Free chapter 路 Read without an account
Chapter 9
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Anyi hanyaniyar biki har an gode Allah.
Amare sunyi kyau har seda sukagaji da yin kyau, ayayinda hotunansu ya cika social media, duk inda kashiga sune, hoton ya faty da Al-amin dakuma ya meeno da halifa sede kaga ana cute couples (lol馃槄).
Sumayya tayi bajinta wurin tabbatar da kayansu yayi kyau, duk top designers dinnan se neman designer din da tai musu dinki suke.
Sumayya duk bata wani yi shiga ko ta fito a matsayin amarya ba, dan sede waenda suka sani ne suke mata magana, ana Allah bada zaman lafiya, anma komai a matsayin kanwarsu takeyi, ta maidashi tamkar bikinsu ne su biyu babu ita.
Ranar daurin auren ma kasa kunne tai taji za'a daura da ita kokua, she was very disappointed dataji harda ita aka daura.
Wannan wane irin aure ne inbanda sadaki babu abinda aka kawo? Taita de saqe saqe azuciyanta sannan tace ya Allah ka zaba mani mafi alkhairi. Amin
Inkuma jarabawa ne, ya Allah ka bani ikon chi!
"Amin"
Bayan tagama dua sannan ta fita daga waje domin daukan hotuna.
Ayau za akai amare, ya faty za'akaita unguwar bompai itakuma ya amina za'akaita NDIC Quarters.
Mummy bataje kaisu ba se su umma saadatu ne zasu kaisu, duk aka rarrabu biyu kowa da gidan dazashi.
Yauwa! thank God nasamo ki sakinah ta fada yayinda taje dakin mummy ta tarar da sumayya akwance kamar ba lafiya, kitaho mutafi, munce motarki zamu bi.
Am not going!
Stop joking sakinah ta fada tareda janyo hannunta.
Sumayya ta kwace hannunta tace ga key din mota na nan ku dauka, anma bazani ba, and handle my baby with care.
Sakinah jin muryarta na rawa tasan cewa kuka take, se cewa tai su ya faty will not like this!
Ou ai nagaya musu dama bazani ba.
Well shikenan sakinah tafada tareda daukan car key din sumayya akan side drawer tai gaba.
Jin ta rufe kofa, sumayya ta saki sabon kuka.
Haka aka kai amare gidansu, sunsha wa'azi kumasun sha kuka, akai siyan baki wanda Al-amin ya bada 50 thousand shikumaa halifa ya bada 60 thousand duk aka tafi aka barsu.
*Gidan Al-amin*
Bayan ya raka abokansa ya dawo wurin karfe sha daya, yai dakinta ya tarar da ita azaune a tsakiyan gado kanta a qasa ya zauna gefe tareda yimata sallama, ta amsa tana shessheqar kuka, becemata komai ba se cewa yai dan Allah kitashi kiyo alola muyi sallah, nima zanje nai alola, bata ansa ba, shikuma ya miqe ya bar dakin ya tafi dayan dakin domin dauro alola.
Itama hakanan ta miqe ta bude wardrobe tana neman wasu kayan mara nauyi domin ta chanja, sumayya tace ta jera mata su, aikuwa tana dubawa ta hango wata doguwar riga, kawai ta dauka, ta dauka hijab dake kan dadduman dake side drawer ta fada bandaki.
Tana fitowa ta tarar dashi a zaune a kan dadduma da alama idar da sallah yai, ga kuma tata daddumar itama ya shimfida mata.
Bayan sun idar da sallah ne, ya juya ya mata yan tambayoyi ta ansa sa murya na rawa, se hawaye take, ta rasa tayaya zata dena hawayennan, anma inaa se zuba suke kaman famfo.
Al-amin ya tashi ya fita se dawowa yai da plate wanda yake dauke da chicken, chips se juice da cup and bottled water, ya ajje mata akan side drawer sannan ya dauko sachet din magani daga aljihunsa yace am sure you are hungry and tired, just try to eat sekisha panadol, it will help you sleep better.
Thank you! ya faty ta fada yayinda takarbi maganin.
Good nyt Al-amin ya fada tareda jawo mata kofa ya rufe.
*GIDAN HALIFA*
Bayan halifa ya raka abokansa ya dawo ya nemi gu a sitting room ya zauna, tareda duba wayarsa, yaga missed calls din hafsa rututu da text messages, be mata reply ba ya maida wayar ya ajje.
Ya dade a zaune kafin ya tashi domin ya tafi dakinta ya tarar hartayi shirin bacci addua take zata kwanta.
Nazata amare se an bude kansu anga suna kuka se abasu hakuri sanan ku nemi gu ku kwanta, halifa ya fada tareda nade hannayensa.
Banda wannan amaryar ta amsa.
Do you know what? Ta tambayesa,
What? He asked,
I like you better online.
ouu!! I also like you better online.
Inbaka da abin fada get out of my room, am tired and sleepy, thank you ta fada tareda kashe fitila.
Tini ya kunna sannan yace dauro alola muyi sallah. Bata musa ba ta tashi ta dauro alola sukai sallah.
Bayan sun idar halifa se cemata yai, yunwa nakeji.
Ina kazar amaren da ake kawowa? Ya amina ta tambaya.
Ughhh kamar nura yace yasaka a fridge, banaje na duba.
Aiko sejitai yana kwala mata kira, ta tashi ta bishi.
Ta tarardashi zaune a dining yasa leda agaba.
It's cold ya fada, nikuma i don't take nor eat cold things, se anyi heating.
Jin haka ta hararesa ta juya zata koma, please ya fada, ta juyo tace ranar dana diro gidannan kakeso na fara shiga kitchen? Haba kaikuwa ya halifa.
To ai yayi sanyi ya fada, sede mushiga tare ta fada tareda kallonsa challengingly.
Ehh! na yadda.
sukayi heating suka saka a plate daya suka zauna suka chi sukasha yoghurt.
Ya meeno se cewa tai thank you and good nyt, kawai yabita da ido yana wani mugun smirking, bata dade da kwanciya ba segashi ya shigo da pijamas dinshi ya nemi gu chan nesa da ita ya kwanta, kawai ta bishi da ido tareda cewa azuciyarta *da matsala*.