Free chapter · Read without an account

BABI NA TAKWAS

by Fatima Eshak · BISHIYAR TSIYA....

*BISHIYAR TSIYA*


*DAGA ALKALAMIN YAN TAGWAYE*


*Umm Asghar*

*Sadiya Nasir Dan*


Arewa book

@ummasghar


Page 8


Da shigar Abdul-Hameed part ɗin shi shirin bacci yayi ya haye gado ya zuba wa fanka idanu, ta ina zai fara neman macen data dace dashi ya aura kamar yadda Hajiya ta bukata? Bayan zuciyarshi ta makance da soyayyar mace ƙeaya ɗaya jal da tayi nasarar sace zuciyarshi gashi tayi mishi nisan da ba zai iya mallakarta ba, ta ina zai samu yarinya mai nutsuwa da kamala irin nata, ga Addini! Haƙuri ga ganin girman manya? Runtse ido yayi take kyakkyawar fuskarta ta baiyana a idanunshi, a hankali ya buɗe idon gami da sauke ajiyar zuciya yana jin zuciyarshi babu daɗi. Shi kanshi yasan auren shine zaman lafiyar shi, musamman da ƴan-mata marasa kamun kai na Abuja suke kawo mishi hari, duba da irin yanayin halittar shi mabuƙaci ne na sosai, yana tsoron kar shaiɗan yayi tasiri akan shi, Auren shine mafi alkairi, to wacece zaka Aura? Yaji zuciyarshi ta jefo mishi tambayar, miƙewa yayi daga kwancen da yake ya ɗaura hannayenshi biyu kan kuncin shi, hirarsu da Hajiya ke dawo mishi cikin ƙwaƙwalwar shi, "Abdul! Yarinyar nan Saudat tana ƙaunar ka, ka duba yadda take sintiri gidan nan idan tasan kana gari, duk da rashin sake mata da baka yi hakan bai taɓa hanata zuwa ganinka ba, ina ji a jikina idan ka aure ta zaka samu nutsuwa, duba da irin son da take yi maka, ina so ka zauna kayi tunani sosai, kaga tsatson data fito ae, kasan dai Hajiya Rabi ba sai na tsaya sanar da kai wacece ita ba." 


Matuƙar shi zai nema wa kanshi matar aure to tabbas ba zai yi aure ba, don ba zai taɓa samo macen daza maye gurbin macen da tayi mishi illah a zuciya ba, ba laifi Saudat tana da kyau, kuma akwai nutsuwa dai-dai gwargwado, sai dai yanayin life style dinta kwata-kwata bai yi mishi ba, da ganin yanayin ɗabi'unta za taso abun duniya, "Majority mata haka suke Abdul, kai dai kawai nemi yardar Allah, domin zamanka haka babu aure Matsala ce, kayi addu'a hakan ya zamo alkairi tunda Hajiya na so." Zuciyarshi ta bashi amsar gaskiya. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi ya koma ya kwanta zuciyarshi na ƙara samun nutsuwa da auren Saudat, a haka har bacci ya ɗauke shi.

   Koda ya dawo daga sallar asuba baccin ya sake komawa, sai ƙarfe goma da rabi ya farka, sakamakon ringing da wayarshi take yi, ganin number Oga yasa ya ɗauka da sauri, kusan 20 minutes ya ɗauka kafin ya ajiye wayar ya shiga toilet ya watsa ruwa, ƙananan kaya ya saka ya ɗauki wayarshi ya nufi cikin gida wajen Hajiya.

      Hajiya na hakimce a kujera tana kallon Sunna TV Abdulhamid yayi sallama ya shigo, idonshi akan side table dake gefen Hajiya, ganin jerin warmers yasa ya saki murmushi ya ƙarasa cikin palon, waje ya nema ya zauna kusa da kafarta. "Hajiya ta an tashi lafiya?"

"Lafiya kalau Abdul ya gajiya? Tunda naga baka shigo ba nace to bacci kake yi, jira nake sha biyu tayi nasa Hafsa ta kira mini kai a waya ka fito ka karya."

