Free chapter · Read without an account
{33..}
Farooq ya buɗe back seat ya ciro bag da trolley, ya kalli Nurain da ya gama stretching kansa yace "wai ka gaji ne?", Nurain yayi ƙass ƙass da fingers ɗinsa yace "yeah, am exhausted". da sauri Garba ya taho wajen, har ƙasa ya durƙusa yace "sannu da zuwa Alhj ƙarami, an dawo lfy", Nurain yace "yauwa Garba, ya ƙasa?", Garba yace "ƙasa tana nan yadda ka barta", tashi yayi ya gaida Farooq ma snn ya amshi bag da trolley. huge luxury main building ɗin gidan suka nufa, suna isa balcony Nurain ya danna bell, few seconds Noor ta buɗe, ta daka tsalle tace "oyoyo Yaya" sai kuma ta koma cikin palourn tana cewa "the groom is here Mami", sosai abinda ta faɗa yayi hitting eardrums dinsa, wai the groom, ya juya ya dubi Farooq yace "you", Farooq ya girgiza kai yace "nope", ai tini Noor ta shige part din Mami, Farooq ya zauna a daya daga cikin executive sofar dake babban palourn, Garba ya ajiye kayan da ya shigo dasu yayi waje, Nurain kam part din Mamin sa ya nufa, Mami ta fito daga bedroom ɗinta knn ya shigo, Pcap ɗin kansa ya cire ya zo ya rungumeta yace "i missed you Mami", Mami tace "Nurain...", Noor da ke murmushi all her white tooth out tace "Yaya sannu da zuwa", yace "lil iron lady, how are you doing", tace "am great alhmdllh", Mami tace "ina Umar ɗin?", yace "yana palour", tace "Ohk, muje can", main palourn suka fito, Mami ta zauna tace "mijin Hajiya", Farooq yayi murmushi yana shafa kansa ya zamo ƙasa ya gaidata, Mami ta amsa tace "ka ɗakko brother ɗinka knn?", yayi murmushi yace "Eh", Nurain ya zauna bisa lallausar rug din palourn ya gaisheta shima, ta amsa tana saka masa albarka, Kitchen Noor ta shiga ta ɗakko ruwa da drinks with glass goblet ta fito, kusa da Farooq ta ajiye tace "ina yina ya Farooq", yace "lfy lou Noory", tace "yasu Ummi da Aysha?", yace "suna nan lfy". Nurain yace "Abba fa?", Mami tace "yana ciki", yace "ohk bari naje wajensa", ya dubi Farooq yace "muje dude", a tare suka shiga part din Abba, Mami ta dubi Noor dake operating waya tace "ohh kin fara jarabar danna wayar ko?", tace "No Mami, course mate ɗita ce ta turomin da question na assignment", Mami tace "toh tashi ki shirya musu dining kafin su fito", tace "tom", ta ajiye wayar ta gyara hular kanta ta shiga kitchen. Abba ya kawar da system da yake operating ya daga kai yana kallon zaratan samarinsa, da Farooq suka fara gaisawa kana Nurain, Abba yace "ya aiki Engineer?", Farooq ya shafa kansa yace "alhmdllh Abba", Abba yace "toh madallah Allah ya temaka", Farooq yace "Ameen", Abba yace "Uthman..", Nurain yace "na'am", Abba yace "ya karatun, an gama lfy?", Nurain yace "Eh alhmdllh, an samu abinda aka je nema", Abba yayi ajiyar zuciya yace "masha Allah, Allah yasa ya amfana", tare suka amsa da Ameen snn suka fito. already Noor ta gama setting table, Mami tace "ga abinci kan dining", Farooq ya dubi tsadadden agogon wrist dinsa yace "wllh Alhmdllh, am full, zan wuce yanxu", yayi musu sallama ya tafi, har compound Nurain ya rakasa snn ya dawo, Noor ya saka ta kawo masa abincin nan palour ya ci don shi he don't like it eating on table, ba laifi yaci abincin cause yaji taste en abincin na Mami