Free chapter 路 Read without an account

Chapter 27

by Rashida Adamu gwaram 路 HAKURINMU

HAKURINMU 馃憣馃徎馃尲

Yau satin mummy daya da komawa kano, sumayya tana ICU din asibitin ya faty da mijinta, sabo da suka bude, ya amina da ya faty sun gayawa mummy abinda ya faty take ciki, mummy tai mata wa'azi, sannan tace the best thing to do is taje tai jinyar mamansa, mummy tai mata wa'azi sosai.


Ya faty taiwa mummy godiya, tareda zuwa ta hada kayanta dan da yamma Al-amin zezo ya dauketa.


Ta saka riga da skirt na atamfa, abinda bata fiye sawa ba, tafison dogon riga sabida zuwa aiki, it's more comfortable, tasaka atamfar ta red da touch of ash, dinkin yayi kyau sosai ya mata kyau kuma sosai, ta dauka ash mayafi da black bag and shoe.

Iyyeeee ya amina ta fada, yau so kike ki rikitawa ya Al-amin lissafi ko? Shisa jiya kika tada mana da hankali se an miki lalle?

Ya faty tai dariya tareda cewa, kina gani sumayya bata nan na rasa ma tayadda zan daura dankwalin.


Toh nima de ba gwanar daura dankwali bace, kema kin sani, da de rolling kikace na miki.


To zo mu jagwalgwala adaura ya faty ta fada tareda miqa mata dankwalin.


Haka suka daura dankwalin yayi kyau kuma sosai, anma ansha drama kan a daura.


Ta dauka turare ta fesa.

Kai ya faty yaushe kika zama haka ne?

Turaren wutan da kikayi be isheki ba sekin kara tirare? Ya amina ta fada tana boye dariyarta.


Ke! Ki rabu dani.


Ana haka ko wayarta tayi kara yayinda sunan habeebi a screen din wayar yafito.


Tana gani tai murmushi, tareda daga wayar domin ta amsa. Gani nan fitowa, ta fada.


Amina, ya faty ta kira sunanta, dan Allah ki gayawa mummy Al-amin ze mata gaisuwa, yana waje, dan Allah ashigo da shi.


Toh ya amina tafada tareda miqewa.


Itakuma ya faty tana miqewa zata jawo dan karamin akwatinta, ya amina da take tsaye bakin kofa se cewa tai, wallahi kayannan ba karamin matseki sukai ba, ni bansan yaushe kika zama haka ba.


Bazakije kiyi abinda na saki ba? Ya faty ta fada da alamar fada.


Aure me chanja mutane, dadinta muma munyi.


Au bazaki tafi ba?


Toh al masifatu, na tafi.


Hakade mummy suka gaisa, ita kuma ya faty ta ware mayafinta ta rufe jikinta dashi tareda karasawa dakin mummy tai mata sallama.


Ya amina ta rakata har mota sukai sallama sannan ta koma.


Tinda ya faty ta fito,Al-amin kawai binta yake da kallo, hartashiga mota, shima yashiga yaja, babu wanda yai magana acikinsu, Al-amin ko se satar kallonta yake.


Ugh zamuje gida na dauka wasu kayan ko? 

Kafin mu karasa gun mama?.

Al-amin ya furzar da iska tareda jan wannan dogon hancin nasa sannan ya budi baki yace.

" hajiya ai babu inda zaki yau, se jibi zan kaiki"

Ya faty najin haka kawai tadanyi sitting up tareda juyowa ta kallesa, anma jikin mama fa?

Mama can deal with herself, kuma akwai masu aiki agunta.


So you think you can look and dress like this?

Sannan nikuma Mr.husband kawai senaje na ajje ki agun mama, after nayi few days ban ganki ba gashi se baza kanshi kike, sannan kinyi wani dope lalle.


Kawai senaje na ajje ki gun mama?


Impossible ya fada.


Ya faty kawai tai murmushi.


Se bayan kwana biyu, Al-amin ya kai ya faty gidansu.

Shigarsu suka tarar da mama da wata black beauty azaune agefenta, sanye da riga da wando, se daddana waya take tana taunar chewing gum, ko dago kai ta kallesu batai ba.


Al-amin ya durkusa ya gaida mama, itama ya faty ta durkusa domin ta gaida ta.

Bazan amsa ba, mama ta fada.

Shine kika gudu, bayan kin gudu, kin ma dawo garin anma bazakizo kiyi jinya ba ko?


Wato na mutu?


nace na mutu ko? Ke kinje kin killace taki uwar, anma shi da yake bashida wayo bayason tasa uwar, kawai ta mutu ko? Mama tafada da masifa da jaraba. Se haki take.


Budebain dayai ze magana mama takatsesa.