"Hajiya kin san a Abuja bana samun hutu, ko yaushe cikin aiki shi yasa idan nazo gajiyar take yi mini yawa, Hajiya tunda na shigo palon nan ƙamshi ya cika mini hanci." Yayi maganar tare da kai hanu yana ƙoƙarin buɗe jerin abincin dake ajiye a gefen Hajiyar. 


Murmushi Hajiya tayi, "aikin Saudat ce Abdul, ina zaune a inda ka ganni kawai na ganta ɗauke da kwando, ashe Hafsa ta shaida mata ka dawo, da yake jiya na aiketa wurin Hajiya Rabi." 


"Allah sarki Saudat, ita dai bata gajiya da ɗawainiya."

"Nima hakan nace, Allah ya ɗora mata sonka gashi kai sam hankalinka baya kanta, har cikin zuciyata Saudat tayi mini, ina ƙaunar yarinyar ta zamo surukata, Allah yayi muku zaɓin alkhairi gaba ɗaya." Ta ƙarasa maganar fuskarta da alamun damuwa. Gyara zama Abdul-Hameed yayi ya fuskacenta sosai. "Hajiya ki kwantar da hankalinki In Sha Allah Saudat zata zamo matata, na amince da zaɓin ki Hajiya nasan ba zaki haɗani da abinda zai zamo mini damuwa ba, a shirye nake zan aureta Hajiya matuƙar hakan zai sakaki farin ciki."

"Da gaske Abdul?" Hajiya tayi maganar cike da mamakin abinda ya fito daga bakinshi wanda ba tayi zato ba ko tsammani. "Ƙwarai Hajiya, na shirya aurenta kafin na koma Abuja." Farin ciki sosai ya baiyana akan fuskar Hajiya, "Gaskiya naji daɗin abinda ya fito daga bakinka Abdul, Allah yayi maka albarka, In Sha Allah zaka yi alfahari da uren Saudat, yanzu ba sai anjima ba zaka kira mini Hajiya Rabi na sanar da ita wannan abun farin ciki. Hankali na zai kwanta idan kayi aure Abdul kai ma ka zama cikakken mutum magidanci." 


"Kinga bari na kwashi girkin amarya." Yayi maganar da zolaya ya ɗauki plate ya ɗebi abinci ya soma ci a hankali. "Sai ka samu lokaci kaje ku fahimci juna, bana son auren ya ɗauki lokaci, tunda kaga suma suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, sai ayi kawai a wuce wurin."

"Haka ne Hajiya, In Sha Allah yau zuwa gobe zan je." 

"Shikenan Allah ya kaimu yayi maka albarka". 

"Ameen Hajiya ta," yayi maganar yana jin wata nutsuwa tana saukar mishi.


****

Batulu gaba ɗaya lissafinta da tunaninta sun raja'a ta yadda zata dawo da wayarta kafin Suleiman ya dawo kamar yadda ya ambata, zugum tayi na rashin mafita, ga tsananin zazzaɓin dake dafa naman jikinta, tsawon lokaci ta ɗauka tana tunanin yadda al'amarin zai zo mata da sauƙi, "Yauwa," ta ambata da sauri ta miƙe ta shiga ɗaki har tana ƙoƙarin faɗuwa saboda rashin kuzari, drawer ɗin kayanta ta nufa tasa hannu can ƙasa ta janyo wata karamar container ta buɗe ta fito da ɗan kunnen gwal da Suleiman ya saya mata lokacin haihuwar Fahad.

    "Batul rufe idonki ki miƙo mini hannunki my love." Yayi maganar yana ɗaukar Fahad dake cinyarta, rufe idonta ke da wuya taji ya kama hannunta ya damƙa mata abu, "bude farin ciki na," ya ambata yana shafa hannunta. Ganin ɗankunne da abun wuya na gold yasa farin ciki yalwatuwa a fuskarta, "Babe wannan fa?"

