Free chapter 路 Read without an account

PAGE THREE

by Nanameera 路 SHEIKH HEESHAM

*馃尮SHEIKH HEESHAM馃尮*



*MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*





Nanameera.




03.



Tafiya kawai suke inda shi kuma tunaninsa ya ke wani wajen daban,

"Ya Allahu, ya Rahmanu"

Shine kawai abinda bakinsa ke furtawa har suka 茩araso filin jirgin....


A vip yake ya kishingi蓷a da bayan kujera idanunsa a lumshe shi ka蓷ai yasan iya abunda ke damunsa gashi kuma ciwon kansa nason hargitsashi, ahaka yana wannan tunanin bai san bacci ya 蓷aukeshiba dan baccin Sheikh sai dai 蓳arawo......


A nutse yake tafiya guards 蓷insa na biye dashi har ya'isa gaban motar suka bu蓷e masa, zama ya yi yana kiran sunan Allah a cikin ransa kamar koda yaushe. Ganin drivern ya茩i tafiya yasa ya ce

"lpia?"

"Sheikh daman yarinyarce ba'a 蓷auko ba"

Sai asannan ya tuna dan kwata-kwata ya manta da wata yarinya ya ce" ina take?" tana can kwance har yanzu bata farfado ba za'a saka guard ya 蓷auketa ya kaita asibiti"

Bai ce komai ba ya sauka daga motar ya bisa da kallo yana da蓷a jinjina hali irinna Sheikh Heesham.....


Kwance ya tarar da'ita har sannan kuma batada niyyar farfadowa, a hankali ya sanya hannayaensa duka biyun ya 蓷auketa, ji yayi kamar bai 蓷auki komai ba saboda rashin nauyinta ni kuwa nace ya za'ayi tayi nauyi??????..


Kai tsaye asibitin Abdullahi wase dake nassarawa ya kaita, sosai sukayi murna ganin babban malami a asibitin cikin mutuntawa kuma suka kar蓳eta shikuma ya shiga mota dan tafiya gida......


Tsaye take saman benen gidan taga motocin na reton shigowa, da gudu ta sauko 茩asa tana kallon Mami ta ce" Mami Sheikh"

Murmushi Mami ta yi ta ce" ai naji ajikina ya dawo tun 蓷azu" bata rufe baki ba ya shigo parlon 蓷aukeda sallama, da murmushi afuskarsu suka amsa masa sannan ya zauna kan kujerar yana kallonsu ya ce

"Mami ina yini"

"lpia lao Heesham ya hanya?"

Ya ce"lpia lao Alhamdulillah" da murmushi a fuskarta ta ce" yaya ina yini"

"lpia lao ya karatu?"

Shine abinda ya tambayeta sannan ya mi茩e ya ce" zan watsa ruwa" daga haka ya shige apartment 蓷insa.......


Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da hancinsa ya sha茩i dadda蓷an 茩amshin airfreshner da akayi amfani da'ita a 蓷akin, a hankali ya shige bedroom 蓷insa yana jan jiki dan ya gaji sosai........


Zama ya yi gefen royal bed 蓷in dake 蓷akin, ko ina tsaf yake gwanin sha'awa kuma yasan babu wanda zaiyi wannan aikin sai Mami dukda yasan wajen a gyare yake amma wannan sabon gyarane, ganin lokaci na shigewa yasa ta tashi yana sakin ajiyar zuciya a karo na babu adadi ya shiga ban蓷akin......


Fitowa ya yi jikinsa yana 蓷iga alamun wanka sumar kansa ta zubo har fuskarsa, ga wani faffa蓷an 茩irjinsa sai gashi da ya yi luf akai a hankali yake goge jikin nasa kamar wanda kwai ya fashewa ajiki har ya gama sannan ya sanya wasu riga da wando farare sol dasu ya shafawa sumar kansa mai sannan ya tufketa da ribon ta zubo har bayansa, sosai take damunsa kuma ahakama ana rage masa ita, ya taje gemunsa wanda yake dogo kuma atsaye irinna ri茩a茩茩un malaman nan.

"Alhamdulillah"

Shine abinda ya furta sannan ya hau kan royal bed 蓷in nashi ya kwanta nan da nan bacci ya yi awon gaba dashi.........



A hankali ta fara 茩o茩arin bu蓷e idanunta wa蓷anda suka mata nauyi sosai, sosai ta firgita ganin inda take dan bata ta蓳a ganin makamancin irin wannan waje ba a rayuwarta iya kacin abinda tasani bukka, sai kogi. Yun茩urin tashi tayi amma taji wata irin azaba ta ziyarci kwakwalwarta dole ta ha茩ura ta cigaba da kwanciya nan take kuma duk inda jikinta ya fara mata ciwo, batasan ina take ba kuma batasan dalilin kawota wajen ba duk zatonta ma ko siyar da'ita su Ammi sukai, wasu hawaye ne suka wanke mata fuskarta babu abinda take tunawa sai irin yanda aka dunga dukanta akan laifin da bata aikata ba, tunanin hakan yasa ta sake fashewa da kuka dan ita ka蓷ai tasan yanda takeji a zuciyarta......




