Free chapter · Read without an account

15

by Ameera Adam · UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA

*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*


      ©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

  

 SHAFI NA SHA BIYAR


*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*

*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*

*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*

*Saiwowin tsumi*

*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*

*Saiwowin matsi gangariya*

*Original gadalin mata*

*Ƴaƴan gadali na asali*

*Original gumba*

*Tsumin Saiwowi*

*Tsumin kwakwa da Dabino*

*Igiyar alkairi*

*Zumar goran tula*

*Hakkin daka na musamman na asali*

*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.

*Akwai bridal package*

*Mai jego package*

*Ƴar gata package*.

*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*

*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*

*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*

*****

*Iyah Basiru na gaisuwa*😅


  Jafar na shiga da ya ga a halin da Mami take ciki turus ya yi, da sauri ya juya cikin damuwa ya dubi Uwani ya ce. "Maza ki shirya ta za mu wuce asibiti." 


 Uwani da ke gimtse dariyarta ta wuce sumi-sumi kamar sabuwar munafuka ta ƙarasa wurin Mami da ke sharɓe a ƙasa. 

 Baba tsoho shi da Lado dama tuni suka fito harabar gidan, suna nan tsaye Jafar ya fito abin duniya ya dame shi.

 "Kai Jafaru, wai ya aka yi ƙadangare ya shiga har banɗakin mahaifiyarka? Ko dai ture aka yi mata?" Jiki a sanyaye Jafar ya ce, "Wallahi Baba tsoho ban da masaniya, ka na gani dai kune kuka kira ni ina ɗaki." Daga haka gabaɗaya suka yi jigum-jigum.


 Abin ka da mai ƙiba Uwani da ta ɗago Mami sai dai ka ji ta sake komawa sharaf, kuma har lokacin idanun Mami a rufe suke. Da ƙyar Uwani ta samu ta ja Mami a ƙasa kamar rago, ta ƙarasa da ita bakin gado tana zaunar da ita a kai ta sake tafiya sharaf, kayan da ta gani a gefe wanda Mami ta ɗauko za ta sa su ta fara dubawa. Rigar maman Mami ta ɗauko ai kuwa Uwani tana ɗaga wa ta faɗi a wurin tana ƙyaƙyata dariya saboda girmanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe ta fara kiciniyar saka wa Mami. 

 Da ƙyar Uwani ta samu ta shirya Mami sannan ta leƙa waje ta kira Jafar, yana zuwa nan take ya kama Mami ita ma Uwani ta kama ta suka fita ita. A kujerar baya suka saka Mami, Jafar ya kunna motarsa suka wuce asibiti. Suna zuwa asibiti da sauri aka karɓi Mami aka shiga da ita, aka fara ba ta agajin gaggawa. Sai da Jafar ya ga Mami ta samu bacci sannan ya samu sukunin kiran Daddy ya sanar da shi halin da ake ciki, a nan take yake sanar da shi yana hanyarsa ta dawowa.


 Lokacin da Mami ta farka gabaɗaya iyalanta na wurin, Daddy ne ya matsa gaban gadon ya fara yi mata sannu. Da wani irin kallo take bin sa ta yunƙura ta cukumo wuyan rigarsa a zabure tana faɗin. 

  "Wallahi ba zan aure ka ba, ni ina da aure har da 'ya'yana!" Da sauri Daddy ya riƙo ta, Mami ta ɗago kai tana ƙare masa kallo sai gani suka yi Mami ta sake tafiya luuuu a sume. Har rige-rigen fita kiran Likita suke yi, babu jimawa Dr Nura ya shiga cikin shigarsa ta likitoci. Sai da ya gama jin bayaninsu sannan ya ce gabaɗaya su fita, don yana son ba ta kulawa babu buƙatar hayaniya. Daddy ya so zama don ciwon na Mami ba ƙaramin tsoro ya ba shi ba amma Dr ya ce ya fita.


  Wata allura ya yi wa Mami ba ta fi minti ɗaya ba ta sake farfaɗowa, tana daga kwance ta ga Dr Nura tsaye a kanta cikin fararen kaya ga farin gilas maƙale a idonsa. 