"Tukuicin haifo mini kyakyyawan yaro mai kama dani da kika yi ne." "Kai babe duk wannan ɗawainiyar da kake yi dani bai isaba? Allah ya saka maka da alkhairi, ya tabbata bani da bakin gode maka irin kyautatawa da kulawa da kake nuna mini, Ubangiji shi zai baka lada." Ta ƙarasa maganar hawaye na zubo mata, da sauri Sulaiman yasa harshe ya lashe hawayen duka, "Ba nason ganin hawayenki kona farin ciki ne Batul, ki sani ni kaina na kine bare abinda na mallaka, don haka kada ki sake yi mini asarar hawayen nan naki." Ƙoƙarin yin magana take yayi saurin haɗe bakinshi da nata, hakan yasa tayi shiru.

 Wani irin kuka ne yazo mata mai ƙarfi ta durƙushe a wajen, "Me yasa ka canza? Me yasa komai yake so ya zamo mini tarihi? ko a mafarki idan aka ce Sulaiman zai zamo haka ƙaryatawa zan yi, ya Allah kana gani kuma kana ji." Tayi maganar cikin muryar kuka, ta jima sosai a haka kafin ta janyo ƙaramar wayarta ta kira Mus'ab, yana ɗauka ta aro nutsuwa suka gaisa, "Mus'ab kana ina?"

"Gida Aunty Batulu, lafiya? Naji muryarki wani iri ko ba lafiya ne?"

"Babu komai, don Allah kazo yanzu zan aikeka kasuwa ne."

"Shi kenan Aunty gani nan zuwa yanzu In sha Allah." Ya ambata kafin ya katse kiran. A daddafe ta miƙe ta shiga toilet ta wanke idonta ta dawo palo ta kwanta tana jin kanta na tsananin sarawa, A haka Mus'ab ya shigo ya sameta, "Suhanallah, Aunty ba lafiya ne?"

"Zazzabi ke damuna Mus'ab."

"Allah ya baki lafiya amma kin sha magani?" 

"Aa da yake sai bayan fitar Abban Fahad ciwon ya sauka mun, taimaka ka sayo mun ko paracetamol a bakin hanya sai kazo kaji aiken." 

"To," yace ya fita da sauri, kafin ya dawo ta samu ta ɗauko receipt da gidan sarƙar ta ajiye a gefenta, yana shigowa kai tsaye kitchen ya nufa ya ɗauko ruwa a cup ya ɓalle maganin ya miƙa mata, tana sha ta ɗan kishingiɗar da kanta na ƴan mintuna kafin ta ɗago ta miƙa mishi gidan sarƙar, "Kaje kasuwa ka sayar mun, sai ka tsaya ka saya mini sabuwar waya irin wacce na baka ka sayar mini lokacin da Baba yake Asibiti." "Aunty Batulu ban gane ba?"

"Mus'ab kaje kayi mini abinda nace maka don Allah kaga bani da lafiya bana son yawan magana."

"Shi kenan bari naje." Ya miƙe ya fice zuciyarshi na saƙa mishi abubuwa da dama. 


******

Sulaiman har ya isa office zuciyarshi tafasa take yi, tunanin irin rashin mutuncin da zai yi wa Batulu yake idan ya dawo gida bai samu waya ba, domin ya fahimci rainin nata yayi yawa, ɗan sake mata da yake yi ne yasa take ganin ta ha'ince shi. Iska mai zafi ya furza, zuciyarshi na hasaso mishi irin ɗaure wa Batulu da zai yi na irin raina mishi da tayi.


*******

Batulu ganin Mus'ab da waya yasa taji kaso sittin na zazzaɓin da take ji ya kau, sai da tasa Mus'ab ya taimaka mata suka gyara gidan kafin ta tsakuri wani abu cikin sauran kuɗin ta bashi ya kai wa Inna ko wani abu zai taso, Mus'ab na tafiya kitchen ta shiga ganin Fahad ya kusa dawowa, haka a daddafe ta samu ta ɗora jollof rice.


*******

Abdul-Hameed kamar yadda yayi wa Hajiya alƙawari idan ya samu time zai iya zuwa wurin Saudat bayan la'asar su fahimci juna hakan aka yi, yana idar da sallar key yayi wa motarshi ya nufi Unguwar, bashi da lambar wayarta, hakan yasa ya tura yaro cikin gidan kiranta. 


