Free chapter 路 Read without an account
Chapter 23
HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲
Ya amina nakiran mummy tagaya mata halinda da ake ciki, mummy tai salati anma kuma calmly ta ansa su tareda yin addu'a, Allah sa tana cikin koshin lafiya.
Allah sa kuma ba mugun hannu ta fada ba.
Amin! duk suka ansa.
Ya amina harda cewa ai in ba ai wasa ba ashraf ne ya dauketa, tinda shima an nemesa an rasa.
Mummy najin haka ta kwabe ta, tareda cewa babu kyau zargi, kuma ai ashraf mijinta ne, mesa ze dauketa.
Mummy dan bakisan halin da take ciki bane shisa,ita take cewa ai kar mu fada miki, ya amina ta fada.
Itade mummy tai addu'a tareda katse wayan.
Bashiri ta dauka waya takira ummah (maman su halifa, matar uncle sulaiman) tace mata gatanan zuwa hope mijinta na gida.
Tace yana nan Allah sa de lafiya? Ummah ta tambaya.
Itade tace seta karaso kawai saji.
Aikuwa mummy taje ta juyewa uncle sulaiman duk abinda yake faruwa, komai ta fada masa.
Tareda cewa da yamma zata siya ticket ta dira a abuja.
Uncle sulaiman da tsabar yashiga shock kasa magana yai se salati yake, ummah kuwa ta kawo tray da drinks ta kasa direwa tin daxu, tayi mutuwar tsaye, abin mamaki yake bata.
Se bayan yan mintuna sannan uncle sulaiman yace, zaki ajje tray din kokuwa? , bashiri umma ta dire ta nemi wuri ta zauna, sannan ya juya gun Hajiya Altine tareda cewa, karki dauki wani harsh decision, nasan ki da bin abu calmly dan Allah ki bari abi al-amarinnan ahankali.
Ai bance zan je nayi wannan abun bane, kawai de i have had enough ne.
Kaima kasan yadda akai bikinnan, yaron nan ko bi takanta beyi ba, bexo ya gaisheni ba, kuma kaima bexo ya gaisheka ba,anma yarinyannan tai biyayya ban tabaji tace afasa auren ba, dukda de mutuminnan bebi takanta ba, kuma bayan auren, nasan tana cikin matsala anma bata taba kira takai kara ba, yanxu ni abun ya isheni tsakani har ga Allah, idan ansamo sumayyan atambayeta, intanason auren kokuma araba, kuma wallahi kotu tai mishi iyaka da ita.
Ah ah hajiya altine meyai zafi haka?
yi hakuri mana, duk naji abinda kika fada, kuma zan bi lamarin ahankali, idan an samo yarinya se asan yadda za'a magance ita wannan matsalar, yanxu zankira' shi farouq (babban ashraf da su umaima) din, se mu hadu a abujan.
Dan Allah karmu tadawa da tsofaffin mu hankali.
Toh naji,
Nakuma gode.
Allah saka da alkhairi. Mummy tafada.
Amin duka suka amsa harda umma.
Hajiya altine ta miqe zata tashi kenan se ummah tace inkinje chan ina zaki zauna? Dan umma saadatu da take dan zama achan jefi jefi sabida aikin mijinta, itama tana kano, kinsan anata shirye shiryen bikin danta da sakinah.
Nasani mummy tafada, nacewa fatima ta kama mana hotel mu uku.
Toh shikenan ma, uncle sulaiman ya fada, nida halifa zamu karaso idan nayi magana da farouq naji yaushe ze zo shima.
Ashe shisa halifa yadawo gida yace matarsa tayi tafiya, kuma yasan meke faruwa anma yai mana shiru, dan na tabbata aminatu zata fada masa halin da ake ciki, ummah ta fada kasa kasa irin tagano abu dinnan.
Haka de mummy tai musu sallama ta tafi gida domin hada kayanta.
Bata dade da isa abuja ba uncle sulaiman yakirata yace mata gobe da yamma baban ashraf din ze karaso, sabida haka da yamma ana so kowa ya hallara agidansa, za ai magana.
Shima da safe ze taho da halifa.
mummy tayi bacci, ya amina ta fada yayinda ta shigo dakin hotel din dasuke sharing da ya faty.
Zan kiraka nan bada jimawa ba, ya faty ta fada tareda katse call din, ta juyo tai facing ya amina data zauna akan vanity stool, itakuma tana kan gado.
Ansamu tai bacci kenan? Ya faty ta tambaya, ehh ya amina ta amsa, hankalinta wallahi ba karamin tashi yai ba, she is just trying to be strong for us.
Allah sarki mummy ya faty ta fada.
In sha Allah sumayya zata fito.
In sha Allah ya amina ta maimaita.
Kekuma ya amina ta fada.
Nikuma ya faty ta maimaita tareda nuna kanta.
Menai? Ta tambaya.
Ai kinsani!!
ya amina ta bata amsa.
