Free chapter · Read without an account

KADDARA CE... 2

by Salma Ahmad Isah · KADDARA CE!

*ƘADDARA CE!*



*©SALMA AHMAD ISAH.*

*CANDY🦋*


_ArewaBooks @SalmaAhmad_

_Wattpad @Salma_Ahmad_Isah_



_Perfectly pen's 🖊️_



*Paid book*



*02*


*No.53, off Justice Clara Ogunbiyi street, Asokoro, Abuja.*


MU'AZ POV.


Mutum biyar ne zaune a kan dinning table suna yin breakfast. Shi kaɗai ne a cikinsu yake cin abinci da hannunsa. Yayin da kowa yake ci da spoon. Mahaifiyarsu Hajiya Hauwa, wadda suke kira da Mummy ce ta dube shi.


Yanda ya dage yake cin abincinsa bil haƙƙi da gaskiya. Dan idan kana so ku saɓa da Mu'az a ƙi ba shi abinci lokacin da yake jin yunwa. Idan kuma kana so ka burgeshi ka masa kyautar abinci ka ga ƙauna. Shi da abinci 5 and 6 ne.


Shi ya sa kaf yaran gidan su biyar. Wanda suka ƙunshi babbar yayarsu 'yar matar Daddynsu ta farko wadda Allah ya yi wa rasuwa. Me suna Farida. Sai shi da ya kasance ɗan Mummy na farko, sai Mariya da take bi masa. Sanna Safiyya da ta ci sunan mahaifiyar Daddy, suna mata inkiya da Mima. Sai auta Na'im. Duk cikinsu ya fi kowa ƙiba. Duk da shi ma ba wai ƙibar ya cika ba. Amma ya fi su jiki. Sai Mima da ita ma take da 'yar ƙiba.


Kuma a duk cikin yaran Daddy su biyar, ya fi kowa farin fata. Dan shi farin Mummy ya biyo su kuma duk baƙin fatar Daddy suke biyowa. Hakan ya sa ya fita da ban a cikinsu. Idan ka ganshi ba lalle kace ɗan gidan ba ne. Saboda yana da fari sosai, saɓanin sauran 'yan uwansa da suka kasance baƙaƙe.


“Mu'az!”


Mummy ta kira. Hakan ya sa ya ɗago da fararen idanuwansa ya ɗora a kanta yana amsawa.


“Na'am Mummy”


Cikin tsare shi da ido Mummy tace.


“Me ka je ka aikata a gidan Hajiya Hadiza?... Jiya da daddare bayan ka dawo daga gidan ta kirani tana ta masifa!”


Maganar Mummy ta janyo hankalin kowa kansu. Shi kuma sai ya yi murmushi yana maida hankalinsa kan cin abincinsa. Dan ya tuno da tsiyar da yaje ya yi a wurin yarinyar aminiyar Mummy da tace masa ya je dan su daidaita juna.


“Ka san baka da gaskiya ke nan?”


Faɗin Mummy. Alhaji Jibrin Gimba Gashuwa ya kalli matarsa yana faɗin.


“Me ya yi kuma?”


Cike da jin haushin abin da ya aikatawa 'yar aminiyarta Mummy tace.


“Tsabar shi abin magana ba ya masa kaɗan. Ya taka ya je har gidan aminiyata Hajiya Hadiza, dan ya ga 'yarta Rashida su daidaita. Tun da shi ya kasa zaɓawa kansa matar aure. Wai ya dubi Rashida ya ci mata mutunci, har da cewa wai ita ƙazama ce. Kuma ta masa kaɗan a matsayin matar aure!... Maganganu dai babu daɗin ji!”


Daddy ya dubi Mu'az dake murmushi. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Mu'az yace.


“Iyaka abin da na ce kawai ta faɗa. Ba ta faɗa miki abin da ita 'yar tata ta min ba?”


“Me Rashidan ta maka?”


