Free chapter · Read without an account
9
*TSARIN ALLAH*
(_Bamai iya canzawa_)
DAGA ALKALUMMAN YAN TAGWAYE BIYAR
Arewabook@Nana diso10
NA
NANA DISO
&
ASMY B ALIYU
9...
A ranar hajja,tayi magana da Aunty maimuna dake Tareda mijinta a Abuja.ita kanta Aunty Maimuna tayi murnar da wannan batun ,saboda tasan aminatu itace zata dace da rayuwar sadauki Allah ya kawo masa mata har a gida.sosai hajja ta tattauna da Auntyn Maimuna ,saboda babu irin wannan kunyar a tsakaninsu ta ya'n fari ko shawara hajja ke nema zata fara zaunawa da ya'yanta kafin maganar ma ta fita.anan Aunty Maimuna ke cewa tayi magana da baffa ko a waya ne.itama tana saka ran nan da sati ɗaya zasu baro Abuja.
hajja ta gamsu da bayanin Aunty maimuna.bayan ishaai ta kira Alh.Usman Sadauki suka tattauna sosai shima yayi na'am da zancen.
Dan yana son Sadauki ya aje iyali a kusa dashi a matsayinsa na babban ɗan kasuwa wanda kasa ke damawa da business dinsa Gabaki ɗaya.washe gari Hajja ta tunkari Hajiya bilki da maganar Auren Sadauki da Aminatu
Da shock Hajiya bilkin kebin hajja da kallo sai kace a mafarki addu'a take in ma mafarki ne ta farka dan tasan Sadauki yafi qarfin yarta ta kowace siga.bilki kinyi shiru kodai Bazaki bawai Sadauki Aminatu ba.?"Hajiya bilki da tayi nisa cikin tunani taji zancen Hajja,cikin rawar murya take faɗin."hajja shi sadaukin ne yaga Aminatu yace yana so?"naji kamar jia ne mafa ya dawo duka -duka yaushe yaga Aminatu har yaji yana sonta.
Hajja ta girgiza kai cike da damuwa tace faɗin.shin bilkisu ko baki yadda da tarbiyar sadaukin bane shiyasa kike konkonto.da sauri hajia bilki ta girgiza kai tana faɗin.ko kaɗan hajja wannan tunanin bai zo kaina ba .
Kawai dai ina mamaki ne.ki daina mamaki da ikon Allah Hajiya bilki
Ina son kiyi magana da mahaifan Aminatu maza.ko nan da sati ɗaya ne za'a je nemarwa Sadauki auren aminatu.shock yasa Hajiya bilki ta kasa magana.tana jinjina karamci irin na hajja,da duka ma ya'yanta.bayan sun kammala magana.hajja ta bata takardun gidan da Sadauki ya mallaka masu harda key.murna yasa Hajiya bilki fashewa da kuka a gaban hajjar ta durkushe.Sai da hajja tace bata son irin wa'yannan abubuwa kyauta ce daga sadauki kuma karta yi tunanin wai saboda zai auri yarta ne
Ya mata wannan kyautar.tun shekarun baya ya dauki wannan alkawarin.hajia bilki dai kasa magana tayi Gabaki ɗaya.sai bayan ishaai tayiwa hajja,sallama sadaukin da take jira ya dawo tayi masa godiya bai dawo ba.sai da suka zo kwanciyya ta shiga yiwa aminatu bayanin Aurenta da sadaukin ke sonyi ko a fuska aminatun bata nuna komai ba saboda miskilance ta gaske Amman Acan qasan ranta damuwa ce sosai.tana tunanin kamar Sadauki yafi karfinta ta koina taya zai fito neman aurenta lokaci ɗaya.daga haɗuwarsu a jia wacce gaisawa