 "Wato wannan karon rikiɗe mini ka yi zuwa wannan surar kenan? Wannan fa idan ba da gaske na yi na ƙwaci kaina ba sai ya illata ni ya cuci iyalina." Duk waɗannan maganganun Mami na yin su a cikin zuciyarta ne, ta dai kafe Dr Nura da kallo ko ƙiftawa ba ta yi. Ta fara motsa baki a hankali tana biya Ayatulkursiyyu.


 "Sannu Hajiya! Yanzu yaya kike jin jikin na ki?" Dr Nura ya tambaye ta yana gyara tsayuwarsa. A hankali ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan dafe kanta, cikin shammata Mami ta suri dogon ƙarfen nan da ake maƙala ledar ƙarin ruwa a jiki ta shiga zungura masa tana kwaɗa masa. Idan Mami ta karanta Ayatulkursiyyu ta tofa masa sai ta ɗaga ƙarfen ta ba shi ƙwal.


 Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar ɗakin yana faɗin.

 "Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa ƙarfen tana faɗin.


 "Wato don ubanka har surar Nasara kake rikiɗewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya taƙarƙare cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient ɗin nan za ta halaka ni." 


 Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su buɗe ƙofar, sai dai da yake Mami na jingine da ƙofar tana jin alamun za a buɗe ta sake danna ƙofar da ƙarfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya faɗa ƙarƙashin gadon asibitin, da ƙyar su Daddy suka turo ƙofar suna ganin ta da ƙarfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya murɗe hannun Mami ya karɓe ƙarfen ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce.


 "Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?" 


 Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga ɗakin, glass da takalmansa kusan lokaci ɗaya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar ɗakin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya ɗebi abin sa.


 Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana faɗin. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar ƙaramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru. 


 Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar ƙadangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin banɗakin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su kaɗai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na rakuɓe a gefe ta yi zuru tana ƙarewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zuƙe a wuni guda, suna haɗa ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe.


  Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da ƙyar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata ƙarin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko kaɗan ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ɗebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta ƙi yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta.


 Su Shukra sun ɗauki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya ɗauki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya ƙissima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a ɗaura musu aure. 

 Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ƙofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara faɗuwa a hankali ya yi ta maza ya ƙarasa jikin gate ɗin ya fara ƙwanƙwasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta.


 "Waye nan?" 


 "Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya miƙa masa mukullin motarsa ya ce.


 "Shiga ka tuƙo motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya daɗe ni da ko mashin ban iya tuƙawa ba, ina ni ina tuƙa mota?" 


 "Lado amma gidan nan ba ku kaɗai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da ƙarfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce. 

  "Ranka shi daɗe naka ai mai sauƙi ne." To yau dai in faɗa maka tik da ka sani haka ƙadangare ya tarfa Hajiya tumɓur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gabaɗaya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka taɓa jin ƙadangare ya auri mutum? Wai ƙadangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka taɓa ganin ƙadangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana ƙadangare? To ɗazun nan sun zo ɗiban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta faɗa mini." Take cikin Salim ya sake kaɗawa, ganin ya ɗan fara ja da baya Lado ya ce.


 "Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har ƙadangare zai auri Hajiya ni waye da ƙangaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta murƙushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa ya ce. 


"Ranka shi daɗe ina za ka je ne? Ka shigo ka ɗauki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta. 

 "Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a ɗaukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri.


 Da zuwan su Mami Kura ba a ɗauki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gabaɗaya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta.


 Sannu a hankali jikin Mami yake ƙara samun sauƙi, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Alƙur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gabaɗaya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba.


 Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da ƙyar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar ɗaki da Daddy, ita ta koma ɗakin Daddy shi ya koma ɗakinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga ɗakinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lallaɓa ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta.


  Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sauƙi. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi.


 Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan ɗaurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano. 

 Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra ɗaki.


 "Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan ɗin da na shirya ya wargatse. Kin san dai matuƙar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce. 


 "Hanya ɗaya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai." 

"Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce. 


 "Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri. 

