Free chapter 路 Read without an account

{29..}

by Feenerh Feeche Studios 路 HAJAR

馃挍 HAJAR 馃挍



Wani mugun murmushi Balaraba tayi tace "wnn ai bai kai abinda zaki shiga uku ba 茩awata, karki damu..", Maama ta katseta da fa蓷in "ya za kice kar na damu.., nace miki fa bana son yarinyar da uwarta su cigaba", Balaraba tayi tsaki tace "ai bazasu cigaban ba, me kike so ayi?", Maama tace "kar ayi auren nan ko ta halin 茩a茩a ne", Balaraba tace "kinxo ta gidan sau茩i, malamin tsamiya shi zai zartar miki da aiki kina zaune hankali kwance, wllh aikinsa kamar yankan wu茩a", Maama tace "yo ai idan ana neman ruwan kashe gobara har na kwata 蓷iba ake, sai muje wajen nasa", Balaraba tace "hmm matsalarsa ku蓷i, baya aiki sai yaji dumuss", Maama tace "wnn ba matsala bane, kamar nawa zan tanada?", Balaraba tace "A茩alla ki ri茩e dubu hamsin a hannunki", Maama ta gwalo ido tace "dubu hamsin, jar bala'i ina naga dubu hamsin", Balaraba tace "dole kam kiyo kashinsu in kina son burinki ya cika", Maama ta zabga tagumi tana tinanin a ina zata samo wa蓷annan ku蓷i, Balaraba tace "uhmm idan so samu ne ma ace yanxu haka kinada ku蓷in, in ban manta ba dududu saura wata 蓷aya da sati biyu bikin ko?", Maama tace "haka yake", Balaraba tace "gsky dai ya kamata ki farga, ki nemo ku蓷in nan fa", Maama tace "bani kwana uku zan nemosu kuwa", Balaraba tace "A toh kika tsaya bacci dai kwa蓷o ne zai miki 茩afa", Maama tace "ke an ma samu fa an gama wa蓷annan ku蓷i", Balaraba ta mi茩e tace "to nidai nabi ta nan, daman cewa nayi bari nayi maza na ankarar dake", Maama tace "sai kin jini", Balaraba ta fito tsakar gida Maama biye da ita, a lokacin Hajar ta fito daga bayi knn, ta gefen ido Balaraba ke kallonta snn tayi soro, ta juya ta dubi Maama tace "itace ko?", Maama tace "itace shegiyar..", Balaraba ta jinjina kai sukay sallama da Maama ta tafi. Washe gari Hajar ta ha蓷a 拼an kayanta a Jaka zata wuce gidan Anty Jamila, tin ranar da aka kawo lefe Anty taso ta bita gidan amma Umma tace malam bazai bari ba, yanxun ma dai da kyar Baban ya amince, da yamma ta tafi bayan ta gama shirinta, murna wajen Hafsa ba'a cewa komai tace "yanzu fa shknn, ba zuwa gidan nan zaki ringa yi kina kwana ba", Hajar ta juya idonta tace "kin san me?", Hafsa tace "A'a saikin fa蓷a", Hajar tace "nifa banga lefen ba, ranar da aka kawo bana nan ina gidan Iya, kuma dana dawo ban bi takansu ba kar Umma tace min mara kunya", Hafsa tace "toh yanxu ya za ai?, gani za kiyi ne?, sai Anty tace miki mara kunyar", Hajar tace "A'a ke ni ba gani zanyi ba, ki gayamin mene ne aciki", Hafsa tace "chabbbb ai ki gani da idonki yafi, gsky fa ya sayyadinki ya zuba miki kaya", murmushi Hajar tayi tace "Allah..", Hafsa tace "Anty ta kira wacca za ta ringa yi miki gyaran jiki, ina jin ma jibi zata fara zuwa", Hajar ta gwalo lulu eyes 蓷inta tana kallon jikinta tace "Me za a gyara", harararta Hafsa tayi tace "zaki gani ne aii". Humaira ce ta shigo tace "yaya Hajar wai kixo inji Anty", Hajar ta tashi tace "toh", suka fita tare da Humaira, room 蓷in Anty suka shiga, Anty na zaune gefen gado ga boxes nan sun cika sararin 蓷akin, Anty ta kalli Hajar tace "ki ma kwa ga kayan?", gya蓷a kai Hajar tayi tace "Eh", Anty tace "toh daman kiran da nay miki knn, tinda kin gani shknn", Hajar ta juya ta fita ta koma wajen Hafsa, tace "kiran da tay min tambayata tai naga kaya, ni kuma nace mata Eh", Hafsa tace "kinga kwantar da hankalinki, nasan Anty a wnn week 蓷in ma saita fita, tinda bana zuwa schl an mana hutu mu bari idan ta fita sai muje kiga lefenki a tsanake".


