Free chapter · Read without an account

15

by Nana Disoo · TSARIN ALLAH (BA MAI IYA CANZAWA)

*TSARIN ALLAH*

(_Ba mai iya canzawa_)



DAGA ALKALUMMAN YAN TAGWAYE BIYAR


Arewabook@Nana diso 10

NA

ASMY B ALIYU

&

NANA DISO


15


A hanƙali tadago manyan idanuwanta ta zubasu a kofar da mami tafita wani kaļar ajiyar zuciya ta saki atake kuma taji hawaye ya cika idonta dan Aduniya bataso taga iyayenta ciƙin damuwa hakan zai sanya duk wani kuzari datake dashi yabarta, hannunta ta dauka tana share hawayen fuskarta cike da Addu'a Allah kataimaka min gurin mamii ta fahimceni. Tabbas batacewa ta kamu da son saleem amma kuma tana mutukar son tayi aure a wannan gabar.


Zaune yake a makeken office dinsa wanda yacika da kayan alatu haɗe da wata lafiyayyar farar computer dake gabansa. Idansa ya zuba akan wanda yake gaban kujerar sa da alama yana jiran umarni kokuma suna magana. " Sir gobe ne tafiyar taka dan ganin samples din nan kuma 2days zakayi dan munada wani meeting da company a bangaren kudu." Ya dauƙi tsawan mintuna kusan biyu kamin ya dago fuskarsa yana kallon matashin dake gabansa " babu ta yarda za'ayi cancelling din tafiyar nan ne?" Cikin girmamawa yace " No way sir dan wannan shine karan mu na 5 na aika musu gayyata but basa amincewa sai yanzu suka yarda." "Okay ba damuwa ka shirya komai but maganar yaron nan saleem fa?" Murmushi yaron yayi yace " Gaskiya sir bashida matsala dan kuwa mahaifiyarsa mutuniyar kirki ce sai dai kuma.." yayi shiru batare da yakarasa ba " Kuma me? Please say it." " Gaskiya yaron

Yanada fitina harma yana shaye shaye After that babu matsalar komai akansa yanzu haka abokanannasa da nayiwa magana su suka sanarmini gaskiya yanzu ya rage shaye shaye ya Nutsu." Dan gyara zamansa yayi yana juyawa akan lafiyayyar kujerarsa yace " Well that's good you can go." Okay sir thank you. Dan jan ajiyar Zuciya yayi kamin yacigaba da aikinsa.


****


Kwanaki kusan uku kenan mami taki sakar musu fuska acikin gidan dan ta tuburi akan babu mai aurawa diyarta Saleem Tun yaran suna ganin mamin nasu zata sakko Amma ina taki sauka. Ta wani bangaren kuma bakaramar soyayya aka dara da saleem da batool ba ko da tace bata daukar wayarsa bata iyawa kwatakwata wani sa'in har Allah Allah takeyi taga yakirata tun abun tana ganinsa acikin takura yanzu tafara sakin jiki sosai dashi. Duk da wani bangaren ranta na mata zafi ganin yadda mahaifiyarta ta canza mata, sanin cewa Abhuu ya dawo yasanyata jindadi aranta tasan xai fahimtar da mami.


Mami ce tashigo dakin batool din tana faɗin " yaya" Batool ce tatashi zaune tana faɗin "Naam mamina" tana dan marairaice idanuwanta. " yanzu bazan gayamiki kiji ba Abhuu yakirani yace yaron nan zaizo ya gaishemu yanzu ke bazan ce ga abunda zakiyi kiyi ba batool." Shiru batool tayi batace komai ba dan ko kadan bataso maminta takara fushi da'ita. " Kowa yanason yasamarwa ya'yansa uba nagari ke kuma zaki.." " mamina please kiyi hakuri wallahi saleem yanada tarbiya sosai kuma wallahi ba mutumin banza baneba kawai kaddararsa ce ahaka." " Kome zakice nacemiki ban amince ba ko? Ki gaggauta samun mahaifinku kice kin fasa" tafada a fusace tana barin daƙin. A hankali hawaye yacika idanuwanta ohh yaa Allah kataimakamin kan mami, yau zataje birthday din Jb dan ma abhuu yana gari batasan ta yadda zata fita ba gashi sai 10 za'a fara birthday din.



Amma mami yakamata ki fahimci yaya batool please ba ki dauki zafi damu ba. Wani mugun kallo ta jefawa Aysha dake magana agefenta tace " Duk Duniya kunada wacce ta fahimceku ne bayan ni? Tayaya zan amince diyata ta aure dan shaye shaye shi mahaifin naku wannan ce kalar soyayyar da yake faɗin yana muku to wallahi wallahi akan wannan maganar bakaramin bata muku rai zanyi ba, A ina akace Ka aurawa diyarka mutumin banza." " Mami danAllah kiyi hakuri Ni banason ranki ya baci akan maganar saleem." Wani kallo tabi batool dashi duk da zuciyarta ta karye kan maganar diyar tata hakan yabata damar zama kusa da batool din tace " Bazaki taba fahimtar illar abunda nake hango miki ba batool sai gaba, banason yaron nan badan kaddararsa ba sai dan lamarin shaye- shaye abune mai mutukar wahala sannan..." " Mami please ki barni Nayi auren tunda inaso." Karon farko jikin mami yayi sanyi Tace " " Ban amince ba nace miki ko kar.." aysha ce ta kalli batool alamun tayi shiru har sai da sukaga fitar mami daga daƙin sannan tace " Yaya kicigaba da Addu'a please idan Allah yayi mijinki ne mami bazata hanaba." Dagawa Aysha kai kawai tayi tasamu kan gadon Ayshan ta kwanta dan tana jiran zuwan saleem yace mata yana hanya zaizo yagaida mutanen gidan nasu.