Daddy ya tambaya.


“Saboda Allah Daddy. Kamar ni Mu'azzam Jibrin Gimba za ta shanya a ƙofar gida ina jiranta. Wai tana kwalliya?. Ko me za ta yi wa kwalliyar?. Wannan mummunar baƙar ƙazar fuskar tata da bata rabo da majina sanda tana yarinya ko me?... Kuma da ma can fa ni ba ta min ba. Yarinyar ba class ɗina ba ce. And ta cika rawar kai da yawa!”


Cike da mamakin abin da yayanta ke faɗi a kan Rashida Mima ta ɗaga kanta sama tana hango fuskar Rashidan. Ko ita da take mace Rashida na burgeta. Saboda iya wankanta da son gayu. Amma tsabar wulaƙanci irin na Mu'az cewa yake wai ƙazama ce!.


“Ya Mu'az Rashidan ce ƙaz...”


Shiru ta yi saboda kallon da ya mata. Ta haɗiye maganar ta kora da miyau ɗin bakinta. Mu'az ya harareta yana faɗin.


“Ƙaramar mara kunya!...”


“Sannu shugaban marasa kunya!...”


Faɗin Mummy a ƙufule ita ma tana wurga masa harara.


“Mu'az”


“Na'am Daddy!”


Ya amsa a ladabce.


“Rashida ce ba ta maka ba ko wata ɗabi'a ce gareta wadda baka so?”


Ya yamutsa fuska yana faɗin.


“Ta min ƙanƙanta da yawa. Sa'ar Mima ce fa Daddy. Kuma taba da rawar kai. Ga ta cika iyawa... Gaba ɗayanta ma bata min ba. I dislike her at all!...”


“Ka kyauta. Ka kyauta da ka zubar min da mutunci a idon aminiyata”


Mummy ta tari numfashinsa.


“Hauwa! Kin san ni me son abin da yarana suke so ne. Tun da har baya sonta babu yanda za ayi na aura masa ita. Da ace yana sonta kuma sai inda ƙarfi na ya ƙare wurin neman aurenta!”


“Shi ya sa nake sonka Daddy. You're the best!”


“Ban gama da kai ba ai... Dan baka son Rashida bai kamata ka riƙa kusheta ba. Hakan babban kuskure ne. Da fatan za ka kula nan gaba!”


Sai ya sunkuyar da kansa yana faɗin.


“To Daddy. Za a gyara!”


Wayarsa dake aje a gefen plate ɗin da yake cin abinci ce ta shiga ringing. Hakan ya sa ya ɗauka domin duba me kiran, ganin Faruk ne ya sa ya amsa.


“My Gee what's up?”


“Fine Wallahi. Ya ? Me ya sa ba ka zo barrack ba har yanzu?”


Mu'az ya miƙe tsaye wayar kare da kunnensa ya nufi sink domin wanke hannunsa da yaci abinci da shi. Saboda shi duk rintsi duk wuya ba ya cin abinci da spoon ko fork.


“Cin abinci na tsaya. Ka san aikin nawa ma ba zai iyu ba ba tare da na cika cikina ba!”


“Aikin ke nan ai. To sai ka yi sauri ka zo dan mu je mu haɗu da Muktar (Ɗan sandan da yake bincike a kan case ɗin mutuwar Munira) ɗin. Tun da yace gobe zai yi tafiya”


Mu'az ya goge hannunsa da toilet paper yana faɗin.


“On my way”


Daga haka ya sauƙe wayar ya dawo dinning area.


“Mummy ni zan tafi... An jima zan aiko driver ya zo ya karɓa min abinci!”


Mummy ta wurga masa harara tana faɗin.


“Saboda ga Mummy baiwarka ka aje za ta maka girki ko?”


Mu'az ya ƙunshe daiyarsa.


“Oh lord of mercy!”


Ya faɗa, sannan ya kalli Mima.