鈽匘a daddare Maama ta tarfa Sa'adatu da Maimuna a 蓷aki, Sa'adatu tace "wllh Maama ni ba nida ku蓷i, ina naga wata dubu talatin, ina ma laifin dubu goma amma shine za kice na baki dubu talatin, wllh ban dasu ba nida dalilinsu...", Maimuna da ta tamke fuska tamkar tsohon ba茩in hadari tace "yo kema knn, bare ni, wai dubu ashirin", Maama tayi kwafa tace "duk za kuci gidan ku, dani kuke zancen, toh wllh ko kun茩i ko kun so sai kun bani ku蓷in nan, yanxun nan ma kuwa", Maimuna tace "nidai Maama saidai ki yanka ni amma ban dasu eheee", Nabilah dake sauraron su tace "anayi ina cin indomie, ni kam ko ta kaina ba a bi sbd ansan babu, Hajjajai maza ku bu蓷e lalita hajiya Maama na jiran dumuss", Sa'adatu tace "ai kam dai baxa ta ji wani dumuss ba, Maama nidai kin san in ina dashi zan baki", Maimuna tace "nima dai in ina dashi zan.....", katseta Maama tayi da fa蓷in "茩arya kike uwar mamma茩o, a gidan ubanwa kike ban iyee?, toh bari kuji in gaya muku karku zata ban sani ba, sarai nasan cewa ba makaranta kuke zuwa ba daga zarar kun fita sai ko waccen ku ta wuce shu'uninta, ko ku bani ku蓷i ko na gayawa Babanku, kuma kun san cewa Nasiru na gida, babu abinda ya shalleni haka zan bada fuska ya zane muku jiki, kai wllh har ziga mal zan ringa yi dan jikinku ya gaya muku, ni zaku mayar yarinya kucemin wai baku da ku蓷i..", Sa'adatu tace "to ki fa蓷a mana ai nace miki banda su...", Maama tace "haka kika ce ko?", Maimuna tace "Maama ai gaskiyar knn", gya蓷a kai Maama tayi ta isa bakin 茩ofa ta 蓷aga murya tace "Malammm", da wani mugun zafin nama Sa'adatu ta rufe mata baki, Maimuna kuma ta kama zaninta sai muzurai take, habawa ai Nabilah kifowa tayi daga kan gado sbd dariya, Maama ta kwace bakinta tace "zaku bayar ko a'a?", ha蓷a baki sukay su kace "zamu bayar", Maama ta hura tukubar hanci tace "jikinku ya huta" ta fizge zaninta daga hannun Maimuna. daga waje Baba ke neman ba'asin kiransa da akay, Maama ta sake 蓷aga murya tace "daman cewa nayi barka da hutawa". A take Maimuna ta bu蓷e jakarta ta lalo duba ashiri ta mi茩a mata a wula茩ance, Sa'adatu kuma ta kira Zeenatu tana mata wata maganar 茩irsa tace ta turo mata mutsabbai, da kyar Sa'adatu ta lusar da Maama cewa gobe da safe zata fita Pos ta ciro mata ku蓷in. Da sassafe kam Maama ta tayar mata da mandiran zuciya, haka ta fita tasha wahala harta nemo pos ta ciro ku蓷in ta kawo mata, tinda Maama taga dubu hamsin dumuss a hannunta ta fara shirin zuwa gidan Balaraba, 茩arfe goma na safe ta fice don saida ta bari Baba ya fita, tana isa gidan abokiyar cin mushen nata ta azalzale ta, sharp sharp Balaraba ta shirya suka sa蓳i hanya, tin 茩arfe sha 蓷aya suka fita amma basu dawo ba sai yamma li茩is, gidan Balaraba Maama ta tsaya ta huta snn kuma ta amsa mata tambayoyin da take ta ri茩onsu tin bayan fitowarsu daga wajen malamin tsamiya, ruwa kawai tasha ta hau surfa mata tambaya, Balaraba tace "kai Jama'a tinda fa yace aiki ya kammala to mgana ta 茩are", Maama da idanunta sukay jajur tsabar wahala ta tafiyar mota da 茩afa tace "da farko fa cewa yayi tabbas yaga ana biki, kuma aure sai an 蓷aurasa", Balaraba tace "ai kece kika ringa cewa ga abinda kike so ayi, kinga kin ce masa a sawa yaron tsanar yarinyar kuma da ya duba allon bokancinsa yace miki hakan bazai yiwu ba sbd yaron akwai addini, ba za a iya samun galaba dashi cikin sau茩i ba, idan kwa aka matsa to lokaci zai 茩ure har ranar auren tazo ba a samu galabar ba, shine yace ya sami lagon yaron wanda dashi zaiyi amfani, kuma ma yace aiki ya kammala kawai ki jira lokaci", Maama ta sauke wata gauruwar ajiyar zuciya tace "yanzu dai ba matsala knn?", Balaraba tace "kwarai kuwa, ki saki jikinki ki shiga bidirin biki, daga gefe kuma ki zubawa sarautar Allah ido kiga ta inda 蓳araka zata 蓳ullo", tin daga wnn moment Maama ta samu peace of mind, daga gefe guda kuma tana jiran ranar da fa蓷ima da shegiyar 拼arta za suji kunya.


