Free chapter 路 Read without an account
Chapter 8
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Akwana atash ba wuya, yau saura sati daya bikinsu, Anata shiri.
Kanwar mummy,wato aunty safiyya tazo tareda da ya'yanta mata suma su uku nabila, ihsan da ummu hani, se sakinah qanwar halifa wacce ya amina taita roqa tace seta zo itama,
harda zuwa tambayan umma dan Allah tabarta tazo.
Gida de ya tara jama'a se shirin biki ake.
Sumayya ma ta dage ita ala dole se yayunta sunfi kowa kyau da bikinsu.
ita dakanta ta dinga dinka kayan kuma tahanasu gani, tace se ranar.
Ya amina da ya faty sude sun zubawa sumayya ido, sunaganin ikon Allah.
Sunayya na tsaye gaban akwatinansu ta bata se tinane tinane take tana saqe saqe.
Sumayya!!
ya amina takira sunanta, jin sunanta daga sama yasa ta dan ji tsoro tareda juyowa ta ce na'am?
Tinanin me kike?? Ya faty ta tambaya.
Am counting my future akwatuna.
Ta faty tai dariya sannan tace tayaya?
Sumayya ta matsa kusa da akwatunan ya faty wanda yake milk colour ta nunasu tace ke ankawo miki 8 akwatuna and ta matsa gun na ya amina waenda black leather akwatine tace ita kuma se akai adding two numbers on it aka kawo 10. So i bet nawa will be 12 and they will be gold in colour or maybe peach ta fada with a dreamy look afuskan ta.
Ya faty da ya amina jin haka kawai suka kashe da dariya.
Ooh God sumayya we are soo going to miss you and your drama.
Anma kuma anya bazamuyi calling off wedding dinnan naki ba? kamar basu damu dake ba ma at all, kamar baza ai wedding ba.
Sumayya ta dago ido ta kall ya Amina dake magana sannan tace noo!
No way so kike abarmiki royal chair dinnan da mummy ta siyo min, toh naqi wayon ta fada tareda fita daga dakin.
Ya amina taiwa ya faty wani pitiful look with tears in her eyes.
Sumayya ta fita tai dakin mummy kawai ta shige bandakin mummy, sabida akwai baqi adakin, shisa ma mummy tace adauke kayan lefen daga dakinta akai dakin sumayyan tinda a nan zasu dinga zama kuma su kadai ne bame shiga.
Tana shiga bandakin kawai tasa kuka, ta damu, yes, abun yadameta but yazatai she had to put on a brave face, else inta nuna ta damu suma kuma zasu shiga cikin damuwa especially mummy. I just have to be brave, ta fada tareda share hawayenta ta dauro alola domin tai sallah.
A yau daren laraba suna zaune suna hira da ya'yan aunty safiyya da sakinah dakuma ya'yan uncle ma'aruf , aisha da asama'u waenda sukace bazasu sauka babban gida ba wato gidan kakanninsu dake nassarawa GRA acewarsu akwai mutane dayawa achan sabida haka yacika.
Bayan kowa yasan so suke suzo a hadu ai dapdala asha hira.
Sunata hira abinsu adakin su ya fati, se tsokanar su suke. Zamusha biki inji nabila gobefa za'a fara har sunday ana biki,
kuma za'a kwashi gajiya ba, inji Aisha.
Sakinah ta katse musu hira tareda cewa but it's worth it ai.
Akwai fa biki dayawa wannan shekarar inji asama'u, ai uncle sulaiman ya dage, ya faty ta kalleta tace Allah fa?
"Wallahi" inji Aisha ai bakiga yadda yaimana ba, yace matasan sunqi aure shine fa ya zauna yaita hadakar nan, kinga next month fa akwai three weddings also haka ma na samansa akwai wani wedding din, ai yayi maganin mu bakadan ba wlh, hardani ya hada inji aisha, gidan uncle farouq ne kawai be taba ba sosai, kinsan yadda uncle farouq dinnan yake se addua,
Duk ya daukemu ba abakin komai ba, seyaga dama yake abu kuma ba wanda ya isa dashi, asama'u ta katseta tareda cewa wace ma zata auri dan gidansa ashraf?
Ya meeno ta nuna sumayya to shawara gareki ki rike Allah ki watsar dakomai, dan bakisan ma tayaya ya yadda ba shi uncle farouq din.
Wai shi baza'a takura yaransa ba. waennan matannan guda biyu sangada sangadan matan nan! Atabau yace wlh se wanda sukeso ze aura musu, bazemusu auren hadi ba anma ga ashraf nan in yanaso zemasa magana.
Sakina ta tambaya, "wenan matan nan nasa umaima da maimuna ko?
Sufa inji Aisha.
Sakinah tace ina basune suke yawon wanan kasar ba da waccan kasar da sunan karatu, wayasani ma ko suna karatun.
Ko shekara nawa zasuyi suna karyar karatun oho?
Kullum fa basa kasar inji asama'u.
Allah de ya kyauta ihsan tafada
Amin ya amina ta amsa.
Kune ai bakwa shiga dangi sosai, shisa duk bakusani ba aisha ta fadawa ya faty, ya amina da sumayya.
Ya faty tareda miqewa tace ai yafi dan ni wannan tada mana da hankali zeyi.
Ai shikenan inji aisha.
Ya faty you should sleep early akwai fa hurdle gobe, sumayya ta fada tareda janta bakin kofa, gobe dinner dinkifa karki manta you need your sleep.
Ya amina dake zaune a kan center carpet din dakin tace ehhh ai ni banda ni a dinner din shisa baza ace na kwanta ba.
Anma ai ba gobe bane, sefa friday sumayya ta fada.
Niya sequence din bikin yake ummu hani ta tambaya, sakinah dake gefen ta, tasa hannu kan vanity table ta dauko kati guda hudu ta miqa mata tace ta karanto.
Ummu hani tai gyran murya sannan tace, gobe dinner din ya faty, sannan tai swiping to the next card din tace jibi dinner din ya amina and on saturday kamu da yini nasu gaba daya sunday daurin aure da safe se kai amare da yamma, shikenan ummu hani ta fada tareda ajje cards din.
Sumayya dataji haka se cewa tai naso ace adanyi squeezing walima da tea party but abin yazo a wani ahaka ahaka ne.
Muyi tea party just us, da daddare mana on saturday after all the hayaniya sakinah ta fada.
Nabila tai dan dariya tareda cewa, wannan sede night tea party.
Nabila stop laughing aisha ta fada, its actually a good idea, se mu dan basu advice ma.
Ya faty ta sauke gilshinta ta kalleta tace after all the advice dasu aunty safiyya da aunty mariya da umma maryama da umma saadatu suka dinga bamu? No way am i going through that hell again.
Aiko duka suka kwashe da dariya.
Then its settled akwai night tea party on saturday night, sumayya tafada tareda yimusu seda safe.
Su ya faty da ya meeno ma sukacemusu seda safe suka fita don komawa dakinsu...