 "Sata kawai za mu laƙa mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu kuɗi masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi ƙasa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci ɗaya suka saki dariyar samun mafita.


 Suna gama tattaunawa Mami ta ɗebo damin kuɗin ta damƙa wa Shukra, Shukra ta ɓoye su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da ƙawarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan ɗin su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau ɗaya Shukra ta taɓa shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu.

 Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta rangaɗa daga cikin ɗaki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo ɓangarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta ɗan saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma ƙawata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana ɗaya da har Shukra ta sakar mata fuska, a sanyaye ta amsa mata sannan ta wuce kiran da aka ce Mami tana yi mata. Uwani na fita Shukra ta faɗa ɗakin Uwani bayan da Fatima ta fita yin alwala, ta janyo drowar madubin ta saka kuɗin a ciki ta mayar ta rufe. Ba su wani jima sosai ba suka fice daga ɗakin bayan Fatima ta idar da Sallah, a ɓangaren Shukra dama kuma buƙatar maje Hajji Sallah tun da buƙatarta ta biya ba ta ga amfanin zaman nasu ba.


 Uwani na zuwa ta samu Mami a falo ta tsugunna har ƙasa, a lokacin Mami zaune take da matan Baba Mustafa sai ƙawarta Hajiya Falmata.


 "Uwani ku je ke da Auta ki taimaka mata ku ciro mini wayata ta faɗa bayan gado." Babu musu Uwani ta yi wa Auta magana suka shiga ɗakin Mami, sun sha wahala sosai kafin su samu damar ɗauko wayar tun da can ƙarshen gado ta faɗa. Abu ɗaya ne ya tsaye wa Uwani a rai, a iya sanin ta tun ranar da ta zo gidan Mami ba ta taɓa saka ta aiki tare da Auta ba. Amma sai ta sa a ranta ko don ganin mutane ne ya sa Mami ta yi hakan, don kar a ce har yanzu ba ta ƙaunarta.


 Wurin sallar Azahar bayan Mami ta yi sallah ta fito falo ta fasa kukan an sace mata maƙudan kuɗin da Daddy ya ba ta ajiya har kimanin raina miliyan biyu da rabi, nan da nan hankulan mazauna gidan ya tashi. Dada na jin haka ta fara sababi rai a ɓace.


 "A gaskiya ni kam idan aka kwashe kuɗin nan an cuci Mamman, saboda Allah a tara mutane domin harkar arziƙi su ɓige da harkar tsiya? Shi dai ɓarawo bai ji daɗin halinsa ba, ba don sai Hajji zan je Saudiyya ba da babu abin da zai hana na kai ƙarar ɓarawon nan wurin Ubangiji a ɗakin Allah ba."

  Haka dai kowa da abin da ya dinga faɗa, daga ƙarshe aka ce su waye suka shiga ɗakin Mami a ranar su za a bincika, nan take aka bada shedar Uwani ce da Auta suka ɗauko waya. Kiransu aka yi aka tambaye su kowacce ta ce ba ta ga kuɗi ba, Mami ta bada shawarar a duba ɗakunan kowaccensu, haka aka kasu gida biyu wasu suka yi ɗakin Auta wasu suka wuce ɗakin Uwani. Falonta aka fara dubawa har da ƙasan kujeru, sannan suka wuce ɗakinta, masu duba drower saka kaya na yi, wasu kuma har da leƙa ƙarƙashin gado suke. Kwatsam ana duba drower madubi sai ga kuɗi, nan take mutane suka ɗauki salati. Aka wuce wurin Mami da kuɗi, saboda tashin hankali Uwani jikinta har karkarwa yake yi.


 Duk yadda Uwani ta so fitar da kanta abin sai ya gagara, ta yi kuka ta yi rantse-rantse babu wanda ya yarda da ita. Hatta Dada a wannan karon ba ta yarda da ita ba, Uwani ta rarrafa gaban Dada tana kuka cikin takaici Dada ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗa ta gefe. Daddy ne kaɗai da ya zo ya lallashi ta, a ransa yana wasu-wasin wannan abin da ya faru. 


