Free chapter 路 Read without an account
Page 02
by Nanameera 路 BA ITA BA CE
*BA ITA BA CE!...馃挅馃挅*
*MIKIYA WRITERS ASSO...*
*Follow my account both arewabooks nd Wattpad*
*nanameera 08* _arewabooks_
*@Nanameera08* _wattpad_.
*Nanameera*
# *SQUAD 2024*.
```Page 02```
*Rugar Jama'are*
Dur茩ushe take gabansa ta zuba masa idanu tana kallonsa 茩aramar yarinya ce ba zata shige 4 to 5yrs ba tana sanye da kayan Fulani Blue colour as usual gashinta dake zube a gefenta wanda aka kalbaceshi irin manyan kalbar nan guda biyu yabi da kallon a hankali kuma ya sake lumshe idanunsa shi ka蓷ai yasan irin tsananin azabar da yake ji, kamar zatayi kuka take kallon mahaifin nata cikin wata siririyar murya mai Matu茩ar za茩i da 蓷aukan hankali take cewa"Papina sannu zaka samu sau茩i kaji sannu dan Allah" bata rufe bakinta ba aka 蓷aga labulen wanda ya kasance asabari ne suka shigo da sauri kuma cikin 蓷aga murya Dada ta ce"Baba kura zo ki dubashi aradu mun higa uku ya Gani sannu Allah zai tashi kafa蓷unki" da sauri wanda take cewa Baba kuran ya 茩araso yana zuwa ya zube a gabansa hannunsa ya kai ya ta蓳a wuyansa sosai yaji zafi a jikinsa hakan yasa duk hankalinsa ya 茩ara tashi a matu茩ar razane kuma ya mi茩e ya fice daga cikin bukkar, da kallo suka bisa kafin Dada ta kalleta da idanunta wanda suka sauya launi ta ce"kai Muhaira 蓷ebo ruwa a bashi yasha" da sauri 拼ar 茩aramar yarinya ta mi茩e ta 蓷auki 蓷an 茩aramin jallan ruwan tayi waje saidai kafin ta fita ta juya a hankali tana kallon fuskarsa ga mamakinta sai taga shima ita yake kallo wani tattausan murmushi ya yi mata dukda yanda bakinsa yake a bushe wanda ke nuni da asalin ciwon da yake ciki a hankali itama ta mayar masa da nata kyakkyawan murmushi ya ilahy wani irin sihirtaccen kyau 拼ar yarinya ta yi tamkar wata 拼ar aljanu haka ubangiji ya yi mata kyau kwayar idonta blue colour ce irin mai hasken nan sai wani irin she茩i suke sa蓳anin na sauran mutane da suka kasance ba茩a茩e. Da hannunsa ya yi mata alama da tazo hakan yasa ta ajiye jallan ta 茩ara sa gabansa 蓷an 茩aramin hannunta ya kama a hankali kuma ya bu蓷e bakinsa wanda yawo yake shirin 茩afewa daga cikinsa ya ce"Baddon Papi!" da sauri ta 蓷aga kanta tana kallonsa wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa kan kuncinsa da sauri ta saka 蓷aya hannun nata tana goge masa kwa蓳e fuska ta yi cikeda shagwa蓳a ta ce"Papi kadaina kuka kaji dan Allahhhh" shafa fuskarta ya yi hannunsa na kakkarwa ya gya蓷a mata kai dan bakinsa ya yi masa nauyi, Bani kura ne ya shigo bukkar shida wani mutum a bayansa da alama kuma mai magani ne. Bayan sun zauna ya kalli Papi sai kuma ya kalli Muhaira dake gefensa ya ce"Baddo maza jeki gidana ki kar蓳on 茩warya" mi茩ewa Muhaira tayi ta fice tana tafiya da a sauri a hankali kuma take waiwayen bukkar tasu.