ne, ya ture plate din daga gabansa ya buɗe bottle water ya zuba a cup ya sha, stretching kansa yayi yana lumshe ido, duk gajiya ce ajikinsa, duk lokacin da yayi tafiya a jirgi sai yaji kamar nerves ɗinsa sunyi freezing, shiyasa yake yawan yin miƙa, Mami tace "ka je ka huta Nurain", yayi ajiyar zuciya yace "yeah", ya tashi yana massaging neck dinsa, trolleynsa ya janyo yace "ga stuff na India", Noor tace "Yaya a New Delhi ka zauna?", yace "yap, that's where my school is", da haka ya ɗauki bag ɗinsa ya haye stairs still massaging his thick neck, ya tarar da room ɗinsa a gyare tsaf tsaf komai tide, ƙamshin freshner da traditional scent mai dadi ne yake tashi, ga sanyin Ac, huge Chinese comfortable bed ɗinsa malale da white bedding. wayarsa ya ɗakko daga bag yayi powering dinta, ya cire Sim card ɗin ciki ya musanya da ainahin nasa na Nigeria, ya ajiye wayar akan mirror ya shiga bathroom domin ya sakarwa kansa warm water, ko 1min beyi ba da shiga wayarsa ta fara tsuwwa, kiran na yankewa wani ya sake shigowa, shima yana katsewa wani ya biyo baya, haka kiran yayi ta shigowa ba ƙaƙƙautawa, da sauri ya gama abinda zai ya fito, yayi wrapping kansa da bathrobe, gefen kunnensa duk kumfa sbd saurin da yayi ya fito don yaga wane yake masa wnn mummunar kiran daga kunna waya, ɗaukar wayar yayi wacca take ringing har lokacin, ya tattare gira gami da tsuke piercing eyes ɗinsa yana kallon screen ɗin wayar, sunan da yake jiki da kuma numbern ba baƙinsa bane, tabbas beyi blocking numbern ta ba amma kuma bai sake kira ba, wani ɗaci yaji a throat ensa, ya dangwarar da wayar yace "Damn it.."
★Kaf waɗanda suka zo biki sun ɗaɗe, mutanen Yola kam ana gama ɗaurin aure suka saɓi hanya, Anty Jamila sai Hafsa wacca aka bari domin ta ɗebeba Hajar kewa ne kawai suke rage a gidan, Wasila kuma ta tafi da zummar insha Allah gobe da sassafe zata dawo. da hijab ɗin da tayi sallar isha'i ta ƙudunduna ta takure waje ɗaya, a kwance take kan dardumar da ta idar da sallah, hawaye na zuba daga manyan lulu eyes ɗinta waɗanda suka ƙanƙance tsabar kukan da ta sha, ƙirjinta da maƙoranta har zafi suke sbd shessheƙar kuka, Anty ta tsaya a kanta tace "hasbunallah, Hajar ba zaki dena kukan nan ba ko?", da dasasshiyar murya tace "ba kuka nake ba", Anty tace "toh tashi zaune", a hankali Hajar ta miƙe zaune ta jingina da bango, sosai ta bawa Anty tausayi tace "za kici abinci?", ta girgiza kai tana goge kumatunta tace "na ƙoshi, bazan iya ci ba ƙirjina ciwo yake", Anty tace "sannu, ai baza ki kwanta da yunwa ba bari a siyo miki yoghurt" da haka ta fita daga ɗakin. Hafsa ta matsa kusa da Hajar tace "sannu sister", Hajar tace "wllh ji nake kamar zuciyata zata fashe, wai ba ya sayyadina na aura ba, na shiga uku Hafsa", ta rufe fuskarta da hijab ta sake rushewa da kuka, Hafsa tace "Allah ya ƙaddara ba shine mijinki ba, kiyi addu'a Allah yasa hakan alkhairy ne a gareki", Hajar na shessheƙar kuka tace "ban san fa wanda aka aura min ba, ban san wane irin mutum bane". Hafsa tace "koma waye insha Allah alkhairy ne", jinginar da kanta tayi a bango ta lumshe idonta, hawayen da suka taru suka fara zarya a kuncinta. Sallama aka rangaɗa daga soro, Anty dake tsakar