Saudat tunda ta samu labarin amincewa da aurenta da Abdul-Hameed yayi ta nemi nutsuwarta ta rasa, duk gidansu babu wanda bai fahimci tana cikin farin ciki ba, ƙarfe uku ta sake wanka ta zauna ta tsantsara kwalliya sai kace wacce zata biki, zuwa ƙarfe huɗu da Rabi ta gama shirinta cikin material mara nauyi red color da yasha ado da kananan duwatsu black. Hajiya Rabi tana ganinta ta kama baki, "Kar dai kice mini gidan su Abdul-Hameed zaki?" Murmushi tayi bata amsa ba, "gaskiya Saudat kada kije, haba zai ga zumuɗin ki da yawa, ki haƙura daga nan zuwa sati guda na tabbata zai zo gareki tunda maganar aure ce a tsakaninku yanzu." Ɗan turo baki Saudat tayi, "Mummy har sati ban sakashi a idona ba? Kiyi hakuri daga yau bazan sake zuwa ba, ki duba jimawar da nayi ina make-up duk saboda shi fa kuma ace ba zai ga kwalliya ta ba. Sallamar yaro shi ya hana Hajiya Rabi amsa maganar Saudat. "A waje akace ana kiran Saudat, yace ince inji Abdul-Hameed."


Cike da zumuɗi tace "don Allah da gaske?"

"Kai jeka kace tana zuwa," Hajiya tayi maganar tana hararar Saudat dake ƙoƙarin bin yaron. Hajiya ta daka mata tsawa, "ke wai wacce irin ballagazar yarinya ce wawuya? Kin kama hanya zaki bi shi ko ruwa ba zaki ɗauka ba? Sannan ai Abdul-Hameed ɗan gida ne, sai ki tsaya kisa turaren wuta palon Abbanku kiyi shirin na tarbanshi sannan ki fita, amma kin sa ƙafa zaki bi yaro kamar wacce ke jiraye?" Saudat gaba ɗaya ta ruɗe, so take taje ta tabbatar da gasken shi ɗin ne, kai tsaye ɗakin Hajiya nufa ta zuba turaren kamshi cikin kasko ta nufi ɓangaren Abbansu, cikin sauri ta gyara komai ta saita nutsuwarta ta fita. "Da gaske shine," ta ambata a hankali ganin motarshi, sake saita nutsuwarta tayi ta soma takawa a hankali zuwa jikin motar. Abdul-Hameed kuwa tun fitowarta yake ƙare mata kallo ta jikin glass, Tabbas Saudat ta haɗu tana da surar da dole taja hankalin mutum, sai dai matsalar ɗaya, baya tunanin zuciyarshi zata iya amsar soyayyarta yadda ya kamata, soyayar mace daya ce ta gama tasiri a zuciyarshi tasa baya ganin farin kowacce mace face ita.....


*ƳAN TAGWAYE BIYAR*


*GONAR SHARRI*

Billy S Fari & Hajja ce


*IDANIYAR RUWA*

(Mai wuyar toshewa)

Ayusher Muhd & Jidda Aliyu 


*WATA ALAƘA*

Zee Bawa & Stylish bch


*BISHIYAR TSIYA*

(Wanda bai jiba bai gani ba ke girbar ki)

Umm Ashgar & Sadiya Dan.


*TSARIN ALLAH*

(Ba mai iya canzawa)

Asmy b Aliyu & Nana Diso


*ZAI IYA BIYAN*

GUDA 1 akan 500

GUDA 2 akan 800

GUDA 3 akan 1200

GUDA 4 akan 1600

GUDA 5 akan 2000


*BANK ACCOUNT*

8098456130

Opay digital services

Shaidar biya ***


*KATIN MTN*

***

Shaidar biya ta lambar.


_*ƳAN TAGWAYE BIYAR*_


#SADIYANASIRDAN

#UMMASGHAR

#ƳANTAGWAYEBIYAR

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.