Free chapter · Read without an account

Page 14

by Halima Salahu Adamu · SUMAYYA

*SUMAYYA*

 _Wattpad@SaNaz_deeyah_

_Arewabooks@sanazdeeyah_

Youtube: ***

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*

_[tushen mu'amula tagari]_



```Page 14```


_Cigaban Labari_


"Ba zan taɓa yafe wa ko waye ya yi min fyaɗe ba, an wulaƙanta rayuwata an cutar dani, anyi wa iyayena silar barin duniya. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta tana jan majina, tare da tashi zaune. Har tayi kuka ta gama ta share hawaye babu wanda ya san tayi. 


Rayuwa ta cigaba da tafiya biki ya cigaba da matsowa, sai dai kuma tana ganin wasu 'yan sauye-sauye daga Jamilu, sam yanzu ya canja mata, har sai da ta kasa haƙuri dashi ta tambaye shi sai ce mata ya yi ai hidimar biki ce ta saka ya zama haka amma ta masa uzuri zai canja bayan komai ya lafa.


Kamar kullum haka yau ma ta tashi da aikin gidan, ta haɗa kayan wanke-wanke ta wankesu tas, sannan ta fara sharar tsakar gidan, ta gama tana ƙoƙarin hura murhu Umma ta fito daga ɗaki, ɗan duƙawa tayi sannan ta gaisheta "Sumayya har kin gama kintsa gidan?"

"Eh Umma, dama ina shirin ɗora ɗumame ne"

"To Allah yi albarka"

"Amin Umma"

"Jiya Jamilu ya dawo kin yi bacci"

"Eh jiya da yake ina ɗan fama da ciwon kai"

"Shiyasa ma nace ya barki"

Murmushi kawai tayi.

"Yau ne ake ɗaura auren Atika na san kin sani ko?"

Ji tayi gabanta ya yi mummunar faɗuwa, ta sauke kanta ƙasa, ita sam ta manta saboda ba lissafi take ba.

"Sumayya sai haƙuri, fatan zaman lafiya za ki bisu dashi sai ki ga Allah ya dai-daita lamuran"

Kai kawai ta gyaɗa ba tare da ta ce komai ba. "Ki shirya in kin karya kije ki ganta, babu yadda kika iya kece babba kinji"

"To" Ta faɗa sannan ta juya da sauri dan bata son hawayenta ya zuba a gaban Umma.


Tana shiga ta kwanta kan katifar tare da fashewa da kuka, ta san in da Amarya da Baffa suna raye, ba zasu taɓa yarda ayi wannan auren ba. Miƙewa zaune tayi, idanunta sharkaf da hawaye, ta saka hannu tana gogewa, a fili take furta "Allah ka bata zaman lafiya, kasa mijinta ya zame mata mijin marainiya, ya Allah kasa a dalilinta ya shiryu ya daina abinda yake." 


Suna gama karyawa ta yi wanka ta shirya. "Umma zan tafi" Ta furta tare da tsugunnawa gaban Umma. "Gashi kuwa kin yi kyau sai ƙamshi kike, Allah ya sanya alkhairi ki gaisheta"

"Za taji insha Allah."


             ***** *****


Murmushi tayi lokacin data fito daga toilet, tana ɗaure da ƙaramin towel ɗin da, da kaɗan ya kai cinyarta. "Sweet wai har yanzu baka tashi ba?" Ta furta tana ƙarasawa jikin mirrow ta zauna."

"Hamdis!" Ya faɗa cikin shauƙi kafin ya ɗan lumshe ido yana faɗin "Ni fa ban gaji da kasancewa dake ba" 

Murmushi tayi, sannan ta miƙe ta ƙarasa gaban gadon ta zauna "Me kake ci...? Ai ni da kai yanzu aka fara, sai dai in bamu samu space ba"

"Hamdiyya kenan, da na san haka kike da ban auri Jidda ba, ni sam sai nake jin kamar ba da mace nake zaune ba, salonki na musamman ne"

"Kamar yadda nima nake ta musamman" Ta furta tana kashe masa ido ɗaya, sannan ta sunkuya ta fara kissing lips ɗinsa, shi ma tuni ya burkice ya janyota cikin blanket ɗin suka koma ruwa. Kusan mintuna talatin suka ɗauka kafin suka tashi zuwa toilet, tare sukayi wanka sannan suka samu suka fito, a gado ya kwantar da ita ya ƙarasa mirrow ya shirya tsab, tana kwance tana faman lumshe ido alamun bacci take ji, yana gama saka kaya ya ɗauketa cak, bai direta a ko ina ba sai a bedroom ɗinta dake side ɗinsu, shi ya ɗauko lotion ya shafa mata tare da turaruka, tana nan kwancen "Ni da kaina zan zaɓa miki kayan da za ki saka"

Murmushi kawai tayi ba tare da ta ce komai ba, ya buɗe wardrobe ya ɗauko wata doguwar riga kenan kawai yaji horn ɗin mota. Da sauri Hamdiyya ta miƙe, shima da sauri yaje ya buɗe cotton ɗin window, kawai ganin motar Sadeeq ya yi ta kunne kai ciki. "Kamar Sadeeq ne ya dawo?"