gida tana waya da Mu'azzam da take basa saƙon siyo yoghurt, kashe wayar tayi ta amsa sallamar da akay, Umma ta fito daga ɗakin Baba tace "waye?", matar da tayi sallama ce ta shigo tace "Larai ce", Umma ta tsaya tana kallonta da taimakon hasken kwan lantarki sbd akwai nepa, Umma ta shimfiɗa tabarma tace "Bismillah" duk da dai bata shaida wace ce ba, dattijuwar da ta kira kanta da Larai ta zauna akan tabarmar da Umma ta shimfiɗa, gaisawa sukay, Anty ma ta gaisheta, ta dubi Umma tace "baiwar Allah kece mahaifiyar Hajara", Umma tace "Eh nice", tace "Alhmdllh, wllh tllh nice nayi muku laifi, dan girman Allah kuyi haƙuri", Umma tace "Allah sarki, laifin me kika min baiwar Allah?, ai ni ban ma shaida ki ba", tace "mahaifiyar Nuraddeen ce wanda za a ɗaura masa aure da ƴarku", tini Umma ta canza fuska, Anty da ke zaune kan ƙaramar kujera ta ɗaure fuska, Umma tace "oho, to ince dai lfy?, ai an mayar muku da kayanku", Hajiya tace "ba wnn bace ta kawoni, dan girman Allah kuyi haƙuri akan abinda mu kayi muku, wllh laifina ne shiyasa na taso takanas nazo domin na baku haƙuri", Umma tayi murmushin yaƙe tace "ba komai mun haƙura, muma Allah ya yafe mana", Hajiya tayi ajiyar zuciya tace "Alhmdllh, Allah yayi albarka, auren da aka fasa ɗaurawa da rana sai a ɗaurasa yanxu da daddare", Umma ta ajiye numfashi tace "bari nayi miki magana da baban yarinyar" da haka ta miƙe ta shiga ɗakin Baba, kaf yaji abinda ya faru don haka bai bata damar magana ba ya fito tsakar gidan, Anty ta tashi ta shiga ɗaki. Baba ya gaisa da Hajiya wacca ta shiga basa haƙuri, yace "Allah sarki, ai komai muƙaddari ne..", Hajiya tace "haka ne, amma wllh nice nan silar wnn babbar ɓarna, dan girman Allah ku yafe min, a ɗaurawa ɗana Auren da yarinyar ku", Baba yayi ajiyar zuciya yana jujjuya wnn lamari, Maama ta fito da ɗauri ƙirji da mafici a hannunta tace "haba don Allah, wllh kun fiya gutsittsira zance, kawai ku gaya mata cewa an ɗaurawa Hajara aure da wani a maimakon ɗanta", da matuƙar mamaki Hajiya ta dubeta sai kuma ta kalli Baba tace "wai haka ne?", Maama tace "Yo ya faɗa miki da bakinsa kiji, shi ya aura mata wani da ɗanki yace ya fasa", Hajiya ta fara matsar kwalla tace "wllh babu ruwan Nuraddeen, nice me laifi, ni nace a fasa auren, wllh lokacin da nake faɗa ma ban san inda kaina yake ba, dan Allah dan darajar alƙur'ani mai girma karku hana ɗana auren ƴarku", Baba yayi ajiyar zuciya gami da yin gyaran murya yace "Hajiya ai bakin alƙalami ya bushe sai dai ɗanki ya nemi wata, yanzu maganar da nake miki na aurar da Hajara", Maama na fifita da mafici tace "Atoh ai yafi dai ka gaya mata gaskiya", Hajiya ta zabga wani uban salati sai kuma ta ɗaga murya tace "Nuraddeen...", Nura ne ya shigo da sallama, daman yana soro a tsaye shine ma ya rako Hajiyar. wata iriyar zabura Hajar tayi ta miƙe tsaye jin muryarsa, ta tsaya a jikin window tana leƙen tsakar gida, wani shauƙin kuka ne taho mata da taga fuskarsa, Hajiya tace "Nuraddeen, basu haƙuri da kanka, ni kam sun ƙi amsar nawa", Nura da har fuskarsa ta faɗa na wuni ɗaya ya durƙusa, ya gaishe da Baba kana Umma da hankalinta ya fara tashi, fuska babu yabo ba fallasa Baba yace "ba ƙin haƙura mukay