Tafiya kawai take da sauri da sauri dan ko wasa bata tsaya ba haka har ta baro rugar tasu, kasancewar su a cikin gari suke ya sanya ta 蓷an yi tafiya mai yawa kafin ta 茩araso 茩ofar gidan, "Wundo!! Wundo!! Wundo!!" turo baki Muhaira ta yi bata ce komai ba har sannan, da sauri ya'acca ta kalleta cikin 蓳acin rai ta ce"ke kam Muhaira bakida mutunci ko?, banda iskanci ki shigowa mutane gida babu sallama sannan kuma ji ana waye kinyi tsif abinki ko?" sosai yarinyar ta tsorata da tsawar da tayi mata bakinta na rawa ta ce"unn...uhhhmm...dan...daman Bani kura ne ya ce a bashi 茩warya" tsaki ya'acca ta yi ta ce"shine zaki tsaya kina mana shashanci" sunkuyar da kanta ta yi bata ce komai ba amma duk a tsorace take, shiga 蓷aki ta yi ta 蓷auko 茩waryar ta mika mata, da sauri Muhaira ta kar蓳a sannan ta juya da gudu tayi waje, tsaki ta yi tana kallonta ta ce"shashasha kawai".
Da sauri ta shigo cikin bukkar hannunta ri茩e da 茩waryar saidai me?, babu Bani kura wanda ya aikata haka zalika babu mai maganin da aka 蓷auko sai Dada wacce ke zaune gefensa banda kuka babu abinda take yayinda Papi aka rufeshi da wani tsohon bargon, da sauri ta 茩arasa wajensa tsugunawa tayi gaban Dada tana cewa"Dadana Papi ya yi bacci?" kallonta Dada ta yi amma bata ce mata komai, sosai idanunta sukayi jajur ko ba'a fa蓷a maka ba kasan ba 茩aramin kuka tasha ba, kuka ta fashe dashi tana murza idanunta da kallo kawai Dada ta bita dan ita tama gagara magana ganin Dada bata kulata ba har sannan yasa ta kwanta a wajen tana birgima, Bani kura ne ya shigo shida masu maza a bayansa suna zuwa kai tsaye inda Papi ke shimfi蓷e suka nufa ganin yanda take kuka yasa Bani kura ya ce"Aishatu ke dawa?" daga yanayin muryarsa zaki fahimci irin damuwar da take tare dashi, da sauri Muhaira ta tashi jin ya kira sunanta ta 茩arasa wajensa har Sannan kuma kuka take ta ce"Bani koba Dada bace" janta ya yi jikinsa ya rashe mata hawayen fuskarta sannan ya ce "to kiyi ha茩uri zauna anan" shiru tayi ta zauna a gefensa tana kallon bargon da suka rufe Papi.
茦arasawa suka yi bayan sun yaye bargon suka kamashi suka fita daga cikin bukkar duk wannan abun da ake banda kallo babu abinda Muhaira ke yi dan ita bata gane ba mene ne abinda ya faru ba, Dada kuwa 茩ara sautin kukanta ta yi jikinta na wani irin kyarma, tashi Muhaira ta yi ta koma kusada ita ta zauna amma bata ce komai ba sai kallon mahaifiyar tata take, ita kuwa Dada tunanin yadda rayuwarsu zaka kasance take, tunanin rayuwar Muhaira take, zuciyarta cike take da tausayin tilon 拼ar tata, tabbas 茩addara ta riga fata domin Papi ya tafi ya barsu a lokacin da suka fi bukatarsa. Tunawa da wannan yasa ta sake rushewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya ita kuwa Muhaira bata fahimtar komai 茩an茩antar shekarunta da kuma 茩arancin shekarunta sune suka yi tasiri wajen gazawa kwakwalwarta ta fahimtar da ita duk a tunaninta Papi 蓷in wani waje zasu kaishi wanda zasu dawo mata dashi. Amma saidai abinda bata sani ba shine Papinta ya tafi kenan tafiyarda duk wanda ya yi ta baya ta蓳a dawowa,tun tana tambayar Dada ina Papinta har ta fahimci cewa Papinta ya bar duniyar a hankali mintuna ke komawa awanni awanni ke komawa kwanaki kwanaki ke komawa sattituka sukuma suke juyewa izuwa wattani wattani kuma ke juyewa izuwa shekaru, tafiya ta tafi a 茩alla Papi zai yi shekaru uku da barinsa duniya zuwa wannan lokacin kuma Muhaira tanada shekaru 8 a duniya.