Al-amin ka fita daga ido na na rufe. Baka da wayo se juyaka ka ake kamar waina, uwar ka bata da lafiya? Anma ka tafi kana lallaba wata chan, har kanada bakin cemin bazata samu damar zuwa ba dan tagaji daga tafiyar datai, wani wai batajin dadi.


Ina rashin jin dadin a nan? Mama tafada tareda nuna ya faty data kara wani haske se glowing take.


Nace ina rashin jin dadin a nan? Tazo gidanka ta samu abinchi me kyau, sede achi asha ajuye, ai bacci, babu abinda ake tsinanawa.


Mama! Mama! Al-amin ya kira sunanta, kiwa Allah dan Allah kiyi hakuri mama. 

Ba laifinta bane mama.

Kai dallachan kamin shiru, mijin kan tache.

Anma mama Al-amin dake durkuse agun ya fada tareda katse mama, be karasa maganar ba sabida jin hannun ya faty dayai tayi squeezing hannunsa alamar yai shiru.

Karasa mana, mara kunya

Ban mutu ba za'a nuna min duniyanchi.


Da badan nasa an dauko min muhasin ba da shikenan sede kazo ka dauka gawata, ita kuma suje suyita murna.

To baze yuwu ba, ina nan da rai kuma sena rabaka da mayyar nan, mama tafada tareda nuna ya faty wacce idannunta duk ya chiko da qwalla.


Al-amin de se bata hakuri yake.

To qawayena zasuzo dubiya anjima, wuce kimusu girki.


Al-amin jin haka, se cewa yai

Mama yaushe akewa waenda sukazo dubiya girki eh? Su da zasu kawo, kuma ai da masu girki naga.


Fita daga idona na rufe kajiko? Mama tafada tareda nuna Al-amin.


Ya faty jin haka kawai ta miqe, tareda cewa, akwai abinda kikeso adafa?

Mama ta kalleta sama da qasa, ta harareta tareda jan tsaki, sannan tace muhasin duk zata gaya miki.


Toh ya faty ta amsa tareda wucewa kitchin.

Mayyya kawai mama tafada, tareda binta da harara.


Tana wucewa, Al-amin shima ya tashi ze bita.


Ina zakaje? Mama ta tambaya.


Al-amin ya ma kasa magana.


Dawo nan ka zauna.


Toh ya fada, tareda dawowa gefenta ya zauna, sannan ya dora hannu a ka.


Muhasin babu abinda tai, duka ya faty ce tayi, muhasin kawai gaya mata abinda za ai tayi, shikenan takoma gefe tachigaba da waye waye da danne danne.


Haka ya faty tagama taje tajera akan dinning.


Kawayen mama sukazo, Suka chi suka sha suka gama hiransu. 


Bayan sun gama ya faty taje ta kwashe ta wanke, sannan lokachin maganin mama yai, taje ta bata.

Mama takarba da harara.

Ahaka de har dare yai, se bayan mama takwanta bacci, sannan ya faty ta samu kanta, tana shiga daki taga wani akwati bayan nata, sannan kawai setaga mutum ya fito daga bandaki.

Me kakeyi a nan? Ya faty ta tambaya.

Is that how to greet your husband?


Al-amin ya fada.


Well not when he is not supposed to be here, ya faty ta amsa.

Oh just admit it, you are happy to see me.

Ofcourse i am, ya faty ta amsa truthfully.

But you can't stay here, kaima ka sani.


I just can't stay away, besides you'll be bored agidan nan, if you stay ke kadai.


So allow me to stay pleaseee Al-amin ya fada, tareda yin kallar tausayi.


Kai! Stop it ya faty ta fada, irin wannan pity face din bemaka kyau.


Whatever! Nasan i have won you over.

Haha ya faty tai dariya tareda cewa, yaushe za'a karayiwa mama chest x-ray?


Wallahi ban sani ba, me kika gani? Al-amin ya tambaya,

Naga daxu tana riqe gefen chest dinta due to pain, so am thinking consolidation din akwai har yanxu, maybe za'a dan chigaba da bata analgesics for the timebeing.


Toh duk yadda kika gani.


Al-amin ya fada, pneumonia dinnan ya dan wahalarda ita ba laifi.


Allah ya bata lafiya, ya faty ta fada.

Amin Al-amin ya amsa.


Ugh habeebty about daxu abinda mama tace,

Shuuuuuu ya faty ta fada tareda dora hannunta a lips dinsa.


Batace komai ba ta tashi ta shige bandaki.


Washe gari, ya faty ta duba mama, tai mata breakfast sannan ta wuce aiki, ba karamin makara tai ba, sabida abubuwan da mama tadinga sata tayi.


Tana dawowa kuwa ta rufeta da jaraba da masifa, wai ta rabuda ita dan tanaso ta mutu, ya faty batace mata komai ba, bayan mama tagama jarabarta, kawai ta bata hakuri.


Al-amin na dawowa mama tagaya masa yadda akai, shide bece komai ba se hakuri yachigaba da bata.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.