鈽匴ani irin fresh Hajar tayi, fatarta tayi luwai luwai har wani she茩i take sbd gyaran jikin da akai mata na sati biyar, ga wani sassanyar kamshi da yake tashi ajikinta, duk inda ta gifta sai 茩amshi, ko a waje ta zauna sai ya 蓷auki lokaci 茩amshin bai baje ba, ilahirin jikinta kamshi yake, gashinta kam tamkar gonar furanni masu 茩amshi, babu inda take zuwa, ba ta shiga rana shiyasa gyaran yayi armashi, ko kitchen Anty ta hanata shiga, idan ma aikin za tayi iyakacinta palour da 蓷akuna amma banda gaban wuta da rana, Nura kam kullum yana kan hanyar zuwa, 蓷ai蓷aikun ranaku ne kawai baya zuwa, ji yake tamkar ya janyo lokacin akay masa ita kawai, wata sha茩uwa ce ta shiga tsakaninsu a wnn ta茩in, Yau ma dai mai gyaran jiki tazo tayi mata ta gama ta tafi, toilet ta shiga tayi wanka, ta fito tana wani 茩amshi na daban wadan ya gauraya da wanda take zubawa kafin shigarta wankan, zama tayi kan stool ta janyo sabon man da take shafawa na gyara fata da saka glowing, a tsanake take tattale fatarta da tayi wani laushi da santsi, ita kanta yaba kyan da tayi take a zuciya, Hafsa ce ta shigo hannunta ri茩e da cup, ajiye cup 蓷in tayi kan mirror tace "ki shanye yanxu ki bani kofin na mayar mata", Hajar ta 蓷auki kofin ta kwankwa蓷e ta mi茩a mata empty, ( Ehen ba fa maganin mata bane, it's not good a bawa budurwa, maganin infection ne da cire dattin golden organs of a woman). doguwar riga ta material ta saka snn ta fita palour, zama tayi kan kujera tana latsa wayarta, tanan suke magana da zainab akan bikin musamman ma walimar da zatay, Anty ta fito da shirin fita da jaka a hannunta tace "ina Hafsa?", Hajar tace "tana kitchen", kitchen 蓷in Anty ta shiga, bayan few seconds ta fito tace "na tafi", Hajar tace "A dawo lfy", tace "Ameen", snn ta fita, su Anty an shiga ruruma don yanxu bikin saura 1week, sha'anin jera gidan amarya suka karkata. A hankali Hajar ta dafe kanta tace "subhanallah innalillah wa'inna ilayhirraji'un" sakamakon gabanta da ya yanke ya fa蓷i ba gaira ba dalili, sau hu蓷u yana mata haka bayan zamanta a palourn, wayar ta ajiye ta mi茩e ta tafi kitchen wajen Hafsa, Hafsa tace "Abu zaki 蓷auka ne?", girgiza kai Hajar tayi tace "nope nagaji da zama ni ka蓷ai", Hafsa tace "kinga ki fita ynxu zan fito bari na gama zuba seasoning a miyar", Hajar tace "kawo na 蓳are miki maggin", Hafsa tace "A'a zanyi da kaina, Anty fa tace ki dena shiga kitchen", turo baki tayi ta bu蓷e fridge ta 蓷auki ruwa ta fita, tana 茩o茩arin zama gaban nata ya sake fa蓷uwa, nan ma dai Addu'ar tayi, har bayan Sallahr isha'i abinda take fama dashi knn, a hankali ta tashi daga kan dardumar da tayi sallah ta nanna蓷e, wayar tace tayi 茩ara wanda ya razanata tsabar rashin sukunin da ya risketa a bazata, ta 蓷auki wayar tana kallon mai kiranta, ( ya sayyadi na) haka tayi saving, picking tayi ta kara wayar a kunne, ajiyar zuciya taji ya sauke snn yace "Hajar", tace "Na'am", yace "dan Allah fito na ganki, gani nan a 茩ofar gida".......鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.