“‘Yar lukuta ki min girki zan aiko a karɓa min. Yau Mummy ta yi fushi da ni!”


Ba dan Mima ta so ba haka ta gyaɗa masa kai. Dan ita yau ta riga da ta tsara fita tare da ƙawayenta. Kuma bata isa ta masa musu kan ba za ta yi ba. Ita a wa?. Yanzu sai ya hauta da bala'i. In ba sa'a ba ma ta kaisu ga duka.


“Oga tulele ka gama mu je na sauƙeka?”


Ya faɗi yana kallon Na'im. Na'im ya ɗauki bagpack ɗinsa yana faɗin.


“Eh na kammala mu je”


Suka yi wa Daddy sallama suka fita tare. Mummy ta yi ƙwafa.


“Wai yanzu haka za'a zuba masa ido ya zauna babu aure?. Ga shi Mariya da take ƙanwarsa har da yaro ɗaya. Amma shi tsayuwa da 'yan matan ma ya ƙi. Ballantana har a fara batun yin aurensa!”


Daddy ya yi murmushi yana sipping tea ɗinsa. Ya aje mug ɗin yana faɗin.


“Hauwa ke nan!. Shi fa aure da mutuwa duk lokaci ne da su. Idan Allah ya nufa sai ki ga an yi nan kusa. Wata ƙila kuma shi nasa rabon a nesa yake”


“Hum-um. Ai bana jin Ya Mu'az zai yi aure kwana kusa Daddy. 'Yan mata nawa Mummy ta masa?. Amma duk cikinsu cewa yake babu wadda ta masa. Har da wadda yace warin baki take. Ai babu me iyawa wannan mutumin sai Allah. Ga zafin zuciya kamar garwa shi. Ga hancini!. Ga faɗar baƙar magana kamar jikan kutare!...”


“Duk zai daina with time. Har yanzu Allah bai haɗa shi da wadda za ta dace da shi ba ne...”


Daddy ya katseta. Mima ta taɓe bakinta tana ganin rashin iyuwar hakan. Dan a ganinta, babu budurwar da za ta iya zama da yayanta da halayensa. Su ma da suke 'yan uwansa wasu lokutan kasa ɗaukan halin nasa suke ballantana wani da ban.


*Nigerian Army resources center, Mambilla Barrack, Asokoro, Abuja.*


“Hello! Sirikina ina kwana”


Faɗin Mu'az a lokacin da ya shiga office ɗin Faruk dake jiransa. Dan bayan ya je ya aje Na'im a school kai tsaye ya wuto nan barrack ɗin. Saboda daga gidansu zuwa Barrack ɗin ba nisa.


Faruk dake tsaye a jikin shelf yana duba wani file ya jiyo ta kalli Mu'az ɗin dake shigowa office ɗin. Kamar kullum, sanye yake da wandon kakin sojoji, da kuma rigar da suke sakawa a ƙasan rigar uniform ɗin nasu me kama da T-shirt. Amma shi kam da ma abu ne me wuya ka gan shi sanye da complete uniform.


A cewarsa waccan ta saman takura shi take. Saboda shi da riga kamar maƙiya suke. Idan ka gan shi da complete uniform to meeting zai shiga, ko kuma akwai wani wurin da zai je ba barrack ba.


“Sannu da zuwa sir”


Faɗin Faruk yana sarawa Mu'az ɗin. Kasancewar shi ne sama da shi. Mu'az ya cire glasses ɗin idonsa yana faɗin.


“Karka sa na ji kunya mana sirikina. Ni ban san wannan abin. Ka share kawai”


Faruk ya sauƙe hannunsa yana murmushi. Dan wannan ɗin magana ce wadda ya haddaceta a cikin kansa.


“Ina ɗana?”


Mu'az ya tambaya.


“Lafiyarsa ƙalau.”


