Free chapter · Read without an account

Chapter 4



Page 4


   A hankali take tafiya part ɗin nashi wasu matsatsun kaya ne jikinta sai ka ce ba Musulma ba haka take ƙarin gashi an sha kitson zare ta na isa kai tsaye ta tura kofar palorn ɗakin bata gan shi ba tai Zaman fitowar shi kusan minti 7 daga shi sai tawul wani na saman kanshi ya na goge gashin kanshi ta zo ta bayan shi ta ɗan rumgume shi da sauri ya juyo tare da balla mata harara ta ce'' am sorry yaya Sameer mistake ne wallahi kanta a ƙasa"


     Is okay please get!!


 Yar ƙwalla ce ta zubo mata ta ce'' ai nace kai hakuri banyi da wata manufa ba ni''..

   Sashen Hajiya babba ta tafi tana kuka mai dan sauti tana shiga ta tare ta ta ce "aleesha mai ya faru kike wannan kukan"


Dan sauti ta kara ta ce" don naje part ɗin shi ne ya koroni fa gaskiya hajiya gani nake Sameer bazai aure ni ba"!


.


   Zainab

Alhamdulilah yanzu kwanciyar hankali ko sai dai ta ba wani labarin ta taɓa shan wahala baya amma yanzu Gata take samu kamar me kamar kullum yau ma akwai dandali tun la'asar take shirin zuwa tsohuwa gyaɗa kawai take mata shima sai ranar dandali karfe 7 na dare aka tafi tallar gyada tsohuwa ta tsinto mata kaya a gwanjo masu ɗan kyau wajen kala 5 dai don ta riƙa kwalliya tana isa ko aka dinga siyan gyadar saboda wani irin farin jini Allah ya sako mata a garin gashi samari suna ta mata zarya ta ki basu dama saboda ita hamza take so shi kuma zata aura.....

   Dare sai ƙara yi take gashi yau bai zo ba hankalin ta kuma ya ƙi kwanciya saboda rashin zuwan shi bai iso ba sai ƙarfe 8 30 dai-dai sannan ya iso farin ciki fal ran ta na ganin masoyin ta!!


   Ta turo baki ta ce'' hmm Yaya har na cire ran ganin ka fa saboda jin shirun da na yi"..


  Dan gemun shi ya shafa ya ce''haba kanwaty na kinsan tunda nace maki zan zo to zanzo ina can ina magana da mai gari ya matsa dole sai natafi birni karatu gaskiya ni kuma mafi son idan mukai auren mu sannan sai na tafi"


          Ajiyar zuciya ta sauke ta ce'' a'a yaya ka tafi kabi umarnin iyaye idan ka dawo sai mu auren mu in sha Allah ina nan zan jira ka kuma zan riƙe maka alkawarin mu kaima ina so don Allah ka riƙe min nawa alkawarin kada kaje birni kaga mata ka ƙyale ni ta idasa maganar na mai sharar hawaye"


   Allah sarki shi ma kanshi "hamza ɗin ƙwallar ya ke amma bai bari ta gani ba haka sukai ta fira kamar ba gobe ya fiddo dubu uku ya ce wannan ki riƙa siyan wani abu in sha Allah idan naje can birnin zan riƙa aiki na rika turo maki kuɗi ni yanzu sauran kwana biyu na tafi kada ki damu zainabu na in sha Allah ke mallaki na ce"


   Sai ƙarfe 10pm suka rabu da juna cikin kewa da rashin san rabuwar suka tafi ko da taje gida "tsohuwa ta dunga faɗa yau taje tayi tare karfe 9:30 take dawowa gashi yau har wajen goma ta wuce ta shigo gida ita ta marasa abinda zata ce mata sai dai ta aje farantin ta mika mata kudin gyadar tare da kuɗin da hamza ya bata"


              Ai ko tsohuwa ta wuntsulo daga gadon da take tace innalilahi wa'inna ilahirir raji'un ni na shiga uku yanzu "Zainab ina kika samu wannan maƙudan kuɗi?"


   Ita ma kanta tasan haka zata faru ta ce'' a'a wannan kuɗin Hamza ne ya ban duk ta faɗa mata yadda sukai da shi sannan hankalin ta ya kwanta"

          Abincinta ta ɗauka ta fara ci sai dai duka koma biyu taji ta ƙoshi haka ta aje ta dauro alwala ta kwanta..


   

   Hamza

Tun akan waya zuciyar shi ta tsinke gani yake kamar zai sara tane idan ya tafi shi dai a so samun shi ace sun yi aure sannan ya bar garin sai dai mai gari ya takura mai dole zai tafi ba don san ranshi ba haka ya isa gida yana zuwa ya haɗa kayan shi duk ya kammala su domin tun da yaga babu "Zainab kusa dashi to gwanda ya bar garin" washe gari tun da safe ya fito ya ce ma mai gari shi ya ce ya shirya daman gobe ne zai tafi to gwanda ya tafi tun yau ya yi hidimar rijistar gobe ya ida sa..... kuɗi ne ya bashi masu yawa sai birnin kano!!




  haba hajiya ya kamata ace "Sameer yana min haka ne shi yasa na ce maki gida zan koma Allah bazan iya ganin yana min haka ba abin ba daɗi Kinga fa a gidan mu ina da masoyana over cewar aleesha,"


      tsaki hajiya tai ta ce'' wai aleesha mai kike ci na baka na zuba ne kinsan shirin da nake maki ne ko ko kinsan mai zan maki ne Kinga na samo wani boka walllahi Allah an ce aikin shi na ci amma kuma sai munje ya yi amfani da ke"



    Haka suka dunga wannan firar har ta samu aleesha ta sakko...

   

 

  Zaune yake a falon "Ammi kan shi ƙasa ya ce ammi garin nan yamin zafi gaskiya so nake na barshi don Allah ki amince min ba don ni ba"

    Hmmm ita tarasa mai zata ce mai ma tun da ya fara magana take jin shi amma tarasa mai ke damun ta ita ma shin ina zai je kenan?? Wani tunani tai gwanda ta tura shi ƙauyen su da ya tafi inda bata sani ba





Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.