Babban ƙauye ne da sai dai mai mashin yashiga dakai dan kuwa babu wata alamar mota ma aciki, manyan mata guda biyu ne abayan mai mashin din dayar da aka kira da sakina sai faman masifa take tana fadin "Kema Aunty maryam ke kika fara raga musu tun farko ai nagayamiki gidan sadauki sai da malamai idan bahaka ba wallahi kina kallo za'a riqa cuta miki." " kinsan sakina banda matsalar komai agidan mijina dan shi sadauki mutum ne kaifi daya idan zaiyi zaiyi idan bazaiyi ba kuma bazai taba yiba adalci kuwa wallahi kowaccen mu sai dai tafadi son zuciya kuma maganar da kikeyi wallahi idan yana gurina haukacemun yakeyi nifa har mamaki nakeyi yadda kikasan sabon aure da macce narasa dalili." " To ko ita uwargidan nasa bata tarairayarsa." " Anya kuwa sadauki zai iya zama da macce mara tarairayarsa? Ai bazai iyaba mutum ne dakeson macce ta kula dashi kawai dai inajin haka yake." " Kokuma yafi sonki ba ke wannan uban kudin da kike kashewa na magungunan mata ai dole ya haukacemiki Aunty maryam." " Ni matsalata wannan diyar tasa batool da bai haɗata da kowa yanzu ma fa wai ɗan mataimakin shugaban kasa ke sonta wallahi wallahi banyi bacci ba dana jiyo hirarsu." Aunty maryam kenan kada ki damu indai maganar Aurece to tabbas tagama mutuwa." Mai mashin ne yace bafa ashiga cikin dajin can da mashin sai dai da kafa shiyasa na tsaya ku sauka. Amsa masa sukayi suna biyansa sukayi cikin dajin. " Ni wallahi tsoro nakeji sakina." " aunty maryam kenan kedai muje zakiga ikon Allah." Tafiya ce da bata wuce mintuna 5 ba takaisu har cikin wani babban gida da sallama suka shiga suna gaisawa da matansa kamin su shiga filin da malamin yake ciki. " Barka da warhaka malam yau gani tafe da ƴar uwata." Kallonsu yayi babu alamar fara'a ko daya a fuskarsa yace " Na bincika tun kamin tazo wannan yarinyar da takeso a hana ubanta sonta ko aiki dubu zamuyi bamu iyawa sabida soyayyar yarinyar tun daga uwarta ce dan haka ko kinyi aiki akan haka nagayamiki bai tasiri sannan ita yarinyar macece mai addini sosai banajin aiki zaiyi sauki akanta sai dai kuma zamu iyayimata turen aure aljani bazai zauna ajikinta ba amma yana kusa da'ita ko wanne lokaci zai sakawa samarinta ƙinta daga karshe aikinki dubu dari ne." Murmushi aunty maryam tayi tace " Nagode malam hakan ma yayi sosai." " Ga wannan ki tabbatar ta shaqa kokuma taci abinci data shaqa ko taci to tabbas aiki zaifara." " Wallahi malam bazata shaqa ba dan bangaren kowa daban gwara gwara abinci inada tabbacin zataci." " Kai Aunty maryam ke ko kissan nan ta jan yaran miji har yanzu baki iya ba? " " ko bataci ko ta shaqa ba aiki zai fara akwana uku idan kuma taci tabbas take aiki zaiyi." Godiya sukayi masa sannan suka fito daga kauyen.


Kyakyawan matashin dake tsaye gaban lafiyayyar motar da driver yakawoshi, kallonta yayi yana mai dan maida idanuwansa ya rufe haɗe da faɗin " my love kinyi kyau." Murmushi tayi zuciyarta nakara mata wani sanyi da farin ciki tace " kaima kayi kyau baby." A hankali yace " I soo much love your voice." Dan kallonsa tayi taga yadda yake wani narai narai da ido yasanyata katse maganarsa dan har cikin ranta takejinta jikinta sai yashiga mutuwa " kataho muje Abhuu yana ciki da mami." Baice mata komai ba sai hannunta da ya rike da sauri ta fisge hannunta suka nufi part din Abhuu ko da sukaje yana zaune akan carpet da Alama wasu takardu yake dubawa sallamarsu yasanya shi ajiyewa gefe yana amsawa haɗe da zuba masu ido . Har kasa saleem ya durkusa ya gaida abhuu. Nan yashiga tambayar mutanen gidansu duk ya amsa da suna lafiya. " To mashaa Allahu." " Daman munyi magana da dadyna yace sunaso suzo cikin week dinnan." " Badamuwa Allah yakawosu lafiya." " Nagode Abhuu Allah yakara girma yakara lafiya." Murmushi kawai yayi yana kallon batool yace " Kaishi gurin maminku ko?" Mikewa tayi sukayi bangaren mami da sallama suka shiga inda mami ta amsa sama sama tana wani basarwa. saleem ya gaidata babu dai fuska ta amsa hakan yasa yayi mata sallama suka fito." " Mami batasona ko batool?" Kallonsa tayi da mamaki." Tabbas nasan ba kowacce uwar kirki zataso ɗanta ya aure dan sha..." cikin sauri batool tace " Please stop it jarabawa tana kan kowa ne baka fahimci mami baneba..." katseta yayi yace " please batool kada ki gujeni I love you wallahi tallahi and am ready to change saboda ke da mumyna I will be a better person." Hawaye taji ya zubo mata tace " I love you too and bazan gujeka ba saleem please kadaina maganar nan ko mami bataso abhuu Yana sonka ai."




#NANA DISO

#ASMY B ALIYU

#Batool Sadauki

#Saleem

#Hot love/Romance







Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.