“An jima muna da meeting da general Haladu Mansur. Gwanda mu je mu ga Muktar kafin lokacin ya yi”


Ya faɗi yana maida glasses ɗinsa.


“Okay”


Daga haka suka fita zuwa FCID domin jin yanda binciken mutuwar abokiyar aikinsu ya kwana.


*FCID (Force Criminal Investigation Department), Moshood Abiola Road, Garki, Abuja.*


“A halin yanzu mun yi nasarar gano wuri na ƙarshe da ta halarta kafin ta ɓata. Kuma abin da muke ta ƙoƙarin yia yanzu shi ne gano wanda ta haɗu da shi a wurin. Saboda mun gano wani saƙo a wayarta dake nuna cewa wani ne ya kirata zuwa wurin domin su haɗu. Daga zarar mun samu damar gane wanda ya aiko mata da saƙon za mu iya cewa mun kama me laifin. Saboda shi ne abin zargi na farko!”


Mu'az da Faruk suka dubi juna a tare. Kafin suka kalli Muktar ɗin da ya gama zayyano musu bayanin.


“Lord have mercy!”


Faɗin Mu'az yana furzar da iska ta bakinsa. Yayin da Faruk da ya fi kowa shiga damuwa a kan case ɗin ne ya shafa kansa cike da damuwa.


Saboda ɓatan abokiyar aikin nasu me suna Munira tashi ɗaya ya basu mamaki. Hakan ya sa suka bazama nemanta a ko ina. Bayan sati ɗaya da ɓatanta kuma suka samu labarin tsintar gawarta a wani layi. Babban abin tashin hankalin ma shi ne an tsinci gawar tata ne ba tare da wasu sassa na jikinta ba.


Saboda tsabar yanda makashin ya bata wahala wurin kasheta ya sa su kansu ba su tabbatar da cewa gawarta ba ce sai da iyayenta suka zo suka tabbatar da cewa ita ce. Kuma tun bayan rasuwarta da Mu'az Faruk ba su huta a kan binciken wanda ya kasheta ba.


“Ka yi haƙuri Kaigama. Da yardar Allah za'a kama mai laifin”


Faɗin Mu'az a ƙoƙarinsa na kwantarwa da Faruk hankali. Ganin yanda suka fito daga headquartern duka a dame. Cike da damuwa Faruk ya dube shi yana faɗin.


“Har yanzu na kasa mantawa da hoton gawarta da na gani a idona MJ. Kuma hoton tashin hankalin da ahalinta suka shiga lokacin mutuwar ya kasa fita daga kaina. Ba na jin hankalina zai kwanta idan har ban kamo me laifin nan ba MJ!”


Mu'az ya dafa kafaɗarsa.


“Insha'Allah za mu kamo shi!”


“Allah ya yarda”


MAIMUNA POV.


Kamar yanda ta saba farkawa sassafe haka ta farka a asubar yau ma. Abu na farko da ta fara yi shi ne alwalal sallahr asuba. Ta dawo ɗakinta ta tada sallahr. Kuma bayan ta idar ta fita tsakar gidan ta fara aikinta na safiya kamar yanda ta saba.


Duk da yanda sanyin safiyar yake sauƙa a kanta bata haƙura da aikin ba. To da ta isa ma ta haƙura da aikin?. Ita a wa?, Kare da gudun layya?. Sai da ta yi shara. Sannan ta wanke kwanukan da aka ɓata a daren jiya. Kafin ta zauna ta fara firar doyar da za ta dafa ta kuma soya domin kai wa makarantun safe dake kusa da su. A lokacin Auwwa ta fito daga ɗakinta tana hamma.


Kanta ta ɗaga ta kalli Auwwan. Sannan ta gaisheta a ɗarare. A ranta take ƙiyasta lokacin da Auwwan ta tashi. Dan ta san lokacin dai ƙarfe bakwai za ta yi. Kuma ita ba ta isa ta tasheta a bacci ba. Saboda kyakkyawan warning ne daga Auwwan, kan kada ta kuskura ta tasheta idan tana bacci.


