Free chapter 路 Read without an account

{18..}

by Feenerh Feeche Studios 路 HAJAR

馃挍 HAJAR 馃挍


After the silence of about 5mins Mami tace "kuma kai hakan shi yafi yi maka?", Nurain ya kalleta yaga har lokacin idonta na kan TV, ya shafa kansa ya kwantar da voice yace "yeah Mami hakan shi yafi min", tace "Ohk shknn, Allah ya bada sa'a", yace "Ameen". Mami ta tashi ta fita 蓷akin, bata da蓷e ba ta dawo da tray a hannunta, akan carpet ta ajiye ta koma position 蓷inta ta zauna, ta kalli Nurain tace "saika sauka kaci abincin", ya kalli trayn snn ya ajiye wayarsa akan hannun kujera ya sauka kan carpet, wamers 蓷in ya fara bu蓷ewa snn ya 蓷auki plate ya zuba abincin, yana fara cin abinci akay knocking door, Mami tace "shigo" cause tasan waye, Laure ce ta shigo hannunta ri茩e da tray mai 蓷auke da bottle water sai lemon kwali da cup, Mami ta nuna mata Centre table tace "ajiye anan", a hankali ta ajiye kana ta juya ta fita, a hankali Nurain yake cin abincinsa har ya gama, ya 蓷auki bottle water ya tsiyaya a cup ya sha, Mami tace "karka yi tafiyar nan ba tare da kaje kunyi sallama da Hajiya ba", yace "insha Allah Mami, zanje muyi sallama". tace "yawwa", ya tashi ya 蓷auki wayarsa yace "zan 蓷an fita", tace "wajen Hajiyar zaka?", yace "No", tace "Okay, ka taho min da counter", yace "tom" snn ya wuce 茩ofa ya mur蓷a handle ya fita, room 蓷insa ya wuce ya 蓷akko mu茩ullin Mota, daga nan ya fita compound ya shiga motarsa, slowly yake driving listing to the qira'a of Sheikh Husary, A wani annakakken wajen siyar da wayoyi yayi parking, same wajen da ya siyi sabuwar wayar hannunsa, bayan ya shiga building din da akay molding dinsa da pattern 蓷in cell phone, tsayawa yayi yana tunanin wace wayar zai siyawa Noor, ta蓳e baki yayi ya nufi 蓳angaren iPhone cause yasan sune ake yayi, ko wace 拼an mata tafi son iPhone, Shi kam waya indai ba Samsung bace ba toh a barta, iPhone mai kyau da tsada ya siya full series, credit card 蓷insa ya mi茩awa cashier ta cire ku蓷in snn ta mi茩a masa with due respect, yana gamawa ya fito ya shiga motarsa, A junction yaga mai counter ya siyi guda uku mai ha蓷e da agogo, lokacin da ya koma gida har Magrib tayi, saida yayi sallah snn ya shiga ciki, Noor ta amsa sallamarsa, tayi wani dafa'an tana kallon stuff dinta na Kdrama, tace "yaya ina yini", yace "lfy lou", zama yayi akan kujera duk da ba hakan yaso ba, with stern Voice yace "zo nan", ta matsa gabansa ta zauna daga 茩asan carpet, ledar da ya shigo da ita ya ajiye mata akan cinya yace "your birthday presence", Noor tayi murmushi snn ta bu蓷e ledar, ai tana ganin abinda yake ciki ta daka tsalle ta rungumesa tace "thank you so much, nagode Allah ya saka da alkhairy yayana", yace "you know the rules right?, kuma kinsan warning 蓷in da nayi miki ko?", ta gya蓷a kai da sauri all her white tooth out, ya shiga part din Mami ya kai mata counter, ya fito ya haura room 蓷insa cause yana so ya gama duk wani shirye-shirye kafin nanda Wednesday.


