Free chapter · Read without an account

14

by Nana Disoo · TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)




DAGA ALKALUMMAN YAN TAGWAYE BIYAR



Arewabook@Nana diso 10


NA

NANA DISO

&

ASMY B ALIYU



14.


Duk da ransa a ɓace Yake da duka matan nasa guda biyu a kowane gefe kowace da matsalarta.idan kuma ya tuna zai yiwa yaransa aure a wannan qaron sai yaji zuciyarsa ta sauka farin cikin haka yana danne ɓacin ran da yake jin kansa cikinsa.


Kasa bacci tayi a tsayin daren bata san Meyasa takejin tsoro ba.idan ta tuna da kanta ta faɗawa Abhuun su aure takeso,sai taji wata irin kunya ta lallubeta .sai dai kuma Acan kasan ranta damuwa ce fal aranta da wata irin fargaba.Batasan meyasa ta faɗawa Abhuu tana son aure ba.Yaushe ma ta haɗu da saleem,da zatace akwai wata soyayya a tsakaninsu."abu ɗaya tasani saleem din,ya damu daita yana sonta yana bata kulawa fiyeda yadda xata iya kwatantawa yana bata wani irin respect da mata dayawa basu samu ya basu ba.wannan kawai ya isheta.bata taɓa jin son saleem Aranta ba.tasan bayan Aurensu komai zai canja, shaye-shayen da yakeyi tasan yana cikin qaddararsa zai daina ko yanzu yana ta qoqarin ya daina duk saboda ita.agogon bangon dakin qarfe biyu da rabi na dare ,bazai yuyu ta kira Saleem a wannan lokacin ba duk da tana da tabbacin xai dauka.kara ta bari sai xuwa gobe suyi magana a natse.ganin har kusan qarfe 3 na dare ta kasa bacci yasa ta miqe tsaye ta nufi toilet fitsari tayi.gamida dauro Alwallah,a haka ta riqa raya daren tayi addu'a sosai idan saleem alkhairi ne acikin rayuwarta Allah ya tabbatar da Aurensu.ba ita ta samu tayi bacci ba sai bayan gama sallar Asuba.wani bacci mai ddi ya dauketa akan abunda tayi sallah.

Har Sadauki ya fita office Batool na bacci ba ita ta tashi ba sai qarfe goma sha daya,bude idonta tayi a hankali tana karanta addu'ar bacci.kanta taji yayi mata nauyi sosai alamar son yake yayi ciwo,tana gama karanta addu'ar tana nan kwance na kusan minti goma.sa'annan ta miqe tsaye ta cire rigar jikinta ta bacci kai tsaye toilet ta nufa.ta sakarwa kanta ruwa,

Koda ta fito daga wanka lotions din da take using dasu suta shafa gamida saka turarrukanta masu qamshi ddi

daman ita ba maabuciyar yin kwalliyya bace a fuska daman Aysha ce mai son make up itada Farrah har koya sukayi saboda su riqa yiwa kansu koda light make up ne da anyi maganar rashin son make up din Batool sai suce ita tana da kyau ne sosai shiyasa dan har hasken fata ta ɗan fisu.


Rigar shan iska ta saka marar nauyi ajikinta.xama tayi a bakin bed dinta bata iya jin zata iya fita yanxu ga yunwa ga ciwon kai.daga Wayarta tayi ta kira mami.cike da kulawa Mami ta daga wayar tana tambayarta ya ta tashi?"itama cikin tata kulawa da irin kaunar da yaro keyiwa uwa take faɗin."Alhmdullahi ta saka a kawo mata break fast a dakinta ,kanta na mata ciwo.nan take mamin ta rude ta shiga jera mata tambayoyi jia anya ta samu bacci Meya hanata bacci ko sai an kira family doctor dinsu ya dubata.?"ko Mp ɗinkine zaizo."Yadda Batool taji Mamin nasu ta daga hankalinta lokaci ɗaya yasa ta saukar da murya tana faɗin."ciwon kaine kurum Mami ,idan nayi break fast Nasan zai sauka.tana jin yadda Mami ke sauke ajiyar zuciya tana faɗin."yanzu za'a kawo mata break fast tayi tasha magani idan kan bai sauka ba tayi mata waya.



da haka ta sauke wayar mintuna qalilan akayi knocking bakin kofar dakin su sai da ta bada umurni aka turo kofar dakin nata.nuni tayiwa mai aikin nasu ta aje kan sida table dake gefen dakin.cikin bin umurni mai aikin tayi yadda aka umurceta duka hankalin Batool na kan wayarta.har ta juya ta nufi kofar fita Batool ta tsayar daita kafin ta ɗora da faɗin."nan da rabin awa mai mata gyaran daki tazo cike da bin umurni mai aikin ta daga kai tana faɗin."in sha Allah Hajiya.


Bayan ta gama cin abinci tasha magani tana nan kwance akan soofa tana chart mai mata gyaran daki ta shigo da sallama dauke da Parker da broom a hannunta.cikin girmamawa ta gaisheda Batool."ta amsa cike da yanga da kasaita.ki fara wanke toilet,da haka ta cigaba da danna Wayarta mai aikin bata dauki awa ɗaya ba ta gama gyaran dakin,saboda ba wani datti bane a tare dashi saboda Batool akwai tsafta ayi mata sharar safe ayi mata na yamma haka ake mata kullum.


