Free chapter 路 Read without an account

Chapter 4

by Ikilima Adam 路 RAMIN KARYA

馃崅馃崅_*RAMIN K'ARYA*_ 馃崅馃崅




 NA 



IKILIMA ADAM 


 *( Kyauta daga Allah)*


Marubuciyar da ta nishandantar daku a littafanta kamar haka:


Kai ka jawa kanka



Kanwata



Rai daya ( Jan zaki)



Rudani



Makauniyar shari'a


And now


Ramin karya yan karin magana suka ce kurarre ne , mu je zuwa.



Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai .




 SHAFI NA HUDU



 " Hajiya ban taba kusantar Laila ba".


 " What wannan wace irin tatsuniya ne Prince ". Ta magantu cikin tsananin damuwa.


 Hannun Hajiya ya kama , cikin kankance idanu, tare da dan matsa hannunta .


" Kin san duk duniya ina son haihuwa, kuma ina son yara , kuma Lailat kanwar margayya Maryam ce ciki daya , taya zan mata sharri Hajiya ". ya yi shiru yana jin mugun dacin rai a kasar zuciyarsa.


" Wallahi Prince na san karya ba dabi'arka ba ce , kuma baka son me yin ta , ni dai kawai na fi tunanin kila ka kusance ta , baka sani ba ".


Cikin sauri ya dago kai yana kallon Hajiya , cike da mamaki.


  " Eh ka san mace in ta san namiji baya son ta kuma tana son shi , zata iya yin komi dan cika burinta , kila wani abun ta sanya maka a ruwa ko abinci , in har zaka iya tuna ka taba tashi da yanayi da baka san kanka ba , to shine in kuma babu , gaskiya akwai lauje cikin nadi". 


 Cikin rudewa da tsananin tashin hankali yake kallon Hajiya , kana babu abunda ke yawo kwanyar kansa irin wannan hoton da Laila ta nuna masa a dakinsa.


 " Ya kayi shiru ne Bin Adam" cewar Hajiya tana matsa yatsun hannunsa.


 " Humm babu komi , zan je ana jirana " ya fada yana mai sakin hannun Hajiya.


 " Prince Adamsy kayi nazari sosai ka san muna da tarin makiya a Gidan nan kiris suke jira".


 " Na gode Hajiya in sha Allah ba zamu ji kunya ba , na tafi ki min adua" ya fada yana mai kallon yaransa dake buga game da tablette.


 " Yan biyu na , na tafi sai na dawo" be jira cewar yaran ba ya fice .su Kuma bye bye suke masa hankalinsu na kan wayar tablette.


Hajiya da adua ta bisa yana amsawa da Ameen har ya bar sashin.


**********************


Misalin karfe uku na yamma , Lailat zaune a kuryan dakinta , gefenta Nura ne a bakin gadon ta.


" Nura ka san ina son prince wallahi shiyasa ma nayi...".


 Dakatar da ita yayi ta hanyar fadin.


" Ba sai kin karasa ba , ai babu namijin da ze samu mace kamarki ya raina gaki black beautiful kalar amerikawa , ga tsayi ga abubuwan marmari" ya fada yana mai shafa bayanta.


" Nura kai de ka fiye dadin baki wallahi , mu bar wannan zancen , ayi mai fishe mu".


 " Ina jinki " ya zuba mata mayatattun idanu.


 " Cikin jikina , prince ya kyakyashe idanunsa yana fadin be taba kusantata ba , kai me kake tunanin ze faru a gaba , gaskiya bana son na rasa shi , kai ma ka sani" ta fada cikin rauni.


 " Kwantar da hankalinki ai wallahi be isa ba sai ya zauna dake ko baya kaunar Allah , zancen ciki kam , zamu san abun yi , dan da kansa ne ze fara shelar wannan cikin a masarautar nan , dan haka , taho mu kwanta wallahi nayi mugun miss dinki " ya fada yana rungumota , tare da fadawa kan gado.


Wa'iyabuzillah



 Bangaren Prince Adamsy zaune yake a katafaren kamfaninsa na sabulun wanki dana wanka . Mai suna *KYAUTA SOAP* babban ma'aikata ne , wanda yake da tambarin Gidan sarauta a kofar shiga, ma'aikata ne da aka gina shi da ginin zamani, domin kana isa bakin ko wani office , kofar ze bude kansa , banda kofar office din da Prince yake ciki . Sai ya ganka ta cctv sannan yake bude maka da remote kana ka samu damar shiga , cikin office dinsa kamar dakin hotel, tsabar tsaruwa komi tsaf da kujerun sa na zaman baki da tv an fridge.


Lilo yake daga zaune saman kujerar , inda gefensa babban Amininsa ne , Zahradeen.


" Wai kana nufin Laila ciki ne da ita ?" .Deen ya tambaya cike da mamaki.


 " Eh ciki ne da ita , amma kuma ba nawa bane , matar nan ko yatsar hannunta ban taba tabawa, ta ina ta samu ciki, wannan hoton da ta nuna min duk cikin shiri ne ai idanuna a rufe suke , ka taimakeni Deen wallahi ina cikin tsaka mai wuya " .


Numfashi Deen ya fesar yana mai daukan lemu tare da zubawa a cup.


 " Kawai ka sake ta " cewar Deen cikin bacin rai.


  " In sake ta fa ka ce !".


 " Kwarai kuwa haka nace ".


 " Ka san sakin nata abun da ze janyo min ga iyayena kuwa?".


