Free chapter · Read without an account

Chapter 3

by Maryam Abdul'aziz · FATIMA ZAHRA



FATIMA ZAHRA


©Mai kosai


     FCWA



Wattpad@maryamad586

Arewabooks@maikosai53




3.


Da wani irin kallo Fahima ke bin ta da shi, tabbas Zahra ta yi nisan da ba za ta ji kira ba, ita kuma ko kaɗan bata so kawancensu ya samu matsala, sai dai duk da haka ba ta jin zata iya bari kawarta ta tahau layin da ba daidai ba.


  "Shi ke nan Zahra, ki yi addu'a da neman zabin Allah, amma ki sani karki kuskura su Abba su san wannan batun domin na tabbata ransa ba za ya yi daɗi ba."


  "Karki damu kawata ba za su sani ba har sai lokaci ya yi."


A haka har aka tashi daga makaranta suna ɗan tattaunawa. Bayan an tashi kowacce ta nufi gida.


Daf da zata shiga gida ta ji sautin muryarsa,


  "Barka da zuwa gimbiyata."


Waro idanuwanta ta yi, 'me ya sa zai zo kofar gidansu bai san hakan hatsarine a gareta ba.' 


Da sauri ta tari numfashinsa da ya buɗe baki yana son yin magana.


  "Ka yi hakuri don Allah ka bar nan wajen bana so Abbana ya ganka."


  "Ba zan iya cirar kafa na bar wajen nan ba Zahra muddin ban ji daga gareki ba."


 "Ka bani zuwa gobe za ka ji amsata." tana gama faɗin haka ta shige gida da sauri har tana sauke ajjiyar numfashi.


***

Shakuwa ce sosai ta shiga tsakaninsu, soyayya mai karfi ta kullu ya junansu. Sukan yi waya da shi a wayar Fahima saboda ita tana da waya, sukan kebe da juna ita da shi a gidansu Fahima, daga baya kuma suka koma haɗuwa kan layin gidansu saboda ita ma bata so iyayenta su fahimci komai. Zahra ta yi nisa sosai cikin soyayyarsa duk wasu kalamai da suke zuwar mata na rashin kirkin abin da ta ɗakko bata gani don idanuwanta sun toshe ba ta ji balle gani sun tafi akan soyayyar wani daban. A haka karatunta ya soma samun tangarda saboda ta saka soyayya a gabanta. Har takai ga ya siya mata 'yar karamar waya ta kuma killaceta killacewa ta musamman babu wanda ya sani a gidansu.


A haka rayuwar ke gangarawa har takai ga sun zana jarrabawa, inda ta zana jarrabawar science and technical ita da Fahima, cikin sa'a exam ta fito kuma sun samu kyakkyawan sakamako inda suka ci boarding school Da fari Abba bai son tafiyarta amma ganin mahaifin Fahima ya fahimtar da shi muhimmancin karatun ya sa ya ji ya aminta da tafiyar tata boarding ɗin tare da yi mata fatan alkhairi. Nasiha kuwa sun sha ta wajen iyayen nasu.


Sai dai kafin tafiyar tasu, sun yi alkawari da Abdul zasu haɗu inda zata ba shi wata kyauta, kyautar littafi wanda ta cika shi da kyawawan kalamai wanda ta sake buɗa masa yadda take sonsa.


Alhamis.


  Da yammacin wannan ranar ne suka yi zasu haɗu a layinsu Zuhra, sai dai sauri da ɗokin su ga juna ya sa ta manta wannan littafin, wanda shi ne masomi da silar samun saɓani da iyayenta. Littafin da ya samar mata da kunci da rashin kwanciyar hankali.


Bayan sun haɗu da Abdul ta ba shi hakuri kan ta manto littafin amma zata san yadda zata yi littafin yazo hannunsa, bayan sun rabu ta juyo gida da tunanin inda ta ajjiye littafi, haɗi da fargabar Allah ya sa ba wanda zai ga littafin. Sai dai kash! Hakarta ba ta cimma ruwa ba, domin ko da ta yi wa gidansu tsinke gaba ɗaya ta rasa annuri da walawa daga fuskokin jama'ar gidan, musamman ma umma da ta ɗauke mata kai. Tun a sannan ta sha jinin jikinta ta tabbatarwa da kanta cewa lallai sun ga littafin.


Babu wanda ya tanka mata har sai da aka zo cin abincin dare sannan Abba ya zo mata da maganar.


 "Zahra!"


Ba ta iya dago da kanta ba da ke sunkuye, balle ta iya kallon fuskar abban nata. Shi ma ganin hakan bai sa ya sake kiran sunan nata ba sai ya ɗora daga inda ya ke son ɗorawa.


  "Na yarda da tarbiyar da muka baki, ina da yakini ba za ki watsa mana kasa a ido ba don Allah ki ajjiye komai ki fuskanci karatunki, ban da biyewa kawayen banza, ban da biyewa samarin zamanin nan waɗanda za su kai ka su baro ka, su barka da takaici da da na sani, tashi ki je Allah ya yi miki albarka."


Jiki a salube ta mike ta shige daki, zuciyarta na ta yi mata sake-sake, tare da tabbatar mata da cewa Abdul sam baya daga cikin samarin da Abbanta ke nufi, nan da nan ta sake jin wani soyayyarsa ta sake zame mata sabuwa dal.


Washe gari ta kama juma'a, burinta gari ya sake nutsawa ta san yadda zata yi takai masa littafin nan, duk da bata da tabbacin a inda yake shin yana wajen ummanta ko abbanta? A ina zata fara nemansa?


Rashin sanin amsar ya sa ta nufi dakin abbanta kai tsaye, kan teburun da ke ajjiye litattafansa ta soma farawa da shi wajen bincikawa, cikin ikon Allah kuwa ta yi gamdakatar da littafin, tana fara'a ta zaro shi ta juyo da nufin fita, turus ta yi ganin umma tsaye kanta fuskarta a haɗe tamkar kakkauran haɗin ruwan shayi.


  "Me za ki yi da littafin?" ta ji tambayar cikin kunnuwanta.


Inda-inda ta fara yi, ganin umman ta nufota ya sa ta fara ja da baya, tsoro da fargaba ya shiga zagaye zuciyarta, yana haddasa mata bugun zuciya da karfi domin ta tabbata yau babu mai kwatarta sai Allah, domin umma mace ce mai zafin rai, ba kamar abba da yake da sanyin zuciya ba da saukin kai ba.


Don't forget to VOTE, COMMENT and SHARE.


Mai kosai

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.