Ta kira Abhuunta sukayi waya ya tambayeta yau babu lecture ne?"ta faɗa masa kanta na ɗan ciwo sai dai zuwa gobe."addu'a yayi mata haka yace ta samu ta samu bacci idan ta tashi zai sauka.ya qara tuna mata akan ta kira Saleem suyi magana akan maganar aurensu,su daidaita kafin iyaye su shiga maganar ya yadda ya amince kaddarar saleem dince a haka.

Duk da Batool Babu abunda ta boye masa na halayyar saleem din,kuma ta faɗa masa yana fatar ya bari saboda ita.shiyasa hankalin Sadaukin ya ɗan kwanta.


Sai bayan azzahar da ta tashi ta samu tayi wanka ta qara yin wani wanka

Sai lokacin ta samu sukayi magana da saleem tasan kuma aranar zai bar qasar.sai dai bata san lokacin da zai tafi ba."tana jin yadda saleem ke ihu ta cikin wayar tana jin yadda Muryarsa ta canja tana jin wani irin bayyanannen farin ciki acikin muryarsa.

Haka ya tabbatar mata maganar fitarsa babu,zai shigo bayan la'asar su tattauna sosai.daga nan ya mata sallama ya faɗa mata zai kira mum dinsa ya faɗa mata.


Tana gama wayar taji an turo kofar dakin nata.daga ido tayi da Masifa dan ta tsani a shigo mata daki kai tsaye batareda izininta ba.Farrah ce da kayan makaranta ajikinta da alamar yanxu ta dawo makaranta kallon da Batool ke jefawa ta saitinsa yasa tasan ma'anarsa ware mata ido tayi ta ɗan bar jikin kofar tana nuna mata Mami,wacce ke sanye cikin kayan alfarma bayan Mamin kuma mai aiki ce dauke da madaidai cin tray a hannunta ,tana aje tray akan side table tabar dakin.


Mami ta zauna gefen Batool din

Ta kai hannunta akan fuskarta tana taɓa ko'ina cikin fuskar damuwa take faɗin."Yaya ciwon kan ya sauka?"ɗagawa mamin kai tayi gamida kwanciyya akan kafadarta cikin zallar shagwaba.kakaf cikin ya'yan mamin Batool duk tafi kannenta sangarta da shawagaba,

Idan tana ciwo hankalin kowa tashi yake daga uwar har uban da kuma yan uwan nata.idan ka ɗebe matar ubansu Maryam mai son taga Batool din kullum tana ciwo har addu'a take karta tashi saboda yadda ta tsaneta.


"Yah Batool yaya jikin?"Yanxu mami ke sanar mun bakya jin dadi ko school baki samu zuwa ba."Farrah ta faɗa tana kallon yayarta."naji sauqi little sis.na xuba maki abinci?"Farrah ta faɗa tana kallon Batool daga kai tayi kafin ta ɗora da faɗin "kaɗan zaki zuba Farrah.!"haka farrah ta xuba mata farar shinkafa da miya da taji naman kaji a sama,da kuma haɗin,coslow a gefe....


Bara naje na watsa ruwa na dawo. Farrah ta faɗa tana barin room din.mami,ta riqa baiwa Batool a baki.babu laifi ta ɗan ci Mami ta xuba mata xobo acikin cup glass.batool tana kaisa bakinta ta kalli Mamin da sauri wani wide smile ta sakarwa Mami ,tana faɗin "Mami ke kika haɗa wannan "murmushi kawai mamin tayi.


Bayan ta kammala cin abincin ta sanarwa da mamin yadda sukayi da Abhuu ajiya. dan ajiyar zuciya Mami ta sauke yadda Abhuu ya hau jia abunda bai tabayi ba marin Batool,bata dauka zai sauko har haka ba."to ke yanxu akwai tsayayyen ne?"naga duka samarin naki sai a hankali "ko nace ruwan idonki ya hanaki ki zaba.



Dan tura baki Batool tayi tana faɗin "Mami ba haka bane kawai dai hankalina bai kwanta dasu bane,

Nifa na fadawa Abhuu na samu mijin aure.!"da mamaki Mami,ke kallonta dan ba abunda Batool din ke boye mata,batasan dai tana da wani saurayin ba.sai idan a kwanakkin nan tayisa.


"Mami saleem fane dan gidan Abdullahi shantima vice president!"lokaci ɗaya yanayin mamin ya canja.dan shaye-shaye zaki aura Batool da hankalin ki da tunaninki da gatanki!"to Ni ban yadda ba qarama ki hakura da wannan yaron tun wuri.lokaci ɗaya jikin Batool yayi sanyi ,ta kamo hannayen Mami tana kallonta cikin fuskar tausayi take faɗin."Mami Saleem ya daina shan komai saboda ni wallahi.!"kuma shi kaɗai ne na yadda da soyayyar da yake yimun.lokaci ɗaya Mamin ta fisge hannunta ta miqe tsaye tana faɗin."da ki auri saleem qara Hamzan da kike gudu ɗan Aminiyata ga natsuwa ga hankali ban san meye aibun Hamza ba.da sauri batool ta shiga girgiza kai tana faɗin "karki yimun haka mami,ki fahimceni nifa ba abunda zanyi da Hamza dan ko kaɗan ba kalar aure na bane."!"wani kallo Mamin ta watsa mata tana juya ta nufi kofa duk ranta a ɓace,wane irin rashin hankali ne SADAUKI keyi haka zai aurawa Yarinyyarta ɗan shaye-shayen da baya mada cikakken lafiya bazata yadda a bátawa Yarinyyarta rayuwa ba tana ji tana gani in sha Allahu bazata yadda ayi wannan auren ba.




#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#hot love/Romance









Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.