Wani irin sanyin ake mai ratsa 蓳argon da jijiya sanyinne irin wanda ke haddasa cuttukan musamman Asthma, pneumonia, sickler dama wasu ciwukan, safiyar ranar juma'a ce gaba蓷aya rugar Jama'are tayi tsit kowa yana cikin bukkarsa da iyalansa, tsugunne take gaban wata tukunya wacce aka 蓷orata akan dutsuna guda uku wanda suka zama sune murhun da take girkin akai sosai take ha蓷e jikinta yayinda numfashinta ke wani irin fuzga ita ka蓷ai tasan azabar da take ji amma kuma burinta bai shige ta gama damawa Dada kokon ba. Cikin mintuna 茩adan ta kammala ta juyeshi cikin wani tsohon kofi sannan ta tashi da gudunt ta shige bukkar, tana nan yanda ta barta a kwance idanunta a rufe suke amma ba bacci take ba ajiye kofin hannunta ta yi sannan ta shiga kamata tana fa蓷in" Dada tashi, tashi kinji na dama miki kokon tashi kisha sai kisha magani" dakyar Dada ta bu蓷e idanunta ta kama hannun Muhaira ta mi茩e daga kwancen 蓷ora kan Dadar tayi akan 茩irjinta dukda nauyin da tayi mata amma ko ka蓷an hakan bai dameta haka ta 蓷auki kofin kunun ta kai mata bakinta, girgiza kai Dada ta yi tana ri茩e hannunta ta ce"A'a Muhaira bazan iya sha ba akwai abinda nakeson na fa蓷a miki tabbas wannan cutar tawa bata tashi ba ce saida... wani irin jan numfashi ta yi tana saukeshi a hankali runtse idanunta tayi hawaye suka shiga rige-rigen sakkowa kan kuncinta alama ta yi mata data bata kunnenta a hankali Muhaira ta kara kunnen nata kusada fuskar mahaifiyartata dan taji me zata fa蓷a mata. Above 5mins tana yi mata magana zuwa lokacin kuma banda hawaye babu abinda Muhaira ke yi gaba 蓷aya tunaninta ya tsaya cak batada wata sauran dabara zuwa sannan kuma bata iya fahimtar abinda mahaifiyar tata ke fa蓷a mata. Shirun da taji Dada tayi yasa ta kalleta wata irin razananniyar 茩ara ta fasa wacce ta yi daidai da shigowar Falmata cikin bukkar da sauri ta 茩araso tana kallonsu duka ganin yanda Muhaira ta 茩am茩ame Dadan har sannan kuma kuka take yi kallo 蓷aya Falmata ta yi mata tasan cewa Ubangiji ya kar蓳i abarsa, ikon Allah kenan babu yanda mutum ya iya kamar yanda Papi ya mutu haka yanzu itama Dada tabi bayansa
"Dadata! dan Allah dan Annabi ki tashi karki mutu ki barni banida kowa Dadaaaa...ki taimaka ki tashi Dada ko kinfi son nayi kuka har 茩arshen rayuwata?, banida kowa Dada kema kuma bakida kowa Papina ya tafi har yau bai dawo ba kema shine zaki bisa??? kenan duk baku sona? meyasa Dada?, me nayi muku?, ina zani yanzu? wane zai kula dani Dadaaaaa..." maganar ta tsaye a ma茩oshinta sakamakon wani irin nauyi da zuciyarta tayi da gudu ta mi茩e ta fita daga bukkar saboda wani irin amai daya tawo mata saidai me???? madadin amai na abinci ko kuma na ruwa wani irin guda-gudan jini ne ya shiga fitowa daga bakinta sai kuma ta fa蓷i nan 茩asa sumammiya.