鈽匟ajar na zaune a palour tare da Hafsa da Humaira suna kallon wani film a MBC 2 mai suna IT, Humaira duk ta ru蓷e sbd film 蓷in akwai abin tsoro, Hajar kam kwata kwata mind 蓷inta was somewhere else, ita bata ma san me akeyi a film 蓷inba, time to time kuma saita ja long hiss, Hafsa ta kalleta tace "wai me ya faru ne tin 蓷azu kike mana tsaki?", Hajar ta sake yin wani tsakin tace "uhmm bazaki gane yadda nake jin haushi ba ne", Hafsa ta ta蓳e baki tace "toh ki gayamin mana, me ya baki haushin?", Hajar tace "wllh wani 蓷an rainin hankali ne ya ha蓷amin zafi 蓷azu a asibiti", Hafsa ta tare hammar da ta yanko mata tace "ni kam bangane wane rainin hankalin kike magana akai ba?", Hajar tace "ai shiyasa nace bazaki gane ba", Hafsa tace "taya za kice bazan gane ba bayan baki yimin yadda zan gane 蓷in ba", Hajar tace "forget it kawai, Allah ya kaimu gobe, ai zan koma asibitin, wllh sai ya bani takardar test 蓷in Babana", Hafsa ta koma tayi resting a jikin kujera tace "uhmm, ke kika sani dai", Anty ce ta fito daga 茩ofar part 蓷in mijinta, ta 茩are musu kallo snn tace "la'ila 茩arfe nawa har yanzu baki kwanta ba Humaira?", Humaira ta turo baki tace "ai su yaya ne sun茩i zuwa mu kwanta, kuma ni tsoro nake ji", Anty ta zauna ta kalli Hafsa da take ta faman hamma tace "toh kuje ku kwanta mana, sai zabga hamma kike, gobe da schl kinsan da hakan aii", Hafsa tace "Hajar nake jira", Anty tace "Ina ruwanki da ita, ita ba schl take zuwa ba don haka anytime zata iya kwanciya abinta", Hafsa tace "toh saina gama kallon film 蓷in nan", Humaira tace "Anty ni tsoro nake ji, kuma bacci zanyi", Hafsa ta nasa mata harara tace "keee, wuce ki kwanta, tin 蓷azu nayi miki shimfi蓷a", Humaira ta no茩e kafa蓷a ta koma cinyar Anty ta kwanta, Anty ta kalli Hajar tace "An sallami Baba", Hajar tace "yaushe?", Anty tace "蓷azu", Hajar ta gya蓷a kai tace "toh yaga likitan?", Anty tace "Eh, Adda tace har da茩i likita yazo ya dubasa, kuma likitan ne yazo da takardar test 蓷in", Hajar was speechless sbd mamaki, how comes?, a ina doctorn ya samu test 蓷in?, ko dai result 蓷in biyu ne?, ganin bata da amsar wa蓷an nan questions 蓷in saita 蓳ige da jinjina kai, sai kuma tace "gobe da safe zasu tafi gida knn?", Anty tace "Eh". Washe gari da wuri Hajar ta gama gyara gida, ta shiga toilet tayi wanka, ta fito ta 蓷auki mai ta shafa, wardrobe ta bu蓷e ta 蓷akko kaya ta saka, Hafsa dai saida ta jere mata kayan nan a press snn ranta yayi sanyi, wani material ta saka mai kyau, Anty ce ma ta bata shi ita da Sabra waccan sallar da ta wuce. gaban mirror ta tsaya tana kallon gashin kanta mai cika, yaushe rabon da ta ta蓳a sa, gashi nan kam duk ya cukurku蓷e alamar ba a untangling 蓷insa frequently amma kuma babu datti, cause tana wankesa akai akai amma fa tajewa ne yake mata wahala sbd cikarsa, most of the time ma Umma ce take taje mata, roban hair oil ta bu蓷e ta zauna akan stool, she spent almost 30mins making her black silky hair tide, a 茩eya tayi parking ta 蓷aure da ribbon, ta tufke jelar wacca ta saukar mata har midback. ta mayar da comb 蓷in cikin drawer snn ta rufe roban hair oil 蓷in, ta 蓷aura dan kwali ta fita palour, kitchen ta shiga ta tsiyayi ruwan Lipton a cup, ta ha蓷a tea snn ta 蓷auki 4slice of bread ta koma 蓷akinsu Hafsa. tana cikin ci wayarta ta fara ringing, sosai tayi mamakin wane yake kiranta at this time, cup 蓷in tean ta ajiye ta mi茩e ta 蓷akko wayar, kallon screen 蓷in wayar ta tsaya yi ganin bata son numbern dake kiranta ba, har kiran ya yanke wani ya sake shigowa, slim finger 蓷inta ta kai tayi picking snn ta kara wayar a right ear 蓷inta ha蓷e da yin sallama with her cool voice, 蓳oyayyen ajiyar zuciya taji an sauke snn aka amsa mata sallamar, ta yamutsa fuska jin muryar namiji, ta ciro wayar daga kunnen dama ta mayar da ita na hagu tace "Ahmm bangane mai magana ba?", yace "Eh, am Ahmad, na samu numbern ki a wajen friend 蓷inki", ta ta蓳e baki sbd ta fahimci shine wanda Zainab tace zata basa digit dinta, tace "okay, but how can I help you?", yace "i want to talk to you", tace "Sorry, ba sai kayi magana ba ma, ina fatan dai Zainab tayi maka bayani", yace "wane bayanin?", tace "akwai baiko a kaina", daga haka ta katse kiran ta cigaba da shan shayinta, tana ajiye wayar saiga wani kiran nan yana shigowa, saida tayi ringing twice kafin ta 蓷auka, yace "why did you hanged up?", ta juya lulu eyes 蓷inta tace "ina aiki ne", yace "Okay, a gama lfy, zan kira later plxx pick up", tace "tom" ta katse.