kawai sukayi batama tsaya tantance kamanni sadaukin ba yaya yake.Amman ummah,bai taɓa cewa yana sona ba haɗuwarmu daga jia nefa.baki Hajiya bilki ta buɗe tana kallon miskilar yar tata.taya Allah ya kawo mata miji cikin sauqi mijin da ta shagori kafin ta samesa yanxu shine har take tunanin wani so.tunda har ya amince zai aureki ai kin san yana sonki."daman amincewarki nake nema kafin na kira dangin Mahaifinki gobe da safe.kin amince suzo neman auren naki Aminatu?"Hajiya bilki ta faɗa cikin sanyin murya ganin yadda yar Tata tayi sanyi lokaci ɗaya.na amince ummah ,Nasan duk abunda kika zabarmun bazai cutar Dani ba."a boye Hajiya bilki ta sauke ajiyar zuciya.washe gari ta kira dangin mahaifin aminatu da kuma yayanta ta sanar masa komai.Tun daga lokacin aminatu bata kara zuwa gidan hajja,ba itama hajja bata matsaba akan lallai sai aminatun tazo.haka ta saka Sadauki yaje su zanta da aminatu.shi kansa ya zama busy bawai zama yake ba haka yaci ace yaje din ya ganta.duk da har yanzu bai dora matsayin da ya aje Aminatu ba acikin zuciyarsa.kwana biyu da hajja tayi masa maganar.yaje ya samu Aminatu abunda ya lura dashi miskilace ta gaske kamar yadda yake miskilin in da Faiza ta banbanta daita kenan ,ita Faiza ko saboda surutunta yadda take tattalasa shiyasa watarana yake sauke duk wani miskilancinsa ya kula Faiza.Amman ya lura wannan Aminatu miskila ce baisan kuma ya zamansu zai kasance ba.shi duk wannan bai damesa ba auren kawai yakeso ayi.da sati ɗaya su baffa sukaje nemar masa auren Aminatu anan take aka yanka sadaki aka bayar aka sa auren da wata daya,sai bayan da Su baffa suka dawo sukayi maganar da hajja.hajjan ma ta dauka ko sati biyu za'a saka.baffa yace haka suka so
Su iyayen nata ma wata biyar suka saka saboda kayan dakin yarinyyar suna so su shirya da kyau baffa yace dai abarsa a wata ɗayan,babu komai duk gidane suyi hidimarsu yadda sukejin zasu iya kar su wahalar da kansu.da dare da Sadauki ya shiga wurin hajja tayi masa bayanin ranar
Da aka saka.ko a fuska bai nunawa hajjan yayi masa yawa ba addu'a kawai yayi akan Allah ya kaisu lokaci
da kwana biyu aka cire kananun abubuwan da basayiwa aminatu a lefen saboda tana da babban jiki
Fiye da faizar da siririce shiyasa aka siya wasu abubuwan aka zuba.sa'annan aka kai kayan lefen
Dangin ango da amarya aka shiga
Shirye-shirye biki ana cikin ma shiryen-shiryen Sadauki ya daga kasar germany.sai ana sauran kwana biyu daurin aure ya dawo daga shi har amaryar babu mai neman dan uwansa duk da Aunty Maimuna ta
Siya mata babbar waya har number Sadauki ta saka mata.shima a bangaren Sadauki Aunty Maimuna ta tura masa lambar tace ya kirata sai dai har yaje ya dawo bai samu ya kira Aminatun ba.da Aunty Maimuna suke shirya komai dan tamkar itace ango.