Allah sarki rayuwa tabbas babu abinda ke 蓷orewa sai ikon Allah cikin 蓷an lokaci 茩alilan Muhaira tarasa iyayenta guda biyu wanda hakan shine mafarin 茩addararta, tabbas labarin rayuwarta akwai ta蓳a zuciya, musamman daya kasance tanada 茩arancin shekaru Hakazalika kuma babu wani wanda zata kama ta ce wannan danginta ne kasancewar iyayen nata Fulanin tashi ne, tarasa gatanta tun tana jaririya sannan kuma ta sake rasa wa蓷anda suka maye mata gurbin wannan gatan data rasa ya zatayi??dawa zata rayu?? wace irin 茩addara ce ke bibiyar rayuwarta??...
*17 years*.
*Maitama district, Abuja*
*No:113*.
*Mai Zamani pov.*
Wani zazzafan numfashi ya sauke bayan ya saki curtain 蓷in, a hankali cikin tafiyarsa mai nuni da isa ya 茩araso gefen kujerar dake gaban gadon ya zauna sanye yake da wata Polo T-shirt white colour sai kuma wani Cargon Three-quater black colour a jikinsa ba wani fari bane can haka zalika kuma ba ba茩i bane yana dai da haskensa dai-dai misali, 蓷an 茩aramin tsaki yaja sannan ya bu蓷e system 蓷in gabansa ya shiga dubawa. Duba da irin yanda yake kallon system 蓷in zaka fahimci tabbas wani abu mai matu茩ar muhimmanci yake gabatarwa, turo 茩ofar 蓷akin tayi bakinta 蓷auke da sallama a ciki ya amsata sannan ta 茩araso gabansa zama tayi gefensa tana sanye cikin wani material black colour mai adon flower pink 蓷inkin doguwar riga A-shape mug 蓷in gabanta ta ajiye masa gefen table 蓷in gabansa ta cigaba da kallon abinda yake, above tens minutes sannan ya kammala ya rufe system 蓷in sai a sannan ya 蓷ago yana kallonta fara ce tass kuma asalin kyakkyawa dan ko ba'a fa蓷a maka ba kasan ita 蓷in ba ta kasance cikin 茩abilar Hausawa ba ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta sunkuyar da idanunta 茩asa tana wasa da fingers 蓷inta masu 蓷auke da zanen flower wacce tayi matu茩ar amsar farar fatarta ta蓳e baki ya yi sannan ya 蓷auki mug 蓷in data ajiye a hankali kuma yakai tea 蓷in bakinsa wani runtse ido ya yi saboda wani irin za茩i da yaji har cikin kansa da sauri ya ajiye mug 蓷in yana mata wani hargitsatsen kallo ya ce "Ma'eesha I'm play with you?" kallonsa ta yi fuska a kwa蓳e ta ce" A'a yaya I'm sorry wlh banson sugar ya yi yawa ba I'm so sorry" kallonta ya yi from head to toe sannan ya yi tsaki ya tashi bai tsaya cigaba da jin abinda take fa蓷i ba ya 蓷auki wayarsa 茩irar iphone 14pro max ya yi waje. Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe 茩irjinta sanin halin yayan nata sai kuma ta mi茩e itama tabi bayansa.
