Free chapter · Read without an account

Page 3

by khadijah danasabe · ALƘALAMIN SO

ALKALAMIN SO


        BY


  DIJAHAM(Oum Amani)


Page 3


Alhamdulillah na gama exam lafiya in sha Allah zaku dinga samun update kullum kamar yadda muka saba banda weekend ranar hutu ce da kula da Oga😎✊🏻


Yadda muka fara lafiya Ya Allah yasa mu gama lafiya Ameen🥰 Ina Kaunar ku❤️




BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



Mai da kallona kan sa nayi ganin yana kallona yasa ni murmushi na nufi inda yake zama nayi a gefen katifar kusa da shi sosai cikin shagwaba nace “Uncle”


Turo baki gaba nayi cike da shagwaba bace “baka amsa ba Uncle na Kira ka amma kayi shiru”


Murmushi ne yake son subuce masa ya danne shi ya hanyar shafa girar sa cikin muryar sa mai kaushi da taushi a lokaci daya yace “naam yarinya ta”


Washe baki nayi wanda ya kusa saka shi dariya, kau da kan sa yayi kawai yana janyo bag din dake kan katifar ya dora min akan cinya ta.

  Zuba min shanyayyun idon sa yayi kamar yadda nima nake kallon sa Ina so ya ce min wani abu. Dan lumshe idon sa yayi wanda bacci yake cike dasu cikin kasala yace “bude little bacci nake ji”


Bude wa nayi Ina ciro jakar system din dake ciki, ware manyan ido na nayi na dago na kalle sa cikin matsanan cin farın ciki, ban dai ce komai ba sai na ciro System din kara bude ido na nayi ganin MacBook din daya siyo min.


Kallon sa nake Ina shafa ta nace “Jazakallah Bil Jannah Uncle Allah ya Kara arziki mai albarka da lafiyar nema kullum Allah ya raba ka da Iyayen ka lafiya kuma ya baka mata ta gari wacce zan tare a can baxa ta ce komai bah”


Murmushi kawai yayi yace “Ameen tashi ki tafi sai da safe Ina da flight by 6”


Mayar da ita nayi cikin jakar ta sannan na mike Ina sake masa godiya sosai na fice da sauri, na dade Ina son a siya min system dana fadawa Dada ce min yayi sai na shiga 15 tukun nan da 3 months In Allah ya nuna mana zai siya mun.


  Dakin Sultan na tsaya Ina bugawa da dan karfi sbd wannan abin farin cikin shi nake so na fara fada wa, zaku yi mamaki in nace muku yadda nake da sultan ba haka nake da Maryama ba duk da kuwa shi namiji ne, duk wani Sirri na Sultan ya sani don shine abokin shawara ta kamar yadda in abin farın ciki ya same ni ko bakin cikin bayan Uncle da Mami sai shi suke fara sani.


Bude kofar yayi jin irin bugun da ake masa sai dai gani na yasa shi fito wa yana rufe kofar dakin nasa tunda bana shiga ciki in ba babban abu bane, da hannun sa yake min alamar lafiya.


 Juya manyan ido na nayi Ina kai jakar kusa da fuskar sa, hannu yasa yana karbar ta daga hannu na da sauri ya dago ya kalle ni yana kuma leka cikin jakar, dariya nayi nace “ya kaga ni yaro?”


Da sauri yace “kutttt Ya Aliyu ne ya siyo miki?”


Fari nayi nace “ynxu ya bani ko part din mu ban koma ba nace sai na nuna maka”


Gyada kai yake fuskar sa dauke da murmushi yace “na miki murna sosai A’isha ynxu kallo ba kama kafar yaro shiyasa ni dai nace Ya Aliyu na spoiling din ki da yawa”


Dariya nayi nace “in bai yi spoiling din yarinyar saba kai zai yi spoiling toh?”


Dan harara ya sakar min yana murmushi mai fadi. Tare muka nufi part din mu sai hirar series din da za’a saka min a ciki muke, tura kofar gate din nayi na shiga Ina sallama a hankali duk kuwa da ba kowa a wajen don madaidaicin compound ne wanda yake dauke da kujeru na shan iska daga can gefe inda aka sa buka, kujerun guda hudu ne sai table a tsakiyar su.


Bakın mu dauke da sallama muka shiga cikin palon da sanyin Ac ke tashia nutse ba da ywa sosai ba yadda zai takura ka.


Duka iyalan gidan suna zaune a palo, Abba da Mami na zaune suna kallo suna hira kuma da Ya Aliyu sai Ya Kausar dake dan magana lokaci zuwa lokaci hankalin ta yana kan wayar ta.


Da gudu gudu na karasa kusa da Mami Ina rungume ta, dariya ta saka tana shafa bayana tace “mai muka samu ne Shatu”


Abba shima da yake Murmushi yace “da alama kam Shatu tayi babbar tsintuwa”


Ya Haidar da yake kallon su yace “ai daga wajen Ya Aliyu take ya bata wani abun ne da take so, little din Uncle mai aka samu ne?”


Dagowa nayi daga jikin Mami Ina Washe baki na ware hannu Ina nuna hannun Sultan, shi kuma daya ciwo system din daga jakar ta daga wa yake yadda kowa zai gani yana dariya.


Addu’a sosai su Mami suka dinga yiwa Uncle suna taya ni murna ni kuwa baki na yaki rufuwa sbd Jin dadi ni ji nake ai kamar baxan iya bacci bama.


Ya Kausar da take Kara duba System din tace “yarinyar nan Uncle bata ki kawai yake wallahi”


Turo karamin baki na nayi nace “Ya Kausar kamar dai ban fahimci mai kike nufi ba sbd Allah taya ni farın ciki kike ko akasin haka”


Harara ta watsa min tace “zan make miki bakin nan wallahi ni zaki ce Ina miki bakin ciki?”


Marairaice wa nayi na kalli Abba Ina kif-kif ta ido nace “sbd Allah Abba kaji nace Ya Kausar na min bakin ciki daga shigo wata gidan nan nidai ka taya ni bata hakuri in ma taji ba dai dai bane ba abinda zai sa na bata mata rai taku turo min fina finai haka kurin”


Murmushi Abba yayi yana biye mun gurin bawa Ya Kausar hakuri, ita kam bata ce komai ba sai harara ta da tayi.


Rungume ta nayi cikin marairaice wa nace “I lobiyu da yawa da yawa Ya Kausar small Mom dina nidai sbd son da nake miki ma ranar da kika yi aure tare zamu tare tun ynxu zan fara fada wa Uncle Jabir a fitar min da daki na a gidan ku”

(Shatu kin man ta kin cewa Uncle din ki zaki tare a gidan sa neh ya haka kuma?😏)



Ya kuka ji salon labarin🤌❤️




DijahAM

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.