Free chapter · Read without an account

{27..}

by Feenerh Feeche Studios · HAJAR


Da mamaki a fuskar Anty ta amshi kuɗin tace "toh, na mene?", Hajar ta girgiza kai tace "bansani ba amma tace za kuyi waya", Anty ta gyaɗa kai tace "Okay". Hafsa ta tashi ta nufi ɗakinsu, wayarta da ke kan mirror ta ɗauka, call log ta shiga ta nemo wata number ta shiga dialing, tana fara ringing akay rejecting few seconds kira ya shiga daga same numbern, ta kara a kunne tace "Assalamu alaikum", from the other side Ahmad yace "Wa'alaykissam salam, young lady", tace "yawwa, nace ba, yau idan babu damuwa zaka iya zuwa na cika alkawarin da nayi maka", keenly yace "Okay, na ɗauka ma kin manta ashe ba haka bane", tace "yap, sai kazo immediately after Asr prayer", yace "insha Allah", kashe wayar tayi tace "kar alƙawari ya zarbaɗo ƙafata ranar lahira ya hanani gudun famfalaƙi..", palour ta fito ta zauna, Anty ta kwashe kuɗin da ta ajiye hannun kujera ta shiga room ɗinta, wayarta ta dauka, missed call ta gani daga ƴar uwarta, zama tayi gefen gado ta shiga kiranta, Umma na dauka suka gaisa, Anty tace "Hajar taxo da saƙo, Adda kuɗin na mene?", Umma tace "kinsan jiya aka kawo kuɗin auren Hajara, Jamila ba a fafe gora ranar tafiya, wnn kuɗin wnda nake ɗan tarawa ne tin tini, shine nace bari na turo miki su sai a fara mata ƴan tsince tsince sha'anin aure da yawa..", Anty tace "gaskiya haka ne ba a fafe gora ranar tafiya, toh mai za a tsinto da wadan nan kuɗin?", Umma tace "abinda kika ga ya dace Jamila, koma mene asiya a ajiye", Anty tace "wata shida suka sa ko?", Umma tace "Eh, kinga kwa ba lokaci, yanxu sai kiga abin yaxo kusa, idan na sake tara wasu saina turo miki kafin lokacin muga abinda za muyi", Anty tace "gsky kam, toh wnn kuɗin dai saidai na siya mata decorants, kayan kitchen nawa ne ni zan mata", Umma tace "Kaii Jamila abun fa da yawa", Anty tace "she's my daughter fa, insha Allah zan mata duk wani abu da ya danganci kitchen, cikin rufin asiri zamu kaita insha Allah babu me rainata a dangin miji ko kuma a goranta mata". Umma ta ajiye numfashi tace "toh Ameen, Allah ya tabbatar mana da alkhairy", Anty tace "Ameen". Hafsa ta kalli Hajar tace "gsky fa zanyi amarancin a bikinki, daman nice ƙirjin biki kuma babbar aminiyar amarya", Hajar tayi murmushi tace "yayi kyau..", Hafsa tace "anko kala uku zan fitar mana na ƙawayen amarya snn kuma zan shiga na ƴan gida, ga wanda zanyi iri ɗaya da amarya ranar yini, kai abinfa ba a cewa komai gsky zan zuba amaranci", Hajar dai ta ringa binta da ido tana murmushi, wai itace wacca ake maganar bikinta, bikin ma da rabin zuciyarta Nura. Hafsa tace "amma dai ba yau zaki tafi ba ko?", harararta Hajar tayi tace "chab ana yin sallar la'asar zan samfe..", Hafsa tace "kaiii dan Allah ki kwana", Hajar tace "yau naga jalala daga zuwa kuma sai kwana, A'a wllh tafiya zanyi", Hafsa ta haɗe gira ta tashi tace "sai ki ta tafiya" ta wuce kitchen, Hajar tace "ai daman tafiyar zanyi", Abinci ta zubo musu ta kawo ta ajiye, ta koma kitchen ta ɗakko gaseous drink da pure water ta kawo ta ajiye, tana hararar Hajar ƙasa ƙasa tace "saiki matso muci", salon ta sake bata haushi tace "na ƙoshi", Hafsa ta ajiye spoon ɗin hannunta tace "ke kin isa, kadan ba sai kinci ba", Hajar ta tashi ta cire hijab ɗinta snn ta zauna ta ɗauki spoon, Hafsa ta kai spoon baki tace "toh ki bari ƙarfe biyar da rabi ko shida saiki tafi", Hajar ta noƙe kafaɗa ta cigaba da cin abincinta, suna gama ci Hafsa ta tattare plate da empty bottle na drink ɗin ta wuce kitchen dasu, ganin ta daɗe bata fito ba Hajar ta bi bayanta, tarar da ita tayi tana wanke wanke bakin sink, Hajar tace "Au wanke wanke kika tsaya", Hafsa tace "harda left over na safe da banyi ba". Hajar ta tattare hannun rigarta ta matsa gaban sink ɗin ta fara temaka mata da ɗauraya, Hafsa tace "kina fa da kirki amma kaɗan" Hajar tace "point of correction bani dashi". wata small pot Hafsa ta ringa gurzawa soson ƙarfe tace "Abdallah ne ya babbaka indomie da safe", Hajar ta leƙa cikin tukunyar ganin yadda tayi baƙi ta fashe da dariya tace "amma dai Indomien ba tada maraba da gawayi", Hafsa tace "uhmm gobara ya kusan tayarwa fa, ba kiga faɗan da yasha ba kuwa wajen Abba, har suka fita kasuwa Abba na faɗa", Hajar tace "wai Allah ya kiyaye". Ana yin sallar la'asar Hajar ta fara shirin tafiya, ta tsaya gaban mirror tana gyara ɗaurin dankwali, hijab ɗinta ta janyo zata saka Hafsa tayi wuf ta amshe tace "ki bari ba yanzu ba", Hajar ta riƙe ƙugu tace "ka jimu da mata, toh wai me zan miki?", Hafsa tayi serious face ta nuna mata kusa da ita tace "dan Allah zauna kiji", Hajar ta zauna tana kallonta tace "what..?", Hafsa ta marairaice fuska tace "tin kina nan gidan nayi masa alƙawari", Hajar da ta ƙosa taji mene tace "wa knn?", Hafsa tace "wnn mutumin da muka haɗu a supermarket", Hajar ta ƙanƙance ido tana nazari, lokaci guda ta gwalo ido waje tace "alƙawarin me kikai masa", kaf Hafsa ta gaya mata abinda ya faru, Hajar tace "toh yanxu ya kike so ayi?", Hafsa tace "so nake idan yazo ki fita, ni ko biki masa magana ba hakan ya wadatar", Hajar tace "da baikon a kaina zan tsaya da wni namijin", Hafsa tace "ai manufar abin zaki duba, bawai zaki tsaya dashi bane a matsayin saurayi, dan Allah don't turn me down just say Hi shknn", Hajar ta dafe kanta tace "wllh kin tafka wauta, idan ya wuce huɗu da arba'in tafiya zanyi wllh", Hafsa tace "bazai ma kai haka ba..." ko gama rufe baki ba tayi ba saiga kira nan yana shigowa wayarta, numbern kawai ta gani tayi ajiyar zuciya ta ɗauka, kara wayar tayi a kunne, yace "nazo", tace "Alright, wait a minute". ta kashe wayar ta kalli Hajar dake kallonta tace "yazo", gyaɗa kai Hajar tayi tace "toh sai muje ko", Hafsa ta gwalo ido waje tace "wai tare zamu, kefa kaɗai zaki", Hajar ta gyara zama tace "kince kar naje knn", Hafsa tace "toh sai ki yiwa Anty sallama daga nan ki wuce kinga na samu hanya sai nace rakaki zanyi", Hafsa ta saka hijab dinta, dakin Anty Hajar ta shiga tayi mata sallama, Anty ta bata 1k kuɗin mota, Hafsa tace "Anty na fita rakata", tare suka fita gate, Hajar ta matsa gefe tace "fara fita", buɗe ƙofar gate ɗin Hafsa tayi snn ta fita, yau ma dai a wata jugunanniyar motar yazo saɓanin ta ranan, yana hangota ta tint glass ɗin ya buɗe motar ya fito, mayar da door yayi ya rufe snn ya ƙaraso wajenta yayi sallama, tace "wslm, ina yini", yace "lfy lou, ykk?", tace "alhmdllh am great", juyawa tayi da nufi mgana da Hajar ai kam taga wayam, tace "lemme get her" ta shiga gida, a tsaye ta ganta da wani expression bisa fuskarta, Hafsa tace "toh muje", Hajar tace "wllh ban san me zance masa ba", Hafsa ta ja hannunta tace "anything" saida ta kaita har gabansa snn ta cikata, Hajar ta ja baya making some distance between them, Hafsa tace "As promised", waje ta basu ta shiga maƙotansu, gefe Hajar ta kalla tace "ina yini", bai amsa ba ya jefa mata tambaya "you blocked my number right?", kanta a ƙasa tace "yess", kallon fuskarta kawai yake yace "why?", tace "sorry you ask for a chance da bazan iya baka ba, kayi haƙuri dan Allah, wllh a lokacin inada manemi wnda yaje wajen iyayena, bana so na ɓata maka lokaci shiyasa", wani iri ya ji har cikin zuciyarsa yace "Alright, ynxu fa?", tace "ynxu kam an riga an min baiko, kayi haƙuri..", wani deep breathe ya sauke yace "ba damuwa Hajar, loosing you is one of my destiny, may Allah choose the best for us", a karo na farko da ta ɗago ta dubesa, ta mayar da kanta da sauri tace "Ameen, nagode", gidan da Hafsa ta shiga ta nufa ta fara knocking, Hafsa ce ta buɗe ganinta ta fito tace "har ya tafi..." shiru tayi ganinsa a tsaye yana kallonsu, ta ƙarasa inda yake tace "then ynxu dai na fita daga jerin masu yanke fate, na cika alkawari", yace "thank you", tace "don't mention, sai anjima", yayi waving ɗinta slightly snn ya juya ya shiga motarsa zuciyarsa a dagargaje, wani irin cin taya yayi ya juya kan motar, da gudu yabar unguwar tamkar zai tashi sama, Hajar tabi ƙurar da ya tayar da kallo snn ta matsa kusa da Hafsa suka sauka kan titi, Hajar tace "ya bani tausayi wllh", Hafsa tace "Allah ya basa wata". da haka Hajar ta tsari Napep ta wuce gida.


★A kwana a tashi lokaci bashi da wuya wajen shuɗewa a wajen Ubangijin talikai, mu shagalallun bayi mu muke ganin jimawarsa harda ɗokin cika burikan rayuwa ( yau HAJAR ya ɗakko wani daga cikin scene na littafina SOHANA), A wannan rana ta laraba saura wata ɗaya bikin Hajar, kuma a wnn rana aka kawo lefe, manya manyan tabarmi har guda biyu aka baje a tsakar gida da yamma ana jiran ƴan kawo lefe, Maama da ƴaƴanta sai shige da fice suke suna yaɓa baƙaƙen maganganu, tin Anty Jamilah na sharesu har ta fara mayar musu da wacca tafi tasu zafi da ciwo. an zuba bajinta gsky, lefen Hajar san kowa ƙin wanda ya rasa, dangin Ango suna gama sauke kayan lefe suka ce suna buƙatar a ƙara musu wata ɗaya domin ango ya gama shirye-shiryen sa, kai tsaye aka amsa musu dan Anty da Umma suma suna son su gwangwaje ƴarsu, tray tray su Anty da wasila da sauran ƴan uwan Umma suka ringa fitarwa na kayan motsa baki da kaji da kuma steak suka bawa ƴan kawo lefe, ga kuma kuɗin tukuici mai tsoka da aka basu, sunji daɗin karamcin da iyayen Hajar sukay musu, nan fa aka baje kaya ana musu ɗaɗɗai kowa na sanya albarka, maƙwabta da abokar arziƙi kowa shigowa yake yana kashe kwarkwatar idonsa, a duk wnn zazzafar wainar da ake toyawa Maama da ƴaƴanta sun ƙule ɗaki saidai fa komai akan micimicin idanunsu tinda laɓewa sukay jikin labule da window suna leƙe. baƙin ciki da hassada ainun suke nunawa, Anty sai ɗaɗɗaga kaya take tana saka albarka, wasila kuma na rangaɗa guɗa, da baƙin ciki ya ishi Maama da sauri ta bar bakin labule ta zauna ƙasa daɓas ta dafe kai, Sa'adatu kam tsaki tayi ta koma gado tayi kwanciyarta tace "ko sha'awa", Maama tace "ƙarya kike munafuka, wane mai zuciyar ne zaiga uban kayan nan yace basu birgesa ba..", Nabilah ta rage murya tace "haba Maama kiyi magana a hankali kar ace baƙin ciki muke", da ƙarfi Maama tace "Eh aji ɗin mna" sai kuma ta miƙe ta gyara ɗaurin zaninta ta saɓi hijab tayi waje, da sauri Maama ta fice daga gidan zuciyarta na tafarfasa ta saɓi hanya........✍️


🔔*WEDDING BELL*🔔 

Ehen it's ringing...... ƙalalannnn 🔔


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.