Free chapter 路 Read without an account
Chapter 22
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Nabeel haka ya isa gida, ya gaya wa mommansa duk abinda ya faru, momma tai mishi fada tare da cewa yabi ahankali sabida matar aurece.
Nabeel yacewa momma in sha Allah he will be careful.
Allah ya kareka.
Amin ya amsa, tareda miqewa yace banai wanka na koma na dubata, dan har yanxu ban samu nakira ya'nuwanta ba.
Toh Allah bada lada, momma ta fada.
Nabeel ya fita yai dakinsa, ya dauko wayar sumayya fayakarba gun megadi bayan yadawo da ita daga gyara yasaka a charge sannan yashiga wanka, bayan ya fito ya shirya, ya dauka wayar sumayya ya kunna.
Ya duba last call dinta yaga ansaka sisto no 1 and sisto no 2.
Ya kwafa both numbers din awayansa tareda dialing sisto no 2 din.
Bayan an dauka yai introducing kansa tareda tambaya ko sunsan sumayya, yana fadan sunanta duk ta hargitse, inata kiran line dinta akashe, dan Allah kasan inda take?
Be samu yayi magana ba yaji an karba wayan, yaji wata muryar daban tace please is our baby sister ok?
Nabeel de yamusu bayanin komai, tindaga yanda ya sameta har izuwa yanxu, sannan yagaya musu asibitin da take, sukai mishi godiya tareda cewa gobe zasu zo, seya ce musu shikuma akwai inda zeje gobe, se after two days kuma ze dawo.
Ya amina tace bakomai, tareda kara mishi godiya.
Nabeel ya koma asibitin ya hadu da abokinsa Dr. Mukky (short for muktar), tareda tambayan ko ansamu progress, Dr mukky yace she is stable.
Nabeel ya masa bayanin yanuwanta zasu zo gobe, shikuma zeyi tafiya bayanan, anma in akwai wata matsala dan Allah ya kirashi ya gaya masa, ko text ne.
Washe gari da sassafe Dr. Mukky ya nufo asibitinsa, tin daga gate yaga security asume a kasa kaman anyi drugging dinsa, ba shiri yai parking ya fito da sauri, ya tarar gate abude, kofan asibitin abude, bega nurse ko daya ba, doctor on call dinma beganshi ba, sejiyai kaman ana bubbuga kofa daga wani office,
da sauri ya karasa office din sejiyai mutane nata bubbuga kofa, Dr. Mukky yace musu yana zuwa,da sauri ya karasa office dinsa yajawo drawer din desk dinsa ya dauko bunch of keys, dayake asibitin sa ne, yanada key din ko ina.
Ya koma da sauri ya budesu.
Lafiya ya tambayi nurse din, da duk ta fita hayyacinta.
Sir, dukkansu sukazo at night zasu dauka patient muka hanasu.
Sun saka kayan doctors ajikinsu da nurses, damuka hanasu se muka gano ashe criminals ne, shine sukai threatning namu with guns sukache mushiga nan, suka kullemu suka tafi da key din.
What patient? Dr. Mukky ya tambaya.
That patient that was in a coma.
Dr. Mukky najin haka da gudu yai dakin da sumayya take, yaga wayam, se ya hau salati, ya zauna a gun ya dora hannunsa a kai yana salati.
First of all reputation din asibitinsa yanzu yadan samu matsala, wannan wace irin kasa ce? Wai ashigo asibiti.
Shi besan me ze cewa nabeel ba, kuma ga yanuwanta zasu zo, shide kam besan me ze che musu ba wallahi.
A wannan yanayin ne su ya faty da ya amina suka karaso suka tarar da shi.
Assalamu alaikum, me gilashin (ya faty) ta fada, dan Allah nan aka kwantar da sumayya?
Dr.mukky be ce musu komai ba, se cewa yai su hadu a office dinsa, yasa aka kaisu office dinsa sannan ya shigo.
Ya basu hakuri sosai, su kuma jin yana basu hakuri hankalinsu ba karamin tashi yai ba.
Ka gaya mana menene? Ya faty ta fada cikin tashin hankali.
Dr. Mukky ya furzar da iska, sannan yagaya musu duk abinda ya faru tin daga safiya izuwa yanxu.
Ya faty da ya amina sukai shiru, ya amina se bude jakarta tai zata dauko waya.
Mezakiyi? ya faty ta tambaya.
Mummy zan gayawa.
Ah ah ya faty ta fada, tsaya tukunna.
Mu je chan gidanta mugani, in bata nan se muje gidan uncle farouq before mudauka mataki.
Sukai masa godiya.
Zasu tafi kenan se ya amina ta juyo, tareda cewa ina wanda ya kirani jiya yagaya min? Ta tambaya.
Ou nabeel, yayi tafiya, yanxu ma nake so nakira na gaya masa.
Yi hakuri dan Allah ya faty ta fada, wallahi bawan Allahn nan ya mana wahala dayawa, ka bari in abun ya fita out of hand se a gaya mishi.
To shikenan Dr. Mukky ya fada, am so sorry i couldn't be of help, in baku sameta ba se ayi involving police officers, ga card dina ya fada tareda miqa musu card dinsa da number dinsa ajiki, ya amina tasa hannu ta karba tai godiya.
Shikuma Dr. Mukky shima zeje wurin yansanda akan anshigo masa asibiti.
Haka sukaje gidanta bakowa, sukaita dube dubensu se dan akwatinta dasuka gani ta hada, se kuma kofar dakinta aballe, ahaka suka bar gidan. sukayi gidan uncle farouq, as usual kamar babu mutane agidan se masu aiki, straight sukai dakin umaima da maimuna, suka tarar dasu suna bacci.
Aiko tini ya amina ta janye bargon tareda kiran sunayensu da karfi.
Whatttt!!
umaima ta fada tareda tashi ta zauna, maimuna kuwa ta murtuke fuska ta tashi ta zauna.
We are looking for our junior sister, ya amina ta fada and we can't find her nor your brother.
Suna gidan su mana, maimuna ta fada.
Munje basa nan ya faty ta fada.
Then we don't know, ku rabu damu muyu baccinmu, bamuyi bacci jiya ba umaima ta fada tareda komawa ta kwanta.
Kiranshi zakuyi muji inda yake, ya amina demanded.
No way in hell maimuna tace.
Ni nayi fada dashi so bazan iya kiransa ba, umaima ta fada.
Ya amina tana jin haka ta dauka side lamp tareda jawo gashin maimuna dake kusa da ita tace, ZAKI KIRASA KOKUWA.
umaima tana ganin haka da sauri ta bar gadon.
Umaima please call him, maimuna ta fada.
Haka sukaita kiransa anma sede wani kato ya dauka yace he is not available ya kashe.
Haushi ya ishe su.
Aiko tini ya faty ta karba card din Dr. Mukky ta kirashi ai involving police officers, itakuma ya amina ta kira mummy ta juyemata komai.
Mummy se salati take.