鈽吰榓rfe goma da rabi na safe Naseer da Mu'azzam da kuma Huzaifa wanda ya baro lectures 蓷insa ya dawo gida suka shigo gida tare da mahaifinsu, Baba duk ya fa蓷a ya rame sosai, Umma ta fito 蓷akinta tana musu barka da dawowa, ta wuce 茩ofar 蓷akin Baba ta bu蓷e padlock, Huzaifa ya tallafi Baba ya shiga 蓷akinsa, 蓷akin a gyara yake fes fes sai 茩amshin turaren tsinke yake, Umma ce ta gyara sa da sassafe tinda a gida take kwana. Mu'azzam ya shigo da ledar drugs 蓷in Baba ya ajiye gefe, Umma ta fita tana kallon 蓷akin Maama ta shiga nata, flask 蓷in da ta dama kunun gya蓷a ta 蓷auka da cup ta fita, ta kalli Mu'azzam da yake 茩o茩arin fitowa daga 蓷akin tace "zaka sha kunu na zuba maka?", ya gya蓷a kai yace "Eh zan sha", ta 茩arasa shiga 蓷akin Baba, ta ajiye flask din gefe, Huzaifa ya jingina pillow a bayan Baba snn yace "sannu Baba, Allah ya baka lfy", Baba yace "Ameen, Allah yayi muku albarka", Huzaifa da Umma suka ce Ameen, Umma tace "Huzaifa ina Naseer?", yace "ya shiga 蓷aki", tace "ga kunu idan zaku sha na zuba muku?", Huzaifa yace "tom". cup guda uku Umma ta cika da groundnut pap, Huzaifa ya 蓷auki nasa dana Naseer ya shigar musu dashi 蓷akinsu, Umma ta rufewa Mu'azzam nasa da ya shiga toilet, Baba ya kalli Umma yace "ina Hajara?", tace "tana nan", yace "kirowamin Rabi", Umma ta waro ido amma ba tace komai ba ta tashi ta fito tsakar gida, A 茩ofar 蓷akinsu Naseer ta tsaya ta kira Huzaifa, ya fito hannunsa ri茩e da kofin kununsa da har ya kusa shanyewa yace "na'am", tace "ka kira Maamanku tazo inji Malam", yace "tom" ya shiga 蓷aki ya ajiye kofin kunun snn ya fito ya wuce 蓷akin Maama, Umma tana ganin ya shiga wajen Maama ta koma 蓷akin Baba tace masa gata nan zuwa. Huzaifa ya ringa kallon Maama wacca take zaune dafa'an akan 茩ullin kayan wanki, ya dur茩usa yace "Maama barka da safiya", tana karka蓷a 茩afa tace "ba yawwa ba, tinda kwanten gaisuwa zaka jefeni da ita, wai har waccar mayyar matar ta fini daraja a idanunku kai da Nasiru, 茩iri 茩iri bakwa kallona a matsayin mahaifiyarku, ace mi茩iyyata itace wacca zaku fifita, koda yake ba laifin ku bane tinda an zuba a kunu an baku kun tan蓷e..", Huzaifa dai ya shafa kai yace "Baba yana kiranki", ta ta蓳e baki tace "toh me zan masa da yake kirani, ince dai ga mayyar matarsa nan a tare dashi koh", shiru Huzaifa yayi baice komai ba. Maimuna da take kan gado rashe rashe itada Nabilah ce ta mi茩e zaune tana hamma, wani irin wage baki