"Shi ne" Ya furta yana kallonta.

"Kuma Yaya Kamal ka tsaya anan ka fita dan Allah" Ta furta tana miƙewa.

Murmushi ya yi yana faɗin "Matsoraciya kawai."

"Eh ɗin naji" Ta furta tana tura shi, yana fita ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido.


Tana gama zura kayan ta ƙarasa gaban mirrow kenan ya turo ƙofa ya shigo, da sauri ta juya ta kalleshi, murmushi ta sakar masa tare da faɗin "Welcome my love" Ta ƙarasa gabansa tana karɓar briefcase ɗinsa. Ɗan peck ya mata a goshi tare da faɗin "Babe you look beautiful kullum ƙara kyau kike" Matsawa baya tayi tare da faɗin "Babe kana da zolaya, yanzu dai kaje kayi wanka, kafin ka fito na gama shirya maka abinci"

"Allah ya miki albarka"

"Amin" Ta furta tare da juyawa ta ƙarasa gaban side drawer ta ajje briefcase ɗin, sannan ta tayashi ya cire kaya ya shiga wanka. Ta ɗan taɓe baki a hankali ta furta "Ɗan wahala" Sannan ta koma gaban mirrow ta ƙarasa shiryawa ta fita.


Kitchen ta shiga ta haɗo komai data dafa ta kai dining ta ajiye, sannan ta koma ɗakin, har lokacin bai fito daga wanka ba, dan haka kawai ta haye gado ta janyo wayarta ta cigaba da latsawa. Ya ɗan juma a toilet kafin ya fito, yana ɗaure da towel a ƙugunsa, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai, ya ƙarasa gaban mirrow sannan ya kalleta ya ce "Babe ba zaki tayani shiryawa ba?" "Haba Babe kayi kawai, wallahi a gajiye nake, ba dan yamma tayi sosai ba da bacci zanyi ma" "No kin san bana son baccin yamma ko?" "Ai shiyasa ba zanyi ba"

"Yawwa Babe, ni kaina na san kina ƙoƙari, shiyasa nake so a ɗan rage min time na aiki ko na samu na kasance dake, na ɗan taimaka miki da wani abu, nayi deciding samo 'yar aiki ko da da shara da wanke-wanke sai ta tayaki tunda matar Kamal ba zama take sosai itama tana school"

"Karka damu Babe zan iya fa"

"Kiyi haƙuri ni kaina na san aikin ya miki yawa dan har nayi magana da Mommy za a samo mana 'yar aiki, wadda zata zauna anan ba wai day ba"

"Shi kenan amma bana son tsohuwa, baku na son budurwa, a samo yarinya wadda bata wuce shekara sha biyu zuwa sha uku ba, kuma ƙwaila" Murmushi ya yi wanda har sai da haƙoransa suka bayyana, ya kalleta ya ce "Baby kishi" "Eh mana ai dole nayi kishi, su tsofaffin nan da sun ga gida zasu fara hango ina ma ace jikarsu ce a ciki, 'yammata kuma su fara karairaya suna jan hankalin maigida, dama zaurawa ba a magana wannan taƙadaraine, to amma yara basu da hankalin da zasu iya wannan, da kin fara girma kawai zan ajjeki na nemi wata"

Dariya sosai ya yi lokacin da ya ji Hamdiyya na rattabo bayanai ita a dole kishi take.


           ***** *****


"Ashe za ki zo, na ɗauka ai ba zaki zo ba" Atika ta furta tana kallon Sumayya, tana sanye da wani rantsatstsan lace black da touch ɗin golden, kana ganin lace ɗin ka san mai tsada ne.

Murmushin ƙarfin hali Sumayya tayi tare da faɗin "Bikin ki ne Atika, meyasa zan kasa zuwa in har da lafiyata?"

"Kin daina fushin da jin haushin kenan"

"Ba wannan maganar nazo mu tattauna ba Atika, farin ciki nazo tayaki, dan Allah mu ajje waccan maganar a gefe."

"To shikenan mun ajje amma fa nan gaba zamuyi ta, dan yaƙe nake gani a fuskarki ba fara'a ba"

"Ni ba ƙanwarki bace da za ki sakani a gaba kina min wannan maganganu, mu cigaba da abinda ya dace"

"To mu shiga ciki ki gaisa dasu Inna mana?"

"Inna? Ai ni babu Innata a gidan nan, bani da kowa sai ke, kuma tunda naci karo dake a waje ba sai na shiga ba"

Murmushi Atika ta yi tare da faɗin "To matsalar dama dake ne ba dani ba, shiyasa ni suke yin nan-nan dani."

"Yanzu ba wannan ba, Atika ina so mu koma gefe muyi magana"

"Wace magana kenan?"

"Ke dai muje" Ta furta tana jan hannunta suka koma inda ba mutane sosai.


