Free chapter · Read without an account

Page 19

by Halima Salahu Adamu · SUMAYYA

*SUMAYYA*

_Wattpad@SaNaz_deeysh_

_Arewabooks@sanazdeeyah_

Youtube: ***

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*

_[tushen mu'amula tagari]_


```Page 19```


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Amira ta furta tana ƙarasowa da sauri. Ayrah kuwa tuni ta sauke gwiwoyinta ƙasa a gabanshi. "Yaya!" Ta furta a kiɗime, sannan ta ɗago ta kalli Amira "Me kika faɗa masa?" Ta furta tana kuka, ita kuwa Amira da sauri ta nufi kiran Dr dan bata tsaya bawa Ayrah amsa ba.


_30 Minutes Later_


Yana kwance a gado an saka masa oxygen, su kuma suna daga waje dan an hanasu shiga. "Dan Allah ki faɗa min me kika faɗa masa?" Ayrah ta faɗa tana kallon Amira, har ta buɗe baki za tayi magana kawai su Mommy suka ƙaraso, da gudu kuwa Ayrah ta rungume Goggo. "Ina Sadeeq ɗin?" Shi ne abinda suke tambaya.

"An hana a ganshi Goggo yana ciki bai san inda kanshi yake ba."

"To mene ya jawo hakan?"

"Nima ban sani ba, naga sun yi magana da ƙanwar Aunty Jidda sai ya dawo yana ce min na kaishi gurin Goggo, kawai kuma sai ya faɗi ƙasa"

"Ina Amiran take?" Mommy ta tambaya tana kallon Ayrah, juyawar da Ayrah za tayi taga babu Amira.

"Yanzu muke tare anan ban san ina tayi ba."


A sanyaye ta shiga ɗakin, Jidda ce kaɗai zaune, kujera taja ta zauna sannan ta saki nannauyar ajiyar zuciya. "Ya dai?"

"Laaa babu komai" Amira ta furta tana dariyar yaƙe sai kuma ta kauda kai gefe. "Da alamu fa baki da gaskiya"

"Haba wane irin rashin gaskiya..." Tana gama faɗa aka turo ƙofa. Ji tayi gabanta ya yi mummunar faɗuwa ganin Ayrah da Goggo da kuma Hafsa a ɗakin.

"Goggo barka da zuwa" Jidda ta faɗa tana ƙoƙarin sauka. "Yi zamanki Jidda ba sai kin tashi ba, ke da baki da lafiya"

Murmushi tayi, a lokacin kuma Amira ta miƙa mata kujera ta zauna.

"Ya jikin naki?"

"Da sauƙi Goggo"

"Allah ya ƙara sauƙi kinji"

"Amin" Ta furta kanta a ƙasa. "Ai naso na ƙara dawowa to ƙafa ce ke damuna, yau ɗin ma na dole ne, Sadeeq aka ce ya faɗi shi ne muka taho gabaɗaya"

Da mamaki Jidda ta ce "Wane Sadeeq, yanzu ya bar nan lafiya fa"

Jin haka ya saka Amira sosa kai sai kuma tazura takalmanta "Yaya Jidda ina zuwa"

"Ina kuma za kije Amira ai gurinki muka zo"

"Ni kuma?"

"Eh mana, muna so ki faɗa mana abinda kika faɗawa Sadeeq wanda har ya saka ya faɗi, dan yanzu haka bai san inda kansa yake ba" 

Kallon Jidda tayi suka haɗa ido. "Amira!" Jidda ta furta da mamaki dan tunda taji haka ta tabbatar Amira ta fallasa komai. Turo baki Amira tayi ta ce "Ni fa kiyi haƙuri Yaya Jidda dan na faɗa masa komai"

"Ya Salam" Jidda ta faɗa tana dafe goshi.

"Kenan kema kin san komai?" Cewar Goggo.

"Ai ita ta fara gani ma" Amira ta faɗa.

"Idan kika sake magana wallahi sai na wanka miki mari" Jidda ta furta rai ɓace. Goggo ta mayar da kallonta ga Jidda.

"Kenan kema kin sani, to idan kun ɓoyewa kowa ai ni bai kamata ku ɓoye min ba."

"Goggo na roƙeki da girman Allah ki bar maganar nan bata da amfani wallahi, kuma sai dana gargaɗi Amira nace karta faɗa amma shi ne ta faɗa"

"To wai mene wannan?" Shiru suka yi. Haka su Goggo suka kaɗa suka raya amma Jidda taƙi faɗa, kuma ta gargaɗi Amira ma, ƙarshe dai kuka ta saka musu.