A kan idonta Auwwan ta ɗauki buta ta yi alwala. Sannan ta shiga ɗaki domin yin sallah. Sai da a kammala fere doyar sannan Gambo yayanta ya shigo gidan. Kallonsa ta yi tana gaishe shi. Ko kallon arziƙi bata samu daga gare shi ba. Ballantana har ta yi zaton zai amsa gaisuwar tata.


A tasowarta a gidan bata jin akwai rana ɗaya da suka taɓa yin magana da ɗan uwan nata ta minti biyar ta arziƙi. Ko kalo bata ishe shi ba ballantana har su samu damar yin hira. Kuma da ma shi ba zama yake a gidan ba. Kullum yana waje wurin abokansa masu hayar napep.


“Ke Maimuna!”


Auwwa ta ƙwala mata kira daga cikin ɗakinta bayan Gambo ya shiga ɗakin.


“Na'am”


“Ki yi maza ki ɗora ɗumamen tuwo yanzu. Gambo yace yunwa yake ji”


“Auwwa na ɗora tukunyar doya fa”


Tsautsayin shan zagi ya sa bakinta ya suɓuta wurin faɗar hakan. Ai ko an danƙaro mata zagin. Dan sai da Auwwa ta zaɓo wani zagi tun na zamanin maguzawa ta makawa uwarta dake cikin ƙasa.


“...Gidana ko gidanki?. Da har zan ce ki yi abu ki kawo son ranki”


“Allah ya baki haƙuri”


Maimuna ta faɗi. Tana nadamar maganarta ta farko. Jiki na rawa ta sauƙe ƙatuwar tukunyar doyar da ta ɗora. Sannan ta ɗora ta ɗumame.


“Kuma ki cire bayan tuwon da ya bushe”


Ta ji Auwwa ta sake faɗi daga cikin ɗakin.


“To”


Ta amsa wani sashi na zuciyarta na farin ciki. Dan ta riga da ta san yau babu rabonta a ɗumamen nan. Kuma tun da Auwwa tace ta ɓare bayan tuwon tana nufin ta zubar bata so. To ita kuma da wannan damar take amfani wurin rage yunwar da take damun cikinta. Dan idan ta ɓare bayan wankewa take, sai ta ɗan saka yaji ta ci.


Yau ɗin ma haka aka yi. Tana ɓarewa bayan tuwon shinkafar da ya bushe ta saka musu tuwon a cikin miyar dake kan wuta. Yayin da ta zube bayan tuwon da ya bushe a roba, ta wanke shi, tafaki ido ta zuba yaji a ciki. Ta koma gefe ta cinye.


Sannan ta wanke robar ta aje. Ta dawo ta sauƙe tukunyar ɗumamen. Ta sanar da Auwwa cewa ɗumamen ya kammala. Kafin ta mayar da tukunyar doyar kan wuta. Tana zaune a wurin. Auwwa ta fito ta zuba ɗumamen a kwanika biyu, ɗaya nata ɗaya kuma na Gambo.


Maimuna bata ta shi daga gindin murhun nan ba sai da ta gama dafa doyar, sannan ta soyeta da fulawa tas. Ta faɗawa Auwwa cewa ta gama. Auwwan ta zo ta zauna ta lissafa kuɗin doyar. Sannan ta saka mata a cikin bokiti fallasa.


“Ta dubu uku da ɗari biyar ce. Saura kuma yau ma ki bada bashin”


Faɗin Auwwa tana hararta. Maimuna ta gyaɗa kai tana nufar randa.


“Ub*n me za ki yi kuma?”


Ta juyo a tsorace tana faɗin.


“Na ga hantsi ya fara ɗagawa ne. Shi ne zan zuba ruwa a bokita na aje a rana. Kafin na dawo daga talla na san ya yi ɗumi sai na ɗan yi wanka da shi!”