Ya faty na roqe ki, dan Allah, dan Annabi, ba dan halin mu ba, karkuma ki ce zaki duba situation din da muke ciki, dan Allah, ki gaya mini meke damunki, wallahi nasan abu na damunki.
Idan baki fada mana ba wa zaki fadawa eh? Ya amina ta tambaya, inkin fada se a magance matsalar.
Ya faty tai shiru sannan tace, naga ba wani huge problem bane shisa.
Ke de ki fada, ya amina encouraged.
Ya amina!! Ya faty ta kira sunanta, kinsan de Al-amin is everything i could ever ask for in a husband, wallahi kullum godewa Allah nake, and his sisters are amazing, kinsan sun koma jordan?
Ya amina ta gayda kai alamar eh.
And kinsan family member dinsa are super amazing bani da problem dasu at all.
Ya amina de se nodding head dinta take in an understanding way.
Anma mamman sa, innalillahi wa inna ilaihir raji'un, matar nan bata sona bata kauna ta, she detest everything about me ingaya miki.
Komai nai ba dede bane, she even believes cutar danta nake.
Imagine ya faty ta fada.
Ya amina jin haka, tini ta miqe da sauri, ta karaso inda take ta zauna tareda cewa, keko ya faty me kikai mata?
Bakomai in gaya miki, kawai dan taso ya auri wata cousin dinsa muhasin, shikuma yace niyake so, kuma babansa ya goya masa baya ya aureni.
Anma yanxu binshi take maman tasa seya aureta, dudu du auren mu watan sa nawa? Ya faty ta tambaya tareda fara hawaye.
Noo, please no, ya amina ta fada tareda zuwa ta dauko tissue a kan side drawer, don't cry please, ta fada.
Ya faty ta karba sannan taci gaba, kwana biyu bata da lafiya, kuma kinsan su twins suna jordan, ba kowa agunta, toh ni ce zan je na zauna gunta, a ranar da zan tafi, aka samu problem ba'a ga sumayya ba, nagayawa Al-amin yace na tafi.
Yanxu kinga ta isheshi ta jaraba da masifa, wai dama so nake ta mutu shisa na taho nan.
Ni na rasa ya zan da ita.
Toh bata da yan uwa ne?
Ina ita muhasin din?
Ai seta kirata ta zauna gunta, ko a hayi nurse ko, tinda aikinsu ne, abiya ta,
Ya amina ta fada.
Ya Allah, ya faty ta fada, tareda dora hannu aka.
Kefa matsala ta dake daukar zafi, wallahi it is in situations like this i wish sumayya is here.
Toh lemme act like sumayyan ya amina ta fada tareda dan tabe baki tace, ya faty yi hakuri, komai na duniyannan hakuri akeyi, komai se labari, yanxu kichigaba da addu'a, inkomai ya lafa se agaya wa mummy, zata fada miki yadda zakiyi.
Kokefa, ya faty tafada, tare da dan smile dinta.
Anma wallahi tallahi daga ke har shi Al-amin din, ku bi ni ahankali, dan zan iya hadaku nai maganinku.
Toh hajiya aminatu, ya faty ta fada tana dariya.
Dr. Mukky na zaune a office dinsa da yamma se gani yai nabeel ya shigo da sauri, ya banko kofar office din ya zo dede kansa tareda cewa.
"Ya akai ka bar yar mutane, har aka sace ta, i thought na barta in your care ne?
Yanxu tana ina?
An nemo ta?
Karkacemin ba labari,
Anma Dr. Mukky u were abit careless wallahi.
"
Dr. Mukky shiru yai, yama rasa me ze che masa.
Toh Amin wa alaikum as salam.
Tinda baka iya sallama ba.
Kuma ga gu chan ka zauna anma ka rufen kofan office tukunna kan ka zauna.
Nima i regretted telling you wallahi, tinda gashi nasaka kayi impromtu dawowa.
And the police are doing everything they can, but i wont tell you anything se ka zauna, ka sha ruwan sanyi tukunna.
Nabeel yai tsaki ze fita kenan seji yai dr. Mukky yace.
Baban ashraf na nemanka.
Nabeel najin haka kawai yai mutuwar tsaye tareda juyowa ya kallesa.
Wasa kake.
Dr. Mukky yai shrugging shoulder dinsa bece masa komai ba.
He left ashraf in my hands da muka bar naija,and ashraf turned out like this, i can't face him.
Dr. Mukky de ya kara yin shiru, bece komai ba.
I couldn't control him, then.
Sekaje ka fada masa haka, Dr. Mukky ya fada.
Nabeel kawai ya rufo kofar ya dawo ya zauna tareda cewa, Dan Allah ina ruwan sanyin yake?.
Authors note
Showing appreciation for the book actually goes a long way.
Mutum seyaji dadin karasa rubutawa anma inkaji shirun nan sekai tinanin ba karantawa akeba.