A nutse take taka stairs 蓷in benen har ta sakko gaba 蓷aya, ya rabbi wani irin ha蓷a蓷蓷en parlon ne irin mai tafiya da imanin mutum 蓷in nan komai na cikinsa golden colour ne tun daga kan kujeru, curtains, carpet, center table even bulb da suke parlon golden colour suke bayarwa banda sanyin A.C babu abinda ka keji a parlon sai kuma wani irin dadda蓷an 茩amshin da yake fita daga kowace kusurwa ta parlon ko ba'a fa蓷a maka ba kasan wannan parlon bai yi kamada na 茩ananan mutane ba ko kuma basu ji da 茩aramin arzi茩i parlon ne irin wanda koda a cikin Villa yake sai ance ya ha蓷u iya ha蓷uwa, parlon ne na irin manyan nan wanda suka ji茩u da manyan ku蓷a蓷e, a hankali ta 茩araso cikin parlon inda ta hangin iyayen nata. Zaune yake kan kujera Three seater yana sanye da wata dakakkiyar shadda Madam gezner blue black 蓷inkin jamfa da babbar riga idanunsa ma茩ale da wani farin tabarau yayinda yake kallon jaridar dake hannunsa da alama kuma karantawa yake duba da yanda ya bada full attention 蓷insa a wajen magidancin mutum ne dan a茩alla zai kai irin 60yrs 蓷in nan amma idan har kayi duba da yanayi na siffarsa zaka iya cewa bai fi 46yrs saboda kwarjini da kuma hutu wanda ya zauna masa. Major General Ibrahim Tijjani mai Zamani kenan wanda ke ri茩eda mu茩amin shugabannin sojoji na 茩asa kuma sanannen 蓷an kasuwa mai tashen arzi茩i mamallakin Companyn mai Zamani corture indai magana kake ta ku蓷i to tabbas M.G Ibrahim 茩arshene sannan kuma uwa uba ya kasance mutum mai taimakon na 茩asa dashi wannan shine dalilin daya sanya yake da mabiya daga kowacce fuska. Da sauri ta zauna gefensa tana shagwa蓳e fuska ta ce" Father narhhhh!!" murmushi 蓷auke a fuskarsa yake kallon tilon 拼ar tasa kallo mai nuna zallar so da 茩aunar da yake mata shafa kanta ya yi cikin kamilalliyar muryarsa ya ce" Shalelen Father what's wrong uhn" turo baki gaba tayi ta ce" Father ko ba yaya Farooq bane" da sauri Farooq wanda yake zaune kujerar dake opposite tasu ya 蓷ago yana kallonta amma bai ce komai ba, murmushi Father ya yi sanin halin rigimarta ya ce"keda yayan naki ne kuma yanzu?, To kiyi ha茩uri bazai sake ba ya tuba" ta蓳e baki ta yi sannan ta ce"Father kace masa ya kaini saloon 蓷in" dafe kansa ya yi yana zare glasses 蓷in idanunsa ya ce" ohho!! Shalelen Father rigima ko?, Ki tambayeshi da kansa idan yaga zai rakaki fine idan kuma yanada wasu uzurin sai ki tafi da guards zasu jiraki" girgiza kai tayi ta ce"nooo! nasan ma zai rakani" kallon Farooq ta yi wanda yake kallonsu tun 蓷azu ta ce"yaya zaka rakani ko?" da sauri ya gya蓷a mata kai ko babu komai ya samu damar da zai gasa mata aya a hannu, murmushi 蓷auke a fuskarta ta kalli Father ta ce"yawwa Father kaji ko ya ce zai rakani" numfasawa Father ya yi ya jinjina mata kai sannan ya mi茩e yana ri茩e da hannunta ya ce"na tayaki murna amma karku da蓷e zan fita byee" gya蓷a masa kai ta yi tana murmushinta mai kyau ta ce"ok Allah ya tsare hanya Father narh" kissing goshinta ya yi sannan ya yi waje.
# *BA ITA BA CE*
# *Human trafficking*
# *Destiny*
# *love*.
# *SQUAD 2024*
# *Nanameera ce!*.