da ya yi mata ce ta tsorata ta.
Ɓare baki tayi ta sa kuka ta fita da sauri ta yi gida.
Ihunta Baba Delu ta ji, da hanzari ta tashi tana faɗin" innahu min sulaimana wa'innahu bismillahirrahmanurrahim, ya ya aka yi"
Lube ta ce" ba Zayyanu ba ne dan naje shagonsa tambaya ya ce min Ɓaƙa daddawa" Baba Delu tunda ta ji an ce Zayyad ta san ba maganar zuwa yin tijara tana ganin girman yaron sosai.
Ta ce" shi Zayyanun da kansa dan yagansu farare to haka Allah ya yo ki kuma haka yake son ganinki,kowa ya raina tsaiwar Wata to ya hau sama ya gyara,ina ganinsa mai hankali" Lube ta ce" ki zo muje ki rama min" Baba Delu ta ce " zo zauna ki gayamin me yasa kika je shagonsa me za ki siyo?" tusa ta danno mai ƙara da wari ta na hura hanci.
Baba Delu ta kamo bakin zani ta toshe hanci tana faɗin" maza ɗauki buta ki zaga kar abu ya kume miki a ciki"ganin yanda Baba ta toshe hanci ya ƙara ƙular da ita, aikuwa ta hau bori. Da ƙyar ta lallasheta sannan ta ce zata sa a kawo mata man indai akwai shi, fari sai ma ta sanwa wani(da ke ana haka a garin nasu na GULU lolll🤪).
GIDAN GANDU
Gida ne wanda ya tara mata da yawa ma'ana faccaloli da kishiyoyi, gami da tarin ƴaƴa masu yawa, asalin gidan gado ne wanda mahaifinsu Ali ya mutu ya bari, Baba Sa'idu shi ne Babba, yana da mata Adama da ƴaƴa guda biyar maza uku mata biyu, Ɗan asabe shine babba ya yi aure shima ya yanki fili ya gina nasa sashin, sai Manu wanda yake saurayi ne sai Zainab da Suwaiba duk sunyi aure a wani gida daban.
Mai bi masa shine Baba Lawan yana da mata Karima da ƴaƴansa Aliya wacce tayi aure, sai Fatima itama tayi aure,saura Saratu da Lawisa sai Azima Halifa(Umar). Sai Baba Rabe da mata biyu Abu da Laure da ƴaƴansa Uzairu,Yunusa,Habu,Hamisu,Amina, Hafsa Usman sai auta Haruna, kuma har yanzu basu daina haihuwa ba. Sai Ali mahaifin Lubabatu wanda ya auri Maryama wacce take a Rimin gado, shekara bakwai da rabuwarsu ada duk tare suke a cikin gidan nasu, har mahaifiyarsu wato Baba Delu, tunda aka auro Maryama ta ke fama da faccaloli kasancewarta ƙaramar yarinya cikinsu, mace ce mara son hayaniya, mijinta Ali ba mazauni ba ne ba, yakan tafiya gari-gari neman arziki mutum ne mai neman nakansa.Duk inda yaje bai yarda noma ba da zarar damuna ta faɗi zai dawo dan yin aikin gona ya sami amfani ya barwa iyali ya koma nemansa, haka Maryama ta rayu tsawon shekara biyu a gidan Gandu, lokacin da ta sami cikin Lube babu irin abinda baa ce ba har ce wa ake ba cikin Ali ba ne, duk ba babu inda take zuwa kullum tana gida tana hidima wa Sirikarta Baba Delu, zuciya na son mai kyautata mata, hakan sai ta zama suruka mafi soyuwa a wajen Baba Delu, ganin irin wahalar da take a gidan ya sa Baba Delu ta tashi ƴan hayar da ta sa a gidanta wanda ta samu sanadin tumunin takaba ta ce su koma can ita da Maryama domin goyon ciki, haka akaita surutu da cari akan haka, Maryama ta koma can da zama farkon zaman nasu abun shaawa, ranar da abun ya fara lalacewa zuwan wata mata ƴar me ganye garin, Zainabu ƴar Baba Adama ba lafiya akai kaita wajenta da niyar magani, ƴar me ganye na ganinta ta ce mayya ce ta kamata kuma mayyar a jikinsu take, hankali ya tashi, gidan gandu ya hargitse kowa tana tofa albarkacin bakinta, Baba Delu ta dinga sirfa zage-zage tana an auro musu annoba ko wace ce sai ta sakar mata jiki.
Maryama da ke gida tana fama da naƙuda bata san abinda ke faruwa ba.