tayi babu addu'ar neman tsari ga shai蓷an bare ta kai ga rufe wawakeken bakinta, bu蓷e idonta tayi tana soshe soshe snn ta zabga tsaki tace "Allah ya isa wllh, Sauro da ku蓷in cizo sun suburbu蓷e ni yasin, shiyasa Sa'adatu ta tsani gidan nan wllh, nima dai daf nake da barin kangon nan alkur'an...", dakatawa tayi da tijarar tana micincina idanu ganin Huzaifa, ta sakko daga gadon tace "Laa yaya ina kwana", tsaki yayi ya mi茩e ya fita a 蓷akin. Maimuna ta ta蓳e baki tace "ni kam Maama sai naga kamar yaya Huzaifa yana juyewa kamar yaya Naseer", Maama tayi kwafa tace "uhmm shima ai an shanyesa, har kunu fa ake damawa a basa, kinga kam bayan shanyewa har damesa akai". Maimuna ta cigaba da soshe soshe kafin tace "ni kam Maama wai ina ragowar piya-piyan nan yake yau na fesa a katifa?, ku蓷in cizon nan yayi yawa", Maama ta 蓷auke kanta tace "ya 茩are, daman Sa'adatu ce mai siya kuma kinga tin shekaran jiya rabonta da gidan nan, itace mai zuciyar siyar piya piya ayi feshi, ke kam tsimilmila da ma茩o bazasu barki kiyi abin arzi茩i ba, koni nan uwarki ba morarki nake ba, ko ku蓷in kika samo saidai ki cinye ke ka蓷ai sbd rowar masifa, nasan yanzu haka kinada uban ku蓷i a 茩ugunki amma bazaki iya fitar da 蓷ari biyar a siyi piya piyan ba kin gwammace ku蓷in cizon suyi ta cizonki....", Maimuna tace "kaiiii Maama", Maama ta harareta tace "gafara can za wani kicemin kaiiii, aa ba kaii ba hannu ko 茩afa, sakarya kawai, ki kira Sa'adatu yanzun nan kice mata ta dawo gida an sallamo malam, jiya naga kunyi waya da ita kuma nasan 拼an albarkar 茩awayenta har sun mayar mata da tsaleliyar wayar da ta rasa", Maimuna ta ringa 茩un茩uni snn ta 蓷auki wayarta a 茩ar茩ashin pillow ta shiga dokawa Sa'adatu kira, sau uku ta kira wayar na ta ringing amma ba a 蓷auka ba, ta zabga tsaki tace "Maama kinga dai bata 蓷auka ba ko?, ni dai ba ruwana idan yaya Naseer ya sake laka蓷a mata na jaki", Maama ta harareta tace "sake kira", Maimuna tace "bafa 蓷auka za tayi ba don nasan bacci ma take yanxu" ta shiga kiran Sa'adatu for the fourth time. daf kiran zai tsinke aka 蓷aga, Maimuna tace "ke Sa'adatu toh ki taho gida inji Maama an sallamo Baba daga asibiti kuma yaya Naseer yana nan..". 茩it aka kashe wayar bayan wani dogon tsaki, Maimuna ta kalli screen 蓷in wayar ta mulmulo ashar tace "Alfarmar Annabi da Alkur'ani sai Yaya Naseer ya laka蓷a miki duka"......鉁嶏笍


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.