Murmushi ta yi tana kallonsa ta ce

"Laaa yaya Bilal sai yau kazo?"


Fuskarsa a sake ya ce" Eh mana ina Sheikh?"


Dariya ta yi ta ce"daman nasan saboda Sheikh kazo wlh Mami tana ta zancenka amma gashi kanaji ance Sheikh ya dawo shine kazo, ai shikenan ina Junior?" Murmushi ya yi yana shafa kansa ya ce "wlh yana gida ina Mamin?"


"batanan taje gidansu Nihal"

Ta bashi amsa gaba ya yi yana cewa " ok ina nan har ta dawo ai".......



Zaune ya same shi yana danna system kana gani kasan abu mai muhimmanci yake yi, zama ya yi kan bedside drawer 蓷in yana murmushi ya ce " su Sheikh manya wato shine sai yanzu kaga damar zuwa 茩asar ko?"


Shuru yayi masa kamar bdashi yake ba, girgiza kai Bilal yayi dan yasan hali ya ce


"Wai kai harnima 蓷aukemin kan ka keyi?"

Shuru Shaikh ya yi kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" amma kana sane da bakayi sallama ba"


Kwa蓳e fuska ya yi ya ce" sorry i forget assalamu alaika"

"Wa alaika salam" Shaikh ya amsa masa, murmushi ya yi ya ce" yanzu sai a kulani ko?"


Murmushin sa mai kyau ya yi dan yana matu茩ar girmama abotar dake tsakaninsu dukda cewa shi蓷in 蓷an uwansa ne dan 蓷an 茩anwar Mami ne kuma bazai wuce shekara 35 ba dan kusan tare aka haifesu da Sheikh Heesham.........



Hira suka fara yi akan rayuwarsu amma duk rabin hirar Bilal ke yinta dan shi Sheikh sai Umh, un'un, har lokacin kiran sallah ya yi. Mi茩ewa Shaikh ya yi ya shiga toilet dan 蓷auro alwala domin shine yake jan sallar masjid 蓷in gidan nasu............




Zaune suka tadda Mami suna ta蓳a hira da Shareefat, Bilal ya ce "Mami ina yini" harararsa tayi ta ce" yana gidan biki, sai yau kaga damar zuwa?" shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce" sorry Mami wlh abubuwane suke ri茩eni" ta ce" amma ai dayake 蓷an uwanka ya dawo gashi na ganka yanzu babu abinda ya ri茩eka kenan" kasa magana ya yi sai sunkuyar da kansa ya ce banda dariya babu abida Shareefat ke yi ta ce


"Toh yanzu ba gashi yazo ba Mami?" ta ce" yimin shuru kina goyan bayan yayanki kawai"


"Sheikh akawo maka abinci?"


Girgiza kai ya yi ya ce "azumi" ta ce" toh Allah ya ha蓷amu a ladan"..........



Shigowa ya yi ya ce" Sir yarinyar ta farka"


"Wace yarinya?"

Mami ta tambaya, tashi Sheikh ya yi yay gaba batareda ya amsa tambayar Mami ba, Bilal ne yabi bayansa yana cewa


"Wai bazaka tsaya niba"


Driver sit ya zauna bakinsa 蓷aukeda addu'a ya yiwa motar key ya fara tafiya cikin nutsuwa, ganin yanda yake tafe slowly yasa Bilal ya ce" wai dan Allah kayi sauri mana" kamar bazai magana ba sai kuma ya ce" so kake natafi da gudu wani ya mutu?" "wane zai mutu?" murmushi ya yi ya ce" ni mana" da mamaki Bilal ya ce" Eh lallai kaga kuwa bai kamata ka mutu ba bayan baka tara iyaliba, wai yaushe zakayi aure ne?" "sanda Allah ya yi" Sheikh ya bada amsa. Murmushi Bilal ya yi ya ce"wlh inada wata yarinya zan baka ka aura plx" girgaza kai Sheikh ya yi sanda yake parking ya ce" Allah ya tsare" dariya ya yi ya ce" au hakama zakace?" bai ce masa komai ba ya sauka daga motar shima ya fito.........


Tafiya kawai yake amma shi yasan yanda zuciyarsa ke wani irin bugawa ya ce" ya Allahu ya rahmanu" shine abinda yake furtawa har ya kai bakin 茩ofar ward 蓷in, a hankali kuma ya mur蓷a kofar bakinsa 蓷auke da sallama........





*SHEYKH HEESHAM*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.