Free chapter · Read without an account

2

by Nana Disoo · TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)


NA

NANA DISO

&

ASMY B ALIYU




2...

Bayan yayi mata huduba sai ya kafeta da idanuwa yanajin wani irin sonta acikin ransa a hankali kuma sai yaji zuciyarsa tafara karyewa duba da yadda yarinyar tashiga rangada kukan jarirai wato "enyea !!" Firgicewa yayi haɗe da rikicewa ga kuma  da kuma tausayi ga damuwa yashiga da sauri ya shiga faɗin "  Nurse yanzu yaya za'ayi da jaririyar.?" Wacce aka kira da Nurse ce tajiyo tana kallonsa da faɗin " Babyn nan da alamu Yunwa takeji ga takardar Madarar da za'a siyo mata danAllah." Kukan da yasuɓuce masa Fatimatul batool tana hannunsa yasaka Anty maimuna sauri da hanzarin karasowa gurin tace " SADAUKI wannan kukan babu abunda zaiyi mana danAllah kayi hakuri  ince kayiwa yarinyar huduba yanzu." Batare da yace mata komai ba ya Mika mata jaririya yana faɗin " fatimatul batool zanje in sanar dasu Baffa zan taho mata da madara zan karasa clearing na kudi kamin nawuce yanzu. Hajja na masa magana haka yayi shiru yacigaba da tafiya zuciyarsa Na masa wani kalar zafi ga sabbin hawayen tausayin batool yana zuba. Hajja dake gefe guda tace " Maimuna badai huduba yayi mata ba?" " To hajja saboda Allah wazaiyi mata." Mahaifinta mana Maimuna me isa kukeyin haka maza kirashi awaya ki sanar masa zancen rasuwa ?" To hajja bari in kirasa yanzu tafada tana dauƙar wayarta tana neman Numbarsa kusan ringing Hudu amma ba'a dauka ba " Kinga hajja har yanzu fa ba'a dauka ba." " Kiyi hakuri kicigaba da kira ko baya kusa." Tana cikin kira dai bai daga ba sai daga baya kuma takara kira wanda yayi daidai da kukan batool da  yacika dakin Hakan kuma yayi daidai da dawowar SADAUKI Tare dasu kawu da sauran mutan gidan Nan aka shiga yiwa juna ta'aziya wasu kuma Anata kukan rashin mahaifiyar batool Haka aka dauketa suka wuce zuwa gida. Daga farkon gidan zaka tabbatar da gidane Namasu wadata Don yakasance babban gida ga maƙeken gate daga wajen gidan tun kamin ma su karasa kofar gidan yacika makil da ƴan 'Uwa kowa cikin jimammin wannan babban rashi da akayi Na inna bintu. Sai da suka shiga da'ita aka shiga yimata suttura yan ' uwa masu kuka kuma duk sunayi. SADAUKI ke zaune daga gefen hajja yana rike da fatimatul batool Nan hajja tace " Nikam nasaka gane maka SADAUKI saboda Allah da hankalinka da iliminki kaketa zubda hawaye ka kasa tashi ma kuje akaita gidan gaskiya." Batare da yace komai ba yace " Hajja Nakasa samun Nutsuwa ne." Kallonsa tayi tana ganin yadda gabadaya Fuskarsa ta canza zuwa jajir ga idonsa ko ba'a gayamaka ba yaci kuka. Kamin ma takarasa kawu yace " SAUDAUKI hakuri zamuyi gaba dayan mu jiranmu takeyi ai." Bai cewa kowa komai ba yami kawa daya daga ciƙin yaran jaririyar Sukuma suka fita domin sadata da gidanta Na gaskiya. Gidan dinkewa yayi da mutane anata shigowa ta'aziya hakan yasa hajja tsam tashi daga falon inda ƴan'uwa suka cika Anty maimuna ce da jaririyar tabi