Ƴar maigaye ta zuba wuri ta shiga surutanta na hauka ta na ɗagowa ta ce" Baba kina tare da mayyar ai kuma ke take hari bayan ta gama da wannan" take wajen ya ɗau salati Adama ta ce"ko shakka babu Maryama ce mayya dan ita ce baƙuwa a cikinmu" take kowa ya amince da hakan, ciki kuwa har Baba Delu.
Haka sukayi zuga guda zuwa gidan Maryama halin da suka tarar da ira ciki yasa Baba Delu sallamarsu, suna faɗin "ba za su yarda ta haifo musu jaraba a dangi ba" sai da ƙyar ta sa suka saurara Maryama ta sauka lafiya, ana ta faman turara mata tureren mayu.
Babu wacce ta ɗauki jaririyar da aka haifa sai Baba Delu take ƴar ta shiga ranta, ita ta gyara maijego da jariryarta tana ta faman "faɗin innaka mayyatuna wa innahu mayyatun, namana ɗaci garai ba ki iya taunashi.Tun Maryama bata fahimta ba har ta gane da ita ake.
Duk abinda Ali ya bari na haihuwa Baba Delu ta hana ayi banda yanka babu abinda aka yi wa Maryama, tun daga lokacin tsana da tsangwama ta ke fuskanta ga kowa baga dangin mijin ba baga surukarta ba baga mutanen gari ba.
Da nono ma suka hana ta bawa ƴarta saboda maita, Maryama tayi kuka tamkar ranta zai fita, sai da aka samu masalaha ana haɗawa Lube da nonon Jaka dan gudun kar ta tsotsi maita a nonon uwarta, da Ali ya dawo ya yi baƙincikin wannan ƙazafi da aka ɗorawa matarsa, sai dai yayi ta lallashinta tana faɗin babu komai watarana gaskiya zatayi halinta.
Baba Delu ta dinga muzgunawa Maryama Lube kuwa haka aka dinga faman ɗura mata magunguna kar ta gado maita, har Zainabu ta warke Maryama bata fita daga zargi ba. A haka har Lube tayi shekara shida.
Ranar da ta zama ranar baƙin ciki ga Maryama.
Goshin magriba tana kwasar tuwo, Baba Delu ta fito ta dinga masifa akan sai Ali ya rabu da matarsa.
Kuka Maryama ta ke tana ba da haƙuri Ali kuwa baya ce wa komai sai kwallah da yake sharewa, "kalle ni nan Ali" ce war Baba Delu, cikin biyayya ya kalleta ta ce "me ne matsayina a gurinka?" ya ce" ke mahaifiyata ce" ta ce" in dai ni na haifeka ina so ka saki wannan baƙar mayyar mu huta da cututtukan da ake bin zuria ta da su, ana neman mai da Malam Isuhu mai yankakken baya" Dan Allah Baba ki yi haƙuri, wallahi ni ba mayya ba ce kinsan zuri'ar gidanmu ba mu da gadon maita" ce war Maryama cikin tsananin tashin hankali.
"a'a a'a ni bansan asalinki ba dan haka dole ki bar zuria ta, ba da kai nake ba ne Ali ko ban isa ba?" ta ƙara da mai da magana ga Ali.
Zuciyarsa na zafi ya ce" Maryama ki je ki gida na sake ki saki ɗay...."Uku za kayi mata dan bantan ubanka rabuwa ta har abada nake so kuyi" ce war Delu.
"Baba haramun ne saki uku lokaci ɗaya ki yi haƙuri dan Allah" ce war Ali, " ni zaka faɗawa haka to uku na ke so ko in ɗaga maka nono ka bi duniya idan ya so na yafe mata kai" jiri-jiri ya fara gani murya na shaking ya ce" na ƙarasa sauran igiyar na sake ki uku"
"hahhhh Allah ya yi maka albarka ɗan halal, tashi ki ƙara gaba a je abi wani sarkin kuma kar ki sake ki ɗaukar min jika, ni nan zan kula da ita algunguma munafuka haka kamar ta Allah maza-maza ki bar min gidana" Ali zai koma ɗaki "ina zaka je zo nan shiga nan ba za ka shiga ba sai ta bar gidan nan alkur'an" a dole ya juya ya shiga ɗakin Baba Delu, a daren Maryama ta haɗa kayanta ta fita tana kuka,hakama Ali yana ta share hawaye Lube kuwa da ta jima da yin bacci bata san abinda ke faruwa ba. Wannan kenan.