ba, ai haƙurin ne ma yasa na saurare ki, kuma haƙurin za kuyi Hajara matar wani ce", Nura ya zuba guiwoyinsa a ƙasa yace "Baba, dan Allah kar a rabani da Hajar, ku yafe min...", Umma ta tashi ta shiga ɗaki, Baba ya girgiza kai yace "kayi haƙuri Nura wllh an riga an ɗaurawa Hajara aure...", Hajiya ta ɓarke da kuka tace "wllh nice sila, Nuraddeen ka yafe min, ban kyauta maka ba, ban yi maka adalci ba, duk abinda nake so shi kake min, ni kuma na datse maka farin ciki, wllh ban san na aikata maka hakan ba, na ɗauka mafarki nake ashe a zahiri na aikata...", Nura kam ko fahimta me take cewa beyi ba sbd juyawar da kansa yake masa, ga wani raɗaɗi da zuciyarsa ke masa, Baba ya kawar da kai yana jujjuya wnn lamari a kwanyarsa, abu sai kace a film. Nura ya tashi yana layi ya taimaki mahaifiyarsa ta tashi itama yace "Allahumma ajirni fi musibati wa aklufuli khairan nimha", shi wnn babbar musiba ce a wajensa, ya juya yay hanyar soro, Hajar ta sulale ƙasa ta cigaba da rusa kuka da dashasshiyar murya, a ƙofar gida Nura ya haɗu da Mu'azzam da yake shirin shiga gida, cike da mamaki Mu'azzam ya dubesa yace "ya sayyadi..", Nura ya kallesa da jan ido yace "Mu'azzam" da haka yayi gaba ya fara tafiya da sauri tamkar zai tashi sama, gida Mu'azzam ya shiga, yabi Hajiya da ido wacca take ƙoƙarin fita tana matsar kwalla. yayi sallama a bakin ƙofar ɗakin Umma ya bawa Anty saƙon yoghurt da ya siyo. da kyar Hajar ta sha quartern yoghurt din, ta sha panadol sbd kanta da yake mugun ciwo. wnn night shine worst night a rayuwarta, she couldn't sleep at all even a nap.
★Washe gari da safe, Nurain na zaune a balcony perceiving the morning blessings, wayarsa yake latsawa time to tima kuma yana sipping black coffee, last night da kira aka addabesa har saida yayi silencing wayar ya samu yay bacci, da safe kam missed calls da ya shallake expectation nasa ya gani, sai kuma ta ɗora da text message, a ƙalla daga asuba zuwa yanzu da ake maganar ƙarfe bakwai da rabi ta turo masa da messages sama da goma, kuma ko ɗaya bai karanta ba, daga message ɗinta ya shigo yake wipping notifications ɗin wayar, shifa indai ya bar abu to ya barshi kenan no going back, yanada zuciya sosai saidai kuma kafin yayi zuciyar sai ransa ya ɓaci. wayarsa tay vibrating, yana dubawa yaga Abba ke kiransa, picking yayi ya kara a kunne, Abba yace "ka sameni a great room now", Nurain yace "yeah", da haka Abba ya katse kiran, ya ɗaga coffeen sa ya shanye snn ya tashi ya shiga ciki da cup ɗin a hannunsa, kitchen ya wuce ya ajiye cup din snn ya fito ya nufi great room din Abban sa. ya cire soft slippers dake clean legs ɗinsa ya shiga great room din, yana shiga Abba yayi pointing kujera yace "sit", Nurain ya zauna looking at his Father. Abba yace "Uthman, tin jiya naso nayi informing ɗinka amma na bari sai yau", Nurain dai baice komai ba kawai kallon Abban nasa yake, Abba exhale heavily yace "na ɗaura maka aure da ƴar wajen abokina...", with a weird facial expression Nurain ya dubesa, peach lips dinsa ya motsa a hankali yace "marriage..", direct Abba yace "yess, jiya aka ɗaura auren, and insha Allah today za a kai maka matarka gidanka, get ready to settle down Son".....✍️