Walima kawai suka shirya anan gidan hajja tagani ta faɗa Dan ba kananun kuɗi aka kashewa walimar ba yan uwan amarya da ango anci an sha
Washe gari jumu'a aka daura Auren Abubakar Abubakar sadauki da Aminatu wakili.daurin auren da ya samu halartar manyyan -manyya yan kasuwa abokanin kasuwancin sadauki.ba ranar aka kai amarya ba da aka xubamata kayan daki dai dai da karfinsu a katon flat dinta dake (SADAUKI MANTION)yan uwan Aminatun sai santin gidan suke masu tayata murna na tayata masu mata haddasa da kushe auren sunayi.masu gulmar Sadauki yafi qarfinta auren kudi ne da kwadayi tayi suma suna gefe sunayi.Aunty Maimunatu na riqe da Aminatu da dawowarsu kenan daga gidan baffa daita da kanwar mahaifiyar Aminatun da yayar mahaifiyarta.suna fito daga gidan baffan wurin hajja akayo daita cikin wata lafiyayyar liyafa wacce kallo ɗaya zakayi mata kasan Naira ta zauna ba kaɗan ba.daga gidan hajja kai tsaye (Sadauki Mantion)aka nufa daita.nasiha sukayi mata kafin suyi mata sallama,daman can ita bawai ta cika kula kawaye bane sai aka barta da matar yayanta itama kara gyarata ta saka turaren wuta na (DEEJERH BERVERH)wanda nan take gidan ya dauki wani kalar kamshi mai sanyin dadi ,sai da ta kara daukar lokaci kafin tayi mata sallama.wasu irin hawaye Masu dumi ke sauka akan fuskarta.tsoro da fargaba suka mamaye zuciyarta.bata san kuma wani irin zama zatayi da sadaukin ba
Wani irin tsoronsa taji ya shigeta lokaci ɗaya,tana tuno yadda yake haɗe fuska tamkar bai taɓa Daria ba a duniya.tana nan zaune har aka kira sallar ishaai ta shiga kofar da tattabar toilet ne tsayawa tayi tana kallon toilet din irin girman da yake dashi
Tsorata da dukiyar Sadauki ta farayi
A irin fina finan India take ganin irin wannan banɗakin wai yau itace acikinsa kuma wai mallakintane.ganin dai kallo bazai barta tayi Alwallah ba yasa ta hakura da kallon ta dauro Alwallah tazo ta tada sallar.anan kan sallayar tayi zamanta sai lokacin takejin wata irin gajia da ciwon jiki na lullubeta
Har ta fara bacci sama-sama taji an turo kofar da sallama a bakinsa.jin tayi gabanta yayi wani irin faduwa
A daburce ta amsa daga bakin kofar ya tsaya kamshinsa na cika koina na dakin,yana sanye cikin farin yadin da yayi masa matuqar kyau ita kanta
Jin tayi zuciyarta na motsawa ganin irin kyan da yayi.ki dauki kayan da zaki bukata zamu karasa can bangarena."Ya faɗa cikin muryarsa marar amo.ita kam me zata dauka
Tashi tayi a haka tana kallonsa ganin batace komai ba yasa ya juya da ledojin da ya shigo dasu itama bin bayansa tayi duk wani taku da Sadauki xaiyi jinsa take har cikin zuciyarta.bata ga komai ba ashe sai da ya karasa daita babban part dinsa da ake bulla ta cikin part dinsa akwai kofar da ta raba tsakanin part dinta da nashi.sakin baki kawai tayi tana kallon irin dukiyar da aka zuba
Yana kallon yadda take qarewa komai na sashen nasa kallo.abu na farko dake Burgesa daita rashin hayaniyarta shiya fara jan hankalinsa akanta.ganin tana kokarin zama a parlor yasa yace su qarasa sama
Shi kansa ya gaji batayi musu ba tabi bayansa.bugun zuciyarta kusan tsayawa yaso yayi ganin wai wannan dakin duk na mutum dayane,tana kallo ya aje ledojin akan side table dake aje ya shiga balle botirin rigarsa wanka yakeso yayi ya gaji sosai
Ganin yana kokarin cire kaya agabanta yasa ta juya fuskarta da sauri bai damu da yanayinta ba ya cire rigar ya nufi toilet da wandon ajikinsa.sai da taji karar rufe kofar da yayi numfashin da take riqe dashi ta shiga ja tana saukewa a hankali.....
#NANA DISO
#ASMY B ALIYU
#HOT LOVE/ROMANTIC
*