 Lokacin da Jafar ya dawo ya ji labari ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, nan take kuma Mami ta birkice a kan sai Jafar ya saki Uwani a cewarta ba za ta zauna a ɓata mata tarbiyyar yara ba. Shi kuma Daddy ya sake jaddada wa Jafar umarninsa na ko bayan ransa bai amince ya rabu da Uwani ba.


 Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Uwani don haka ta koma sashenta, ta faɗa kan gado ban da rusar kuka babu abin da take yi. Lokacin da Jafar ya shiga ya same ta kallon tsana ya wurga mata sannan ya ce. 

 "Wallahi ni dai an gama cutata, a ce wai matata ta rasa wa za ta yi wa sata sai mahaifina, me aka rage ki da shi ci ko sha? Ƙanƙanuwar yarinya da ke ko a ina kika san kuɗi da har za ki sa hannu ki kwashe miliyan biyu da rabi. Ni kam na yi dana-sanin aurenki, ni dai aurenki wallahi bai amfane ni da komai ba sai tsiya. Ya zame mini dole na yi gaggauwar auren Safna, don ba zan zauna ɓacin rai da takaicinki ya kashe ni ba. Shashasha ɓarauniyar banza da wofi." Jafar ya yi tsaki ya fice daga ɗakin. 

 Uwani ta ci kuka kamar babu gobe, tana nan ɗaki Auta ta je ta same ta.


 "Uwani Allah Ya sani har yanzu ba na jin ke kika ɗauki kuɗin nan, tare fa muka yi komai muka gama." Rai a ɓace Uwani ta ce. "Auta fice mini a ɗaki kada na sauke fushina a kanki." 

"Don Allah ki saurare ni kada ki yi mana jama'u..." Cikin tsawa Uwani ta katse ta. 


"Ki fice mini a ɗaki na ce." 

Auta ta tsorata sosai da yadda ta ga Uwani ta birkice lokaci ɗaya, bayan fitar Auta Uwani ta fara nazarin shigowar Shukra da kiran da Mami ta yi mata. Murmushi ta saki ta share hawayenta a fili ta furta.


 "Wallahi wannan ƙwallar da na zubar ba za ta tafi a banza ba. Ni Uwani za ku laƙa wa sharri, ai ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Daga haka Uwani ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta, ta koma can sashen su Mami. Yadda mutane ke bin ta da kallo ita ma Uwani sai ta murje idonta ta fara bin su da kallo, hatta Dada fushi take yi da ita don haka ita ma ta yi kamar ba ta san da Dada a wurin ba. Duk in da Uwani ta gifta sai dai ka ji ƙus-ƙus na tashi. 

 Auta ta nema ta ba ta haƙurin abin da ta yi mata, ita ma dama Auta ba ta ga laifin Uwanin ba don idan ita ce ma za ta yi fiye da haka. A cikin dabara Uwani ta tambayi Auta Event ɗin da za a yi kamu, Auta ta nuna mata ai sai su tafi tare tun da ba ta san wurin ba. 


 Yamma liƙi jama'ar gidan ana ta hada-hadar tafiya wurin kamu, Uwani ma atamfarta ta saka da mayafi sai dai tun rana Auta ta hana ta yin wannan ɗige-ɗigen kwalliyar. Ita ta biya musu kuɗin make up aka yi muku kwalliya sai ga Uwani ta fito shar kamar ba ita, lokacin da Uwani ta saka ƙafa a cikin hall ɗin ne ta saki murmushin ƙeta da mugunta. Ta zura hannu cikin aljihun doguwar rigarta ta ji fakitin sabuwar rezar da ta saya tana ciki a fili ta furta. 

"Uwani ce fa 'yar ƙashin gwiwa, ai yanzu za mu fara wasan da ku tun da haka kuka zaɓa."


AlhamduLillah a nan free pages na wannan labarin ya ƙare🫠 idan kina buƙatar ci gaba za ki turo 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lamber ***


Sai mun haɗe a shafin gobe idan Allah Ya kai mu domin mu ji tsiyar da Uwani za ta shuka, Fakitin Reza a cikin Hall ɗin kamu na san akwai ƙura.😂


#Ummou Aslam Bint Adam🌚

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.