 " Na sani mana , fushin su na kwana biyu ne , in sun fahimceka , zasu huce , kuma dani ne ke aurenta tuni na sake ta , kamar kai mace , ta haifa maka shege a Gidan ka ,kuma ta lika maka , ai babu biyayya ga sabawa Allah ".


Kyawawan ajiyar zuciya Prince ya sauke, kana idanunsa na kan Deen yanda yake hucin takaici.


" Zan yi tunani , yanzu mu tashi lokacin la'asar tayi daga nan , directl Gida zan nufa , dan ba zan samu ganin sauran customer ba ".


 " Wallahi ka san abun yi , prince Adamsy , kada tsoro ya hanaka daukan responsibility din ka " .


 " Zanyi kokarin hakan " ya fada yana mai tattara wayoyinsa, tare da kiran Secratia dinsa , domin sanar mata da ya tashi daga aiki. .


Bayan sun idar da sallah ne. Deen ya shiga Mazaunin drever , gefensa prince Adamsy ne. 


Sauran motocinsu ne , duk magoya bayansa suka shige domin barin ma'aikatan.


" Haba don Allah, ku tafi gida mana ,kullum kuna tare dashi " cewar deen yanawa magoya bayansa fada.


Prince kallonsa ya dawo kan duk magoya bayansa .

" Kuna iya tafiya , gaskiya yau ina son na dan zaga cikin gari , ni da abokina". ya yi magana yayin da suka juya domin bin Umarninsa.



___________________



Jidda kam sosai aka cika kanta , danma Ummi tana taimakawa wajen service din customer.


" Haba Jidda tun dazun nake nan " muryan wani customer matashi.


 Dago kai tayi ta kalle shi , kana ta sauke kanta kasa .

" Kayi hakuri". Kallon Ummi dake bada awara tayi cikin yanayin aiki n da ke gabanta na suya ta ce " Ummi dan zuba masa don Allah" ta fada tana mai juya awaran dake cikin mai.


" A'a ba wajen Ummi na zo ba , wajen ki ne , ke ce zaki bani da kanki" ya fada yana mai gyara tsayuwarsa.


Kara dago kai tayi tana kallonsa karo na biyu .

" Haba wace magana ce wannan ai ni da Ummi daya ne , kuma maganin korafi ne yasa nace ta sanya maka ".ta fada da dan bacin rai , dan kallon da yake mata kamar ze cinye ta.


" Don Allah kyale shi yayi ta jira" cewar Ummi cikin bacin rai.


 " Oho dai ina nan ba inda zani dan Jidda ce zata sanya min " ya fada yana mai kama kujera ya zauna.


 Sosai sukayi kokarin sallamar mutane , inda ya rage , wannan mutumin shi kadai. Zuba masa abunda yake so tayi da kanta , tare da mika masa .ya karba yana mai kara narka mata zararan idanunsa. 


" Nawa ne kudin awaran nan " ya tambaya da alamun neman tsokana.


Kallon juna suka yi ita da Ummi kana ta furta .

" Dubu daya " .


Mika mata bandir din dubu dari ya yi a hannunta.


A zabure ta ce " wannan fa ".?


 " Kudin awara ne , da kuma kyauta ".


 " Bana so , so kake Umma ta min fada , rike kayan ka ".


 Kamar me shirin kuka ya ce " Dan girman Allah ki amshi kudin nan Kanwata , in kika maido min zan kwana cikin kunci, ni maraya ne , a aikin hajji na rasa iyayena " nan ya shiga basu Labarin yanda akai zafin rana Kuma uwarsa da uban tare suka mutu.

 Daga Ummi har ita din. Sosai suka tausaya masa tare da masa aduar gafara da iyayensa.


" Don Allah ki amsa , don wallahi , kin amsa ze Kara min kunci irin wanda nayi a baya."


 Ummi ce ta ce " Jidda ki amsa, tunda kin ji rokonsa, na san ke mai tausayi ce ".


" Mun gode " shine kalmar da Jidda ta furta tana mai mikawa Ummi kudin ta rike.


"Wow na ji dadin jin haka daga gareki Sarauniya" cewar matashin.


Jidda da sam babu sakewa tare da ita , ta mai da hankalinta akan suya.

___________________


Deen da prince a kasuwa suka paka motarsu domin yin siyayya.


Prince na biye dashi , Dan shine karo na farko da ya shigo kasuwa babu magoya bayansa ,hakan ya sanya kansa a kasa sam baya son a gane shi.


" Prince don Allah zo mu je , siyen awara gashi cen ana suya".


 " Awara kuma ? ".ya tambaya da mamaki.


 " Eh fa ko baka iya ci ba , ai ni na iya " Deen ya bashi amsa yana mai rike hannunsa Prince suka Karasa wajen suya.


" Me awara akwai zafi kuwa , ki bamu na cikin mai ". Cewar Deen , yana mai kallon Jidda da kanta ke kasa.


 Dago kai Jidda tayi zata yi magana , idanunsu ya tsarke cikin na juna ita da Prince .


A tare zuciyoyinsu ya buga , cikin rudewa ta rike daidai satin zuciyarta , haka ma prince ya rike daidai nashi zuciyar . tare da furta " Wash Allah " murya a rikice . cikin hanzari Deen ya je kama prince ganin yana shirin faduwa.


Haka ma Ummi cike da hanzari ta kama Jidd



Mu je zuwa!!


***



KYAUTA DAGA ALLAH




Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.