A tsorace Hamdiyya ta shiga ɗakin, idanunta akan Sadeeq dake kwance har lokacin da oxygen maƙale a hancinsa. Hafsat ta kalleta tare da faɗin "Sannu da zuwa" 

Harara Hamdiyya ta zabga mata, dan ta san cousin ɗinsa ce, kuma kowa yana waje amma dan kilibibi ta shigo tana tsaye gabansa tana goge hawaye har idanunta sun canja kala.

"Ya kike kuka kamar ance miki ya rasu?" Hamdiyya ta faɗa da ɓacin rai, ita dai Hafsat bata tanka mata ba, sai ma fita da tayi ta bar ɗakin.


          ******* *******


Juyi kawai take akan ledar tsakar ɗakin tana cije laɓɓanta, tana jin mararta na mata wani irin ciwo da bata taɓa jin irinsa ba. Cikin ikon Allah sai ga Jamilu ya shigo kamar an jefo sa.

"Lafiya?" Ya furta yana kallonta.

"Marata kamar za ta fashe, kuma na fara zubar da jini"

"Jini kuma subhanallahi" Ya furta a kiɗime sannan ya ce "Maza ɗauki mayafi mu koma asibiti" Sam kasa tashi tayi sai shi ne ya ɗauko mata hijab ta saka sannan ya kamata suka shiga napep sai asibiti.


Bayan an gama mata 'yan gwaje-gwaje ya ce "Tayi ɓari har sau biyu ko?"

"Eh Dr" Cewar Jamilu.

"Mahaifarta bata da wani ƙwari sosai shiyasa ciki yake saurin zubewa, dan haka indai kuna son ta haife cikin nan lafiya to kuyi ƙoƙarin hanata yin aiki mun bata bed rest daga nan har ta haihu, duk wani aiki na wahala kar tayi haka doguwar tafiya ma" Kallon Sumayya ya yi sannan ya ce "To Dr inshallah zamu kiyaye."

Magunguna aka rubuta ya saya sannan suka tafi, ganin ba hanyar gida suka yi ba ya saka da ƙarfin halin ta yi masa magana "Naga kamar ba gida muka nufa ba"

"Eh zan kaiki gidan Umma" Shiru tayi bata ce komai ba, shi kuma ya cigaba da faɗin "Tunda Dr ya ce an baki bed rest gara can ɗin"

"Amma sai in zauna ina ganin Umma na aiki"

"Sumayya baki san yanda nake ƙaunar cikin jikinki ba, wallahi idan kika kuskura kika salwantar dashi za ki haɗu da ɓacin raina, zan kaiki gidane dan na san Umma ba zata sa kiyi aikin komai ba, kuma kema ki kiyaye"

Wani sanyi taji a ranta ta san tunda Allah ya ɗorawa Jamilu son cikin tabbas za ta samu sassauci na azabar da yake gana mata.


Umma hamdala kawai take tana kallon Sumayya kafin ta ce "To Sumayya ban yarda ko tsinke ki ɗaga ba"

"Umma taya za ai ina ganin kina aiki kuma in kasa taimaka miki?"

"Ai na ɗan lokaci ne Sumayya kuma ai kina taimakawa yanzu ma larurace" Shiru kawai tayi ta sauke kanta ƙasa tana jin tsananin kunyar Umma.


Tun daga wannan rana Sumayya take ganin gata daga Jamilu, fruits har yawa suke, kaji kuwa babu irin suyar da bata gani, duk wani abinda take so shi yake mata, har cikin ranta take jindaɗi da ƙara ƙaunarsa, tuni ta manta duk irin wulaƙancin da ya yi mata a baya.


            ***** *****


Tana shigowa ɗaki ya juya kai, jikinta a sanyaye ta ajje basket ɗin da tazo dashi. Har ƙasa ta kai ƙafafunta.

"Mommy ina wuni?"

"Lafiya lau Hamdiyya ya gidan"

"Lafiya lau ya jikin nashi"

"Da sauƙi sosai dan yau muke tunanin za a sallame mu ma"

"To Allah ya ƙara sauƙi"

"Amin ya rabbi."


"Sadeeq ya jiki?" Ta faɗa tana kallonsa, bai ko kulata ba, kamar ma ba dashi take magana ba, ganin haka ya saka Mommy miƙewa "Bari na karɓo wasu magunguna"

"Mommy ki bani sai na karɓo"

"A'a ki zauna ki kula dashi karki damu"

Mommy na fita ta miƙe ta koma kujerar da ta tashi.

"Babe ka barni a duhu ka faɗa min laifin da nayi"

"A gadon asibiti kike so mu tattauna matsala? Da Allah Hamdiyya kiyi min shiru bana son magana"

"Amma..."

"Kin ga idan ba zaki iya shiru ba to ki kama gabanki, ai tuntuni nake faɗa miki ki daina zuwa"

"Taya zan daina zuwa kai fa mijina ne"

"Mtsww" Ya yi gajeran tsaki, a lokacin kuma Hafsat ta kunno kai. Kallonta Hamdiyya tayi taji ranta kawai ya ɓaci ta kauda kai gefen

"Yaya an bamu sallama"

"Ke aka bawa?"

"Eh yanzu haka Daddy ya taho"

"Okay."


           ***** *****


"Ko 1min bana so ki ƙara a gidana ki fice ki bar min, kuma ki tattara komai naki bana son ganin duk wani abu daya dangance ki Hamdiyya." Suna shigowa parlour ya faɗi haka, Hafsat da Ayrah na biye dashi.

"Ban san laifin da nayi maka ba, tunda aka kwantar da kai naga ko gurinka baka son naje me nayi ma?"

"Ki daina ɓatawa kanki lokaci ba zan shiga wancan side ɗin ba har sai na tabbatar kin ɗebe kayanki kin ƙara gaba"

"Babu inda zanje, bayan ni ban maka komai ba" Ta furta a fusace. Kallonta ya yi idanunsa har sun fara canjawa saboda ɓacin rai, hannu ya ɗaga ya wanketa da marin da har sai da ta kusa kifawa.

"Sadeeq meyasa haka?" Hafsat ta faɗa cike da mamaki dan ta san Sadeeq yana da haƙuri sosai.

"Babu ruwanki" Ya furta yana kallonta kamar wani zautacce.


Kamal daya fitowa daga side ɗinsa ya ƙaraso gurinsu, har lokacin hannun Hamdiyya na kan kumatunta.

"Ina ta jiyo hayaniya ashe kune, yaushe aka sallamoka?"

"Ban sani ba" Ya furta rai ɓace.

"Baka sani ba?" Kamal ya maimaita.

"Eh ai so kai na mutu ku cigaba da baɗala da matata to ban mutu ba na tashi"

"Sadeeq kana cikin hayyacinka kuwa, Ka san me kake faɗa?"

"Kamal ƙarya kake ka cigaba da ɓoye min abu, na gano komai kuma ba zan taɓa rufa maka asiri ba, sai na shiga gidan tv da gidan radio na faɗawa duniya kai azzalumine matarka ita ta kamaku kaida matata kuna iskanci a kan gadonka na sunnah Kamal, Me nayi maka?" Sai kuma Sadeeq ya fashe da kuka.

"Duk irin ƙaunar da nake muku ashe da sharri zaku saka min, Jidda ko Amira babu wanda zai muku sharri, kuma kai ka san dalilin daya saka matarka naƙudar dole ta zo mata shiyasa ko dubiya ka kasa zuwa ka fake da jinyar ƙarya."

"Ni zaka yiwa sharri Sadeeq?"

"Sharri fa kake faɗa? Ka daina borin kunya Kamal wallahi har abada ba zan taɓa yafe muku ba, Kamal an faɗa min komai game da cikin Sumayya ma cikin halal ne, kai da kanka kayi mata amma kuma ka ƙaryata dan ka tozarta ta saboda kawai an aura maka ita bada son ranka ba, Mommy tabi bayanka akan rashin gaskiya a kira Laila ai ta san komai, ya juya kan Hamdiyya dake ta kuka ya ce "Hamdiyya naso ki fiye ma da kaina, duk abinda nake ina yi domin ki ne, ban taɓa tauye miki wani haƙƙi ba tunda na aureki, amma ki rasa sakayyar da za ki min sai lalata da ɗan uwana ciki ɗaya, to kije na sakeki kuma Allah ya isa ban yafe ba." Yana gama faɗa ya kalli Hafsat "Bani key ɗin motana"

"Sadeeq..."

"Ki bani key Hafsat" 

Kuka ta saka tare da faɗin "Taya zan barka kayi driving a haka?"

Hannunta ya murɗe ya karɓi key ɗin da sauri ya fita, ita kuma Ayrah da gudu ta mara masa baya, sai dai tana zuwa ya riga har ya tayar da motar, tayi ƙoƙarin bin shi amma sam ta kasa.


          **** ****


"Kin lalata komai Amira, meyasa za ki faɗa masa?"

Murguɗa baki tayi tare da faɗin "Ai dole na faɗa masa, sharri suka aikata fa haba"

"Amma sai ki bari abi komai a hankali ko?"

"Kina so kice min so kike ki koma gidan Yaya Kamal ɗin?"

"Idan zan koma gidansa ai ba zan dawo nan bayan an sallameni a asibiti..." Shigowar Amma ya saka suka yi shiru.


kallonsu tayi sannan ta zauna gefen gadon. "Jidda" Ta kira sunanta a hankali.

"Na'am" Jidda ta amsa a sanyaye.

"Me yasa baki faɗa min duk abubuwan da suka faru ba?"

Ji tayi hawaye ya cika mata kurmin ido, ta saka hannu ta goge. "Ai da kin faɗa bama zan bari ya bar asibiti ba har sai ya baki takarda, dan wallahi ba zan taɓa bari ki cigaba da zama da fasiƙi ba." Ji tayi gabanta ya yi mummunar faɗuwa.

"Amma..." Sai kuma tayi shiru.

"Ina jinki"

"Amma ni na san Kamal yana sona, Amma wallahi na san akwai dalilin daya sa hakan ta kasance." Amira baki ta saki tare da faɗin "Gaskiya Aunty Jidda kin ban mamaki, kina nufin ba laifi ya yi ba?"

"Ni bance ba laifi ya yi ba, amma ina da dalilai guda biyu" Kallon Amma tayi sai kuma ta sauke kai.

"Ina jinki"

"Kamal yana shaye-shaye ta yuwu itace tazo masa sai ya yi tunanin ni ce. Sannan kuma har ma da alhakin Laila wallahi, na ci amanar 'yar uwata"

"Ban taɓa sanin baki da hankali ba Jidda sai yau, ashe har so zai iya rufe miki ido ki kasa gane laifin mutumin da kika kama a gadon aurenki?

"Amma tabbas so ya rufe min ido, saboda hakan ce ta saka na kasa ganin cewar tare da 'yar uwata cousin sister ɗina na gansu suna soyayya amma ya dawo ya yi min daɗin baki tare da ƙaryar ba soyayya suke ba, ni kuma na kasa yin bincike ko kuma tambayarta saboda tsananin son shi dana kamu, ƙarshe dai a ranar dinner ɗinmu tazo tayi tijira"

Miƙewa Amma tayi tana kallonta rai a ɓace "To na rantse da Allah ko son shi zai kashe ki ke dashi har abada, takarda kuwa sai dai ya aiko gida, amma wallahi ba za ki koma gidansa ba" Tana gama faɗa ta wuce rai a ɓace.


           ****** *******


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Shi ne abinda Daddy ya faɗa yana kallon Ayrah.

"Yanzu ke kin san wannan amma kika kasa faɗa, har sai da aka kai sati biyu da faruwar lamari."


Girgiza kai Mommy take kafin ta ce "Inaaa! Ba zai taɓa yuwu wa ace Kamal ya nemi matar ɗan uwansa, hakan ma ba zata taɓa faruwa ba. Ayrah meyasa kike muguwar maƙaryaciya, shiyasa sam baki burgeni"

"Wai kina da hankali kuwa? Ya za ki riƙa faɗar haka a gabanta 'yar da kika haifa ce fa"

"Daddy ni dama na san bata sona, amma wallahi duk abinda na faɗa gaskiya ne, har na Aunty Sumayya, kuma Aunty Hafsat ce ta ce kar na faɗa, idan baku yarda ba ku kirata ku tambaya sannan kuma ku tambayi matar Yaya Kamal ɗinma." Ta furta cikin matsanancin kuka, sannan ta kalli Mommy "Na san baki ƙaunata Mommy kin tsaneni ban san mene nayi miki ba, dan haka zan bar miki duniyar kawai" Tana faɗa ta miƙe da wuce da sauri, Daddy yana kiranta amma sam taƙi ta saurare shi.

"Nihal ki kirata kar taje ta yiwa kanta illa" 

Da sauri Nihal ta bi bayanta sai dai tana zuwa ta tarar ta kulle ƙofa.


_SaNaz_deeyah_🌸

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.