bayanta dan indai hajja tayi haka to tabbas akwai magana bakinta. Sallamar da SADAUKI yayi ya shigo idanuwansa sunkara jajir sun kumbura Nan Aunty maimuna take cemasa " yakarin haƙurin mu?" Sai da yakarasa ya ƙarbi fatimatul batool a hannunta sannan yace " Da godiya Inna bintu tarigamu gidan gaskiya Allah yayi mata Rahama." " Ameen yaa Allah sukace." " Tasha madarar kuwa anty maimuna? Sadauki yayi tambayar yana kallonta." " Tasha yanzu ma wanka zan mata sai acanza kaya." Daga can gefen da hajja take zaune sukaji takara waya tana fadar " salamu Alaikum Malam kabiru ne a layi?" Tafada tana kara kara wayar ciƙin kunnenta wanda yasa SADAUKI canza fuskarsa da duk annurinsa atake. Dayake wayar a hands free take yace " Wacece wai take damuna da tambayane." Cikin dan zafi tace " Nice Nan hajja Anata kiranka kaki daga wayar." " To lafiya kuke nemana Tunda anriga anyimana tsakani da juna idan kanwarki ce ince nagayamiki saki uku nayi mata? To menene kuma." " Allah sarki Ai kabiru tunda kaji ankiraka awaya to tabbas kasan akwai dalili ita Bintu tarigamu gidan gaskiya gakuma abunda ta bari nan fatimatul batool." " tsohuwa ina ganin mutuncinki, dan haka da Mutuwarta da rashin mutuwarta babu damuwata aciki yarinyar da kukeson ku kakabamin ban karbarta dan ba diyata bace ba dan haka kusan can yadda zakuyi da'ita daga yau kada kusake ku Nuna Kun sanni Kokuma da wata alaqa tsakanin mu Daga yanzu Na datse duk wata DANGANTAKAR DAKE TSAKANIN MU dani daku kuje can idan ma yar da yarinyar zakuyi sai ku yarda ita Amma banida wani alaqa da diyar." Cikin rawa jiki da baisan ma ya karasa kusa da hajja ba yana kokarin fizgar wayar hajja tayi hanzarin kashewa tana jan hannun SADAUKI ta zaunar dashi.  Duk tunda akayi rasuwar sun kasa gane komai game dashi a hankali ta kirashi duk da itama jarumta takeyi kawai amma zuciyarta takai mata gurin baƙin ciki da Nadamar kiran malam kabiru shiƙam wani kalar halittar mutum ne? Banda azabar da yadinga rangadawa yar'uwarta bintu babu wani abu da ya tsinana musu dashi da dan hanzari ta ƙalli dan nata tace " Nikam SADAUKI Wannan zafin ƙan naka yana bani tsoro wannan mutum idan ma ya cuta mana ai Allah baya barinsa kuma tunda yariga Ya nuna bayason yarinyar Ai mu muna santa zamu riketa ahannunmu Amma ina rokonka da Allah kada ka tada fitina tana kwance kana gani ko kwana bintu batayi da rasuwa ba kabar zancen nan anan gurin Allah yashiryashi watarana yagane." Baicewa hajja komai ba sai Saurin Miƙewa da yayi wani sabbin hawaye  yana zubo masa yashiga bangaren sa. Aunty maimuna datayi Nisa gurin yiwa Batool wanka tace " Amma hajja wannan mutumin bashida mutunci." Jin Anfara sallama ana shigowa yasa hajja fita tana amsa musu tunda bintu ta rasu sai yanzu ne tasamu damar saƙin kuka dan bakin cikin da yarinyar nan ta ƙunsa arayuwarta sai dai Tace Allah yayi mata tukwaici da Aljannah Nan mutane suka shiga bata baki da hakuri akan mutuwa tana kan kowa. kuma yazo da sai ya jajanta yar jaririyar data bari.