Auwwa ta maka mata harara haɗi da jan tsaki. Sannan ta miƙe ta ja tulelen jikinta ta shiga ɗaki. Maimuna ta zuba ruwa a bokita. Ta aje a rana. Sannan ta shiga ɗakinta ta saka hijabina ta fito tana ɓoye kuɗin babur ɗin da Mummy ta bata.


Ta ɗauki bokitin doya da fulawar ta fita. Kasancewar yau ƙafar tata bata ciwo ya sa ta isa makarantar Famfo goma da ta fi kusa da su da wuri. Dan a yankin unguwar tasu kusan makarantu shida ne. Kuma duk ciki babu wadda bata kaiwa tallahr doya da fulawa da safe.


Tana isa makarantar ta wuce sashin da 'yan tallah ke taruwa a babbar makarantar ta 'yan mata. Kasancewar government school ce ya sa masu kawowa tallar kayan suke taruwa da yawa. A kusa da wadda ta fi sani cikin 'yan tallar me suba Rahina ta aje bokitinta.


“Yau kin zo da wuri Maimuna. Dan sauraminti goma a fito tara”


Faɗin Rahina. Mamuna ta yi murmushi.


“Dan Allah Rahina so nake ki jire min kayana zan je asibiti a dubani!”


Rahina ta dubeta. Kasancewar ta san cewa su masu scikler ba'a raba su da jinya, ballantana kuma yanzu da ake cikin lokacin sanyi da cutar ta fi yawan tashi yasa tace.


“Ƙafar ce ko bayanki ne yake ciwo?”


“A'a. Ai yau da na tashi ban ji ciwon ƙafar ba. Auwwa ce ta ƙona ni jiya da dadare!”


Ta ƙarashe tana nuna mata singalin hannunta na hagu da ya yi alamar ƙuna. Dan fatar wurin har ta tashi Cike da jin tausayinta Rahina ta kawar da kanta gefe tana kare fuska.


“Subhannallahi. Wallahi Maimuna Auwwa muguwa ce”


Maimuna ta sunkuyar da kanta tana gyara ledar dake kan murfin bokitinta. Sannan ta ɗaga kai ta kalli Rahina dake kallonta.


“Bari na je”


“Amma kar ki daɗe”


Maimuna ta gyaɗa kai tana miƙewa. Kuma kai tsaye ta nufi bakin titi. Domin hawa napep, wadda za ta kaita Haɗejia general hospital. Duk da asibitin bata da nisa da unguwar Fantai.


Da yake ta san sashin da Mummyn su Maryam take sai bata sha wahalar nemanta ba. Kai tsaye ta je ta sameta a inda suke zama. Kuma Mummy ita ta kaita aka ɗaye fatar ƙunan da ta tashi. Sannan aka saka mata magunguna.


Kuma a pharmacy ɗin asibitin Mummy ta sai mata magungunan da aka rubuta mata, har ma da wanda ba'a rubuta ba. Wato magungunanta na cutar sickler. Kasancewar ta sanar mata cewar nata sun ƙare.


Basu rabu da Mummy ba sai da ta sai mata dafaffen ƙwai. Dan ko ba'a faɗa ba ta san cewa Maimuna na buƙatar kayan ƙarin jini. To kuma sai ƘADDARA ta sa ta taso a gidan da abincin da za ta sa a cikinta ma gagararta yake. Ballantana ta samu wanda zai ƙara mata jini. Haka Maimuna ta yi ta mata godiya har suka rabu ta dawo makarantar Famfo goma.


_Share fi sabillilah❤️_


_______________


_Ya kamata a fara biya tun daga yanzu fa!_


_If you want to subscribe pay ₦300 to._


5487270431

Salma Isah

Monie point


*Daga alƙalamin Salma Ahmad Isah✍️.*

*CANDY CE🦋.*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.