"Atika dan Allah ina son komai ya wuce, kin ga ke kaɗaice 'yar uwata bani da wani samanki a kaf faɗin duniyar nan, dan Allah mu haɗa kanmu kar saboda wani abu da bai kai ya kawo ba ki riƙa jin haushi na, kiyi haƙuri, domin wallahi duk abinda nayi ban yi da niyyar ɓata miki rai ba, bana so ki shiga matsalar rayuwar aure irin wadda na shiga shiyasa ma kika ga na ɗaga hankalina"

"Adda kenan, to ai ba kowa ne zai shiga kalar matsalarki ba, saboda ni dake akwai bambanci, ke aura masa ke aka yi, ni kuma gani na ya yi ya ce yana so"

"Na san haka, amma ance yana da auri saki kuma matansa na shan wahalarsa, akwai maganganu da yawa a kanshi"

"Ni ba zai sakeni ba, domin riritani yake kamar ƙwai, kuma ki daina yarda da faɗin mutane dama in dai kana da kuɗi dole ka tara mahassada, to irin wannan sai kaji kayi kamar baka ji ba, idan kuma ka gani kayi kamar baka gani ba"

Ajiyar zuciya Sumayya ta sauke domin ta lura duk ta inda ta taro Atika sai ta zame, dan haka kawai ta rabu da ita ta zubawa sarautar Allah ido. Tayi matuƙar mamaki yanda taga 'yan gidan na nan-nan da Atika duk irin korar kare da irin wulaƙancin da suka wa mahaifiyarta lokacin suna raye amma tayi kunnen uwar shegu.


Ƙarfe biyar na yamma aka kawo motoci na alfarma, duk wanda zaije gidan amarya sai da aka ɗaukeshi motoci har sun yi yawa. Gidan da aka kai Atika babban gida ne, flat building mai ɗauke da ɗakuna uku, babu abinda bai zuba mata ba na more rayuwa a wannan gida, gida ne daya haɗu ya amsa sunansa gida. Sun ɗan juma kafin Sumayya tayi yunƙurin tafiya ganin har tara na dare na ƙoƙarin yi kuma tsakaninsu da 'yar tazara. Miƙewa tayi ta ɗauki hijab ɗinta ta sa, sannan ta ɗauki ƙaramar purse ɗinta sannan ta kalli Atika.

"To ni zan tafi, Allah ya baku zaman lafiya, yasa gidanki ne na har abada"

"Amin" Farida ɗaya daga cikin matasan gidan nasu wanda yanzu su suka zamewa Atika abokai ganin ta samu mai kuɗi ta ɗago daga danna wayar da take "Tun yanzu za ki tafi, ba zaki bari ayi sayen baki ba"

"Sayen baki!" Sumayya ta maimaita tana murmushi.

"Tafiya zanyi"

Atika ta ɗan buɗe mayafin da aka rufeta dashi ta kalli Sumayya "Amma za ki dawo gobe ko?"

Kallonta kawai tayi, idanunta ƙamas suke, kawai sai ta tuna lokacin da aka kaita gidan Kamal, kuka tayi kamar ranta zai fita.

"Ban miki alƙawari ba, amma dai zan dawo insha Allah"

"Shi kenan, to ki ɗebi kayan bikin yanda zai isheki saboda su Umma"

"Sai dai saboda su Umma amma ni kam alhamdulillah"

Taɓe baki Atika tayi irin ko a jikinta ɗin nan, sannan ta sauke gyalenta.


          **** **** ****

"Sweetheart a kawo abinci nan ko kuma acan parlour za ka ci?"

"Ai naga kamar Kamal yana nan ko?"

"Gaskiya ban sani ba, saboda daga bedroom sai kitchen kaɗai naje, ni ban ganshi a parlour ba, kuma ka san ba ɗakinsu zanje ba"


Ɗan lumshe ido kawai ya yi dan yanda yake jin furucin nata kamar da ɗaci a cikinsu, sai data dire sannan ya kalleta "Kin ji nace haka? Ni fa tambaya nayi saboda naga motarsa a waje, kuma na san yana yawan zaman parlour" 

"To ni ban sani ba" Ta dira daga gadon rai a ɓace, da sauri yaje ya rungumota ta baya lokacin da take ƙoƙarin barin ɗakin.

"Am so sorry babe"

"Your words is too harsh Sadeeq, it seems like kana zargi na"

"Don't think negative, wallahi is just a question, and i don't think it'll hurt you da ban yi maganar ba, but am really sorry please my Hamdis"

Ɗan taɓe baki tayi a hankali ta furta "Karka kuma" 

"Ba zan sake ba, am sorry"

"It's alright" Ta furta tare da kama hannunsa ta cire daga riƙon daya mata sannan ta koma gefen gado ta zauna.


Lallaɓata ya cigaba dayi, dan sam baya son ɓacin ranta, abincin ma anan suka ci bai fita parlour ba.


         ***** *****


Sumayya na sauka a napep ta miƙawa mai napep kuɗin, sannan ta doshi gidan kai tsaye, sai dai tana shiga, taji gabanta ya yi muguwar faɗuwa ganin abinda tayi tozali dashi.



_SaNaz_deeyah✌️🌸_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.