  Babbar macce da kana kallonta kasan shekaru sunja gareta ce ta kalli mai gidan nasu tace " Malam naji kamar ana batun haihuwa? Ko tsohuwar matar taka ta haihu ne?" Dayar matar tasa dake tsintar shinkafa ce tace kai wallahi kema yaya kinfiya jan magana sau nawa Malam zaiyi mana magana akan mu bar ambatar masa matsiyaciyar nan?" Batare data kalleta ba tace " Magana fa nake Malam." Cikin tsaki da Nuna kosawa yace " Abunda kikaji hakane nagayamiki kidaina shiga abunda babu ruwanki acikin gidan nan idan bahaka ba to wallahi wannan ne maganata takarshe akanki." " Gwara dai kayi mata magana yaya dan Lamarinta har mamaki yake bani." " To wallahi Malam kabiru sai nagayamaka gaskiya ko bakaso dan Abunda kayi baka kyauta ba kowa yasan cikin nan naka ne bayan wulakanta baiwar Allah dakuka gama yi ace diyar data haifa ma baka rikewa wannan adalci ne?.." bata karasa ba taji kau saukar lafiyayyan mari afuskarta. Mutuniyar banza kawai munafuka ke kika auromin ita? To wallahi yanzu sai na sakeki akan bintu munafuka kawai." Babbar matar da kana ganinta kasan ta manyanta tatashi tashige dakinta tanajin sautin fadansa yana tayi haɗe da sababi kala kala Duk da tasan halin mijin nasu babban jahili ne na karshe gashi bashida mutunci ko ƙadan Amma tana kokarin ganin ta bashi shawara duk da shawarar datake bashi basutaba wanyewa lafiya ba dan sai yayi mata tsiya tsiya sosai. Can kuma takara jin muryarsa yana faɗin " Diyace nace batawa bace ba sai naga uban da zai mayar da'ita tawa wannan iskancin naku yafara damuna mutanen banza kawai yafaɗa yana mai barin gidan zuwa waje...


    Kasancewa dare ya tsallah babu abunda kakeji na sauti sai ƙukan jaririyar dake tashi " Eyaaa eyaaa.!!! kasancewa yana kan sallaya kur'ani ne a hannunsa yana karatu, ɗan tsayawa yayi yakara sauraron kukan ko shakka babu na Batool ne da ɗan hanzari ya ajiye ƙur'anin sannan ya miƙe zuciyarsa ciƙe da tausayin marainiyar yarinyar har ya fita sashensa ya nufi Na mahaifiyarsa Nan ya gansu cirko cirko A zaune a palour yarinya sai kuka takeyi Anty maimuna na jijjigata. "SADAUKI kaima har ta tasheka?" Batare da yabasu amsa ba ya Nufi Aunty maimuna  ya ƙarbi batool yana ƙura mata idanuwa itama yarinyar binsa tayi tana cigaba da rangada kuƙanta. " Abata madara aga ko yunwa takeji mana." Hajja dake ɗan gyangyadi tace " Kasan kwanan farko ne dole tayi kuka amma babu wani yunwa kawai maraicine." Cikin dan yanayi yace " Narokeki da Allah karki doramata wannan suna wai maraici ƙanwata bazata taɓa zama marainiya ba indai ina doron ƙasar nan." " To Allah yatayaka Hajja tafada tana miƙewa. Shikuma ya nufi flask din tea din yashiga haɗa mata madarar da atake suna kallon shi har yagama yashiga bata aikam dawa Allah ya haɗata sai tashiga zugar madara kamar tasamu kan nono kamin kace me har ta zuƙeta tas Nan ya kalli Hajja,da yar  uwarsa  yana faɗin kunsan babu mai shayar da'ita zata bukaci madarar nan ako wanne lokaci danAllah akula. Nan suka shiga Amsa masa shiƙuma ya samu kan kujera ya zauna har takoma baccinta hajja kam itama nan ta karasa baccin su Aunty maimuna ne suka shige daga daƙi.




#NANA DISO

#ASMY B ALIYU





Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol